KALMA TA SHIDA
NAVIGATION
48. Page
KALMA TA SHIDA
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِ
إِنَّ اللهَ اشْتَرَىٰ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ أَنْفُسَهُمْ وَأَمْوَٰلَهُمْ بِأَنَّ لَهُمُ الجَنَّةَ [1]
{Ciniki da Allah shi ne mafi riba}
Haƙiƙa sayar da kai da dukkan abin da aka mallaka ga Allah maɗaukaki, da bauta da sojantaka a gare shi babu kasuwancin da ya fishi riba da ɗaukaka da matsayi, Idan kana son kasan haka, yi sauraro i zuwa wannan hikayar da aka kawo ta a taƙaice:
{Hikayar wani sarki da ya bayar da amanar gona ga barorinsa biyu }
Watarana an yi wani sarki da ya bawa biyu daga talakawansa amanar gona, kowannen su aka danƙa masa a hannun sa shi kaɗai, a cikin ta akwai komai na aikatawa na daga kayan aiki dawakai da makamai, sai dai lokacin ya kasance lokacin yaƙi ne matsananci; domin haka ba abin da yake tabbata a wajen da yake, ko dai ya gushe ko kuma ya canju.
Hakika wannan sarkin ya aika i zuwa gare su- saboda cikar rahamarsa- manzo keɓantacce mai girman karamci daga manzaninsa, yakasance yana zantar musu da umarnin sarki wanda yake cike da rahma:
[1] Lalle ne Allah ya saya daga muminai rayukansu da dukiyoyinsu da cewa suna da Aljanna. Attauba aya ta 111.
49. Page
{Saƙonsa ga waɗannan barorin biyu}
Ku sayar min da amanata wadda take a hannunku, hardai na kiyaye muku ita, don kada ta tozarta ko ta lalace ta ɓalɓalce, zan dawo muku da ita bayan ƙarewar yaƙi a sura mafificiya, kuma kamar a matsayin wannan amana taku ce, sannan kuma zan danƙa muku dukiya mai yawa, duk waɗannan injinan da kayan aikin da suke cikin masana’antar za su yi aiki ne da sunana a cikin ma’aikatata, ladansu da ƙimarsu za su ɗaukaka daga ɗaya zuwa dubu, sannan in ba da dukkan ribar i zuwa gare ku, ku gajiyayyu ne talakawa, ba za ku iya tsayuwa da wahalolin waɗannan ayyukan masu girma ba, zan ɗauki dukkan wani nauyi da abin da suka lazimci aikin, kuma zan ba ku duk abin da yake shigowa da amfani mai yawa, sannan in tabbatar da ita a hannunku har lokacin sallama, sannan ga ribar ku ta nin-ninka har i zuwa mataki biyar.
Idan ba ku sayar min ba za ta gushe daga wajenku kamar yadda take gushewa daga wajen kowa kamar yadda yake bayyana a fili a gare ku babu wani mutum da yake iya kiyaye abin da yake hannunsa kuma za ta lalace ta ɓalɓalce, sannan kuma a haramta muku wannan ladan mai tsada waɗannan injinan da ma’aunai rantsasstsu masu ƙayatarwa, ingantattu, za su rasa dukkan kimar su, saboda rashin ma’adinai[1] da ayyukan da za a yi amfani da su, wahalar nan ta gudanarwa da ɗawainiya da tsaronta za su hau kanku, Kuma za a yi muku uƙuba irin uƙubar nan da ake yi wa wanda ya ci amanar da aka ba shi, shi kenan ya zama hasara mai ninninkawa har i zuwa mataki biyar! Amma sayar mini, yana nufin dangantuwa i zuwa gare ni a
[1]Arzikin da yake cikin ƙarƙashin ƙasa.
50. Page
matsayin soja na, da aiki da sunana, a maimakon ku zama marasa ‘yanci da ba su da tabbas ko waɗanda ba su da madogara ‘ya’yan hanya, gara ku zama makusantan sarki na musamman masu cikakken ‘yanci ga sarki mai girma.
{Sakamakon da kowanne ɗaya daga barorin nan ya samu}
Bayan sun saurari umarnin wannan sarki, wanda yake a cikinsa akwai girmamawa a gare su, mai hankali shiryayye daga cikinsu: sai ya ce ina mai bi sau da ƙafa, kuma na sayar ina mai dukkan alfahari, sannan kuma ina gabatar da dubun godiya.
Amma ɗaya ruɗaɗɗen mai girmankai mai irin zuciyar fir’auna mai son kai mai magagin maye, kai ka ce shi zai wanzu tutur har abada a cikin wannan gonar; sai ya ce: a halin yana marabkani ne daga ganin girgizawar nan ta duniya da hautsinawar nan tata a,a, wane irin sarki ne wannan? Ni ba zan sayar da abin da na mallaka ba. ba zan ɓata hutu na da nishadi na ba.
Bayan wani ɗan lokaci wannan mutumin na farko, sai ya ɗaukaka i zuwa wata martaba, wadda ta sanya mutane suka dinga burin dama a ce su ne shi, sai ya samu tabsasawan nan ta sarki, sai ya zama yana rayuwa a cikin jindaɗi a tabkeken keɓantaccen gidansa.
Amma ɗayan sai aka jarrabeshi da wani irin hali da ya sanya mutane sukeyi masa kaito suke koka masa, kuma a daidai wannan lokacin suke cewa: ya cancanci hakan; Jin-daɗinsa ya gushe ne, kuma mulkinsa ya tafi ne, sakamakon kuskurensa; don haka yake ɗanɗana azaba da uƙuba.
51. Page
{Haƙiƙar ma’anar hikayar}
Yāke rai mai yawan buri da son zuciya, yi duba i zuwa fuskar nan ta hakika, da irin madubin wannan misalin.
Amma wannan sarkin, shi ne ubangijinki,mahallicinki, wanda shi ne sarkin nan na tun-fil’azal da na har abada.
Amma waɗannan gonakin da injinan da kayan aiki da ma’aunai, su ne dukabin da kika mallaka a cikin kewayen rayuwarki, da kuma abin da kika mallake shi na daga jiki da rai da zuciya, da abin da yake cikin su na daga gaɓoɓin nan masu riskar abubuwa[1] na zahiri da na baɗini, kamar ido da harshe da hankali da ɗarshe-ɗarshen zuciya.
Amma wannanmanzon mai girma shi ne manzo mafi girma, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Amma wannan umarnin yankakke da ya zo daga wajen sarki, shi ne Alƙur’ani mai hikima;dominshi yake bayyana mana abin da muke tattaunawa a kansa na daga babban kasuwanci da ayar sa mai girma
إِنَّ اللهَ اشْتَرَىٰ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ أَنْفُسَهُمْ وَأَمْوَٰلَهُمْ بِأَنَّ لَهُمُ الجَنَّةَ[2]
[1]Kamar su ido, hanci, kunne, harshe da jiki.
[2] Lalle ne Allah ya saya daga muminai rayukansu da dukiyoyinsu da cewa suna da Aljanna Attaubah, aya ta 111.
52. Page
Amma wannan filin na yaƙi mai jujjuyawa da hautsinawa shi ne fuskar wannan duniya matsananciya; domin bata tabbata, bari dai tana jujjuyawa ne da canjawa tana gurɓata, kowanne mutum hankalinsa zai ɗarsa masawaɗannan tambayoyin masu zuwa:
Domin cewa hakika dukkan komai zai tsere daga hannunmu ya ƙare ya faku, ya jama’a; shin ba za a sami wata hanya ta wanzar da shi da dawwamar da shi.?
A yayin da yake wannan tambayoyi kuma yake tunani a kan hakan, sai katsahan ya ji amon Alƙur’ani daga sama yana cewa, na’am za a samu, hakika ita hanya ce tsarkakakkiya mai sauki mai riba har hawa biyar.
Tambaya: wace hanya ce wannan?
Amsa: sayar da amana ga ma’abocinta na hakika, a cikin wannan ciniki akwai ninke-ninken riba har sau biyar.
{Riba biyar na ciniki da Allah}
Riba ta farko: dukiyar nan ƙararriya za ta samu wanzuwa; domin wannan rayuwar mai gushewa idan aka ba da ita kuma aka sarrafata saboda tsayayye, wanzajje ma’abocin girmame-girmame; rayuwar za ta juya ta zama wanzajjiya, ta fitar da ‘ya’yan itatuwa wanzazzu, a sannan ne dukkanin daƙiƙoƙin rayuwa za su ƙare kamar ka ce su ƙwayar iri ne da ƙwallo waɗanda a zahiri suke lalacewa, amma a baɗini suna fitar da furennin farin ciki a duniyar nan ta wanzuwa. Kuma suke fitar da zangarniyoyi, sannan suke zama abin kallo masu haskakawa masu debe kewa a duniyar nan ta barzahu.
53. Page
Riba ta biyu: za’a ba shi lada kamar aljanna.
Riba ta uku: kimar kowacce gaba za ta ɗaukaka da gaɓoɓin riska abubuwa[1]daga ɗaya i zuwa dubu, misali;hankali ala ce wadda idan ka yi amfani da ita saboda kanka, ba ka sayar da ita ga Allah ba. A sannan ne sai ta zama ala mai shu’umanci mai takurawa gajiyayyiya, domin yana sarayowa i zuwa matsayin ala mai shu’umancimai cutarwa,wacce take ɗorawa kanka gajiyayye abin tausayi raɗaɗin baƙin cikin abin da ya wuce, da tsorace-tsoracen abin da yake gaba;domin haka sau da yawa fasikin mutum yana gudu i zuwa maye, ko i zuwa wasanni don ya kuɓuta daga damun nan na tunanin hankali da gajiyarwarsa,amma idan ka sayar da shi i zuwa mamallakinsa na haƙiƙa, ka yi amfani da shi saboda shi sai yazama mabuɗi ne, mai sirri[2] yana buɗe taskokin rahama da bata da ƙarshe kamar yadda yake buɗe taskokin nan na hikima da bata da iyaka a cikin wannan duniya, kuma yanaɗaukaka i zuwa matsayin mai shiryarwa, bawan Allah na haƙiƙa, da yake tanadarwa ma’abocinsa rayuwar farin ciki ta har abada.
Gaɓar gani kamar ido gaɓa ce wadda rai yake ganin wannan duniya ta hanyarta, idan ka yi amfani da ita saboda kanka, ba ka sayar da ita ga Allah maɗaukaki ba, to ita da abubuwan da ta ke gani kyawawa, da wasu ababan kallo da ta ke gani na ɗan
[1] Kamar ji, gani, shafa, sheqa da xanxano.
[2] Kamar na karama.
54. Page
lokaci waɗanda ba sa dawwama, sai ta wayi gari tana ‘yar aiki maƙasƙanciya tana kawalci[1] ga sha’awa da son zuciya, amma da dai cewa za ka sayar da ido ga wanda ya yi idon, mai gani na haƙiƙa, kuma ka yi amfani da shi a tafarkin shi, a ƙarƙashin kewayen izininsa; a lokacin ne wannan idon zai hauhawa i zuwa matsayin maikarantawa ga wannan babban littafin na kasantattu[2] da mai ganin mu’ujizozi na halittar ubangijantakaa wannan duniya, da ƙudan zuma mai albarka da yake tsotso ruwan zumansa, daga furan nin nan na rahma a cikin lanbu nan na ƙwallon duniya.[3]
Misali na uku: idan ba ka sayar da ƙarfin ɗanɗanon nan na harshe, ga maƙaginsa mai hikima wanda ya ƙageshi ba, ka yi amfani da shidan kanka, saboda buƙatar uwar hanji, sai ya sarayo i zuwa matsayin mai kula da ƙofar ma’aikatar uwar hanji da wajen ɗaure dawakin ta, sai dai cewa kai idan ka sayar da shi ga mai arzurtawa mai karamci, sai karfin nan na ɗanɗanon harshe ya hauhawa i zuwa darajan nan ta ƙwararren mai duba i zuwa taskokin rahmar Allahntaka da mai kula mai bincike mai godiya a bisa madafar nan ta mai iko, abin nufi da buƙata.
Yākai hankali; ka faɗaka,ina ƙimar ālan nan maƙasƙanciya shu’uma, daga darajar nan ta mabuɗin nan na kasantattu.
Yākai ido; ka kyautata gani, ina ƙasƙanci darajar kawali daga darajar mai nazari ma’abocin fannoni a matattarar littattafan nan ta Allahntaka.
Ya kai wannan harshe; ka kyautata ɗanɗano ina ƙasƙanci darajar mai gadin wajen ɗaure dawaki, da mai gadin ƙofar masana’anta, daga darajar nan ta mai kula da taskoki keɓantattu na rahma.
[1]Mai haxa alfasha a tsakanin mutane kamar zina.
[2] Dukkan halitta.
[3]Wannan jumlar an yi tashbihi ne da ido.
55. Page
Idan ka ƙiyasta ragowar gaɓoɓin da sauran gaɓoɓi masu riskar abubuwa a bisa wannan misalin, cewa kai za ka fahimci mumini yana samu a haƙiƙa kamannin da suke dacewa da aljanna, shi ma kafiri yana samu a hakika kamannin da suke dacewa da jahannama; haƙiƙa dalilin samun kowanne daga cikin su waccan ƙimar, shi ne amfani mumini ta hanyar imaninsa, amanar mahaliccinsa da sunansa maɗaukakin sarki, a cikin iyakar izinin sa, da kuma amfanin kafiri ta hanyar kafircinsa amanar mahaliccinsa da sunan zuciyar nan tasa mai yawan umarni da munmunar aiki.
Riba ta huɗu: hakika mutum rarrauna ne bala’o’insa masu yawa ne, kuma matalauci ne mai yawan buƙatu ne, kuma gajiyayya ne, sannan kuma wahalhalun rayuwarsa masu nauyi ne sosai, idan bai jingina i zuwa ga mai iko ma’abocin girmame-girmame ba, bai dogara a gare shi ba, bai miƙa wuya a gare shi ba, sai zuciyarsa tawanzu a cikin azaba madawwamiya,wahalhalu, raɗaɗe-raɗaɗe, nadamomi da baƙƙan ciki, za su lulluɓeshi, ba tare da fa’ida ko riba ba; sai su mai da shi mai maye da tanɓele ko dabbar dāji abar farauta ɗimautacciya.
Riba ta biyar: hakika ma’abota ɗanɗanon zaƙin sanin Allah, da waɗanda aka yayewa sanin wasu ɓoyayyun asirai na Allah,sun yi ittifaƙi da wasu ma’abota ƙwarewa a
56. Page
sanin Allah da masu gani, a bisa cewa, ibadar waɗannan gaɓɓai da gaɓoɓin sassa da tasbihohinsu da ƙimominsu masu tsada, da sannu za a ba ka su a cikin sura ta amfanin aljanna, a cikin lokacin da kake mutuƙar matsananciyar buƙata i zuwa gare su.
{Asarori biyar na rashin yin ciniki da Allah}
Idan ba ka yi wannan kasuwancin mai riba a matakansa biyar ba, to za ka sarayo ƙasa i zuwa matakansa biyar na hasara, ƙarin daɗawa kuma za a haramta ma dukkan waɗancan ribobin.
Asara ta farko: abin da kake so na daga dukiya da ‘ya’ya so na fitar hankali da sannu za su tozarta su gushe, kuma abin da kake son sa na daga kanka da son zuciya son da ya kai matakin bauta da abin da ka fitinantu da sonshi na daga ƙuruciya da rayuwa, dukkan wannan zai gushe daga gare ka, tare da cewa zai barka da zunubansa da raɗaɗe-raɗaɗensa, kuma ya ɗora ma su a kafaɗunka.
Asara ta biyu: sannan za ka gamu da narkoncin amana; domin cewa kai ka zalinci kanka, saboda amfani da gaɓoɓinka, da gaɓoɓin nan masu riskar abubuwa, masu tsada a cikin mafi wulaƙanci al’amura da mafi komabayansu.
Asara ta uku: ka yi ƙire a bisa hikimar nan ta Allahntaka ka zalunceta ta hanyar saryarwarka dukkan waɗannan gaɓoɓi da gaɓoɓin sassa na mutuntaka masu daraja, i zuwa mafi ƙasƙancin mataki fiye da matakin dabbantaka.
57. Page
Asara ta huɗu: za ka yi ihu da kururuwa koyaushe,ƙarƙashin buguwar nan ta gushewa da rabuwa, sanadiyarɗorawa kanka nauyayenauyayen nan na rayuwa tare gajiyawarka da buƙatuwarka.
Asara ta biyar: canja kyaututtukan nan na mai jin ƙai; kamar hankali,zuciya,ido da harshe, waɗannan kyaututtuka da aka ba ka su, domin ka samu ginshiƙan rayuwar ta har abada, da abin da suka lazimci arzikin lahira, da juyar da su i zuwa munanan surori, da suke buɗe maka ƙofar jahannama.
Yanzu sai mu yi duba i zuwa cinikayyar. Yā jama’a shin tana da nauyi ne da wahala i zuwa matakin da har mutane da yawa suke gujewa wannan cinikayya? bahaka bane, bata da nauyi bata da wata wahala ko kaɗan; domin cewa hakika kewayen nan na halal yalwataccene ya isa hutuda gamsar da buƙatu, babu wata buƙatar faɗawa cikin haram.
Abubuwan da Allah S.W.T ya farlanta, masu sauƙi ne kuma kaɗan ne, sannan kuma sojantaka da bauta ga Allah ɗaukaka ce ma’abociya daɗi, wanda bazai kwatantuba.
Amma aiki kuwa, yakamata idan mutum zai yi aiki ya fara da sunan Allah a matsayinsa na sojansa, kawai. Ya bayar ya karɓa saboda Allah, motsinsa da kawaicinsa suka kasance a cikin iyakoki da dokokin Allah, ya nemi gafara idan ya yi kuskure, ya ƙasƙantar da kai i zuwa gare shi; yana mai cewa: ya ubangiji ka yi afuwa ga taƙaitawarmu, ka karɓemu a matsayin bayi a gare ka, ka sanyamu mu zama amintattu a bisa amanarka har i zuwa lokacin karɓarta.
رب يا اعف عن تقصيرنا واقبلنا عبادا لك و اجعلنا أمناء على أمانتك إلى وقت قبضها
أمين


