KALMA TA TARA

83. Page

KALMA TA TARA

بسم الله الرحمن الرحيم

فَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ حِينَ تُمۡسُونَوَحِينَ تُصۡبِحُونَ * وَلَهُ ٱلۡحَمۡدُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِوَعَشِيّٗا وَحِينَ تُظۡهِرُون[1]

Ya kai ɗan’uwa ;kana tambayata game da hikimar keɓance Sallah a lokutanan guda biyar,tozamuyi ishara i zuwa hikima ɗaya daga hikimominsa masu yawa ƙwarai da gaske.

Haƙiƙa ka ga lokacin kowacce Sallah, farko ne na wata sassauyawa mai muhimmanci, kuma wani madubin tasarrufi[2] na Allahntaka mai girma , kuma mai hasko dukkan kyautaye-kyautayen nan na Allantaka a yayin wannan tasarrufi; a saboda haka ne aka farlanta Sallah wadda haƙiƙaninta shi ne yawaita tsarkakewa da girmamawa ga Mai Iko Mabuwayi Maɗaukaki a cikin waɗannan lokutan, tare da godiya da yabawa bisa ga tilin ni’imominnan nasa wanda ba su da iyaka wanda yake ba da su tsakanin lokuta biyu[3].

Kuma don fahimtar wani sashi na waccan ma’anar mai zurfi yana da kyau ni da kai mu saurari waɗannan bayanai guda biyar.

Bayani na farko: Haƙiƙar ma’anar Sallah ita ce والتعظيم والشكرالتسبيح tsarkakewa da girmamawa da godiya ga Mai gaskiya Maɗaukaki; ai tsarkake girmansa da faɗin

[1]Saboda haka tsarkakewa ta tabbata ga Allah a lokacin da kuke shiga maraice da kuma lokacin da kuke shiga safiya* kuma shi ne da godiya, a cikin sammai da ƙasa, da lokacin yamma da lokacin zawali (Arum 17-18)

[2]Gudanar da al’amura

[3]Tsakanin sallah da sallah




84. Page

اللَّهِ a faɗe da a aikace, da girmama cikarsa tare da faɗin اللَّهُ أَكْبَرُ a faɗe da a aikace , da godewa kyawunsa tare da faɗin الْحَمْدُلِلَّهِ a zuci da harshe da jiki .

Kenan والتحميد والشكرالتسبيح tsarkakewa da girmamawa da godiya suna a matsayin ɗan iri na Sallah; saboda haka ne ake samun waɗannan kalmomi guda uku a cikin dukan motsi da zikirai na sallah; haka nan kuma waɗannan kalmomin ana maimaitasu a ƙarshen kowace sallah sau talatin da uku don tabbatar da ma’anar Sallah tare da ƙarfafata.

Bayani na biyu: Haƙiƙar ma’anar ibada ita ce sujjadar bawa cikin mamakantuwa da girmamawa da nuna soyayyarsa ga hallarar nan ta Allantaka a gaban cikarnan ta ubangijintaka da Ikon nan na abin nufi da buƙata da Rahamar nan ta Allantaka yana mai riskar kasawarsa da gajiyawarsa da buƙatuwarsa.

Kamar yadda Masarautarnan ta Ubangijintaka take hukunta yin bauta da ɗa’a ;haka nan Tsarki naUbangijintaka ya na lazamtawa bawa – tare da neman gafararsa bayan ya gane kasawarsa – ya shelanta cewa Ubangijinsa abin tsarkakewa ne da kuɓutarwa daga dukkan tawaya , kuma abin tsarkakewa ne da ɗaukakawa daga gurɓatattun Tunanikan ma’abota ɓata, sanan abin tsarkakewa ne daga dukan wata tawaya da kasawar ababen halitta , yana mai tasbihi ya cewa [1] سُبْحَانَ اللَّهِ.

Kuma haka nan cikakken Iko na Ubangijintaka yana hukuntawa bawa da ya fake da Ubangijinsa ya kuma dogara gare shi, ya yi ruku’u tare da ƙasƙantar da kai yana faɗin[2] اللَّهُ أَكْبَرُ, a gaban girman guraben ikon nan na Abin nufi da buƙata cikin kyautatawa da yabawa bayan ya gane rauninsa da gajiyawar sauran halittu .


[1]tsarki ya tabbata ga Allah

[2]Allah mai garma




85. Page

Haka nan taskar rahamar nan wadda ba ta da iyaka ta Ubangijintaka tana hukuntawa ga bawa ya bayyanar da buƙatuwarsa da buƙatuwar dukkan halittu da talaucinsu ta hanyar roƙo da kuma addu’a , kuma ya yi iƙirari da kyautatawar ubangijinsa da ni’imtawarsa ta hanyar godiya da yabo ya na mai faɗin :الْحَمْدُلِلَّهِ[1] .

Wato ayyukan da a ke a Sallah da abubuwan da a ke faɗa a cikinta sun ƙumshi waɗannan ma’anoni, kuma Allah maɗaukakin sarki ya sanyasu ne don waɗannan ma’anoni.

Bayani na uku: kamar yadda haƙiƙa mutam misali ne ƙarami na kasantatu , kuma الفاتحة الشريفةsurar Fatiha misali ce mai haske na Alƙu’rani mai babban Sha’ani ; to haka ma Sallah ita fihirisace mai haske da take tattare da dukan nau’o’in ibadodi , kuma Taswira ce mai tsarki da ke nuni i zuwa nau’o’in ibadodi na dukkan nau’in halittu.

Bayani na huɗu : kamar yadda tsinkayen nuni na agogon sati yake ƙirga sakonni da mintunansa da kuma awanni da ranakunsa, sashinsu ya na kwatankwaci da sashi, haka kuma kowanne ya na kama da kowannen sa, haka kuma kowanne ya na ɗaukar

[1]godiya ta tabbata ga Allah




86. Page

hukuncin kowannen sa, hakanan kuma lallai sassauyawar dare da rana wanda ita ce a matsayin sakan na wannan duniyar wanda kuma ita ce awa babba a wurin Allah maɗaukakin sarki, haka kuma da shekaru waɗanda suke ƙidanya daƙiƙu, da ɗabaƙoƙin rayuwar ɗan’adam waɗanda suke ƙidanya awanni, da zango-zango na rayuwar duniya wadda take ƙidanya ranaku; ita ma hakanan sashinta ya na kwatankwaci da sashi, hakanan kowanne daga ciki ya yi kama da ɗayan, haka kuma kowanne ya na ɗaukan hukuncin kowannensa, kuma sashin su ya na tunasar da sashi.

Amisali: Lokacin ketowar Alfujur zuwa lokacin hudowar Rana yana kama kuma yana tunasar da farkon lokacin kaka, da kuma lokacin faɗawar mutum cikin Mahaifar mahaifiya, da ranar farko daga ranaku shida ta halittar sammai da ƙasai, sanna yana faɗakar da abin da ke cikinta na sha’anin allantaka.

Kuma amma Lokacin Azahar :yana kama da tsakiyar yanayin zafi kuma yana nuni zuwa gare shi da kuma zuwa cikar samartaka, da kuma lokacin halittar mutum a cikin rayuwar duniya, yana kuma nuni da abin da ke cikinsu na tajalolin rahama da kwaranyar ni’imomi.


87. Page

Kuma amma Lokacin La’asar: yana kama da yanayin damina, da lokacin tsufa da lokacin farin ciki na Annabin ƙarshen zamani –amincin Allah ya tabbata a gare shi- kuma yana tunasar da abin da ke cikinsa na daga sha’anin Allantaka da ni’imce-ni’imcen mai rahama.

Kuma amma Lokacin Magariba : shi yana faɗakar da kuma tasar da muta ne daga baccin gafala, kuma yana fahimtar da su tajalolin buwayantaka ta hanyar tunasarwarsa gushewar da yawa daga halittu a ƙarshen yanayin damina, da kuma tunasarwarsa da mutuwar mutum da kuma rushewar duniya a farkon lokacin tashin Alƙiyama.

Amma Lokacin Isha’i : shi yana shelanta tasarrufofin buwayantaka na mai rinjaye ma’abocin girma ta hanyar tunasarwarsa suturce duniyar duhu da baƙin likkafaninsa ga guraban ayyukan Rana, da tunasarwarsa lulluɓewar yanayin sanyi da farin likkafaninsa fuskar ƙasa matacciya, da kuma tunasarwarsa mutuwar ragowar guraben mutum da ya rasu da shigarsu ƙarƙashin hijabin mantuwa, da kuma tunasarwarsa ga rufe wannan duniyar- wadda ita gidan jarrabawa ne- gabaɗaya.

Kuma amma Lokacin Dare : yana tunasar da mutum ga matuƙar buƙatar ran ɗan’adam i zuwa rahamar mai rahama ta hanyar tunasarwarsa yanayin sanyi da ƙabari da duniyar barzahu.

AmmaTahajjudi a cikin dare: yana tunasar da matuƙar lalurar yawan haske da ake buƙata a cikin duhun daren ƙabari da duffan barzahu, kuma yana shelantawa a cikin waɗannan sauye-sauye dukkansu matuƙar cancantar mai ni’imtarwa na haƙiƙa mabuwayi maɗaukaki ga yabo da godiya ta hanyar tunasarwarsa ga ni’imominsa marasa iyaka.

Amma Safiya ta biyu: ita tana tunasar da safiyar tashin ƙiyama, na’am; kamar yadda safiyar wannan dare da kakar wannan yanayin sanyin abin da hankali zai iya karɓa 

88. Page

ne; to tilas ne kuma babu kokwanto a su; to hakama safiyar tashin ƙiyama da kuma lokacin kakar barzahu hakanan suma abu ne da hankali zai iya karɓa take yanke kamarsu.

Kenan kamar yadda kowanne lokaci daga cikin waɗannan lokutan guda biyar tushe ne na wani juyi na musamman, kamar kuma yadda cewa shi ya tunasar da sauye-sauye masu girma; haka nan ma lallai yana tunasar da mu’ujizozi na iko da kyautattakin rahamar ta shekara da na ƙarni da na dukkan zamani ta hanyar nunin tasarrufofin mai girma na kullun ga ikon abin nufi da buƙata.

Kenan salloli ababen farlantawa- waɗanda su aiki ne da ya dace da zubin halitta na asali kuma ginshiƙin bautatuwa da addini tatacce- masu dacewa ce ƙwarai a wannan lokutan.


89. Page

Bayani na biyar: Haƙiƙa mutum yana da rauni sosai a zubin halittarsa, tare da cewa kowanne abu yana iya sa shi damuwa kuma ya yi tasiri a kansa da sa shi jin raɗaɗi , duk da cewa masifu da maƙiyansa da suke kewaye da shi suna da matukar yawa, kuma shi mabuƙaci ne ƙwarai tare da cewa buƙatunsa suna da tilin yawa, sannan kasalalle ne mara katabus tare da cewa nauyaye-nauyayen rayuwarsa suna da nauyi ƙwarai, kuma mutumtakarsa ta sanya shi mai alaƙa da sauran kasantattu tare da cewa gushewa da rabuwar wasu abubuwa da yake so waɗanda suke ɗebe masa kewa suna sa shi jin ciwo da jin ba daɗi ko yaushe, hankali kuma yana nuna masa wasu manyan manufofi da ababan morewa wanzajju a tare da cewa hannunsa bai iya kaiwa gare su sannan rayuwarsa gajeriya ce ikonsa kuma ƙanƙani ne haka haƙurinsa kaɗan ne.

Tunda wannan ne hali da sha’anin ran ɗan’adam, za a iya fahimta tafaraɗɗaya cewa abu ne da ya ya zama lallai bujuro da halinsa (rai) a gaban masarutar mai iko ma’abocin girma kuma mai jinƙai ma’abocin jamala, yana mai ƙwanƙwasa kofarta ta hanyar yin ahi da yin sallah a lokacin fitowar alfijir,tare da neman ɗauki da dacewa daga gare shi, kuma ya girman kasancewarta nuƙuɗar dogaro wadda take ta dole, don jurar abin da zai same shi (rai) da kuma abin da za a dora masa na umarni da kuma ayyuka a lokacin rana wanda yake biyo bayan lokacin ketowar alfijir.

Shi kuma lokacin azahar wanda shi ne wanda lokacin cikar rana da kuma fara karkatarta , kuma shi ne lokacin gama al’amuran wannan rana, kuma lokaci ne na hutun wucin gadi daga ƙuncin ayyuka da matsin su, haka kuma shi lokaci ne na buƙatuwar rai i zuwa hutu da komawa hayyacinsa daga gafala da ɗimuwa da ruɗewa wanda duniyar nan ƙararriya take haifar da su da al’amura masu gushewa masu nauyi masu wahalarwa, wanda kuma shi ne lokacin bayyanar ni’imomimin nan na Allantaka, kuma yin sallar azahar wanda ke nufin neman taimakon ran ɗan’adam da yabawarsa da kuma godiyarsa  a bisa tarin ni’imomin mai ni’imtarwa na haƙiƙa kuma tsayayye wanzajje yana mai buɗe tafukansa ta hanyar fakewa i zuwa masarautarsa (Allah) bayan kuɓutarsa daga wannan ƙunctace-ƙuntace da barinsa wannan gafala da fitarsa daga waɗannan al’amura masu gushewa mawofanta, da bayyana gazawarsa ta hanyar yin ruku’u ga ma’abocin girma da ɗaukaka, da shelanta 

90. Page

mamakinsa da nuna soyayyarsa da narkewarsa ta hanyar yin sujjada a gaban cikarsa da bata gushewa da kyawunsa mara tamka; muna faɗi: mutumin da ba ya gane girman sauƙi da girman larura da dacewar yin sallar azahar-awawnnan ma’anar da aka ambata- lallai baicika mutum ba.

Amma kuma lokacin La’asar yana nuni ne i zuwa yanayin damuna , da tsufa mai baƙanta rai da yanayi mai raɗaɗi na ƙarshen zamani kuma shi lokacine na gama ayyukyan wannan rana kuma lokacin ne na tsattsara tari mai girma na ni’imomin Allantaka waɗanda mutum ya same su a wannan rana, kamar lafiya da kuma kwanciyar hankali da ayyukan alkhairi ,kuma shi lokaci ne da yake shelanta – ta hanyar nuni karkatar wannan tangameman kaskon rana zuwa faɗuwa- cewa mutum baƙo ne ma’abocin ayyuka, kuma kowanne abu na wucin gadi ne zai gushe ba zai tabbata ba.

Kuma daga nan ne ran mutum wanda yake neman dawwama wanda kuma an halicce shi ne don ita, haka kuma wanda yake san kyautatawa i zuwa matakin bauta mai kuma jin raɗaɗin rabuwa; sai ya miƙe a nan ya yi alwala a lokacin la’asar don yin sallar la’asar yana mai bijiroganawarsa a gaban masarautar nan ta abin nufi da buƙata ta dawwamamme wanzajje tsayayye na har abada yana mai yabo da godiya bisa ni’imominsa wanɗan da ba za su ƙidanyu ba yana fakewa i zuwa ga rahamarsa wadda bata gushewa bata kuma da karshe, kuma yana durƙusawa don yin ruku’u yana mai ƙasƙantar da kai a gabanعزة ربوبيتهbuwayar Ubangijintakarsa da yin sujjada da narkewa a gaban سرمدية ألوهيتهDawwamar Allantakarsa; sai ya samu karsashi na haƙiƙa da hutu ga rai tahanya tsayuwarsa da cikakkiyar bauta a hallarar nan ta girmansa.


91. Page

Amma yin sallar la’asar wadda take fa’idantar da duk wannan , wanda ya kasance cikakken mutum ne shi zai iya fahimta cewa ita wani aiki ne maɗaukaki , kuma hidimace mai dacewa , kuma tsayawa da ita a lokacinta addini ne da ya dace da zubin halittar mutum kai barima nasarace da farin ciki da arziƙi cikin matuƙar tausasawa.

Ammashi kuma lokacin Magariba lokaci ne da yake nuni i zuwa lokacin gushewar halittun duniyar yanayin zafi da damuna mai tabshi da laushi da kyau a cikin bankwanansu dake ɗauke da damuwa yayin farkon yanayin sanyi, hakanan yana tunasar da lokacin shigarmutum ƙabari a yayin da ya mutu da raɗadin rabuwarsa da dukkanin masoyansa, hakanan yana tunasar da lokacin ƙaura na mazauna duniyar nan baki ɗayansu i zuwa wasu duniyoyin da ban bayan mutuwar wannan duniyar da girgizarta da magaginta, haka yana tunasar da lokacin bicewar fitilar wannan gidan jarabawar, haka shi lokacin ne da yake farkarwa mai tsanani ga waɗanda suke nuna soyayyarsu ga ababan ƙaunarsu masu gushewa i zuwa matakin bauta.

To ran ɗan’adam wanda shi wani madubi ne mai begantuwa da irin zubin halittarsa ga kyawu wanzajje wanda kuma (rai) yake nufatar yin sallar magariba a irin wannan lokacin, yana kuma fuskantar da fuskarsa i zuwa al’arshin girma na dawwamammen da ba ya gushewa, kuma wanzajjen da ba ya gushewa, wanda kuma yake yin wannan 

92. Page

e

alamura masu girma da yake gudanar da sauya wannan duniyoyin gingima-gingima, yana mai faɗar: الله أكبرAllah mai girma bisa wannan ƙararrun abubuwan, sai ya tsame hannayensa daga su yana mai dangantasu ga hidimtawa shugabansa majiɓincin lamarinsa da tsayawa a hallarar dawwamamme wanzajje da yabo da godiya a gare shi da faɗinsa: ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهَِ godiya ta tabbata ga Allaha bisa cikarsa da ba wata taƙaita a cikinta, da kuma kyawunsa wanda ba shi da tamka da rahamarsa mara iyaka, yana mai neman taimako daga gare shi da yin bauta yana faɗin: إِيَّاكَ نَعۡبُدُ وَإِيَّاكَ نَسۡتَعِينa gaban ubangijintakarsa da bata da mataimaki, da Allantakarsa da ba tada abokin tarayya, da masarautarsa da babu mataimaki gare ta, sai ya yi ruku’u a gaban girmansa mara ƙarshe da ikonsa marar iyaka, da buwayarsa wadda ba gajiyawa a tare da ita, da bayyanar da rauninsa ta hanyar gajiyawarsa da talaucinsa da ƙasƙancinsa haɗe da dukkan sauran kasantattu yana cewa: سبحان ربي العظيمsaiya tsarkake ubangijinsa mai girma.


93. Page

Hakanan (rai) yana yin sujjada a gaban kyaun zatinsa wanda babu gushewa gare shi, da siffofinsa tsarkaka waɗanda ba canji a tattare da su, da cikarnan ta dawwamarsa wadda bata sauyawa, yana kuma shelanta soyayyarsa da bautatuwarsa ta hanyar barin koma bayansa Allah maɗaukaki, cikin narkewa da yabawa, sai ya samu kyakkyawa wanzajje da mai jinƙai na har abada a maimakon dukkan wannan ƙararrun , yana mai tsarkake ubangijinsa maɗaukaki abin tsarkakewa daga gushewa kuɓutacce daga aibuka da tawaya ta hanyar faɗinsa:سبحان ربي الأعلى sannan ya zauna {rai} don yin tahiya sai ya gabatar da kyauta da gaisuwa mai albarka ta dukkan halittu da salatukansu tsarkaka da sunansa a matsayin nasa zuwa ga mai kyau wanda ba ya gushewa mai girman da bai gushewa, da bayyana biyayyarsa ga umarninsa ta hanyar yin sallama a bisa manzonsa mai matuƙar karamci amincin da tsiran allah su tabbata a gare shi, kuma da sabunta mubaya’arsa a gare shi , da shaidawa da kaɗaitakar maƙeri ma’abocin girma ta hanyar dubansa ga tsari mai matuƙar hikima na ginin halitta da nufin haskaka imaninsa ta sabunta mubaya’a, kuma yana shaidawa a bisa manzancin annabi Muhammad balarabe- tsira da aminci allah ya tabbata a gare shi- wanda shi ne mai kira na masarautar ubangijintaka mai isar da abubuwan da suke yardar da Allah maɗaukaki, kuma mai fassara ayoyin nan na littafin kasantattu.

To ka duba ka ga yadda yin sallar magariba- wanda yake ɗauke da waɗannan ma’anoni da aka ambata- ya zama wani aiki ne mai tabshi mai tsafta, haka kuma wata hidima cemaɗaukakiya mai daɗi, kuma yaya girman kasancewarta bautatuwa ce tsarkakkiya kyakkyawa, kuma yaya girman kasancewarta haƙiƙa ce mai matuƙar muhimmanci, kuma wata abota ce wanzajjiya kuma farin ciki madawwami a wannan gidan saukar baƙin ƙararre.

To ta yaya mutum zai zama cikakken mutum idan bai gane haka ba kuma ba ya iya 

94. Page

Amma lokacin isha’i : lokacine na gushewar wannan abin da ya ragu a sararin samaniya na daga guraban rana, da lulluɓewar duniyar dare a bisa kasantattu, kuma shi lokaci ne da yake tunasar da tasarrufin uban gijintaka na mai iko ma’abocin girma wanda shi ne mai juya dare da rana a cikin juyawarsa ga wannan farar takardar i zuwa wannan baƙar, kuma yana tunasar da ayyukan Allantaka na mai hikima ma’abocin cika wanda shi ke hore rana da wata, cikin sauyawarsa ga shafinnan na yanayin zafi abin ƙawatawa kore i zuwa shafinnan na yanayin sanyi mai raɓa fari, kuma yake nuni ga sha’anonin allantaka na mahaliccin mutuwa da rayuwa cikin ciruwar ragowar guraben ma’abota ƙabarurruka tare da tafiyar zamani i zuwa wata duniyar baki ɗaya da kuma ƙaurarsu daga wannan duniyar .

Haka kuma shi lokaci ne da yake nuni tare da tunasar da tasarrufin buwayantaka da tajallolin cika na mahaliccin ƙasa da sammai cikin bayyanar da alam na lahira yalwatacce wanzajje mai girma bayan magagimai girma na rasuwar duniya wadda itaƙuntatacciya ce ƙararriya ce wulaƙantacciya ce, da rusata gabaki ɗaya, ita- hali -tana tabbatar da cewa mai mulki da tasarrufi na haƙiƙa a cikin wannan duniyar kuma abin yi wa bauta da soyayya tahaƙiƙa a gare shi lallai shi ne zatin Allah mai iko na sake baƙaidi, yana juya dare da rana da sanyi da zafi da duniya da lahira cikin sauƙi, kamar sauƙin jujjuya shafin littafi, ya kuma rubuta su ya gogesu ya canjasu ya kuma sauyasu sannan ya yi hukunci akansu gaba ɗaya.


95. Page

To ran ɗan’adam wadda gajiyawarta da rauninta ba su da ƙarshe , wadda take cikin talaucin da buƙata da ba su da iyaka ,wacce kuma take afkawa cikin duffai da ba su da iyaka na zamani mai zuwa, wanda kuma yake rikicewa da jujjuyawa a cikin abubuwan da ke faruwa da ba su da iyaka, wannan ranyayin da yake yin sallar isha’ida wannan ma’anar a lokacin isha’i To shi yana faɗa ne kamar yanda annabi Ibrahim ke faɗi :لَآ أُحِبُّ ٱلۡأٓفِلِين

[1] sannan kuma yana fakewa da yin sallah i zuwa masarautar abin bauta wanda ba ya gushewa kuma masoyin da ba ya gushewa, kuma ya gana da wanzajje na har abada a cikin wannan duniyar ƙararriyya da wannan rayuwar ƙararriya, a cikin wannan duniya mai duhu a lokaci mai zuwa mai tsananin duhu, kuma yana duba da neman kyautatawar da ni’imtawar rahama da hasken shiriyar mai rahama mai jinƙai wanda yake yaɗa haske a cikin duniyarsa a tsakankanin ɗan yanki daga abokantaka wanzajjiyada‘yan daƙiƙoƙi a rayuwa wanzajjiya, kuma wanda yake haskaka lokacinsa mai zuwa, sannan ya maganceraunukansa masu tasowa daga rabuwa da masoya da rabuwa da gushewar dukan samanmu, kuma sai ya manta a wani ɗan lokaci wannan duniyar wadda tamanta da shi ta kuma faku ga barinsa, yana kuma bayyanar da damuwarsa da baƙin cikinsa a gaban masarautar mai rahama ta hanyar kukan zuci.

Kuma tsammanin abin da zai faru sai ya tsayu da aikin bautatuwarsa ta ƙarshe kafin shigarsa barci wanda shi yana kama ne da mutuwa,sai ya tashi ya yi sallah don rufe

[1](bana san masu faɗuwa)




96. Page

littafin aiyukan wannan rana da kyakkyawar rufewa, wato tsayawa a gaban abin bauta kuma wanzajjen masoyi a maimakon dukan masoyansa kararru, a kuma gaban mai iko da karamci a maimakon dukkan gajiyayyu waɗanda yake miƙa ƙoƙon bararsa agaresu, a gaban kuma mai kiyayewa mai jinƙai don kuɓuta daga sharrin ababan halittu masu cutarwa waɗanda suke makyarkyata a gabansa, sai ya buɗe da fatiha ; wato: yana yabo da godiya ga ubangijin talikai wanda shi ne mai cika ta sake ba ƙaidi, kuma mawadaci na sake ba ƙaidi a maimakon yabo da roko - waɗanda ba su da wani amfani kuma marasa dacewa – ga ababan halitta tauyayyu matalauta.

Sannan sai ya ɗaukaka ga matakin tattaunawa da fadin : إِيَّاكَ نَعۡبُدُ wato ya shiga maƙamin baƙo abin karramawa kuma ma’aikaci na musamman a cikin waɗannan kasantattu ta hanyardangantuwarsa i zuwa mamallakin ranar sakamako wanda shi ne sarki na tun fil’azal duk da ƙanƙantarsa da buƙatuwarsa da kaɗaicinsa, sai ya gabatar gare shi ibada da neman taimakon dukkan kasantattu – da sunan dukkan ababan halitta – yana cewa إِيَّاكَ نَعۡبُدُ وَإِيَّاكَ نَسۡتَعِين , sannan ya nemi shiriya i zuwa ga tafarki madaidaici wanda shi ne hanyar haske mai kaiwa ga farin ciki na har abada a cikin duhu na lokaci mai zuwa yana faɗin : ٱهۡدِنَاٱلصِّرَٰطَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ[1].

Sannan ya sunkuya don ruku’u yana cewa:الله أكبرyana mai tunani a cikin girman zatin ma’abocin girma, yana mai bin umarninsa- kamar dai soja- haka dukkan tsirrai da dadabbobi waɗanda suka nitse a cikin baccinsu, da dukkan kaskunan rana da suka faɗi, da taurari masu fitowa da daddare waɗanda yanzu su ne fitilu kuma hadimai gare shi a wannan gidan saukar baƙin.

Sannan sai ya yi tunani a kan sujjada mai girmata dukkan ababan halitta ; wato nau’ikan samanmu , wanda sukatattare da abin da ke kan doron ƙasa da wanda ke cikin duniya a kowace shekara da kowane zamani – kamar ababan halitta masu bacci a cikin wannan dare – suna sujjada kamar tsararriyar runduna, barima kamar soja mai biyayya cikin cikar tsari suna masu faɗin الله أكبر a shinfiɗar nan ta faɗuwar rana a lokacin zawali yayin da a ke sallamarsu daga aiki da umarni na كُن فَيَكُونُ daga aikin bautatuwarsu na duniyya; wato: lokacin da ake tashinsu i zuwa duniyar gaibu hakanan ana tashi tare da taro wani kaso daga cikin – ababan halitta da ainihinsa wani kason kuma da makamancinsa daban wani lokacin a yanayin kaka da tsawa ta rayarwa da farkarwa wadda take tasowa daga umarnin nan naكُن فَيَكُون sai su miƙe suna masu shiri da tanadi yin hidima ga majiɓincin lamrinsu; hakanan kuma wannan mutum( ƙarami ) miskini mai rauni matalauci yana cewa:الله أكبرyana mai koyi da su a gabanmasarautar hallarar mai rahama ma’abocin cika, kuma mai jinƙai ma’abocin kyau, ta hanyar cikakkiyar soyayya da yabawa, da kuma narkewa mai cike da wanzuwa , da kuma cikakken ƙasƙantar da kai wanda yake cike da girma.

Ba kokwanto haƙiƙa kai ka fahimci cewa sau da yawa yanda yin sallar isha’i ya zama abu ne mai tabshi da kyau wanda kuma shi wani nau’i ne na mi’iraji, kuma sau da

[1]kuma ka shiryar da mu i zuwa tafarki madaidaici)




97. Page

yawa shi mai zaƙi ne da ɗaukaka kuma sau da yawa shi girma ne kuma mai daɗi, kuma yadda ya zama shi wani aiki ne da hidima da bautatuwa kuma haƙiƙa ce mai matuƙar muhimmanci, karɓaɓɓiya mai dacewa.

 Kenan kowane lokaci daga cikin waɗannan lokutan guda biyar na sallah nuni ne i zuwa wani sauyi mai girma, kuma alamomi ne na ayyukan ubangijintaka manya-manya, kuma alamomi ne na ni’imce-ni’imcen Allantaka a dunƙule; kenan keɓance waɗannan lokutan da waɗannan sallolin ababan wajabtawa waɗanda su  ba shi ne da yake kan wuya, shi ne matuƙar hikima.

 

لَا عِلۡمَ لَنَآ إِلَّا مَا عَلَّمۡتَنَآۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡحَكِيمُ سُبۡحَانَك


اللهم صل وسلم على من أرسلته معلما لعبادك ليعلمهم كيفية معرفتك و العبودية لك ومعرفا لكنوزك أسمائك ، و ترجمانا لآيات كتاب كائناتك و مرآة بعبوديته لجمال ربوبيتك ،وعلى آله وصبحه أجمعين ، وارحمنا وارحم المؤمنين والمؤمينات ..


آمين، برحمتك يا أرحم الراحمين.