NAVIGATION
Daga Makarantar Rasa’ilun Nur
Mawallafi:
Al-Imam Badi’uzzaman Sa’id Nursi
Xaukar nauyin fassara:
Khairat
Mai fassara:
Dr. Jamilu Abdullahi
Bita da Gyrarraki:
Prof. Attahir Dawud
Ustaz. Muhammad Sulaiman
Bugawa da Yaxawa:
Gidan bugu na Khairat
Yaren Asali:
Turkanci
Yaren Fassara:
Hausa
Tunasarwa: Wanna fassara fassara ce ta Wasiqun Haske (Rasa’ilun Nur) wanda su tafsirine na ma’ana ga Alqur’ani mai girma wanda aka yi su acikin harshen Turkaci na Daula Usmaniyya; an kiyaye matuqa wajen ciro ma’anoni masu zurfi na nassukan asali ba tare da sauyawaba,sannan sai da aka bi matakai har huxu gabanin buga wannan fassara, matakan sune:
1. Masu magana da wannan harshe kuma ‘yan asalin Rasa’ilun Nur su suka tsaya da wannan fassara, wanda kuma sun fahimci Rasa’ilun Nur xin sun kutsa lungu da sakonta sun kakkarantata, kuma sun kware a harshen Larabci da Hausa kuma sun san salo da azncinsa.
2. Bita ga wannan fassara daga daga kwamitin gyara da tacewa domin ganin ma’anar ta dace kwabo da kwabo da ta nassin asali, wanda su xin kuma sun tasone qarqashin kulawar wannan makaranta mai haske ta (Rasa’ilun Nur), kuma suke da guziri ishashshe na masaniya dangane da harshen asalin nassin (Rasa’ilun Nur).
3. Bitar wannan fassara daga kwararru a wannan harshe na Hausa ‘yan takarda.
4. Samun sanya xan bar qarshe na shirin bugawa daga kwamitin fassara bayan duba ga tsokacin da aka samu dangane da gyararraki.
Qari akan duk wannan; Imamun Nursi ya zavi wasu wasiqu daga litattafansa na kangaba kamar: “Al-kalimat” “Al-lama’at” “Al-maktubat” “Ash-shu’a’at” ya kuma shigar da su cikin wasu litattafan (wanda a can ne za a iya samunsu) kamar: “Asa Musa” “Zul fiqar” da “Axxalasim” da “Surajun Nur” da “Katmu Tasdiqil Gaibi”. Saboda haka ne awurin fassara an kiyaye wannan tsari da Imam ya yi da kansa a rubutun asali, an kuma gabatar da su kamar yanda suke dan su da ce da asali, Allah muke roqo ya amshi aikin ya sa a mizanin hasana.


