KALMA TA UKU
NAVIGATION
33. Page
KALMA TA UKU
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِ
يَٰا أَيُّهَا النَّاسُ اعبُدُواْ رَبَّكُم...[1]
{Bambancewa tsakanin mai bin dokokin Allah da wanda ba ya binsu }
Idan kanaso ka san ta yaya ibada ta zama kasuwanci da arziki mai girma, kuma ta yaya fasiƙanci da wawanci suka zama asara da halaka masu girma, to yi duba i zuwa wannan hikayar da aka misalta ta a taƙaice, kuma ka yi sauraro:
{Hikayar hanyoyi guda biyu ɗaya ta bautar Allah ce ɗayar kuma ta kafircewa bautarsa ce }
Watarana wasu sojoji biyu sun karɓi umarni don su yi tafiya i zuwa wani gari mai nisa, sai suka tafi tare, har suka kai i zuwa wurin da hanya ta rabu, a nan suka tarar da wani mutum sai ya ce musu: wannan hanyar ta dama, babu cuta a cikinta, ƙari a kan haka ma, tara a cikin goma na masu binta, suna samun riba da hutu masu girma, wannan hanyar ta hagu kuwa, duk mutum tara daga goma da suke binta, suna cutuwa tare da rashin amfanin dake cikinta.
Dukkan hanyoyin biyu madaidaitane wajen tsawon su da gajartar su, sai dai cewa a tsakanin su akwai banbanciɗaya, shi ne:
Duk mai bin hanyar hagu wadda ba wani shiryayyen tsari a cikinta, kuma ba hukuma a cikinta, to zai tafiya ne ba tare da ya ɗauki jakar guzuri ko wani makami ba, zai ji sauƙi a zahiri kamar babu nauyin komai a tare da shi.
Amma mai bin hanyar dama, wadda take kan tsarin sojoji, to yana wajaba a kansa ya dauki jaka cike da kayayyakin abinci tatattu, masu nauyin Uƙiya[2] huɗu,haka kuma zai dauki rantsasstsen makami na hukuma mai nauyin Uƙiya biyu, wanda ta hanyarsa ne zai samu galaba da rinjaye a kan dukan maƙiyi.
{Zaɓin da sojojin suka yi}
[1] (Ya ku mutane ku bautawa ubangijinku)Surat albaqara, aya ta 21.
[2] Wani ma’auni ne na da, cikinsa goma sha biyu yake Riɗili ɗaya, duk Larabawa ne suke amfani da su.
34. Page
Bayan waɗannan sojoji saurari wannan zance na wannanmutum masani[1].
Wannan sojan mai sa’a, sai ya bi hanyar dama, sai kuma ya dauki wasu kayayyaki gwargwadon nauyin riɗili a kafaɗar sa da bayan sa, sai dai cewa zuciyar sa da ransa sun tsira daga gwargwadon nauyin dubbunnan riɗilai na gorace-gorace[2]da tsorace-tsorace.
Amma ɗaya sojan mara sa’a, sai ya bar aikin sojan ya ƙi bin tsari, kuma ya bi hanyar da take hagu, ya kuɓutar da jikinsa daga daukan nauyi gwargwadon riɗili ɗaya, sai dai zuciyarsa tana nuƙurƙusuwa ƙasan dubbannan riɗilai na gorace-gorace[3]hakama ransa yana nuƙurƙusuwa cikin fargaba da firgici daba su da iyaka. Sai ya bi wannan hanyar yana roƙon duk wanda ya gamu da shi. Kuma yana makyarkyata daga dukkan
[1] Wato ya san komai na cikin wannan hanyoyin.
[2] (Ci a ƙarƙashin tallafin wani).
[3] Nauyi ne na ma’ana ba na zahiri ba, kamar zunubai ko fargaba.
35. Page
shiga cikin dimuwa.! Tabbas Amurka ta taba shiga tsoro a cikin wani zamani da sababin irin wannan tauraro, yawancin Amurkawa suka bar gidajen su a cikin dare.
{Fa’idar da mutum yake samu daga bautar Allah}
Na’am, duk da cewa mutum mai buƙata ne i zuwa abubuwan da ba su da iyaka; to haƙiƙa jarinsa,[1]ba komai ba ne, duk da cewa shi mai gamuwa ne da musibu marasa iyaka; sai dai da’irar ikonsa ita ma ba komai ba ce, tun da kewayen jarinsa da ikonsa gwargwadon inda hannunsa zai iya saduwa i zuwa gare shi ne, amma burace-buracensa da abubuwan da yake so, da raɗaɗin da yake ji da bala’o’in da yake haɗuwa da su masu yawa sun kai tsawon ganinsa da riye-riyensa[2], haƙiƙa idan bai zama makaho na gani da na basira ba duka, tabbas shi zai gani kuma zai riska, haƙiƙa cewa bauta da tawakkali da tauhidi da miƙa wuya su ne mafi girman riba da arziki masu yawa, da ni’ima ga zuciyar don adam mabukaciya, kasasshiya, raunanniya kuma mabuƙaciya har i zuwa wannan iyaka.
{Hanyar bautar Allah babu cutuwa a cikinta}
Tabbas yana daga abin da aka sani amintacciyar hanya ana rinjayar da ita a kan hanya mai haɗari, ko da zaton cutuwa a hanyar mai haɗaridaya ne bisa goma, daɗin daɗawa hanyar bautar Allah – wadda ita ce batunmu anan- babu cutarwa a cikinta, ƙari a kan haka taskar nan ta arziki na har abada tana cikin ta da kwatankwacin kashi tara daga goma, amma hanyar nan ta fasiƙanci da wauta, ita babu amfani a cikin ta, da iƙirarin fasiƙin da kansa. Halaka da tsiya ta har abada tana cikin ta ,da kwatankwacin tara daga goma, wannan zancen da shaidar waɗanda ba sa ƙidanyuwa daga ma’abota ƙwarewa a wannan fagen, da kallo da yayewar da ake yi wa waliyai da ya kai matakin darajannan ta haduwar malamai da bibiyan nan ta hujja; wata-bayan-wata,da shaidar nan da bata da adadi na ahlin wannan fagen, da gaskiya da kuma tabbacin bayanin nan na ma’abota ɗanɗanon zaƙin sanin Allah da waɗanda ake yayewa sanin wasu sirrika na ubangiji.
[1]Na daga dukiya.
[2] Saqe-saqen zuciya.
36. Page
A ƙarshe:
Hakika arzikin duniya yana cikin bauta da kuma zama ɗan rundunar Allah, kamar yadda haka yake a cikin arzikin lahira. A saboda haka ya wajaba a kan mu mu yi ta maimaitawa kodayaushe:
اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلٰى دِينِ اْلاِسْلاَمِ وَكَمَالِ اْلاِيمَانِ[1]
Yana wajaba a kanmu mu dinga godewa Allah kodayaushe a bisa kasancewar mu musulmi.
[1] Muna godewa Allah a bisa yassare mana biyayyar sa da gam-da-katar


