KALMA TA FARKO
NAVIGATION
18. Page
الرَّحِيمِ
وَبِهِ نَسْتَعِينُ
الحَمْدُ لِلهِ رَبِّ العَالَمِينَ، وَالصَّلاَةُ وَالسَّلاَمُ عَلَى سَيِّدِنَا مُحَمَّدٍ
وَعَلَى آلِهِ وَصَحْبِهِ أَجْمَعِين[1].
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN-КAI
Da shi ne nake neman taimako
Ya kai ɗan’uwa; haƙiƙa ka nemi waɗansu nasihohi daga gare ni, to sai ka saurara tare da ni i zuwa wasu haƙƙoƙi guda takwas da aka tsara su a cikin tsari na hikayoyin soja gajejjeru, ana ɗaukar ka a matsayin soja, a yayin da ni nake ganin kaina ni ne mafi buƙata i zuwa nasiha fiye da kowa, haƙiƙa ni na faɗawa kaina waɗannan kalmomin guda takwas a wani lokaci –tare da tsawaitawa – na ciro su ne daga ayoyi takwas[2].
Yanzu da sannu zan ambace su a taƙaice ga kaina, da harshen da kowa zai iya fahimta, wanda yake so sai ya saurara tare da ni.
[1]Dukkan yabo ya tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata a bisa shugabanmu, Annabi Muhammad tare da alayensa da sahabbansa gabaɗaya.
[2]Ayoyin Alƙur’ani.
19. Page
KALMA TA FARKO
بسم الله الرحمن الرحيم
{Bismillah}
[1]بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah”,shi ne tushen dukkan alheri, mu mā nan da shi ne muke farawa.
Ya ke zuciyata ki yi sani cewa wannan kalma mai albarka ba ta kasance wani take na musulunci kawai ba, daɗin daɗawa, ita wani wuridi ne da dukkan samammu suke yi da irin harasan halayensu.[2]
Ya ke zuciyata, idan kin so ki fahimci ta yaya بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah” ta zama ƙarfi ce mai girma wanda ba ya ƙarewa, kuma albarka ce da ba ta ƙarewa, to ki yi duba tare da sauraro i zuwa wannan taƙaitacciyar hikaya mai kamantawa:
{Hikayar matafiya biyu}
Haƙiƙa, duk mutumin da yake so ya yi kai wa da komowa a cikin tsakiyar sahara ta dājin Larabawa, to ya wājaba a gare shi ya danganta kansa i zuwa shugaban wata ƙabila,[3] kuma ya shiga cikin kariyar sa da tsaronsa; domin ya kuɓuta daga sharrin ‘yan fashi kuma ya riski biyan buƙatunsa, idan kuwa ba haka ba zai zauna a cikin halin kaɗaitaka, rashin jin dādi da baƙin ciki a gaban maƙiyansa, da kuma tarin tulin buƙatunsa da ba su da iyaka.
[1]Da sunan Allah.
[2] Ba mutum ko dabba ba kawai, har abubuwan da ba sa motsi kamar duwatsu da makamantansu. (mai fassara)
[3] A al’adar Larabawa, musammam a zamanin da, idan kana so ka kuɓuta daga farmaki, to wajibi ne ka kasance a cikin wata babbar ƙabila ko ka danganta kanka zuwa shugaban ƙabilar. (mai fassara).
20. Page
A cikin yanayi na irin wannan tafiya mutane biyu suke yin tafiya a cikin wannan sahara, ɗayansu mutum ne mai tawali’u, ɗayan kuma mutun ne mai girman kai. Shi maitawali’un nan, sai ya danganta kansa i zuwa wani shugaba, amma mai girman kan nan bai danganta kansa ga kowa ba. Wanda ya danganta kansa ga wani shugaba, sai ya yi ta kewayawarsa ko’ina da ina cikin aminci. Duk sanda suka yi kiciɓis da wani ɗan fashi, sai ya ce masa ni da kake gani na ɗin nan, ina kewayawa ne da sunan shugaba wane. Ɗan fashin nan sai ya juya ya rabu da shi, ba zai iya cutar da shi da wani mummunan abu ba, duk sanda ya shiga wata rumfar tanti sai ya samu kyakkyawar tarba da girmamāwa don albarkacin wannan sunan.[1]
Amma ɗaya mai girman kan, ya shiga wahala sosai a cikin tafiyarsa, ya gamu da bala’o’in da ba za su kwatantu ba, ya kasance yana makyarkyata saboda tsoro, kuma yana roƙon mutane kodayaushe; sai ya wayi gari yana maƙasƙanci wulaƙantacce.
{Haƙiƙar hikayar}
Ya ke wannan zuciya ruɗaɗɗiya mai girman kai, ke ce wancan matafiyin, wannan duniya kuma ita ce saharar, gajiyāwārki da kuma tsananin talaucinki ba su da iyaka, haka nan adadin yawan maƙiyanki da kuma buƙatunki su ma ba su da iyaka.
[1]Sunan wannan shugaban qabila da ya danganta kansa gare shi. (mai fassara).
21. Page
Matuƙar al’amarin ya kasance kamar haka, to ki danganta kanki ga mai mulki na har abada, da Sarki[1] na fil’azal, ga wannan sahara; har dai ki kuɓuta daga roƙo a wajen kasantattu, da kuma matsanancin tsoro daga dukkan abin da yake faruwa.
Hakayake; haƙiƙa wannan kalmar بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah” taska ce mai albarka, kuma gajiyawarki da buƙatuwarki waɗanda ba su da iyaka, su ne suke haɗa ki da ƙarfin iko da rahama waɗanda ba su da iyaka, sai ta sanya gajiyāwār da buƙatuwar su zamo ababen ceto karɓaɓɓu a gaban ƙofar sarki mai cikakken iko da jin-ƙai.
Haka yake; tabbas misalin wanda yake motsawa da wannan kalmar بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah”, kamar misalin wani mutum ne wanda yake shiga cikin tsarin aikin soja yana motsawa da sunan ƙasa, ba ya tsoron kowa ko wane ne shi; saboda yana magana da sunan ƙasa da kuma sunan dokokin ƙasa, kuma yana zartar da dukkan ayyuka, kuma yana jurewa a gaban kowane abu.
[1] Allah (S.W.T) (mai fassara)
22. Page
Haƙiƙa mun faɗa a farko cewa: tabbas dukkan kasantattu suna ambaton:بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah” da irin harasan halayensu, ko ba haka ba ne ba? Eh, haka ne.
Da a ce za ka ga wani mutum ɗaya, ya zo ya kora dukanin mutanen gari i zuwa wani guri ta hanyar tilastawa, ya tilasta musu yin aiki dole, to za ka sakankance cewa wannan mutumin bā da sunansa ko ƙarfinsa na ƙashin kansa yake wannan aikin ba, sai dai tabbas cewa shi soja ne da yake aiki da sunan ƙasa, kuma yana dogaro ne ga ƙarfin sarki, to hakanan dukkan komai yana motsawa ne da sunan Allah. Hatta ƙwallo da ƙwayoyin iri ƙanana masu kama da ƙwayoyin zarra suna ɗauke da bishiyoyi gingima-gigima a bisa kawukansu suna ɗauke da nauyaye-nauyaye kamar duwatsu. Kowace bishiya kenan tana faɗin: بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah” sai ta ciko hannuwanta da ’ya’yan itatuwa daga taskar rahama[1] ta gabato mana da su kamar ɗan kasuwa wanda yake baje hājarsa a kasuwa.
Kowane lambu yana faɗin: بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah” ne, sai ya wayi gari tukunya daga tukwanan madafar[2] nan ta ƙudura,[3] sai a dafa a cikinta abinci mai daɗi iri daban-daban mai tārin yawa da yalwa.
Dukkan dabbobi masu albarka, kamar irinsu shanu, raƙuma, tumaki, da awaki, suna faɗin: بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah” sai su wayi gari hantsarsu ta zama maɓuɓɓugar nono daga makwararar rahama, sai su gabatar mana da sunan ٱلرَّزَّاقُ mai azurtawa, abinci mai laushi, tsaftatacce kamar ruwan rayuwa.
Tabbas jijiyoyin tsirrai da na bishiyoyi da na ganyayyaki da jijiyoyinsu sirara masu laushi da tabshi kamar alharini, su ma suna faɗin: بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah” sai su fasa kurman dutse da tsandaurin ƙasa busasshiya, su nutsa cikinsu suna masu faɗin: بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah” da kuma ambaton sunansa mai Rahama ٱلرَّحۡمَٰنِ, sai a hore musu komai a yalwata shi a gare su.
[1] Jin ƙan Allah (S.W.T) (mai fassara)
[2]Ɗakin girki
[3] Ikon Allah (S.W.T) (mai fassara)
23. Page
Na’am; ka ga yaɗuwar jijiyoyin shuka a cikin kurman dutse da kuma busasshiyar ƙasa mai tsandauri cikin matuƙar sauƙi, da zuba ’ya‘yansu a ƙarƙashin ƙasa, kamar yaɗuwar rassa a cikin iska da fito da ’ya’yansu a jikinsu, hakanan wanzuwar korayen ganyayyaki masu laima da tabshi da rauni a cikin tsananin zafin rana tsawon watanni ba tare da wata illa ta same su ba, duka waɗannan abubuwan suna marin fuskokin ‘yan ɗabi’a,[1] sannan kuma suna sa ɗan yatsansu su tsokane makantattun idanuwan nan nāsu, su ƙara makancewa duɗum, suna cewa: haƙiƙa hatta tsauri da zafi,[2] su biyun nan da a kansu ne kuka dōgora ba sa motsawa sai da umarni. Dubi saiwa a ƙasa rarrauna mai tabshi kamar alharini, amma take keta duwatsu ta shiga ƙasa, kamar irin aikin da sandar Annabi Musa (A.S) ta yi tana mai bin umarni:اِضْرِبْ بِعَصَاكَ الحَجَر[3].
[1] Waɗanda suke danganta faruwar komai ga xabi’a (mai fassara)
[2] Abin da shafi ƙasa da abin da ake samu a cikinta da zafin rana da na wuta. (mai fassara)
[3] Ka doki dutsen da sandarka
24. Page
Haka nan ganyayyakin bishiya marasa kauri masu tabshi kamar takardar taba sigari, suna karantawa a lokacin zafin rana, kamar yadda gaɓoɓin Annabi Ibrahima amincin Allah ya tabbata a gare shi suke karantawa, yayin da aka jefa shi a wuta mai ƙuna:يَا نَارُ كُونِي بَرْدًا وَ سَلَامًا[1] tun da kowanne abu yana furuci da: بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah” a ma’anance,[2] sannan sai ya janyo ni’imomin Allah kuma ya gabatar mana da su da sunan Allah; to don haka wajibi ne a gare mu mu ambaci: بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah” kuma mu ba da, da بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah” mu kuma karɓa da بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah” to kenan ya zama wajibi a gare mu, kada mu karɓa daga hannun gafalallun mutane da bā sa bayarwa da بِسۡمِ ٱللَّهِ“Da sunan Allah”.
Tambaya: Haƙiƙa mu muna bā da kuɗi ga waɗanda su a matsayin masu baje kolin hajoji suke, (idan muna so mu fanshi wani abu) to yā jama’a! Wanne irin kuɗi ne Allah maɗaukakin sarki yake neman su, wanda shi ne mamallaki na ainihi na wannan dukiya?
Amsa: kuɗin da yake nemansu daga gare mu, wancan mai ni’imantarwa na haƙiƙa[3], a madadin waɗancan ni’imomin da kuma waɗannan dukiyoyin masu tsada, abubuwa uku ne kamar haka:
Na farkonsu:الذكر, ambaton Allah.
Na biyunsu:الشكر, godiya Allah.
Na ukunsu:الفكر, tunani a cikin ni’imomin Allah S.W.T.
[1] (Ya ke wuta ki zama sanyi da aminci
[2] Wato ba sai mun ji furucin bisimillah daga bakinsa ba, halinsa da aikinsa shi zai tabbatar ma cewa yana yin bisimillah.
[3]Allah (S.W.T).
25. Page
Da farkon farawa za mu fara da [1]بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah” shi ne ٱلذِّكۡرِ Alzikiri, a ƙarshe kuma za mu faɗi ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِshi ne godiya, a tsakiya kuma za mu dinga yin tunanin cewa haƙiƙa waɗannan ni’imomi masu matukar daraja da ƙayatarwa su mu’ujiza ce, ƙudurar sarki mai cikakken iko maɗayanci abin nufi da buƙata, kuma kyautaye-kyautayen rahamarsa ne, riskar haka to shi ne الفكر tunani a cikin ni’imomin ubangiji.
Kamar yadda sumbatar ƙafafuwan mutum miskini wanda ya kawo ma kyauta mai daraja daga wajen wani sarki, tare da jahiltar sarkin mai asalin kyautar; wauta ce da ta kai matukar wauta; to yabo da nuna soyayya ga masu ni’imtarwa na zahiri da mantawa da mai ni’intarwa na asali, shi ne ya fi zama tsananin wauta daga wancan sau dubu.
Ya ke zuciya idan kin so kada ki zama wawa kamar wancan to:
Ki bayar da بِسۡمِ ٱللَّهِ“Da sunan Allah”.
Ki karɓa da بِسۡمِ ٱللَّهِ“Da sunan Allah”.
Ki fara da بِسۡمِ ٱللَّهِ“Da sunan Allah”.
Ki yi aiki da بِسۡمِ ٱللَّهِ “Da sunan Allah”.
والسلام
[1] Ambaton Allah ko farawa da (bisimillah) kafin fara komai (mai fassara).


