KALMA TA HUDU

37. Page

KALMA TA HUƊU

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِ

الصَّلاَةُ عِمَادُ الدِّينِ[1]

{Sallah ita ce ginshiƙin Addini, kuma dalili na rabauta a Duniya da Lahira}

 Idan kana so ka yi sani, sani na yaƙini – kamar yadda idan ka haɗa biyu da biyu za su ba ka huɗu- ta yaya hakika sallah ta zama ma’abociyar kima maɗaukakiya, da muhimmancinta ya kai matuƙa, kuma ta yaya tsayuwa da sallah yake da sauƙi, kuma yake da sauƙin nauyaye-nauyaye, kuma ta yaya mai barin sallah zai zama mutum ne zararre, kuma taɓaɓɓe; yi duba i zuwa wannan hikayar da aka misalta ta ataƙaice tare da lura:

{Hikayar gonar wani sarki da barorinsa guda biyu}

 an yi wani sarki mai girma, a cikin wani zamani, ya aika mutane biyu daga masu yi masa hidima i zuwa gonarsa, ta musamman mai kyau, wadda take da nisan tafiyar wata biyu don su zauna a cikin ta, bayan ya bawa kowannensu kuɗi gwargwadon lira ishirin da huɗu ta zinare,[2] sai ya ummarce su da amfani da wannan kuɗin a bisa bukatun hanya da tikiti, da kuma sayen wasu ɓangare na abubuwan amfani da suka zama tilas a wajen zamansu, kuma akwai wata tasha wadda take nisan tafiyar kwana ɗaya, a cikin ta akwai mota da kuma jirgin ruwa, jirgin ƙasa da jirgin sama, ana hawan kowanne daga cikin su ne a gwargwadon ƙarfin aljihu.

Bayan an gama yi musu bayanin wannan darasin sai suka fita, ɗaya daga cikin su ya kasance mai sa’a ne, a inda ya yi amfani da kuɗi kaɗan daga dukiyar sa, har ya kai ga isa tashar, bugu da kari kuma ya yi kasuwanci mai riba, wanda za ta ba wa mai gidan sa mamaki, kumajarinsa ya ɗaukaka daga ninki ɗaya zuwa ninki dubu.

Amma ɗaya mai hidimar mara sa’a ne mara hankali, ya kashe lira ishirin da uku na zinare, daga abin da yake wajen sa kafin ya isa i zuwa tasha, ya ɓannatar da su ne wajen caca da wasanni, sai lira ɗaya ce kawai ta ragu a wajen sa.

{Nasihar wannan mai sa’a ga ɗan’uwansa}


[1]Sallah ita ce ginshiƙin Addini

[2] Kuxin qasar Turkiyya




38. Page

 a nan ne sai abokin sa yake ce masa ya kai wannan mutum ka yi amfani da wannan lira ɗayan taka a wajen sayen tikitin tafiyar, har dai kada ka zamo a cikin wannan doguwar hanya kana mai tafiya a ƙasa cikin yunwa, ka ga shugaban mu mai karamci ne, wataƙila ma ya ji-ƙan ka ya yi ma afuwa a kan abin da ka aikata na taƙaitawarka ga bin umarnin sa, ya ɗauke ka a kan jirgi ya sadar da kai i zuwa wajen zaman mu tare, idan ba ka aikata haka ba, to za ka buƙatu da ka tafi kai kaɗai, kana mai tafiya a kan ƙafafuwa a halin kana mai fama da yunwa, a cikin sahara, wadda za ka yi wata biyu kafin ka yanke ta.

Ya ku jama’a! idan wannan mutum ya yi tsaurin kai yaƙi amfani da ragowar lirarsa guda ɗaya tilo ta zinare a wajen sayen tikiti wanda yake a matsayin ɗan mabuɗi na 

39. Page

taska[1]a gare shi, bari dai kawai, sai ya kashe ta a wauta saboda ɗan jin-daɗi na ɗan lokaci, shin ko da mafi dolancin mutane ba zai iya ganewa cewa wannan mutum yana cikin matuƙar wauta da taɓewa da rashin sa’a ba?!

 Yā kai mai barin sallah, yā ke raina wadda take ƙuntatuwa daga ita!

 

{Haƙiƙar ma’anar hikayar}

Wannan sarkin shi ne ubangijinmu mahaliccin mu.

Amma masu hidimannan matafiya, ɗayan su shi ne mai addini da yake yin sallar sa cikinshauƙi, ɗayan kuwa gafalalle ne mai barin sallah.

Amma waɗancanlirorin ishirin da huɗu na zinare, to su ne awowi ishirin da huɗu na kowacce rana ta rayuwa gabaɗaya.

Wannan keɓantacciyar gonar nan, ita ce aljanna.

 Amma wannan tashar ita ce kabari.

 Amma wannan tafiyar, ita ce tafiyar mutum i zuwa kabari, sannan filin tashin alƙiyama, sannan i zuwa tabbata ta har abada, Kowa yana yanke wannan hanyar mai tsawo da darajoji na tserereniya mabambanciya gwargwadon aikinsa da tsoron Allan sa. Wani kashin daga ma’abota tsoron Allah, suna yanke tafiyar shekara dubu a cikin kwana ɗaya, kamar walkiya, ɗaya kashin su kuma suna yanke tafiyar shekara dubu hamsin a kwana ɗaya kamar ɗarsawar zuciya, Alƙur’ani mai girman sha’ani ya yi nuni i zuwa wannan haƙiƙar a cikin ayoyi biyu daga ayoyin sa.[2]

 Amma wannan tikitin shi ne sallah; domin awa ɗaya ta isheka ka yi su dukkan salloli biyar harda alwalar su.


[1] Taska ta har abada wato aljanna

[2] (a) Surat Alma’arij aya ta 4. (b) Surat Alhajj, aya ta 47 (.وان يوما عند ربك كألف سنة مما تعدون)

(تعرج الملاءكة والروح إليه في يوم كان مقداره خمسين الف سنة)




40. Page

{Girman asarar ɓata lokaci ba a bautar Allah ba }

Ya jama’a yaya girman hasara da zaluntar kai ga wanda yake amfani,da awa ashirin da uku saboda wannan rayuwa duniya mataƙaiciya kwarai, amma bazai iya amfani da awa ɗaya ba saboda rayuwa ta har abada mai tsayi ba! Sau da yawa halin sa yana kasancewa ya saɓawa hankali.

Tunda hankalin mutum zai iya yarda da cewa ya zuba rabin dukiyar sa a cikin caca wadda mutane dubu suka shiga, saboda sa ran samun nasarar ɗaya a cikin su dubun nan. Idan dai hankali zai iya karɓar haka, to ta yaya ne halin wannan mutum ya saɓawa hankali da hikima, in dai har shi bazai iya bayar da ɗaya daga cikin ishirin da huɗu na dukiyar sa ba saboda taska ta har abada, wadda ake da tabbacin samunta da kashi casa’in da tara cikin ɗari. Sau da yawa hakan yakan kasance ya yi nisa da hankali! Yanzu ashe wanda yake ƙirga kansa a cikin masu hankali bazai iya gano wannan ba?

{ Sallah na da sauƙi ga kuma fa’ida ga mai tsaida ta }


41. Page

Bugu da ƙari, haƙiƙa sallah a cikin ta akwai hutu mai girma ga rai da zuciya da hankali, ƙari da cewa ita ba aiki ne mai nauyi ba ga jiki, da kyakkyawan niyya ce ayyukan na duniya na halal suke zama a hukuncin ibada ga wanda yake yin sallah, da haka ne mutum yake iya sanya jarin rayuwarsa gaba ɗaya[1]A matsayin amfani na lahira, ta wata fuska kuma ya sanya rayuwar sa wadda take ƙararriya ce, ta zama wanzajjiya.

 


[1] Wato gabaxayan rayuwarsa da lokacinsa da dukiyarsa.