KALMA TA TAKWAS
NAVIGATION
67. Page
KALMA TA TAKWAS
بسم الله الرحمن الرحيم
Muna farawa da sunan Allah mai Rahma mai Jin-ƙai
ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُ
[2] إِنَّ ٱلدِّينَعِندَ ٱللَّهِ ٱلۡإِسۡلَٰمُۗ
{Haƙiƙar addini da ƙimarsa ga mutum}
Idan kana so kafihimci haƙiƙar wannan duniyar, da abin da yake cikinta na daga rai na ɗan’adam, da haƙiƙa addini da ƙimarsa awajen mutum, kuma ba da ban Addiningaskiya ba; da duniya ta zama kurkuku, kuma mutun mai inkari mai musun samuwar Allah, shi ne mafi taɓewar ababan halitta, da kuma cewa:
يا اللهda لاإله إلا هو ya allah da la’ ilaha’ illallah,suna yaye kuma suna warware sirrin wannan duniyar, kuma suna tsamo rayuwar ɗan’adam daga cikin duffai[3]; idan kana so kafahimci haka ,to yi duba i zuwa wannan hikayar da ta bamu misali a taƙaice, ka yi sauraro i zuwa gare ta:
{Hikayar wasu ‘yanuwa matafiya guda biyu}
A zamanin da, wasu ‘yan’uwa biyu shaƙiƙai sun fita tare, saboda yawon shaƙatawa mai tsawo, suna tafiya kaɗan-kaɗan har suka kai inda hanya ta rabu biyu, sai suka ga wani nutsattsen mutun mai kwarjini, sai suka tambaye shi: wadda hanyar ce tafi.?
Sai ya ce da su: hanyar dama dai, a cikinta ya zama tilas Abi dokoki da tsari, sai dai cewa a cikin ɗaukar wannan nauyin, akwai aminci akwai arziki, amma hanyar hagu a kwai ‘yanci da kuɓuta daga nauyaye-nauyaye, sai dai a cikin wannan ‘yancin akwai haɗari da tsiya, yanzu dai zaɓi ya rage a gare ku.
[1]سورة أل عمران2
[2]سورة أل عمران:19
68. Page
Bayan sun ji haka, wanda yake mai nagarta mai kyawawan halaye, sai ya bi hanyar dama yana me cewa: na dogara ga Allah, na yarda da bin tsarin da kuma lazamtawa kaina shi, amma ɗaya ɗan’uwan mai munanan halaye taƙadari, sai ya fifita hanyar hagu kawai don ‘yanci da ke cikinta.
{Halin mabiyin hanyar hagu}
Bari, mubi wannan mutumin -a cikin zuciya- wanda shi yana tafiya a cikin sauƙi a zahiri, sai dai amma akwai nauyi a cikin haƙiƙanin al’amarinsa[1], sai ya cigaba da tafiya ya bi gangare-yabi tudu har sai ga shi a cikin saharar daba komai a cikinta.
Katsahan sai ya ji wani sauti mai tsoratarwa, yana dubawa sai ya ga wani zaki mafaɗaci ya fito daga daji zai kai hari a gare shi, sai ya yi ƙoƙarin ya gudu, har dai ya zo ya tarar da wata ƙafaffiyar rijiya, zurfinta zira’i sittin ne, saboda tsoronsa sai ya afka cikinta, sai hannayensa suka yi karo da bishiya a tsakiyar rijiyar sai ya riƙeta, wannan bishiyar da ta fito ajikin bangon rijiyar, tana da wasu jijiyoyi guda biyu da suke riƙe da ita, wanda aka sallaɗa wasu ɓeraye guda biyu suna ƙoƙarin sai sun
[1] Wato abin dayake baɗinsa.
69. Page
gutsire waɗannan jijiyoyin, ɗaya daga cikin ɓerayen, farine ɗayan kuwa baƙine, sai mutumin da yake riƙe da bishiyar nan, ya dubi sama sai ya ga zakin nan mai ban tsoro yana sauraro a bakin gefen rijiyar kamar mai gadi, sai ya yi duba i zuwa ƙasa sai ya ga kububuwa mai tsoratarwa ta ɗaga kanta ta kusanto i zuwa ƙafafuwansa guda biyu da suka kasance a bisa nisan zira’i talatin daga kububuwar, faɗin bakinta ya yalwaci faɗin rijiyar, kuma ya yi duba i zuwa bangon rijiyar sai ya ga ƙwaruka masu cutarwa masu harbi sun kewaye shi, kuma ya yi duba i zuwa saman bishiyar, sai ya ga ashe bishiyar ɓaure ce, sai dai cewa – ba irin wadda ya saba gani ba ce- tana ɗauke da ‘ya’yan itatuwan bishiyoyi mabambanta masu yawa farawa daga dabino da kwakwa tiƙewa da runman.
Duk da haka wannan mutumin saboda munmunar fahimtarsa da wautarsa, bai fahimci cewa wannan al’amari ba al’amari ne irin na al’ada ba[1], bazai yiyu wannan al’amarin ya faru katsahan ba, a cikin wannan al’amura masu ban mamaki akwai sirruka waɗanda ba a sansu ba, hakanan ma bai fahimci cewa akwai mai jujjuyawa mai girma ƙwarai,wanda yake jujjuya waɗannan al’amura ba, kuma yanzu duk da cewa rai da zuciya da hankali na wannan mutumin suna kururuwa da wayyo Allah a sirrance saboda, da wannan yanayin mai raɗaɗi; sai dai zuciyarsa mai umarni da munanan ayyuka, ta fara cin ‘ya’yan itatuwan wannan bishiyar kamar kai ka ce tana cikin wani lanbu ne, tana mai jahiltar abun da yake kewaye da ita-kamar wani abu bai kasance ba-tana mai toshe kunnuwanta ga jin kukan nan na rai da na zuciya, tana mai yaudarar kanta da kanta, tare da cewa wani ɓangare na waɗancan ‘ya’yan itatuwa masu guba ne,masu cutarwa.
[1] Wato abune na musamman da za a yi izina da shi.
70. Page
Ya zo a cikin hadisi ƙudusi, Allah mai girma da ɗaukaka ya ce:أنا عند ظن عبدي بي[1] ai Ni ina mu’amala da bawa na a yadda ya sanni, yake sa rai dani, hakanan ma, wannan mutumin -mara arziki tare da munmunar zatonsa da wautarsa- ya yi zaton abin da ya gani cewa al’amari ne da aka saba da shi, abin nan da ya gani shi ne ainihin gaskiya, sai aka mu’amalance shi da shi, kuma ana mu’amalantarsa, kuma da sannu za a mu’amalance shi da shi, kamar yadda yake zato, shi bai mutu ba balle ya kuɓuta daga abin da yake ciki, kuma bai rayu ba balle ya ji daɗin rayuwarsa, hakanan yake ta jujjuyawa a cikin azaba.
{Halin mabiyin hanyar dama}
To mu bar wannan shu’umin a cikin azabarsa, mu tafi mu ga halin ɗaya ɗan’uwan.
Wannan mutumin mai albarka mai hankali, sai ya ci gaba da tafiyarsa sai dai shi ba ya shan wahala kamar ɗan’uwansa; domin shi ma’abocin kyawawan ɗabi’u ne, yana tunani a kan kyawawan abubuwa, yana rayuwa da kyakkyawan zato da kyawawan burace-burace, yana ɗaukewa kansa da kansa kewa, ba ya shan wahala da ƙunci kamar ɗan’uwansa; domin cewa shi ya san tsari yana iƙirari da shi, kuma yana binsa;
[1])Ni ina nan inda bawana ya zace ni(
71. Page
domin haka sai ya samu sauƙi, ya na tafiya a matsayin ɗa mai ‘yanci, a cikin aminci da amana, hakanan ya ci gaba da tafiya har ya sadu da wata gona, a cikinta akwai furanni da ‘ya’yan itatuwa kyawawa masu tabshi[1], ƙari a kan haka a cikinta ma akwai abubuwa masu najasa munana; saboda rashin kula da ita, kulawa cikakkiya, kuma yakasance ɗan’uwansa haƙiƙa ya shiga wannan gonar tun kafin shi, sai dai cewa shi ya sa ido a kan abubuwan najasa munana kawai, sai ya shagalta da su, sai ya gurɓata cikinsa, Sai ya tashi ya fita ba tare da ya huta ko kaɗan ba, amma wannan mutumin mai kyakkyawar ɗabi’a, haƙiƙa shi ko sau ɗaya bai kalli waɗannan abubuwan masu najasa munanaba, saboda lurarsa da bin ƙa’ida:
انظر إلى الأحسن من كل شيء
Ka yi duba i zuwa abin da ya fi daga komai ɗan’uwa bari ma dai ka ji, sai ya fa’idantu da abubuwa kyawawa, fa’idantuwa mai kyau, ya huta, hutu cikakke, sai ya fita ya shuɗe a cikin tafarkinsa.
Sannan ya ci gaba da tafiya, kaɗan-kaɗan hardai ya shiga wata sahara mai girmakamar dai ɗan’uwansa.
[1] Masu daɗin kallo.
72. Page
Katsahan sai ya ji ƙugin zaki, zai kai masa hari sai ya ji tsoro, sai dai cewa shi bai ji tsoro kamar yadda ɗan’uwansa ya ji tsoro ba; domin shi ya samu haƙurƙurtarwa – da ya sauƙaƙa masa tsoron - saboda falalar nan ta kyakkyawan zatonsa da kyakkyawan tunaninsa, na ganin cewa haƙiƙa wannan sahara tana da sarki, tana iya yiyuwar wannan zaki mai bauta ne a ƙarƙashin umarnin wancan sarkin, sai dai cewa shi tare da haka ya fita da gudu har ya tarar da wata ƙafaffiya rijiya babu ruwa a cikinta, zurfinta zira’i sittin ne, sai ya jefa kansa cikinta, kamar dai ɗan’uwansa sai hannayensa suka kama wata bishiya da take a tsakiyar rijiyar, sai ya kasance a maƙale da ita, sai ga wasu dabbobi biyu suna ƙoƙarin gutsire jijiyoyin wannan bishiyar, sai ya dubi sama sai ya ga zaki, sai ya kalli ƙasa sai ya ga kububuwa, kamar dai ɗan’uwansa - kwabo da kwabo - ya ga abin mamaki, sai tsoro tare da mamaki suka lulluɓe shi sai dai cewa tsoronsa ya kasance mafi ƙaranci a kan tsoron ɗan’uwansa da – gwargwadon – daraja dubu; domin cewa kyawawan ɗabi’unsa sun sa masa tunani mai kyau, tunanin nan mai kyau, shi yake nuna masa kyawawan fuskoki daga dukkan komai.
Domin wannan sababin; ya yi tunanin cewa, waɗannan al’amura masu ban mamaki, shashinsu a haɗe yake da sashi, yana bayyana cewa suna gudana ne da umarni ɗaya, kenan a cikin waɗannan al’amura akwai wani sirri.
{Fahimtarsa ga abubuwan da suke faruwa}
Na’am, waɗannan al’amura suna gudana da umarnin sarki wanda yake a fake[1], kenan ni bani kaɗai nake ba, wannan sarkin da yake a fake yana ganina, yana bin diddigi na yana jarrabani, yana kira na, ya tura ni i zuwa wata jiha saboda wata manufa, sai son tsinkaye a kan abin da yake gudana ya taso masa, daga wannan tsoro
[1] Sh ine Allah (s.w.t.)
73. Page
mai daɗi da tunani mai kyau, kuma shi ne: yā jama’a wanene yake jarrabani yake so ya sanar dani kansa, yake tura ni i zuwa wata manufa keɓantacciya, ta irin wannan hanya mai ban mamaki.? Sannan sai son ma’abocin sirrin ya taso, saboda son tsinkayen wannan, sannan wannan soyayyar sai ta girma, saboda kwaɗayin yaye wannan sirrin, sannan wannan kwaɗayin sai ya haifar da riƙon wani hali mai kyau, wanda zai yardar da ma’abocin wannan sirrin kuma ya ƙayatadda shi.
Sannan sai ya yi duba i zuwa saman bishiyar, sai ya ga ashe ita bishiyar ɓaure ce, sai dai ita tana ɗauke da ‘ya’yan itatuwa na bishiyoyi dubunnai akanta, a san nan ne tsoronsa ya tafi ya gushe gabaɗaya; domin cewa shi ya sakankance, haƙiƙa ba makawa cewa wannan bishiyar ɓauren da take tsaye fihirasa ce da wajen baje koline, kuma wannan sarkin na fake ya rataya mata wani sirri da mu’ujizar samfura na ‘ya’yan itatuwa waɗanda suke a aljannarsa da gonakinsa a bisa waccan bishiyar, kuma yana bayyana cewa shi ne ya ƙawata waccan bishiyar , domin nuni ga abin da ya tanada na daga abubuwan ci don baƙinsa, idan ba don haka ba, da bishiya guda ɗaya, da ba za ta fitar da ‘ya’yan itatuwa kala daban-daban ba, na bishiyoyi dubu, Sannan sai ya fara ahi da ƙasƙantar da kai, har aka yi masa ilhamar mabuɗin sirrin, sai ya yi ƙara[1] yana mai cewa:
Ya mai mulkin wannan ƙassan na ƙwanƙwasa ƙofarka, na shiga cikin kariyarka, ni bawanka ne ina neman yardarka, ina binciken inda zan sameka, ina neman ka.
Bayan wannan ahi da addu’ar da ya yi mai –cike- da ƙasƙantar da kai, sai bangon rijiyar katsahan ya tsage, sai ƙofa ta buɗe i zuwa wani lambu mai kyau, mai ƙayatarwa, wanda babu gurɓatattun abubuwa a cikinsa,wannan bakin kububuwar ne ya juye ya koma wannan ƙofar, wannan zakin da dai wannan kububuwar sai suka juye suka koma barori guda biyu, suke kiransa da ya shiga, har dai wannan zakin ya juye ya koma doki horarre gare shi.
[1] Ya ɗaga murya saboda shauƙi.
74. Page
{Kyakkyawan sakamako yana zuwa daga kyakkyawan aiki hakanan mummuna shi ma yana zuwa daga munmunan aiki }
Ya ke zuciyata mai yawan kasala, yā abokina a cikin zancen nan na zuci! Ku Zo mu auna a tsakanin halayen ‘yan’uwan nan biyu, don mugani kuma mu sani, cewa ta yaya kyakkyawan aiki yake zuwa da kyakkyawan sakamako, kuma munmunan aiki yake zuwa da munmunan sakamako.
Ku yi duba ta yaya cewa mara arziki wanda ya bi hanyar nan ta hagu, yake sauraron shiga cikin bakin macijiyar nan a kowacce ƙibtawar ido, shi yana makyarkyata, yayin da wannan mai arzikin, shi ana kiransa i zuwa wata gona ƙayatacciya mai kyau, wadda aka rayata da ‘ya’yan itatuwa.
Kuma ta yaya wannan mara arzikin zuciyarsa take nuƙurƙusuwa a cikin tsoro mai girma da mamaki mai raɗaɗi, a yayin da wannan mai sa’ar yake ganin abubuwan mamaki, da izinamai daɗi da tsoro mai tabshi da sani abin ƙauna.
75. Page
Kuma ta yaya wannan mara arzikin yake azabtar da kansa da kaɗaici, da ɗebe ƙauna da kaɗaitaka, a yayin da mai sa’ar yake jin-daɗi da ɗauke masa kewa, da buri da bege.
Kuma ta yaya wannan mara arziki yake ganin kansa kamar shi tsararre ne, wanda aka bijirar da shi ga abkawar nan ta miyagun dabbobin daji, a yayin da mai sa’a ya kasance baƙo mai girma, yake farin ciki yake jin-daɗi yake ɗebe kewa da masu hidimar nan ta ban-mamaki na mai karɓar baƙi mai karamci, wannda ya sauka a wajensa.
Kuma ta yaya wannan mara arzikin yake gaggautawa kansa azaba ta hanyar cinsa ‘ya’yan itatuwa masu daɗi a zahirinsu amma masu guba a haƙiƙaninsu, domin waɗannan ‘ya’yan itatuwa ba komai ba ne su sai dai samfura ne da ake bawa mutum dama ya ɗanɗanesu; domin ya nemi asalansu da maɓuɓɓugarsu, don ya zama abokin ciniki a gare su, ba a ba shi damar haɗiye su ba kamar dabba,amma wannan mutumin arzikin, sai ya ɗanɗana ‘ya’yan itatuwa sai ya gane haƙiƙaninsu, sai ya jinkirta cinsu, sai yake jin-daɗi da jinkirin nasa.
76. Page
Kuma ta yaya wannan mara arzikin saboda rashin basirarsa, haƙiƙa ya zalinci kansa da kansa, ya juyad da haƙiƙa mabayyaniya a fili kamar rana, da halinnan mai haskakawa i zuwa sura ta wahame-wahame da jahannama mai tsananin duhu, shi bai cancanci aji tausayinsa ba kuma ba shi da haƙƙin kai ƙara i zuwa wani.
Misali: idan mutum bai gamsu da jin-daɗin nan na garar baƙi ba mai girma a cikin kyakkyawar gona a tsakankanin masoyansa a lokacin kaka, ya marisantar da kansa da munanan kayan maye, sai ransa take riya masa cewa yana tsakiyar lokacin ɗari a tsakankanin miyagun namun daji, kuma yana tsirara mai jin yunwa, sai ya fara kururuwa yana kuka, to shi ba ya cancanta da aji tausayinsa, shi ne ya cuci kansa da kansa, a inda ya ga masoyansa a matsayin miyagun namun daji, sai ya wulaƙantar da su. Misalin wannan mutumin mara sa’a, kamar misalin wannan mutumin ne, amma mutumin arziki sai ya ga gaskiyar, ita gaskiya a ainihinta abuce mai kyau,kuma fahintarsa mai kyau ga gaskiya ita ke sa ya girmama cikar nan ta ma’abocin gaskiya, a saboda haka sai yake cancantar jin-ƙansa. a nan ne sirrin Alƙur’ani yake bayyana, a inda yake cewa:
مَّآ أَصَابَكَ مِنۡ حَسَنَةٖ فَمِنَ ٱللَّهِۖ وَمَآ أَصَابَكَ مِن سَيِّئَة فَمِن نَّفۡسِكَ
[1]
.
Idan ka auna tsakanin mutanen nan biyu, kana mai lura da dukkan wannan banbance-banbancen da wasunsu, da sannu za ka fahimci haƙiƙa zuciyar nan mai yawan umarni da miyagun laifuka ta mutumin nan na farko, ita ce ta shirya masa jahannama ta ma’ana kuma ta gabato masa da ita, a yayin da kyakkyawan zaton ɗaya mutumin da kyakkyawar niyarsa da kyawawan ɗabi’unsa da kyakkyawan tunaninsa, dukkan waɗannan haƙiƙa sun sanya shi ya na rabauta da alheri babba da arziki mai girma da falaloli masu haske da suke kwarara a wajensa.
1النساء 79(Wato, abin da ya same ka na daga alheri, to, daga Allah yake, kuma abin da ya same ka na daga sharri, to,daga gare ka yake)
77. Page
{Haƙiƙar ma’anar hikayar}
Ya ke zuciya, tare da kai mai sauraro i zuwa wannan hikayar, idan kun yi nufi kada ku zamo kamar ɗan’uwa mara arziki, ku ka nufaci zama kamar ɗan’uwa mai arziki to, ku yi sauraro i zuwa Alƙur’ani mai girma, kubi hukuncinsa, ku yi riƙo da shi, ku yi aiki da hukunce-hukuncensa.
Idan kun fahimci haƙiƙoƙi waɗanda suka zo a cikin wannan hikayar da aka bayar a cikin waɗannan misalan, haƙiƙa cewa ku za ku iya ɗabbaƙawa a kanta, haƙiƙar nan ta addini da ta duniya da ta mutuntaka da kuma ta imani, ni da sannu zan ambata muku mafi muhimmancinsu, ku kuma sai ku fitar da ragowar da kanku.
Amma waɗannan ‘yan’uwan guda biyu, ɗayansu, raine na mumini da zuciyar mutun na gari. ɗayan kuwa raine na kafiri da zuciyar nan ta fasiƙi.
Amma hanyoyin nan guda biyu:
Hanyar nan ta dama daga cikinsu ita ce hanyar Alƙur’ani da imani,amma hanyar hagu ita ce hanyar saɓo da kafirci. Amma wannan gonar da ta kasance a waccan hanyar: ita ce rayuwar al’umma ta wucin gadi ga al’ummar nan ta ‘ya’yan’dam da ci gabansu, domin a cikinta akwai alheri da sharri, da kyau da muni, da tsarki da dauɗa na daga kowanne al’amura a tare, to mai hankali, shi ne wanda yake aiki da ƙa’idar;[1] خذ ما صفا ودع ما كدرsai ya wuce da amincin nan na zuciya.
Amma wannan saharar, ita ce doron ƙasar da wannan duniyar.
[1]ka riƙi abin da ya tsarkaka, ka bar abin da ya gurɓata
78. Page
{Haƙiƙar ma’anar hikayar}
Ya ke zuciya, tare da kai mai sauraro i zuwa wannan hikayar, idan kun yi nufi kada ku zamo kamar ɗan’uwa mara arziki, ku ka nufaci zama kamar ɗan’uwa mai arziki to, ku yi sauraro i zuwa Alƙur’ani mai girma, kubi hukuncinsa, ku yi riƙo da shi, ku yi aiki da hukunce-hukuncensa.
Idan kun fahimci haƙiƙoƙi waɗanda suka zo a cikin wannan hikayar da aka bayar a cikin waɗannan misalan, haƙiƙa cewa ku za ku iya ɗabbaƙawa a kanta, haƙiƙar nan ta addini da ta duniya da ta mutuntaka da kuma ta imani, ni da sannu zan ambata muku mafi muhimmancinsu, ku kuma sai ku fitar da ragowar da kanku.
Amma waɗannan ‘yan’uwan guda biyu, ɗayansu, raine na mumini da zuciyar mutun na gari. ɗayan kuwa raine na kafiri da zuciyar nan ta fasiƙi.
Amma hanyoyin nan guda biyu:
Hanyar nan ta dama daga cikinsu ita ce hanyar Alƙur’ani da imani,amma hanyar hagu ita ce hanyar saɓo da kafirci. Amma wannan gonar da ta kasance a waccan hanyar: ita ce rayuwar al’umma ta wucin gadi ga al’ummar nan ta ‘ya’yan’dam da ci gabansu, domin a cikinta akwai alheri da sharri, da kyau da muni, da tsarki da dauɗa na daga kowanne al’amura a tare, to mai hankali, shi ne wanda yake aiki da ƙa’idar;[1] خذ ما صفا ودع ما كدرsai ya wuce da amincin nan na zuciya.
Amma wannan saharar, ita ce doron ƙasar da wannan duniyar.
[1]ka riƙi abin da ya tsarkaka, ka bar abin da ya gurɓata
79. Page
Amma zaki kuwa, shi ne mutuwa da ajali.
Amma wannan rijiyar, ita ce jikin mutum da lokacin rayuwa
Amma wannan zurfinda ya kai zira’i sittin shi, ishara ne i zuwa shekaru sittin, wadda ita ce matsakaiciyar rayuwar mutum.
Amma wannan bishiyar, ita ce shekaru gaba ɗaya, da tsawon rayuwa gaba ɗaya.
Amma waɗannan dabbobin biyu, baƙi da fari, su ne dare da rana
Amma wannan kububuwar, ita ce hanyar kabari da farfajiyar nan ta lahira, wanda kabari shi ne amatsayin bakin ta; sai dai wannan bakin, shi a wajen mumini ƙofa ce da take buɗewa daga kurkuku i zuwa dausayi[1].
Amma waɗannan ƙwarukan masu cutarwa su ne musibun duniya, sai dai su ga mumini suna matsayin faɗakarwa mai daɗi ta ubangiji, da karramawa da ni’imtawa ta mai jin-ƙai;domin mutun kada ya nutse a cikin barchin nan na gafala.
Amma waɗannan ‘ya’yan itatuwan da suke a kan bishiyar, su ni’imomi ne na duniya, da mai karamci na saki ba ƙaidi ya sanya su a matsayin samfurata ni’imomin lahira, kuma ya sanyasu masu kamanni da ta lahirar, don su ɗanɗana mana ɗan kaɗan daga ɗanɗanonsu a nan duniya, Kuma ya sanyata a cikin surar samfura da suke kiran abokan ciniki i zuwa ’ya’yan itatuwan aljanna.
Amma fitowar ‘ya’yan itatuwa, nau’o’i mabambanta a jikin wannan bishiyar duk da cewa bishiya ce guda ɗaya, wannan ishara ce i zuwa hatimin iko, na abin nufi da
[1] Daga kurkukun duniya i zuwa dauayin aljanna.
80. Page
buƙata, da tambarin nan na ubangijintaka,da hatimin nan na sarki maɗayanci,da cewar haƙiƙa[1]خلق كل شيء من شيء واحد; ai an halicci dukkan tsirrai ne da ‘ya’yan itatuwa daga ƙasa ɗaya, an halicci dukkan dabbobi daga ruwa ɗaya, tare da samar da dukkan gaɓoɓin dabbobin, daga abinci ɗaya sassauƙa, tare da haka[2]جعل كل شيءشيئا واحد; ai ya yi nama na musamman ya sa masa fata sassauƙa, ga ma’abota rayuwa daga abubuwan ci mabambantan jinsuka, waɗanda yake cinsu,domin cewa shi-ai misalin waɗannan abubuwan ƙira ƙayatattu-sitamfi ne na musamman ga sarkin nan na tuntuni na har abada, wanda shi ne zati tilo, abin nufi da buƙata,da hatimin nan nasa na musamman,da tambarin nan nasa waɗanda bazai yiwu ba a kwaikwayi irinsu.
Hakayake, haƙiƙa sanya abu ɗaya ya zama komai, da sanya komai ya zama abu ɗaya, wannan wata alama ce da aya keɓantacciya abar keɓanta ga mahallicin komai mai iko a bisa komai.
Amma wancan sirrin, shi ne sirrin hikimar halitta,wannan da ake yayewa da warwarewa da sirrin nan na imani.
Amma wannan mabuɗin shi ne; [3]الله لا إله إلا هو الحي القيوم *لا إله إلا الله * يا ألله
Amma juyawar bakin kububuwar nan i zuwa ƙofar dausayi, yana nunarwa i zuwa haƙiƙar kabari, tare da cewa shi ga ma’abota ɓata waje ne na matsi mai firgitarwa, kamar kurkuku da za su zama cikin kaɗaitaka ababan mantawa.
Kuma ƙofa ce da take buɗewa i zuwa rami ƙuntatacce, kamar cikin nan na kububuwa, shi (kabari} ga ma’abota Alƙur’ani da imani, ƙofa ce da take buɗewa daga kurkukun duniya i zuwa gonar nan ta wanzuwa, kuma daga farfajiyar nan ta jarrabawa i zuwa dausayoyin nan na Aljanna, daga wahalar nan ta rayuwa i zuwa jin-ƙan nan na mai rahma.
[1]ya halicci kowanne abu ne daga abu ɗaya
[2]ya sanya komai ya zama abu ɗaya
[3]ya Allah* ba abin bautawa da gaskiya sai Allah*Allah, babu wani ubangiji sai shi, rayayye ne
81. Page
{Ma’anar Mutuwa a mahangar ta Alƙur’ani da mahanga ta ɓata}
Amma juyawar zakin nan ɗimautacce, i zuwa bawa mai ɗebe kewa, da juyawarsa i zuwa doki horarre[1], wannan yana nuni i zuwa cewa haƙiƙa mutuwa, tare da cewa ita ga ma’abota ɓata, rabuwa ce ta har abada mai raɗaɗi ga duk masoyansu, da fitowa daga Aljannarsu ta duniya mai fizga, da shiga da tsare su a cikin kurkukun nan na kabari, tare da ɗimuwa da kaɗaitaka da zama waje ɗaya, ita kuma mutuwa ga ma’abota shiriya da ma’abota Alƙur’ani hanya ce don saduwa da masoyansu na da can, waɗannan da suka ƙaura i zuwa lahira, kuma tsani ce don shiga garinsu na haƙiƙa da bigiren arzikinsu na har abada, kuma kira ne daga kurkukun nan na duniya i zuwa gonakin nan na Aljanna, kuma sauraro ne don karɓar
[1] Wanda ake sarrafa yadda ake so.
82. Page
lada daga falalan nan ta mai jin-ƙai sakamakon hidimominsu, sallamace daga ayyukan rayuwa, kaiwa ƙarshe ne na karɓar horo na bauta da jarrabawa.
A ƙarshe :
Haƙiƙa duk wanda ya sanya rayuwar duniya wadda take ƙararriya, ita ce manufa da tushe a gare shi, to shi yana cikin jahannama ta ma’ana [1]koda ya kasance yana aljanna ne a zahiri,[2]amma (ka ga) duk wanda ya kasance ya fuskanci rayuwa ta wanzuwa da ƙoƙari to da sannu zai samu arzikin gidaje biyu, duk yadda duniyarsa ta kasance cikin muni da ƙunci, domin shi yana karɓarta a haka kuma yana haƙuri da ita, yana godewa Allah a cikin haƙuri,don kasancewarsa yana ganin duniyarsa kamar farfajiya ce ta sauraro don shiga Aljanna.
اللهم اجعلنا من أهل السعادة و السلامة و القرآن و الإيمان
آمين
اللهم صل و سلم على سيدنا محمد و على آله و صبحه بعدد جميع الحروف المتشكلة في جميع الكلمات المتمثلة بإذن الرحمن في مرآيا تموجات الهواء عند قراءة كل كلمة من القرآن من كل قارئ من أول النزول إلي آخر الزمان ’ وارحمنا ووالدينا و ارحم المؤمنين و المؤمنات بعددها برحمتك يا أرحم الراحمين آمين . والحمد لله رب العالمين.
[1] Wato hali mai ƙunci a rayuwarsa.
[2] ko da yana cikin jin daɗi ne a zahiri.


