KALMA TA BIYU
NAVIGATION
26. Page
KALMA TA BIYU
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِ
الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالْغَيْبِ[1]
{Imani hanyar rabauta ce ta har abada kafurci kuma hanyar taɓewace ta har abada}
Idan kana so ka riski irin abin da yake cikin imani na daga samun nasara a rayuwa da kuma ni’imomi masu girma, da kuma abin da yake cikinsa na jin daɗi da kwanciyar hankali mai girma; to yi duba i zuwa wannan hikaya da aka misalta ta a takaice, saurari ka ji:
{Hikayar wasu mutun biyu ɗaya mai dogaro ga Allah ɗayan kuma marar dogaro ga Allah mai son kansa}
Wata rana, wasu mutane biyu sun fita a wata tafiya, saboda shaƙatawa da kuma kasuwanci, ɗaya daga cikinsu mai son kai ne, mara sa’a, sai ya bi wani tafarkin, ɗayan kuma bawan Allah ne mai sa’a, shi ma sai ya kama wani tafarkin, kowanne ya kama hanyarsa.
[1] (Su ne waɗanda suke imani da gaibi) Surat albaƙara aya ta 3.
27. Page
Mutumin nan mai son kansa – haƙiƙa shi mai ji-ji da kai ne mai son kansa ne kuma mai munmunan zato ne ga rayuwa – sai ya faɗa cikin wani gari mai matuƙar muni – a irin ganinsa – sakamakon munmunan zatonsa, sai dai duk inda ya duba sai ya ga gajiyayyu marasa komai waɗanda ba su da wata dabara, suna ta kururuwa da ihu daga damƙar nan ta wasu mutane azzalumai masu tsananin zalunci da ayyukan ɓarna suna cewa ya kaitonmu, kuma yake gani a duk inda ya zagaya, yanayi na baƙin ciki, mai sa ƙunar zuciya, kamar irin halin da ya gabata, kai ka ce dukkan garin zaman makoki a keyi, a saboda haka bai samu mafita ko sauƙi daga wannan hali mai raɗaɗi mai duhu da yake ciki ba, sai ta hanyar maye; domin dukkan mutane yana ganinsu a matsayin maƙiya, bare, hakanan kuma yana gani a kowane guri gawawwaki masu ban tsoro a barbaje, da marayu suna ta kuka irin na masu ɗebe ƙauna daga ceto; sai zuciyarsa ta azabtu matuƙar azaba.
28. Page
Amma ɗayan kuma, mutum ne na Allah bawan Allah mai neman gaskiya ma’abocin kyawawan ɗabi’u, sai ya faɗa a cikin wani gari kyakkyawa - a irin dubansa - to wannan mutum na gari sai yake ganin kamar ko ina buki akeyi a cikin garin da ya shiga, sai kuma yake ganin a kowanne guri ana murna da bukukuwa da majalisai na zikiri da suka narke a cikin ambaton Allah, da dai ƙarin murna, kowa a garin sai ya zama kamar aboki ko ɗan’uwa. Sai yake gani a dukkan sasannin garin akwai bukukuwa gagarumai na sallama daga aiki waɗanda suke cike da sowar farin ciki da muryoyi na yabo da kuma kiɗa da nashidodi da suke haɗe da kabbarori da hailaloli a cikin biki mai kamar yanayin bukin ɗaukar sababbin sojoji, a yanayi na murna da farin ciki.
Yayin da mutumin nan na farko mara sa’a yana ɗanɗanar raɗaɗinsa da kuma raɗaɗin da mutane gabaɗaya suke ɗanɗana, sa’ilin nan shi kuma na biyun sai ya kasance mai arziki, yana farin ciki da halin da yake ciki da halin da dukkan jama’ar nan suke ciki, sai ya yi kasuwanci mai riba ya godewa Allah, sannan sai ya komo
{Haɗuwar mutanan nan biyu}
29. Page
Katsahan sai ya haɗu da ɗaya mutumin, sai ya fahimci halin da yake ciki, sai ya ce masa haƙiƙa ka zama zararre[1], da alama abin da yake baɗininka na daga munanan halaye ya fito fili ; domin kai kana zaton dariya kamar kuka ce, kuma sallama daga aiki da karɓar kayan aiki kamar tsiraitarwa ne da ƙwacewa, to ka dawo cikin hayyacinka, ka tsarkake zuciyarka, haddai a yayewa ganinka wannan hijabin mai shu’umanci, ka samu ikon ganin komai yadda yake a haƙiƙarsa.
Haƙiƙa sam ba ya yiwuwa a ce wata kasar mulki maɗaukakiya cikakkiya, da take bayyana wannan gwargwado na guraben hauhawar darajoji da cika a gaban idanuwa da mafi cikar daraja, na sarki wanda yake shi ne mafi cikar daraja da adalci da rahama da kiyaye talakawansa da iko da kula da tsari da kuma tausasawa, ta zama a irin yanayin da zatonka yake riyama ba.
Bayan wannan bayanin, wannan mutum mara sa’a a baya, yanzu sai ya dawo cikin hayyacinsa da shiriyarsa ya yi nadama yake cewa, haƙiƙa tabbas na zama zararre[2],
[1] Mahaukaci, wanda hankalinsa ya gushe.
[2] Mai gurɓataccen hankali
30. Page
da sababin dawwama cikin shan giya da maye, Allah ya yi maka albarka da ka tsamoni daga cikin wannan hali na azaba kamar wutar Jahannama.
{ Haƙiƙar ma’anar hikayar}
Ya ke zuciya, ki yi sani, hakika mutumin nan na farko, kodai kafiri ne ko kuma gafalalle fasiƙi, ita kuma duniya ita ce wajen zaman makokin nan na gabaɗaya a mahangarsa, dukkan masu rai, su kuma su ne marayu masu kūka daga buguwannan[1] na ciwon rabuwa da kuma mangarin gushewa.
Amma mutane da dabbobi, su halittu ne da ba su da masu kula da su zautattu, sai ajali ne kaɗai yake rasar da su, su kuma samammu abubuwa manya-manya, kamar duwatsu da koguna, su suna matsayin gawawwaki ne da suke da ban tsoro kuma ba su da rai, da wasu kuma bayan waɗannan na daga zace-zace da yawa masu ba da tsoro masu tsananin raɗaɗi, dukkan wannan ya faru ne saboda kafircinsa da ɓatansa, kuma sai su azabtarda shi, azabtarwa ta ma’ana.[2]
[1] Nuƙurƙusar da baƙin ciki yake yi a zuciya.
[2] A ma’anar halin da suke ciki ba zahiri ba.
31. Page
Amma ɗaya mutumin mumini ne ya san mahalicci maɗaukaki, kuma yana gasgatashi, wannan, duniya a tunaninsa, gida ce na ambaton Alrahman, kuma farfajiya ce ta ilmantarwa da horaswa ga ‘yan’dam da dabbobi, kuma fagen jarrabawa ne ga mutane da aljanu.
Amma mace-macen dabbobi da na mutane, tamkar sallama ce daga ayyukansu, waɗanda suka gama ayyukan rayuwarsu, suna ƙaura nesuna masu farin ciki na ma’ana daga wannan gida ƙararre i zuwa gidan nutsuwa da kwanciyar hankali[1]; har dai dama ta yalwata don ma’aikata sababbi su zo su yi aiki.
Amma waɗanda aka hahhaifa na dabbobi da na mutane, kamar zuwa ne don aikin soja da karɓar makami da kuma rungumar aiki kai tsaye, kuma haka dukkan ma’abota rayuwa, sojoji ne ma’aikata ne masu farin ciki ababan ummarta ne masu tsayawa a kan gaskiya suna masu yarda.
Amma kururuwar nan da amsa amon nan dukkansu, ko dai su kasance ambaton Allah da tsarkake shi a farkon aiki, ko kuma godiya da farin ciki a ƙarshensa, ko wasu Karin launonin waƙoƙi ne da suke faruwa saboda shauƙin jin daɗin aiki.
[1] Aljanna.
32. Page
A mahangar wannan mumini, samammu dukkansu masu hidima ne masu ɗebewa juna kewa ne, ma’aikata masoya juna, kuma littattafai ne tausasa na shugabansa mai karamci kuma mamallakinsa mai jin-ƙai, da wasun waɗannan na daga haƙiƙoƙi masu tabshi maɗaukaka masu daɗi da zaƙi da suke bayyana ta hanyar imaninsa.
{Ma’anar Imani}
To kenan imani-a ma’anance - yana ɗauke da ƙwayar iri ta bishiyar Altuba[1] ta aljanna , amma kafirci kuma yana ƙunshe - ama’anance- daƙwayar iri ta bishiyar Al zakkum[2] ta jahannama.
To kenan kuɓuta da aminci, suna cikin musulunci da imani, kaɗai, tun da al’amarin haka yake, to ya wajaba akanmu mu dinga faɗi kodayaushe:
الحمد لله على دين الإسلام وكمال الإيمان[3]
[1]“Alxubaالطوبى " bishiya ce mai girma a Aljanna wadda inuwarta mutumin da ke kan abin hawa zai iya tafiyar ɗaruruwan shekaru a cikinta bai ƙure ta ba.
[2]“Azzaqƙum”الزقوم wata bishiya ce mummuna da take tsurowa a cikin wutar jahanama.
[3]‘Muna gode wa Allah a bisa baiwar da ya yi mana na addinin musulunci da cikakken imani’


