KALMA TA BAKWAI

58. Page

KALMA TA BAKWAI

بسم الله الرحمن الرحيم

{Ba da gaskiya da Allah da Ranar Lahira su ne mabuɗan jin daɗi ga ɗan’adam}

Idan kanaso ka fahimci ta yaya cewa: آمَنْت بِاَللَّهِimani da Allah da وَبِالْيَوْمِ الْآخِرimani da ranar lahira suke warware sirrin cukurkuɗe-cukurkuɗen wannan duniyar, kuma suke zama mabuɗan ƙofofin samun sa’a a rayuwa ga ruhin ɗan’adam, sirrika ne biyu masu daraja suke warware matsaloli, kuma tayaya dogaron mutum ga mahaliccinsa da kuma fakewa i zuwa gare shi yana mai haƙuri, da kuma roƙonsa da addu’arsa ga mai arzurtashi yana mai godiya, suke zama masu fa’ida ne, su biyun kuma dai magungunane masu amfani na yankan shakku.

Kuma idan kanaso ka fahimci ta yaya sauraro ga Alƙur’ani da miƙa wuya ga hukuncinsa da tsaida Sallah da barin manya-manyan zunubai, su tikitine[1] da guzuri don lahira da hasken kabari, a cikin tafiyar nan ta har Abadan abada, tikiti ne da yake da muhimmanci da ƙima da haske, yi duba i zuwa wannan hikaya da akamisalta a taƙaice, ka yi sauraro:

{Hikayar wani soja dake fagen daga}

Watarana wani soja ya faɗa matsanancin hali na firgici a filin yaƙi da jarrabawa a tsakankanin kaiwa da komowar nan ta samun nasara ko rashinta, kuma ga shi an yi masa raunuka zurfafa guda biyu agefunansa na dama da na hagu, sannan kuma ga wani zaki gabjeje[2] ya tsaya a bayansa , kamar zai kawo hari a gare shi , sannan an kafa abin rataye masu laifi a gabansa yana gani ana rataye dukkan masoyansa, ana rasar da su sannan shi ma ana dakonsa da saurarensa, daɗin-daɗawa, bayan wannan halin dayake ciki, kuma yana da wata tafiya mai tsawo, wadda dole za a kora shi i zuwa gare ta.


[1] Tikitin abin hawa kamar jirgin sama.

[2] Mai jiki qosasshe qato.




59. Page

{Bayyanar wani bawan Allah mai haske tare da kaiɗauki ga wannan sojan}

Yayin da wannan miskinin yakasance yana tunani a wannan halin, nasa mai ba da tsoro, yana mai ɗebe ƙaunar samun taimako; katsahan sai ga wani mutum mai haske da alheri kai ka ce Khadir ne - amincin Allah ya tabbata a gare shi - ya bayyana a ɓangarensa na dama, yana ce masa: kada ka ɗeɓe ƙauna, da sannu zan  ba ka  wasu sirrika guda biyu zan sanar da kai su, idan ka yi amfani da su, kyakkyawan amfani, wannan zakin zai zama doki horarre gare ka, wannan abin rataye mutanen zai koma i zuwa lilo mai daɗin hawa a gare ka don jin daɗi da shaƙatawa, hakanan kuma zan  ba ka  magunguna guda biyu, idan ka yi amfani da su ta kyakkyawar hanya, waɗannan ciwukan guda biyu masu ɗoyi, za su koma furanni biyu masu ƙamshi masu tabshi, kamar irin furennan da ake ambatonsa da -Furannin muhammadiyya-S.A.W a bisa ma’abocinsa tsira da aminci su tabbata a gare shi, kuma sannan zan  ba 

60. Page

ka tikiti[1] da za ka yanke da shi tafiyar shekara ɗaya a cikin kwana ɗaya kamar kana tashi sama, idan  ba ka  gasgata ba, ka ɗan gwada har kasan cewa ni a kan gaskiya nake.

 Sojan nan kuwa sai ya ɗan gwada kaɗan sai ya samu cewa shi yana kan gaskiya.

Na’am; haka nan nima –almajiri- sa’id, na gasgata hakan, domin cewa ni na gwada shi kaɗan sai na ganshi gaskiyane cikakke.

{ Bayyanar wani makiri ga wannan sojan }

Sannan katsahan sai ya ga wani mutum mai dasisa[2] mai mayen giya makiri kamar shaiɗan, ya zo a tare da shi akwai abubuwa na ƙawa masu yawa da hotunan mata na batsa, sai ya tsaya a gabansa sai ya ce da shi: yā kai abokina, haba zo mana zo mana, mu sha giya tare, mu yi wasa mu kalli waɗannan hotunan na kyawawan matan nan, mu saurari waɗannan waƙoƙi masu daɗin ji, muci waɗannan ababanci masu daɗi.

 

 

{Tattaunawa tsakanin wanan sojan da wanan makirin}

Tambaya:Ha HaHA !!! Me kake karantawa a cikin bakin ka a sirrance?

Amsa: wani sirri ne.

Mai tambaya:rabi da wannan abin daba a san kansa ba, kada ka ɓata mana jin daɗin mu da nishaɗin mu.

Mai tambaya: Ah!! Meye kuma wannan a hannunka?

Amsa: magani.

Mai tambaya: jefar da shi, lafiyarka ƙalau, me yasameka ne? wannan lokacin, lokacin nishaɗi ne. Ha Ha Ha!!! Wannan takardar mai alamomi biyar, ita kuma ta mece ce?

Amsa: tikiti ne amintacce ga abubuwan da aka keɓanta dominshi.

Mai tambaya: kyakketa shi, ina mu ina wannan tafiya a cikin wannan lokaci na kaka mai kyau haka.

Ya yi ta ƙoƙari ya rinjaye shi da dukkan makidodinsa, hardai wannan miskinin ya ɗan karkata i zuwa gare shi.

Hakayake, haƙiƙa mutum yakan yaudaru.-haƙiƙa nima na ɗan yaudaru da irin wannan makidar-

 

{Rushe kaidin wannan makirin}

katsahan sai ya ji wani sauti kamar tsawa daga ɓangaren dama, yana cewa, ina yi maka kashedi da kada a yaudare ka, ka ce da wannan mayaudarin, idan dai kana da dabarar da za ka iya kashe zakin nan da yake bayana ka ɗauke wannan abin rataye mutane da yake gabana, ka magance min raunukannan da suke dama ta da hagu na, kuma ka shiga tsakanina da tafiyar da take gabana, idan ka kasance za ka iya aiwatar

[1] Kamar tikitin jirgin sama.

[2]Mai kai wa da kawowa don ya ɓata tsakanin mutane.




61. Page

da wannan dabarar, to ga fili ga mai doki ka aikata, ka nuna mana don mu gani, sannan bayan haka sai ka ce min: kazo mu raƙashe[1], idan ko bahakaba, to yimin shiru, yā kai wannan wawa. har Sai ya faɗi abin da wannan mutumin nan mai daraja ya faɗa masa,[2] wanda yake kamar Khadirtsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

{Haƙiƙar ma’anar hikayar}

Ya ke raina wadda ta yi dariya a ƙuruciyarta, wadda take kuka yanzu  a bisa dariyarta, ki yi sani, haƙiƙa, wannan sojan abin tausayin nan ke ce, ai mutum.

Amma wannan zakin, shi ne ajali.

Amma wannan abin rataye mutanen, shi ne gushewa da rabuwa; domin tare da jujjuyawar nan ta dare da rana, da yawa daga abokanmu suna yi mana bankwana suna fakuwa ga barinmu.[3]

Amma waɗannan raunukan, ɗayarsu ita ce gajiyawar nan ta ɗan’adam , wadda bata da iyaka da take damunsa, ɗayan kuwa talauci ne irin na mutuntaka mai raɗaɗi, raɗaɗin da  ba shi da ƙarshe.

Amma waccan korawar da wancan bulaguron, su ne bulaguro na jarrabawa mai tsawo, da yake shuɗowa daga duniyar nan ta rayuka i zuwa mahaifar nan ta uwa, sannan ƙuruciya, sannan kuma tsufa sannan duniya, sannan kabari, sannan barzahu, sai kuma taron alƙiyama da siraɗi.

Amma waɗannan sirrukan guda biyu, su ne Imani da Allah da Ranar Lahira.

{Ma’anar mutuwa a haƙiƙaninta ga wanda ya ba da gaskiya da Allah da ranar lahira}


[1] Ciye-ciye da shaye-shaye da dukkan jin daxi na halak da na haram.

[2] Wanda kamar daga sama ya sauko.

[3] ita ce mutuwa.

 




62. Page

Na’am; haƙiƙa mutuwa da wannan sirrin mai tsarki tana ɗauka surar doki horarre ko taguwa, da take ɗaukar mutum mumini daga kurkukun nan na duniya i zuwa lanbunan Aljanna da halaran nan ta mai rahama; domin haka mutane masu cikakken imani, waɗanda suka fahimci haƙiƙanin mutuwa, sun so ta. Bari ma ka ji, su sun yi burin mutuwa tun kafin ta zo musu.

Sannan kuma, haƙiƙa gushewa da rabuwa da mutuwa da shuɗewar zamani, waɗanda suke a matsayin abin rataye mutane, da sirrin nan na imani suke zama wasiɗa don tsinkaye da ganin zanen mu’ujizar maƙeri, ma’abocin girmame-girmame, da keta al’adun ƙudurarsa da tajallin rahmarsa kyakkyawa mai danshi mai ƙyalƙyalin launuka kala-kala mayawaita cikin cikar jin daɗi.

 Na’am; haƙiƙa irin canjawa da sabuntawarnan ta mudubai[1]waɗannan da suke haskako launukan nan da suke cikin hasken rana da kuma cancanjawar nan ta hotuna a cikin allon sinima, suna samar da yanayi mai tabshi kyakkyawa.

Amma waɗannan magungunan guda biyu:


[1] Wanda ake kallon fuska ko kwalliya da shi




63. Page

Ɗayansu, shi ne; tawakkali tare da haƙuri da jinginuwa ga ikon mahallici da dogaro  a bisa hikimarsa, ko ba haka yake ba ?

Na’am; haka yake, wanne tsoro ne kuma zai yi saura awajen mutumin da yake jinginuwa ta hanyar wasiƙar nan ta gajiyawa i zuwa sarkin nan na kasantattu, wanda yake mulki da umarnin nan naكُن فَيَكُون[1] domin shi dangane da mafi tsoratarwar musiba da take bijiro masa yana dogaro ne da ubangijinsa mai jin-ƙai yana mai nutsuwar nan ta zuciya, yana mai faɗin:

إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَٰجِعُونَ[2]

 


[1] (kasance sai ya kasance)

[2] (Daga wajen Allah muke, gare shi za mu koma)Albaƙara aya 156).




64. Page

{Jin daɗin da ke tattare da tsoran Allah}

Hakayake; haƙiƙa masanin Allah yana jin daɗi, ta hanyar nuna gajiyawarsa da tsoron Allahnsa, na’am; haƙiƙa a cikin tsoro akwai jin daɗi, dadai yaron da yake ɗan shekara ɗaya yana da hankali, sannan kuma a tambayeshi: wanne hali ne naka mafi daɗi da mafi zaƙi? da wataƙila sai ya ce: halin nan da nake komawa ina mai fakewa i zuwa mahaifiyata a karo na biyu, a yayin da na ji gajiyawata da raunina i zuwa ƙirjin nan nata mai jin-ƙai, saboda tsoron tattausan marin nan nata. Tare da cewar duk jin-ƙannan na mahaifa, baikai komai ba, sai dai ɗan ƙyallin haske[1] daga tajallin nan na rahmar Allahntaka; domin haka, ma’abota cikar daraja daga mutane tabbas suna samun jin-daɗi, a cikin nuna gajiyawa a gaban Allah da tsoronsa; domin haka suke fakewa da gajiyawarsu i zuwa ga Allah, suna masu tsananin kuɓuta daga dabararsu da karfinsu, suka sanya gajiyawarsu da tsoronsu suka zama masu ceto a gare su.

 Amma ɗaya maganin shi ne nema da addu’a tare da godiya da wadatar zuci da dogaro a bisa rahmar nan ta mai arzurtawa mai jin-ƙai, shin haka ne kuwa?

 Na’am; ta yaya talauci da buƙatuwa, masu raɗaɗi nauyaya za su kasance ga baƙon nan na mai yawan baiwa mai karamci, wanda ya sanya fuskar ƙasa dukkanta ta zama kaɓakin ni’ima. Kuma ya sanya lokacin kaka ya zama kamar dami ne na furanni, da ya jejjera su a gefunan wannan kaɓakin, sannan ya rarratsa su a tsakankaninsa? Bari ma dai ka ji haƙiƙa talaucinsa da buƙatarsa, suna ɗaukan tattausar sura ta kwaɗayin abinci , yana aiki don ƙara talauci kamar sha’awa cin abinci. A saboda haka ma’abota cika a wajen Allah suna alfahari da talauci.[2]

 Ina yima kashedi da kada ka yi kuskuren fahimta, abin da ake nufi, shi ne ƙasƙantar da kai i zuwa ga Allah kana mai ji akanka cewa kai talaka ne, ba ana nufin da talauci ba, ka riƙi bara da bayyana talaucin a gaban halittaba.


[1]Ɗan ƙyallin haske kamar tsinin allura a kan dukkan hasken duniya.

[2] Buƙatuwarsu i zuwa ga Allah.




65. Page

 Amma wannan tikitin, da yake zama sanadin samu shi ne; ba da farillai, wanda sallah take a kan gaba, da nisantar manya-manyan zunubai, haka yake kuwa?

 

{Bin umarnin Alƙu’ani da nisantar hane- hanensa tamkar guzurine na Lahira}

Na’am; haƙiƙa samun guzuri da haske da taguwa[1] a tafiya ta har Abadan-abada, mai duhu da tsayi –tare da haɗuwar dukkanin ma’abotaƙwarewa da ma’abota ɗanɗanar zaƙin sanin Allah, da ma’abota ganin wasu daga ɓoyayyun asirin Allah- Haƙiƙa wannan yana samuwa ne ta hanya bin umarnin Alƙur’ani mai girma da nisantar hane-hanensa, babu wata hanya koma bayan haka. Idan ba hakaba, haƙiƙa dukkan ilimai na zamani da na falsafa, da na siyasar rayuwa da hikimomi, dukkansu ba su kai ƙimar ƙirshi ɗayaba[2] a cikin wannan hanya[3] domin duk hasken waɗannan ilimai suna tiƙewa ne daga bakin ƙofar kabari.

Yāke zuciyata mai yawan kasala!

Da sannu zaki sani –idan kina da hankali wanda bai riga ya gurɓaceba-haƙiƙa cewa ba abin da ya fi sauki, ya fi hutarwa da rashin wahala kamar ba da salloli biyar da nisantar manya-manya zunubai bakwai, wane abu ne ya fi girman sakamako da amfani daga su, ki faɗa ga wannan mutumin da wannan shaiɗan waɗanda suke zuga ki da ƙarfafa ki a bisa fasiƙanci da wauta: idan kun kasance kuna da wata dabara ta kashe mutuwa, da kawar da gushewa daga duniya, da ɗauke talauci da gajiyawa daga barin mutum, da rufe ƙofar kabari; to ku faɗa muna saurarenku, idan ba haka ba ku yi shiru.


[1] Abar hawa wadda ta fi komai sauri.

[2] Shi ne ƙaramin kuɗi a da yawa daga ƙasashen Larabawa.

[3] Ita ce hanyar lahira.




66. Page

Domin haƙiƙa cewa a masallacin nan na kasantattu mai girma ana karanta Alƙur’ani mai girma, mu yi sauraro i zuwa gare shi, mu haskaka da wannan hasken, mu yi aiki da shiriyarsa, mu sanya shi zikiri a kan harasanmu.

Hakayake; haƙiƙa cewa shi ne zance, shi gaskiyane ya zo daga wajen mai gaskiya, yana faɗar gaskiya yana bayyana haƙiƙa, yana yaɗa hikima mai haskakawa.


اللَّهُمَّ نَوِّرْ قُلُوبَنَا بِنُورِ الإِيمَانِ وَالقُرْآنِ، اللَّهُمَّ أَغْنِنَا بِالاِفْتِقَارِ إِلَيْكَ وَلاَ تُفْقِرْنَابِالاِسْتِغْنَاءِ عَنْكَ، تَبَرَّأْنَا إِلَيْكَ مِنْ حَوْلِنَا وَقُوَّتِنَا، وَالْتَجَأْنَا إِلىَ حَوْلِكَ وَقُوَّتِكَ، فَاجْعَلْنَا مِنَ المُتَوَكِّلِينَ عَلَيْكَ، وَلاَ تَكِلْنَا إِلىَ أَنْفُسِنَا، وَاحْفَظْنَا بِحِفْظِكَ وَارْحَمْنَا وَارْحَمِ المُؤْمِنِينَ وَالمُؤْمِنَاتِ.

وَصَلِّ وَسَلِّمْ عَلَى سَيِّدِنَا مُحَمَّدٍ عَبْدِكَ وَنَبِيِّكَ وَصَفِيِّكَ وَخَلِيلِكَ، وَجَمَالِ مُلْكِكَ وَمَلِيكِ صُنْعِكَ، وَعَيْنِ عِنَايَتِكَ وَشَمْسِ هِدَايَتِكَ، وَلِسَانِ حُجَّتِكَ وَمِثَالِ رَحْمَتِكَ، وَنُورِ خَلْقِكَ وَشَرَفِ مَوْجُودَاتِكَ، وَسِرَاجِ وَحْدَتِكَ فِي كَثْرَةِ مَخْلُوقَاتِكَ، وَكَاشِفِ طَلْسَمِ كَائِنَاتِكَ وَدَلاَّلِ سَلْطَنَةِ رُبُوبِيَّتِكَ، وَمُبَلِّغِ مَرْضِيَّاتِكَ وَمُعَرِّفِ كُنُوزِ أَسْمَائِكَ، وَمُعَلِّمِ عِبَادِكَ وَتَرْجُمَانِ آيَاتِكَ، وَمِرْآةِ جَمَالِ رُبُوبِيَّتِكَ وَمَدَارِ شُهُودِكَ وَإِشْهَادِكَ، وَحَبِيبِكَ وَرَسُولِكَ الَّذِي أَرْسَلْتَهُ رَحْمَةً لِلْعَالمَينَ، وَعَلَى آلِهِ وَصَحْبِهِ أَجْمَعِينَ، وَعَلىَ إِخْوَانِهِ مِنَ النَّبِيِّينَ وَالمُرْسَلِينَ، وَعَلَى مَلاَئِكَتِكَ المُقَرَّبِينَ، وَعَلَى عِبَادِكَ الصَّالِحِينَ.. آمين