KALMA TA BIYAR

42. Page

KALMA TA BIYAR

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِ

إِنَّ اللهَ مَعَ الّذِينَ اتَّقَوا وَالَّذِينَ هُمْ مُحْسِنُونَ[1]

{Tabbas Allah yana tare da masu jin tsoronsa da waɗanda sukemasu kyautatawa}.

{tsaida Sallah da nisantar manyan Zunubi shi ne haƙiƙanin Mutuntaka}

Idan kanaso kasan tayaya tsaida sallah da nisantar manya-manya zunubai suka zama su ne haƙiƙanin aiki na mutuntaka, kuma tayaya suka kasance sakamako ne na zubinhalitta wanda ya dace da halittar mutum; to ka yi duba ka yi sauraro i zuwa wannan hikaya da take bamu misali a taƙaice:

 

{Hikayar sojaji biyu jajirtacce da marar jajircewa}

Ya kasance an taɓa samun wasu sojoji guda biyu, a ɗaya daga cikin rundunoni a lokacin kiran gangamin yaƙi, ɗaya daga cikin su horarre ne kuma mai son aikin sa ne. ɗayan kuwa  ba shi da gogewa a kan aikinsa, kuma ga shi yana da son kansa.

{Halin wannan jajirtaccen sojan mai ƙaunar aikinsa mai dogaro ga ƙasa }

Wannan ɗayan da ya kasance yana son aikin sa, yana kula da karɓar horo da kuma yaƙi, sam ba ya tunani a kan abubuwan buƙatu na rayuwarsa da kuma abicinsa[2]; domin cewa shi ya san abincinsa da ciyar da shi da kuma  ba shi kayan yaƙin da yi masa magani idan ya yi rashin lafiya, harma  ba shi abinci a baki idan ya buƙata[3], duk wannan aiki ne na ƙasa. Kamar yadda ya san cewa aikinsa na asali shi ne;karɓar horo irin na sojoji da yaƙi, sai dai ƙari a kan haka, shi zai kasance yana tsayuwa da harkar shirya abin buƙata na rayuwa da shisshirya kayan yaƙi, yana dafa abinci yana wanke mazuban abinci, kuma yana tanadar su, idan da za a tambaye shi, me kakeyi? zai ce ina aiki ne na wajibi na ƙasa ta, ba zai ce yana aiki saboda buƙatun rayuwar sa ba.


[1] Muna farawa da sunan Allah mai Rahma mai Jin-qai.

[2] Abincin da yake ci a kullum.

[3] Idan ya samu lalura, kamar cirewar hannaye.




43. Page

{ Halin sojannan marar jajircewa mai bin son zuciyarsa}

Amma ɗaya sojan mara ƙwarewa, kuma mai yawan cin abinci mai zari, kuma bai damu da karɓar horaswa aikin soja ba, da kuma yin yaƙi ba, ya kasance yana cewa ina ni ina wannan aikin, wannan haƙƙi ne da ya rataya a wuyan ƙasa.

 Koyaushe ya kasance yana tunani a kan abubuwan rayuwarsa, kuma yana tsananin nemansu, yana barin rundunar yaƙin yana tafiya i zuwa kasuwanni don ya yi saye-saye, watarana sai abokinsa wanda ya samu cikakken horo na aikin soja ya ce masa:

{Nasihar da jajirtaccen sojan ya yi wa ɗan’uwansa}

 Ya ɗan’uwana; haƙiƙa aikinka na asali shi ne; karɓar horo na soja da yaƙi, haƙiƙa a dalilin hakane aka zo da kai nan wajen, saboda haka, ka dogara ga wannan sarkin, domin shi bazai taɓa barin ka da yunwa ba, don cewa wannan wajibinsa ne kuma 

44. Page

aikinsa ne, kai gajiyayye ne marashi, ba za ka taɓa iya samun wanda zai ciyar da kai a kowanne waje ba, ga lokaci kuma lokacin gangamin yaƙi ne da yaƙi, idan ba ka tsaya kan aikinka ba zai ɗaukeka a matsayin mai laifi kuma ya yi maka uƙuba.

Na’am, yanzu ya bayyana a gabanmu akwai ayyuka guda biyu:

Ɗayansu: aikin sarki ne; shi ne tsayawa da ciyar damu, mu kuma a ɓangarenmu za mu tsaya da hidima a gare shi a wani lokaci.

Ɗayan kuwa: aikin mune, shi ne karɓar horon aikin soja da yaƙi, shi kuma sarki ta ɓangarensa zai taimakemu da abubuwan da ake buƙata a wajen yaƙi.

 Yā jama’a, ƙaƙa girman wannan haɗarin na wannan sojan mai juya baya ga barin ɗabi’u madaidaita , in dai shi bai yi sauraro i zuwa wancan sojan mayaƙi wanda ya samu horo na yaƙi ba? da sannu za ka fahimci haka.

{Haƙiƙar ma’anar hikayar}

Yāke raina mai yawan kasala:

Haƙiƙa fagen yaƙin nan mai jujjuyawa, shi ne wannan rayuwar ta duniya marar tabbas.

 Amma sojoji waɗanda aka rarraba su i zuwa rundunoni, su ne al’ummar nan ta ‘yan’dam.


45. Page

Amma wannan rundunar[1] ita ce jama’ar musulmi ta wannan zamanin.

Amma sojojin nan guda biyu:

Ɗayan su shi ne, musulmi mai tsoron Allah, wanda ya san farillansa na addini da tsayuwa da su, shi ne wanda yake yaƙar zuciya da shaiɗan saboda barin manya-manyan zunubai, da barin miyagun laifuka.

Amma ɗayan kuwa shi ne: fasiki hasararre, wanda ya nutse a cikin baƙin cikin tunanin rayuwa har ya kai ga matakin da yake tuhumar mai arzurtawa na haƙiƙa[2], shi ne wanda yake barin farillai,kuma yake aikata duk abin da yake gamuwa da shi na zunubi, a saboda ya samu lomar da zai sa abakin sa.

Amma waɗannan umarni da horarwar su ne ibada, wadda sallah take a kan gabansu.

Amma wannan yaƙin shi ne, yaƙi da kai da son zuciya da shaiɗanun mutane da aljanu; don tsamar da zuciya da rai daga zunubai da munanan halaye da halaka madawwamiya.

Amma waɗannan ayyuka guda biyu, wanda ɗayan su, shi ne ba da rayuwa da kuma ciyarwa, ɗayan aikin shi ne ibada da soyayya da iƙirari ga mai ba da rayuwa mai arzurtawa, da ƙasƙantar da kai i zuwa gare shi, da dogaro a gare shi da amintuwa da shi.

{Maƙagin halitta shi kaɗai ne mai iya tafiyar da ita}

 Hakayake, haƙiƙa wanda ya yi halitta ya ba da rayuwa wacce ita ce mafi bayyanar mu’ujiza ta ƙirar abin nufi da buƙata da mafi ƙayatuwar hikima ta ubangijantaka-

[1] Wato rundunar da aka yi misali da ita a cikin wannan kalma ta biyar.

[2]Shi ne Allah (S.W.T).




46. Page

cewa shi ɗaya ne yake dawwamar da ita, yake ciyar da ita da arziki, babu wani bayan shi.Shin kana son dalili a kan haka?

{Arziƙi na da alaƙa da gajiyawa ko rauni}

Tabbas mafi raunin dabba da mafi daƙiƙancinta ana ciyar da itamafi kyaun abinci, kamar yadda yake a wajen tsutsotsin kayan marmari da kifaye, haƙiƙa mafi kasawar abin halitta da mafi raunin su lallai yana cin mafi daɗin abinci kamar yadda yake a halin jira-jirai da ƙananan yara.

 Hakayake; domin ka fahimci cewa hanyar da ake neman arziki na halal bata zamowa da iko ko zaɓi, sai dai da kasawa da rauni;[1] ya isheka ka auna kuma ka kwatanta tsakanin kifi da dila, da tsakanin yara da dabbobin daji, da tsakanin bishiyoyi da dabbobi.

Kenan wanda yake barin sallar sa saboda sabgogin neman abinci, kwatankwacinsa kamar wancan sojan ne wanda yabar karɓar horo na aikin soja da mafakar sa, ya tafi yake bara a kasuwanni

Sai dai cewa kaikawo wajen neman arziki a cikin taskar nan ta mai rahma mai yawan arzurtawa mai karamci, har dai mutum kada ya zama nauyi a kan wasu, bayan mutum ya gama sallah, wannan kaikawo ne mai kyau, banda haka ma jan-mutunci ne da jaruntaka, sannan shi kansa ibada ne.


[1] Wato Allah yana yassare maka gwargwadon kasawarka da rauninka.




47. Page

Sannan zubin-halittar-mutum da tanade-tanadensa na ma’ana suna shiryarwa ne a bisa cewa shi an halicce shi ne don ibada; domin mutum ba ya kaiwa matsayin mafi koma bayan tsuntsu ta fuskar aiki da iko nayin wasu abubuwa na wajibi don rayuwar sa ta duniya,[1]sai dai cewa shi da ilminsa da buƙatuwarsa ta hanyar ibada da kaskantar da kai waɗanda su ne tilas ga rayuwarsa ta ma’ana da ta lahira. yana zama sarki ga halitta gabaɗaya da kuma jagoransu.

To don haka ya ke rai !

Da ki sanya rayuwar duniya ta zama ita ce matuƙar burinki, ki yi aiki saboda ita kodayaushe, da sai ki kasance a matsayin mafi koma bayan tsuntsu.

Amma idan kika sanya rayuwar lahira ita ce matuƙar burinki, kika sanya wannan rayuwar ta duniya ta zama kamar gona ce kuma tsani i zuwa gare ta,[2] kika yi aiki da abin da yake dacewa da hakan; to a lokacin ne za ki zama kamar jagora mai girma ga halittu, kuma ki zama bawa ɗan gata mai ƙasƙantar da kai, kuma baƙo na ubangiji mai girma, abin girmamawa ga ubangiji mai girma da ɗaukaka a cikin wannan duniya.

Ga hanyoyi biyu nan agareki, sai ki zabi wanda kike so daga cikinsu, kuma ki nemi shiriya da dacewa daga mafi jin-ƙan masu jinƙai.


[1]Wasu tsuntsayen suna iya cin abinci mai kamar girman jikinsu kuma su yi jima’i sau ishirin a kullum.

[2] Wato ita lahira.