ABAR GABATARWAR TASHI, (IRIN TASHIN ALƘIYAMA) SHU’A’I NA TARA

66. Page

ABAR GABATARWAR TASHI, (IRIN TASHIN ALƘIYAMA)

SHU’A’I NA TARA

بسم الله الرحمن الرحيم

فَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ حِينَ تُمۡسُونَوَحِينَ تُصۡبِحُونَ * وَلَهُ ٱلۡحَمۡدُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِوَعَشِيّٗا وَحِينَ تُظۡهِرُونَ * يُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَيُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّ وَيُحۡيِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۚ وَكَذَٰلِكَ تُخۡرَجُونَ* وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنۡ خَلَقَكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ إِذَآ أَنتُم بَشَرٞ تَنتَشِرُونَ * وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنۡ خَلَقَ لَكُم مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ أَزۡوَٰجٗا لِّتَسۡكُنُوٓاْ إِلَيۡهَا وَجَعَلَ بَيۡنَكُم مَّوَدَّةٗ وَرَحۡمَةًۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ*وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ خَلۡقُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَٰفُ أَلۡسِنَتِكُمۡ وَأَلۡوَٰنِكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّلۡعَٰلِمِينَ * وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ مَنَامُكُم بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَٱبۡتِغَآؤُكُم مِّن فَضۡلِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَلَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَسۡمَعُونَ * وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ يُرِيكُمُ ٱلۡبَرۡقَ خَوۡفٗا وَطَمَعٗا وَيُنَزِّلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗفَيُحۡيِۦ بِهِ ٱلۡأَرۡضَبَعۡدَ مَوۡتِهَآۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ *وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ 

67. Page

أَن تَقُومَ ٱلسَّمَآءُ وَٱلۡأَرۡضُ بِأَمۡرِهِۦۚ ثُمَّ إِذَا دَعَاكُمۡ دَعۡوَةٗ مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ إِذَآ أَنتُمۡ تَخۡرُجُونَ * وَلَهُۥ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ كُلّٞ لَّهُۥ قَٰنِتُونَ * وَهُوَ ٱلَّذِي يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّيُعِيدُهُۥ وَهُوَ أَهۡوَنُ عَلَيۡهِۚ وَلَهُ ٱلۡمَثَلُ ٱلۡأَعۡلَىٰ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِوَٱلۡأَرۡضِۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

[1]

Da sannu za a bayyana a cikin wannan shu’a’i na tara dalili mai girma da hujja maɗaukakiyana wannan ayoyi masu girma saukakku daga samawannan da suke nuni i zuwa wanirukuni daga rukunanimani da waɗannan dalilai masu girma masu tsarki wannan da suke tabbatar da tashin alƙiyama.

Wannan keɓantace ta ubangiji tattausa: cewa kafin shekara talatin daga yanzu Sa’idu na ya ce a cikin manufa ta biyu na manufofin Alƙur’ani a cikinƙarshen littafin“Muhakamat”ababin rubutawa wannan da ya rubuta shi a matsayingabatarwata tafsiri:“da sannu za a fassara za a bayyana ayoyi biyu da suke nuni zuwa tashin alƙiyama”, sai ya faɗi misali:بِسۡمِ ٱللَّهِٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمsai ya tsaya, bai samu damar ya cigaba da rubutu ba , godiya ta tabbata ga Mahaliccinamai Jin-ƙai da adadin dalilai da alamomi da suke nuni zuwa ga rayarwar nan tatashin alƙiyama  a bisa cewa shi ya kyautata gare ni da ya datar da ni bayan shekara talatin.

 


[1]{Saboda haka tsarkakewa ta tabbabta ga Allah a lokacin da kuke shiga maraice da lokacin da kuke shiga safiya.Kuma godiya tasa ce a cikin sammai da ƙasa da lokacin yammaci da lokacin zawali.Yana fitar da mai rai daga matacce, kuma yana fitar da matacce daga mai rai, kuma yana rayar da ƙasa bayan mutuwarta,kuma kamar haka ake fitar da ku (daga ƙaburburanku).Kuma akwai daga ayoyinSa Ya halicce ku daga turɓaya, sai ga ku kun zama mutum, kuna watsuwa.Kuma akwai daga ayoyinSa Ya halitta muku matan aure daga kanku domin ku nutsu zuwa gare su, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani. kuma akwai daga ayoyinSa.halittar sammai da ƙasa, da saɓawar harsunanku da launukanku.Lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga masu sani.Kuma akwai daga ayoyinSa Barcinku a cikin dare da rana, da nemanku ga falalarSa Lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu saurarawa.Kuma akwai daga ayoyinSa Ya nuna muku walƙiyaa don tsoratarwa da kwaɗaitarwa, kuma Ya dinga saukar da ruwa daga sama, sa’an nan Ya rayar da ƙasa da shi bayan mutuwarta Lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu hankaltuwa.Kuma akwai daga ayoyinSa,tsayuwar sama da ƙasa bisa umarninsa sa’an nan idan Ya kira ku, kira ɗaya, daga ƙasa, sai ga ku kuna fita.Kuma wanda ke cikin sammai da ƙasa Nasa ne, Shi kaɗai.Dukansu masu ƙasƙantar da kai ne gare Shi.Kuma Shi ne wanda Ya fara halitta, sa’an nan ya sake ta, kuma sakewarta ya fi sauƙi a gare Shi,Kuma Yana da misali wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasa, kuma Shi ne Mabuwayi,Mai jin ƙai.}[Ar Rum:17-27].

 




68. Page

Haka yake, haƙiƙa cewa shi Mai girma da ɗaukaka ya yi ni’ima a gare ni tun kafin shekara tara ko goma daga yanzu da“kalma ta goma” da kuma “kalma ta ishirin da tara” waɗannan su biyu da suke ɗauke da hujjoji mabayyana maɗaukaka masu ƙarfi ƙwarai, ga ɗaya daga waɗannan ayoyi biyu na dokokin Ubangiji da tafsirinta kuma ita ce

فَٱنظُرۡ إِلَىٰٓ ءَاثَٰرِ رَحۡمَتِ ٱللَّهِ كَيۡفَ يُحۡيِ ٱلۡأَرۡض بَعۡدَمَوۡتِهَآۚ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِير

[1]

sai na toshe bakin masu inkari.


[1]{Sai ka yi duba zuwa alamomin rahamar Allah yadda Yake rayar da ƙasa bayan mutuwarta.Lalle wannan (Mai wannan aiki), tabbas Mai rayar da halitta ne, kuma Shi Mai iko ne a kan kowane abu}[Ar Rum:50].




69. Page

kuma sai aka yi min karamci bayan shekaru tara ko goma daga waɗannan sansanoni masu ƙarfi na aƙidar tashin alƙiyama da wannan- wasiƙa mai fassarawa ga ayoyin nan masu girma ababan Ambato waɗanda ita ce aya ta biyu.

To wannan shu’a’in na tara ya ƙunshi muƙamai tara masu girma da gabatarwa mai muhimmanci da yake nuni i zuwa gare ta a cikin ayoyi waɗanda aka ambata.

Gabatarwa:Nuƙuɗoɗi biyu suna nuni a kan bayanin fa’idoji na ruhi masu matuƙar yawa ƙwarai na aƙidar nan ta tashin alƙiyama,da natija mai tattarewa daga natijojinta wadda ta shafi rayuwaa taƙaice, kuma da bayyanawar matuƙar larurarta da lazamtarta ga rayuwar mutum musanmam rayuwarsa a cikin al’umma da bayyanawar hujja matattariyadagatsakankanin hujjojin Akidar imani da tashin alkiyama masu matuƙar yawa a dunƙule,da bayyanawa cewa waccan a Aƙidar can ta tashinalƙiyama a fili take ba tare da wani kokwanto ba a cikinta.


70. Page

Nuƙuda ta farko :Muna nuni i zuwa dalilai huɗu-kamar magwajine-daga tsakanin ɗaruruwan dalilai waɗannan da suke shiryarwa a bisa haƙiƙa aƙidar lahira ita ce tushen asasin rayuwar al’umma da rayuwar ɗaidaiku ta mutun, kuma ita ce tushen arzikinsa da jin daɗinsa kuma da cikarsa.

Dalili na farko: Yara ƙananawaɗanda suke kusan su ne rabin mutaneba za su iya juriya a gaban gawawwaki da mutuwa ba wannan da take bayyana a gare su kamar wata abar tsoro mai sa kuka sai dai da tunanin aljanna,kuma za su iya samun ƙarfi na ma’ana da wannan tunanin a cikin zuciyar nan tasu mai rauni da tabshi ƙwarai, kuma suke iya samun buri da raja’i da tunanin aljanna a cikin rayukansu raunana ƙwarai da suke kuka da sauri daga dukan wani abu da yake motsa zuciya, hakan ne zai sa su su rayu a cikin farin ciki da murna. 


71. Page

To misali: Yana faɗa da tunanin nan na aljanna: ɗan’uwana ƙarami ko abokina ya rasu ya zama tsuntsu daga tsuntsayen Aljanna, yana kewayawa a cikin ta yana rayuwa yana jin daɗi fiye da mu; idan bahaka ba sai rasuwar waɗanda suke kewaye da su daga yara ko manya za ta gigitar da duban waɗannan miskinan raunana masudamuwa, kuma ta rusa ƙarfin su na ma’ana, Sannan tasasu kuka da idanuwan su bari da ruhinsu da zuciyarsu da hankalinsu, Sannan su kodai su tozartu , ko kuma su zama kamar wata dabba marar arziki wulaƙantacciya yasasshiya.

Dalili nabiyu:Tsofaffi da gajiyayyuwaɗanda su -daga wata nahiya- rabin adadin mutane neda tunanin rayuwar lahira kaɗai suke iya juriya a gaban kabari da yake kusa da su, kuma suke iya samun haƙurƙurtarwa amaimakon ƙarewar rayuwarsu a nan kusa, wannan da suke sonta, kuma suke rataye da ita da ƙarfi,da kuma maimakon rufewar duniyar su, mai kyau,da burin nan na rayuwa wanzanjiya ne kawai suke iya tsayawa da juriya a gaban ɗeɓe ƙauna mai firgitarwa mai tasowa daga mutuwa da gushewar rayukansu da halin yanayinsu mai tabshi, wanda ya cuɗanya da rauni, wannan da ya zama kamar yaro ƙarami da yake da saurin tasirantuwa.


72. Page

Idan bahaka ba zai kasance waɗannan maɗaukaka abin girmamawa waɗannan da suka cancanci a tausaya musu, da iyaye maza da uwaye mata da suke cikin damuwar halaka waɗannan da suke buƙatuwa i zuwa nutsuwa da hutun zuciya sosai za su ji Kururuwar nan ta rayuka da baƙƙan ciki da shagulgula na zuciya, da za su saduniya ta zama kurkuku a gare su, rayuwa kuma ta zama azaba mai tsanani.

Dalili na uku: Matasa da samari su ne mafi ƙarfin ginshiƙi a rayuwar al’ummar mutane, kuma abin da yake tsayar da shu’uransu masu tafasa da zaɓalɓala, da zukantansu da soye-soyen zuciyoyin su masu wuce gona da iri dagaƙetare iyaka da zalunci da rusa abubuwa, kumaabin da yake sanya rayuwar al’umma ta tafi a matafiyar ta ta ɗabi’a shi ne tuna jahannama, idan ba don tsoron jahannama ba da waɗannan matasa masu maye masu bin son zuciyoyinsu da kwaɗayinsu sun maida duniya ta zama Jahannama a haƙƙin nan na raunana miskinai gajiyayyu gwargwadon ƙa’ida “hukunci yana tabbata ga mafi rinyaje” kuma da sun maida mutuntaka maɗaukakiya zuwa ga dabbantaka mai matuƙar ƙasƙanci.

Dalili na huɗu: Cibiyar da ta fi tattarowa da wajen tasowa mafi ƙarfin tushe, da Aljanna da madogara da hanya don neman arziki da jin daɗin duniya a cikin rayuwar 

73. Page

duniya ga nau’in mutum; ita ce rayuwar nan ta iyali, cewa gidan kowanne mutum shi ne duniyarsa ƙarama,rayuwar wannan gidan da rayuwar wannan iyalin da arzikinsu da jin daɗinsu ana samunsu ne ta hanyar girmamawa tatacciya mai ƙarfia cikin cika alƙawari, da kuma ta hanyar rahma ta haƙiƙa ma’abociyar tausayawa a cikin sadaukantarwa, wannan girmamawa tatacciya da jinƙai na gaske suna samuwa ne ta hanyar abokantaka ta har abada da zamantakewa dawwamamiya da haɗuwa ta sarmadan da kuma ta hanyar aƙida da tunanin - a bisa lokaci da ba shi da ƙarshe da rayuwa da ba ta da iyaka - samun zamantakewa a tsakaninsu wadda take cike da iyayantaka da ‘ya’yan taka da ‘yan’uwantaka da abokantaka. 


74. Page

Misali yana faɗi: Haƙiƙa matata; ita ce abokiyar rayuwata ta har abada a cikin alam da rayuwar ta har abada, to babu laifi ko da ta zama tsohuwa mummuna yanzu; domin cewa tana da wani kyau na har abada da zai zo.

 Zai iya kasance masa ya yi mu’amala da matarsa tsohuwa da soyayya da tausayawa da rahma kai ka ce wata tsaleliyar kyakkyawar mace ce, yana mai faɗin: haƙiƙa ni ina yin dukkan sadaukantar da kai da jin-ƙai saboda abokantaka madawwamiya kamar wannan, idan ba haka ba haƙiƙa waccan abokantaka wadda take haɗuwa da rabuwa na har abada bayan zamantakewa ta zahiri taƙaitacciya da take dawwama wasu ‘yan awanni da za ta iya haifar da – ba da wani kokwanto ba – jin-ƙai na mujazi da girmamawa ta ƙarya waɗanda suke ɗauke a zahiri da tausasawa ta neman biyan buƙata ta jinsi ta ɗan wani lokaci, wacce ba ta da tushe, kamar yadda take a wajen dabbobi.

Wasu amfanunnuka da wasu riskokin-ji na gaɓoɓi mafirinjaye suna rinjaye -kamar yadda yake a wajen dabbobi- a bisa wannan girmamawa da wannan jin-ƙai sai su juyar da waccan aljanna ta duniya i zuwa jahannama.

To wannan natija ɗaya ce daga ɗaruruwan natijojin imani da tashin alƙiyama wadda take da alaƙa da rayuwar mutum ta cikin al’umma, idan ka auna sauran natijojin daga ɗaruruwan fuskoki da fa’idodin wannan natijar ɗaya da waɗannan dalilai huɗu 

75. Page

cewa da sannu za a fahimci haƙiƙar tashin alƙiyama da abkuwarta gaskiya ne da daraja yankakkiya ta haƙiƙa maɗaukakiyata mutuntaka da dukkan buƙatunta baki ɗaya, kai ita -ai haƙiƙar tashin alƙiyama- mafi bayyanace daga shaida da shiryarwar samun buƙata ta wajen uwar hanjin mutum a bisa samuwar abinci, kuma tana ba da labari ga afkuwarta labari mafi ƙarfi sosai.

Kuma tana tabbatarwa cewa da natijojin haƙiƙar tashin alƙiyama suntsiraita daga mutuntaka, da gaskiyar mutuntaka wadda ita ce take cikin matuƙar muhimmanci da martaba da rayuwa ta faɗa i zuwa matsayin mushe maiyin wari kuma ta zama wajen kiwo ne na ƙwayoyin cuta.

To su ji da kunnuwansu waɗanda suka iya hulɗa da jama’a da ‘yan siyasa dama su sanina halayar ɗan’adam, waɗanda suke da matuƙar kula wajen gudanar da mutane da ɗabi’o’insu da tarurrukan suto saisuce mana dame za su cike wannan giɓin, kuma dame za su warkarda waɗannan raunukan masu zurfi?.


76. Page

Nukɗa ta biyu: Tana bayyana dalili ɗaya daga dalilan haƙiƙar tashin alƙiyama waɗanda ba su da iyakayana samuwa daga tatattun shaidunda suke tasowa daga sauran rukunan imani.

Domin dukkan mu’ujizojin shugabanmu Annabi Muhammad -tsira da amincin su tabbata a gare shi- waɗanda suke shiryarwa kan manzancinsa, da dukkan dalilan Annabtarsa, da dukkan dalilai da suke shiryarwa kan gaskiyarsa da cancantarsa dukkansu-da tarayyarsu-suna shaidawa kan tabbatar nan ta haƙiƙar tashin alƙiyama kuma suna tabbatar da ita; domin cewa dukkan mas’aloli na wannan Manzon a cikin dukkan rayuwarsa suna tattaruwa ne a cikin tashin alkiyamabayan tauhidi,kuma dukkan mu’ujizozinsa da hujjojinsa waɗannan da suke gasgata dukkan annabawa kuma suke sanya mutane su gasgatasu suna shaida  a bisa wannan haƙiƙar kanta.

Kuma haƙiƙa shaidarsaكتبه da littattafansawadda ke ɗaga shahadarnan da take zuwa bayan kalmaرسله da imani da manzanninsa i zuwa darajar fahimta a fili ita ma tanashaida kan haƙiƙar nan kanta;domin cewa haƙiƙa dukkan mu’ujizozin Alƙur’ani, 

77. Page

mai mu’ujizarbayani, kuma da haƙiƙoƙinsa da hujjojinsa waɗanda suke tabbatar da cancantarsa dukkansu tare da tattarowarsu suna shaidawa kan tabbatar haƙiƙar tashin alƙiyama da abkuwarta kuma suna tabbatar da ita; domin ɗaya bisa uku na Alƙur’ani yana magana a kan tashin alƙiyama, kuma haƙiƙa cewa dukkan mafi yawan gajajjerun surorinsa suna farawa da ayoyin tashin alƙiyama masu ƙarfi ƙwarai, kuma Alƙur’ani da dubunnan ayoyinsa na ba da labari a fili da isharori kan ainihinhaƙiƙar kuma yana tabbatar da ita da bayyana ta.

A misali: haƙiƙa shi yana nuni a cikin farkon sura talatin ko arba’in zuwa cewa haƙiƙar tashin alƙiyama ita ce -da dukkan tabbatuwarta- haƙiƙa mafi muhimmancin daga tsakankanin haƙiƙoƙin nan na halitta, kuma ita haƙiƙa ce wajiba, wannan shi ne misalin waɗannan surori:

[1]إِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَتۡ

[2]يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡۚ إِنَّ زَلۡزَلَةَ ٱلسَّاعَةِ شَيۡءٌ عَظِيم

إِذَا زُلۡزِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ زِلۡزَالَهَا[3]

إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنشَقَّتۡ

[4]

إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتۡ

[5]

عَمَّ يَتَسَآءَلُونَ

[6]

هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلۡغَٰشِيَة[7]ِ


[1]{Idan rana aka shafe haskenta}

[2]{Ya ku mutane! Ku ji tsoron Ubangijinku.Lalle ne girgizar ƙasa ta tsayuwar Alƙiyama wata aba ce mai girma}

[3]{Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta}

[4]{Idan sama ta tsage}

[5]{Idan sama ta kece}

[6]{A kan me suke tambayar juna}

[7]{Lalle ne labarin (Ƙiyama) mai rufe mutane da tsoronta ya zo maka}




78. Page

Kuma yana bayyana dalilai nau’i-nau’i ga waccan haƙiƙa a cikin wasu ayoyin da ke sa a gamsu da ita.

Ya jama’a! abin mamaki! Shin zai yiwu ta kowacce irin fuska; a ce imani da tashin alƙiyama-wanda yake bayyana kamar rana da dubunanshaidu- kamar yadda aka ambata a baya- a cikin littafi wanda isharar aya ɗaya daga ayoyinsa tana haifar da 

79. Page

haƙiƙoƙi masu yawa na ilimin zamani da ilimin addini a gaban idanuwanmu- ba gaskiya ba ne?!

Shin wannan ba zai zamakamar musun samuwarranace ba ko kamar cewa babu kasantattu ne?! Shin wannan ba zai zama korarre ne mara yiwuwa ne da ɗaruruwan darajoji?

Ya jama’a! Shin yana daga abin da zai yiwu daga kowacce fuska daga fuskoki ƙaryata dubunan zantuka da alƙawarurruka na ni’ima da na narko na Sarki mai matuƙar girmamawa da Buwaya a cikin lokacin da runduna cikakkiya take motsawa take yaƙi wani lokaci har dai don kada ta kasance ishara ɗaya ta sarkin ƙarya ce! Shin zai yiwu dubunnan zantukansa da alƙawarukansa da kashedodinsa su zama ba gaskiya ne ba?

Idan ya kasance ishara ɗaya ta wannan sarki na ma’ana ma’abocin sha’ani, wandaya mamaye abin da ba shi da iyaka na rayuka da hankula da zuciyoyi da zukata a cikin kewayen gaskiya da haƙiƙa,kuma ya rene su yake gudanar da al’amuransu har tsawon ƙarni goma sha uku ba tare da yankewa ba mai isa ce don tabbatar da haƙiƙa kamar wannan; kuma ya ku jama’a! Shin al’amarin ba zai lazamci azabar jahannama ga wawa, jahili da ba ya sanin wannan haƙiƙa ba bayan ya bayyanataya tabbatar da ita-wancan sarki – da dubunnan bayanai a fili?! Shin yin hakan ba zai zama ainihin adalci ba? 


80. Page

Sannan haƙiƙa bayanin dukkan littattafai saukakku daga sama da littattafai tsarkaka waɗannan da suka yi hukunci a bisa zamani daga zamuna, da rawa daga raye-rayen da suke takawa daidai gwargwadon lokacinsuda zamaninsu tare da yarda da waccan haƙiƙar yarda tabbatacciya; haƙiƙarnan ta tashin alƙiyama wandaya bayyanata kuma ya tabbatar da ita da rarrabewa da fito da ita fili da maimaitawa Alƙur’ani wanda ya mamaye a bisa dukkan abin da zai zo nan gaba da dukkan zamuna,muna faɗi, haƙiƙa yin da’awarsu da tabbatarwarsu waɗannan gaskiyoyinda kamanni mai ƙarfi tareda

81. Page

bayaninsu ba tare da rarrabewa ba, da taƙaitawa da kuma karewa; zai gasganta da’awar Alƙur’ani da dubbannan na sitamfai.

Ana sa wa a nan don dacewa da wannan binciken shaidar sauran ginshiƙai, balle ma a ce shaidar ginshiƙin “imani da manzanni da kuma littattafai” a bisa ginshiƙin “imani da ranar lahira” wanda aka ambata a ƙarshen “Risalat zantawa” wadda hujja ce daga hujjojin tashin alƙiyama wannan da aka ambaceta a cikin surar zantawa[1], kuma mai ƙarfi ce sosai taƙaitacciya, tana gusar da dukkan wahamai, an sata a nan kamar yadda take.


[1] A cikin yanayi na munajati.




82. Page

Haƙiƙa ya faɗa a cikin zantawa kamar haka:-

YaUbangiji na mai jin–ƙai, haƙiƙa na fahimta ta hanyar koyarwarnan ta Manzo mai girma da darasin Alƙur’ani mai hikima haƙiƙa dukkan littattafai masu tsarki da Annabawa, da wanda yake a kan gabansu Alƙur’ani da Manzon mafi girma tsira da aminci su tabbata a gare shi suna shaidawa suna shiryarwa suna nuni da haɗuwa da ittifaƙi zuwa haƙiƙa tajalliyoyin nan na sunaye masu jalala[1] da sunaye masu kyau[2]waɗannan da a ke ganin misalansu a cikin kowanne waje a cikin duniyar nan, za su ci gaba cikin abadan har abadan da sura mafi bayyana mafi haskaka, kuma i zuwa kyautace-kyautacenka, wannan da ake ganin su a cikin wannan duniya mai ƙarewa tajallinta da misalanta waɗanda suke a cike da rahama da sannu za su zama wanzazzu,sannan za su dinga cigaba cikin gidan arziki da jin-daɗi a cikin mafi kwarjini da kyawun sura, kuma zuwa cewa masu tsananin soyayya waɗannan da suke ganin waccan kyautayinta hanyar jin daɗi, kuma suna binshi tare da soyayya a cikin wannanrayuwar ta duniya taƙaitacciya, da sannu za su zama tare da shi cikin alaam na har abada sannan za su kasance tare da shi.


[1]Sunaye da suke nuna isar ubanglji da ikonsa.

[2] Sunayen ubangiji wadannda suke tasiri a kan abubuwa masu daxi.




83. Page

Sannan dukkan Annabawa waɗannan da su ne ma’abota rayuka haskaka- a gabansu Manzo mai girma tsira da aminci su tabbata a gare shi da Alƙur’aninka mai hikima- masu dogara ga ɗaruruwan mu’ujizozinsu ƙayatattu da ayoyinsu masu kafa hujjoji, haƙiƙa dukkan waliyai ma’abota zukata masu haske, dasiddiƙai, ma’abota hankula masu zarcewa ma’abota wayayyiyar basira mai rinjaye mai haske mai haskakawa, suna yi wa mutane albishir da samun arziƙi da jin daɗi na har abada suna masu dogara i zuwa dubunnan alƙawarurrukan rahamarka da alƙawarurrukan azabarka wanda ka ambace su da mai-maitawa a cikin dukkan littattafai saukakku daga sammai da littattafaimasu tsarki, kuma suna masu dogara  a bisa siffofinka da sha’anoninka masu tsarki wanda suke tabbatar da samuwar lahira,kamar iko da rahma da kula ta musamman da hikima da jalala da jamala,kuma sunadogaro  a bisa buwaya ta jalalarka da mulkinka na kula da halittarka, da gini abisaabin da  ba shi da iyaka na abin da aka yaye musu da abubuwan da suke ganiwaɗannan da suke bayyana  a bisa guraban nan na lahira da alamominta, da gini  a bisa ƙudurorinsu da 

84. Page

imaninsu wannan da ya sadu da darajar ilmin yaƙini da kuma ainihinyaƙini,da suke ba da labari suke bayyanawa cewa akwai jahannama ga ɓatattu, da aljanna ga ma’abota shiriya, sun yi imani da su imani tabbatacce, sun shaida, shaida mai ƙarfi.

Ya maiiko ya maihikima,ya mairahama yamaijinƙai, ya mai gaskiyar alkawari ya maikaramci, ya mai rinjaye ma abocin girmame- girmame da ma’abocin buwaya da girma, haƙiƙa kai mai tsarki ne da dubunnan ɗaruruwan daraja, maɗaukaki netsarkakke ne tsarkaka da ɗaukaka waɗanda sun tsarkaka daga ƙaryatawa daga waliyanka masu gaskiya, kuma har i zuwa wannan iyaka daga alƙawarurrukanka, haka i zuwa wannan iyaka na daga siffofinka da sha’anoninka, kuma daga ƙaryatawa abubuwa yankakku da suke lazamtar sarautar nan ta rububiyyarka, kuma da rashin tsayuwa da waɗannan ababan lazamtarwar, da kuma ƙin karɓa da rashin ji ga waɗanda ba su da iyaka na daga addu’o’i da kiraye-kiraye mai fuskantuwa i zuwa lahira na daga waɗannan da ba su da iyaka na bayinka 

85. Page

karɓaɓɓu a nan wajenka,da waɗannan da kake sonsu, su kuma da irin rawar da suke takawa suke soyar da kansu gare ka ta hanyar gasgataka da yi maka biyayya, kumada gasgata ma’abota ɓata da ma’abota kafirci waɗannan da suke shafar cutar da -da kafirci da saɓo da ƙaryataka a cikin alƙawarinka- girmame-girmamenka, da suke munanawa buwayar ɗaukakarka, suke munana buwayar Allantakarka, suke cutar da tausayawar nan ta ubangijantakarka, kuma daga tabbatar waɗannan a cikin inkarin tashin alƙiyama.

Muna tsarkake adalcinka na saki-ba-ƙaidi, da kyaun nan naka na saki- ba-ƙaidi, da rahamarka ta saki-ba-ƙaidi, tsarkaka ta saki-ba-ƙaidi daga zalunci na saki-ba-ƙaidi kamar wannan, da muni na saki-ba-ƙaidi kamar wannan. kuma mun yi imani da dukkan ƙarfinmu cewa haƙiƙa shaidar dubunnan ɗaruruwa na manzanni masu gaskiya da Annabawa da tsarkakan bayi da waliyai masu kira ne ga sanin girman mulkin ubangiji masu gaskiya waɗannan da ba su da iyaka da gaskiyar yaƙini da ilmin yaƙini da ainihin yaƙini  a bisa taskokin nan na rahamarka ta lahira, da a bisa taskokin nan na kyautaye-kyautayenka a cikin duniyar nan ta wanzuwa, da  a bisa tajalliyoyi masu kyau masu ƙayatarwa na sunayen nannaka kyawawa waɗannan da suke tajalli a cikin gidan nan na arziki da jin-daɗi tajalli cikakke; gaskiya ne da haƙiƙa, kuma isharorinsu masu gaskiya ne kuma masu dacewa ne,busharorinsu suma na gaskiya ne kuma masu abkuwa ne tabbas.


86. Page

Kuma su sun yi imani cewa mafi girman haske na sunan Alhaƙƙu -wannan da shi ne makomardukkan gaskiya da ranarta da mai kareta shi ne haƙiƙar tashin alƙiyama babba. kuma suna koyar da bayinka wannan haƙiƙa da umarninka a cikin da’irar nan ta gaskiya,kuma suke koya musu ita kanta kamar ainihin nan na gaskiya.

Ya ubangiji ka arzurtamu, ka arzurta ɗaliban Rasa’il nur, da imani cikakke, da kyakkyawan ƙarshe don gaskiya da alfarmar darussa da koyarwar waɗancan ka arzurtamu cetonsu, amin. 


87. Page

Kamar yadda cewa dukkan dalilai da hujjoji waɗannan da suke tabbatar da gaskiyar Alƙur’ani da cancantarsa kuma da gaskiya da cancantar dukkan littattafai saukakku daga sammai, da dukkan mu’ujizozi da dalilai, waɗanda suke tabbatar da annabtar masoyin Allah, da kuma annabta, dukkan annabawa suna shiryarwa a cikinlokacin kansa a bisa tabbatar lahira wadda ita ce al’amarinsu mai girma;hakanan cewa mafiyawan dalilai da hujjoji waɗannan da suke shaida a bisa samuwar wanda samuwarsa ta zama wajibi ne da kaɗaitakarsa, suna shaidawa a cikin wannan lokaci kansa bisa samuwa da buɗewar gidan arziƙi da jin daɗi da duniyar wanzuwa waɗanda su ne mafi girman kewaye da wajen bayyana rububiyya da uluhiyya. 

88. Page

Domin cewa samuwar zati wanda samuwarsa ta zama wajibice da dukkan siffofinsa -kamar yadda da sannu za a bayyana kuma za a tabbatar a cikin muƙamai masu zuwa- da mafi yawan sunayensa da siffofinsa da shu’unansa, kamar rububiyya da uluhiyya da rahma da kulawa da hikima da adalci; sunatabbatar da samuwar lahira da darajar lazamta, suna lazamtar dasamun duniyar wanzuwa da darajar wajabci suna buƙatuwa i zuwa hashri[1]da faruwar tashi bayan mutuwa,don yin sakamako da kyakkyawa da narko da uƙuba har zuwa matakin tilas.

Na’am; domin cewa haƙiƙa Allahna tunfil-azal da har abada yananan; to babu kokwanto cewa haƙiƙa lahira ba ta gushewa a wajen mulkin ubangijantaka samammiya ce.

Domin cewa haƙiƙa akwai ubangijantaka[2] ta saki-ba-ƙaidi a cikin matuƙar girma da hikima da tausayi da ake ganinta a cikin wannan halitta da a cikin ma’abota rayuwa; tobabu kokwanto cewa shi, da sannu zai zama akwai gidan arziƙi da jin daɗina har abada da yake tseratar da girman wannan ubangijantaka daga saraya da

[1]Sake tarowa da sake dawowa da mutane rai.

[2] Halittar abin halitta da renonsa da tanada masa duk abubuwan da suke buƙata.




89. Page

ƙasƙanci,da kuma hikimarta daga wasa mara fa’ida, da tausayinta daga yaudara, da za a shiga cikinsa shi wancan gidan.

Tare da cewa babu iyaka a gare shi na nau’o’in ni’ima da kyautatawa da tausasawa da karramawa da kula ta musamman da rahama da ake ganinsu ƙuru-ƙuru da idanuwa suna nuna samuwar mai rahma mai jin–ƙai bayan hijabi na gaibi ga hankula wanda ba su biceba da zukata waɗannan da ba su mutu ba; tobabu kokwanto zaizama akwai rayuwa wanzajjiya a cikin duniyar wanzuwa da take tseratar da ni’imtarwadaga izgilanci, da kyautatawa daga yaudara, da kulata musamman daga gaba, da rahma daga azaba, da tausasawa da karramawa daga wulaƙanci, kuma za ta sanya kyautatawa ta zama kyautatawa sosai ni’ima ta zama ni’ima sosai. 


90. Page

Tare da cewa alƙalamin ƙudura ya rubuta littattafai dubu ɗari masu shiga juna ba tare da kuskure ba a cikin lokacin kaka a cikin ƙaramin shafi mai ƙunci na fuskar ƙasa, yana aiki a gaban idanuwanmu ba tare da wahala da gajiya ba;Duk da cewa mai wannan alƙalamin yayialƙawari sau dubu ɗari ya ce ni zan rubuta muku littafi ƙayatacce dawwamanme a cikin yalwataccen waje ta hanya mafi sauƙi na daga littafin kaka wanda aka rubuta a cikin cuɗanya da cakuɗa a cikin wannan wajen takurarre kuma da sannu zan karantar da ku shi, kuma yana magana a cikin dukkan dokokinsa a kan wannan littafin;to babu shakka ba kokwanto asalin wannan littafin haƙiƙa an rubuta shi, da sannu za a rubuta hawamishansa[1]da sharhunansata hanyar taro mutane da dawo musu da rai,da sannu za a rubuta ayyukan dukkan samanmu, a cikinsa

Tare da cewahaƙiƙa wannan ƙasar ta fuskar yawan halittu a cikinta ta yadda ita ce mazaunin ɗaruruwan dubunnai na nau’o’i masu yawa na daga ma’abota rayuwa da ma’abota rawuka masu sabuntawa ko da yaushe,da mafararsu da masana’antarsu ce da wajen baje kolinsu ne da wajen taso su, kuma itacezuciyar kasantattu da cibiyarsu

[1]Bayanan kasan littafi.




91. Page

da matatarsu da natijarsu ce da dalilin halittarsu;saboda haka ne tana da muhimmanci mai girma a tare da ƙanƙantarta tana daidaitar waɗannan sammai masu girma; saiace a cikin dokokin da suka sakko daga sama ko da yaushe:رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ[1].

Tare da cewaakwai nau’i na ɗan’adam wanda ya hukunta dukkan geffen ƙasa wadda ita ce take a bisa wannan kama,kuma yana tasarrufi a cikin mafi yawan kasantattunta, yake sauwaƙewa mafiya yawan samanmunta ma’abota rayuwa,yake sanyasusunakewaye da shi, kuma yana tsara mafi rinjayen ababan ƙerawarta kuma yake bijiro su yake ƙawatasu; a cikin matuƙar ƙayatarwa da kyau da ƙirar irin wadda ta dace da abin da yake so da abubuwan da yake ƙwaɗayinsu da dokokin buƙatunsa, kuma yanataro nau’o’inta waɗannan da su nekayayyaki masu daraja da tsada da ƙaranci ƙwaraia cikin waɗansu gurabe Kai ka ce shi yana shiryata a cikin firasa da ƙawatata, ta yadda haƙiƙa shi zai samu muhimmanci da ƙima mai girma ƙwarai,ba da jawo kallon mutane da aljanu kaɗaai ba, bari da jawo hankula da girmamawar ma’abota sammai da waɗannan kasantattun,da kuma jawo duban yabawa na ma’abocin wannan halitta, da wannansiffar ne yake bayyanawata hanyar ilmansa da fannoninsa cewa shi ne hikimarƙera wannan kasantattun da natijarsu mafi girma da amfaninsu mai ƙima,kuma cewashi halifan ƙasane,kuma ana barinsa a cikin wannan duniya ana jinkirta masa azaba duk da saɓonsa da kafircinsa;don cewa shi daga mafuskanta ta duniya yana bijirowayana tsarawa maƙayatan ƙere-ƙere ma’abota mu’ujizozi- na maƙerin duniya bijirowa da tsarawa ƙayatattu,ana jinkirtamasa saboda waɗannan hidimomin nasa, sai a datar da shi.


[1](Ubangijin sammai da ƙassai)

 

 




92. Page

Tare da cewa akwai mai tasrifi mai iko da hikima da tausayi na saki-ba-ƙaidi da ya sanya wannan duniya mai girma ga nau’in nan na ɗan’adam sama da ƙarfinsu da zaɓinsu dukka kumawannan shi ne ainihinsu,tare da cewa su masu rauni ne gajiyayyu ne ƙwarai ta wajen zubin halittarsu da halittarsu, kumasuna da buƙatu da raɗaɗɗuka da ba su da iyaka tare da matuƙar gajiyawarsu da talaucinsu… Ina faɗa haƙiƙa shi ya sanya duniyamai girma kamar wajen ajiya ga dukkan nau’i na nau’ukan ma’adanai waɗannan da suke abubuwan buƙata ne na dole ga nau’in mutum,kuma runbu ga kowanne nau’i na daga nau’ukan abubuwan ci, kuma kanti da yake ɗauke da dukkan nau’o’i na kayayyaki waɗanda nau’o’in mutane suke jin daɗinsu, to haka shi yake kiwon nau’in mutum, yake ciyar da su, yake ba su abin da suke so. 


93. Page

Tare da cewa ubangiji da wannan haƙiƙar yake son mutum, yake soyar da kansa ga mutum, kuma tabbas shi wanzajje ne, yana da duniyoyi wanzazzu, yana aikata komai da adalci, da hikima, haƙiƙa wannan rayuwar ta duniya taƙaitacciya da rayuwan mutuntaka taƙaitacciya ƙwarai da wannan ƙasar abar sawa lokaci mai ƙarewa bata yalwatar girman mulkin wannan mai hukunci na azal da hukuncinsa na har abada,kuma shi zalunci da laifuffuka masu girma waɗanda jinsin ɗan’adam yake aikata su, da waɗannan da suke korewa suke saɓawa tsarin halitta da adalcinsa da daidaituwarsa da kyaun kyaunsada wulaƙancin mutum da inkarinsa da kafircewa majiɓincin ni’imarsa da wanda yake arzurta shi da tausayi,dukkan wannan yana zamaba tare da uƙuba ba a cikin wannan duniyar, sai azzalumi mai tsananin zalunci yake rayuwarsa a cikin hutu, kuma miskini wanda aka zalumta yake rayuwarsa a cikin wahalhalu,amma ainihin adalci na saki-ba-ƙaidi wannan da ake ganin alamunsa a cikin dukkan halitta, mai saɓawa ne dukka ga daidaita azzalumai masu tsananin zalunci tare da ababan zalunta, masu ɗeɓe ƙauna su daidaitu mutuwa ba tare da tashi ba a wani karon ba, ba za ta yarda da ita ba.


94. Page

Tare da cewa ma’abocin wannan halittar, kamar kai ka ce shihaƙiƙa ya zaɓi ƙasa daga kasantattu, kuma nau’in mutane daga ƙasa, ya  ba shi muƙami mai girma, ya  ba shi muhimmanci mai girma ƙwarai, to haka nan ya zaɓi annabawa da waliyai da tsarkakakku zaɓaɓɓu waɗanda su mutane ne na gaskiya daga tsakankanin nau’in mutun wanda suke dacewa da manufofin nan na ubangijantakarsa kuma suna soyar da kawukansu i zuwa gare shi ta hanyar imani da miƙa wuya,sai ya sanya su waliyai masu sauraron zancensa , kuma ya girmamasu da mu’ujizozi da dacewa, kuma ya azabtar da maƙiyansu da bugu na sama, kuma ya zaɓa a tsakankanin waliyansa masu girma ababan so Muhammad alaihissalam shi ne shugabansu abin alfaharinsu, kuma ya haskaka da haskensa -tsira da aminci su tabbata a gare shi, a tsakankanin ƙarnoni masu tsayi rabin duniya mai muhimmanci, da ɗaya daga cikinbiyar na nau’ikan mutane masu muhimmanci,don dukka abubuwan nufi suna bayyana ta hanyarsa da addininsa da Alƙur’aninsa kai ka ce halitta an halicce tane saboda shi, kumahaƙiƙa an  ba shi lokaci taƙaitacce a cikin wahala da ƙoƙari mai wahala, a gwargwadon shekaru sittin da uku, tare da cewa shi ya can-canta ya samu ladan hidimominsa masu tsada da ba su da iyaka gwargwadon miliyoyin shekaru a cikin zamanin da  ba shi da iyaka. 


95. Page

Ya jama’a!Shin akwai wani abin da zai yiwu ko akwai wani kyakkyawan zato da za a yi ko wani ƙwaƙƙwaran shiri daga ko wadda fuska daga fuskoki donkada a aiko wannan manzo -tsira da aminci su tabbata a gare shi- tare da dukkan makamantansa da masoyansa?dakuma kada ya zama a yanzu rayayye ne irin rayuwar ruhi? ko arasar da su ta hanyar rasarwa ta har abada? yin haka ba zai yiwu ba sau dubu ɗari, kuma sam ba zai yiwuba.

Hakayake; haƙiƙa dukkan halitta da haƙiƙar alam suna buƙatadaga wajen mamallakin halitta ya raya shi.

Tare da cewa haƙiƙa shi an tabbatar da ijma’i talatin da uku masu girma -kowanne ɗaya daga cikinsu yana da ƙarfin dutse- ya zo a cikin wasiƙar “Aya mai girma” wadda ita ce “Haske na bakwai”, cewa haƙiƙa wannan halittar ta samu nedaga hannu ɗaya, kuma su abin mulka ne ga wannan da yake shi kaɗai ne, sun bayyana kai tsaye ɗayantaka da kaɗaitaka waɗanda su ne kewayen cikarsa, Kai ka ce dukkan halitta sun zama ta hanyar ɗayantaka da kaɗaitaka ƙarfin wancan ɗayan ne da ikonsa, 

96. Page

kaɗaitaka da ƙaddararsa, kuma dukkan ababan halitta rundunace masu biyayya ga umarninsa, kuma ma’aikata ne ababan ba wa umarni wanda aka sahhale su ga wannan ɗayan, tsarki da ɗaukaka su tabbata a gare shi, kuma cewa shida zuwan ranar lahira ne cikarsa take kubutadaga saraya,kuma adalcinsa na saki ba ƙaidi daga zalunci na saki ba ƙaidi a cikin izgili,da hikimarsa ta gaba ɗaya daga wasa a cikin wauta, da rahmarsa mayalwaciya daga azabtarwa a cikin wasa,da buwayar ikonsa daga gajiyawa a cikin ƙasƙanci, dukkansu suna tsarkaka; tobabu shakka babu kokwanto babu makawa haƙiƙadole ranar alƙiyama za ta tsaya, don lazamta haƙiƙoƙi da aka ambata a cikin“Tare da cewa ”takwas na daga cikin ɗaruruwan nuƙɗoɗi na imani da Allah,kuma haƙiƙa da sannu tayarwa daga kabari da tarowa za ta faru, kuma da sannu za a ɓuɗe gidan uƙuba da sakamako mai kyau har dai ta tabbatar da 

97. Page

muhimmancin ƙasa da muhimmancin kasancewarta cibiya ce wadda aka ambata acan da muhimmancin mutum da ƙimarsa,da tabbatar da adalci da hikima da rahma da sarauta ababan ambato ga mai jujjuyawa mai hikima mahaliccin ƙasa da mutum da mai rainonsu,kuma da kubutar waliyan wannan ubangijin wanzajje da masu shauƙi a gare shi na haƙiƙa daga rasuwa ta har abada, kuma mafi girman waɗancan waliyan da mafi muhimmancin su ya samu sakamakon alheri nahidimominsa tsarkakka wanda yakesa dukkan halitta su yarda, ya sanyasu masu godiya ne da ƙarfi,take tsaftata kuma take tsarkaka kuma take kuɓuta cikar nan ta sarki na har abada daga tawaya da taƙaitawa, da ikonsa daga gajiyawa, da hikimarsa daga wauta da adalcinsa daga zalunci. 


98. Page

A ƙarshe dai:Tunda cewa Allah yana nan; babu kokwanto haƙiƙa lahira samammiya ce.

Kamar yadda yake rukunan imani guda ukun nan da aka ambata suna shaidawa kan akwai tashin alƙiyama,kuma suna shiryarwa a gare shi da dukkan hujjojinsu wannan da suke tabbatar da su; haka nan rukunai biyu na imani waɗannan da su ne -rukunin imani da mala’ikunsa da rukunin imanida ƙaddara mai daɗinta da marar daɗinta daga Allah ne maɗaukaki- suna lazamtar da tashin alƙiyama suna shaidawa suna shiryarwa a bisa samuwaralam na wanzuwa da ƙarfi, kamar haka:

Haƙiƙa dukkan hujjoji da kallo da bayanai da ba su da iyaka da suke tabbatar da samuwar mala’iku da aikinsu na bauta,haka nan ma suke shiryarwa kan samuwar alam na rayuka da alam na fake da alam na wanzuwa da alam na lahira da gidan arziki da jin daɗi wannan da za a rayasu a nan gaba da mutune da aljannu kuma da samuwar aljanna da wuta; don cewa haƙiƙa mala’iku za su iya ganin waɗannan alam-alam da izinin ubangiji kuma za su shigesu,dukkan mala’iku makusanta waɗannan da suke haɗuwa da mutane kamar Jibirilu tsira da aminci su tabbata a gare shi suna ba da labarai suna masu ittifaƙi a bisa samuwar alam-alam waɗanda aka ambata ,kuma su suna zagayawa a cikin wadancan alam alam ɗin.


99. Page

Hakanan kamar yadda cewa mu mun sani kai tsaye samuwar yankin Amerika wadda ba muganta ba, da ba da labarin waɗannan da suke tahowa daga gare ta,haka nan imani yana wajabtar – da wannan tabbatar – da samuwar duniyar wanzuwa da gidan lahira da aljanna da wuta da labaran nan na mala’iku waɗannan da su ne suke da ƙarfin jerin ruwayoyi guda ɗari, to da haka nemuke imani.

Sannan haƙiƙa dukkan dalilai waɗannan da suke tabbatar da rukuninالإيمان بالقدرimani da ƙaddara a cikin “Risalar ƙaddara” wadda ita ce kalma ta “Ishirin da shida” haka nan suna shiryarwa kan tashin alƙiyama da barbazuwar takardu da auna ayyuka a cikin ma’auni mafi girma; domin cewa ƙayyadewa da rubuta abubuwan da aka ƙaddara na dukkan komai a gaban dubanmu a cikin allon tsari da awo, da rubuta abin dayake gudana a cikin rayuwar dukkan ma’abota rayuwa a cikin ƙwaƙwalwarsu da ƙwayoyin irinsu,kuma a cikin dukkan alluna na misalai, da rubuce littattafan nan na ayyukan dukkan ma’abota rai – balle ma a ce mutum – da tabbatar da shi a cikin alluna ababan kiyayewa; babu makawa cewa ƙaddara mai kewayewa kamar wannan da ƙaddarawa mai hikima da ƙayyadewa na sosai da rubutu na kiyayewa;dukkan wannan ba zai yiwu ba ya zama ba sai dai don biya da sakamako na dindindin, bayan 

100. Page

yin hukunci na kowa da kowa a cikin babbar kotu, idan ba haka ba da wannan ƙayyadewar mai kewayewarsosai da wannan kiyayewar sai su zama basuda wata ma’ana ko fa’ida, sai su zama masu saɓawa ne ta dukka ga hikima da haƙiƙa,idan tashin alƙiyama bai faru ba da dukkan ma’anonin littafin wannan halittar, wannan da aka rubuta suda alƙalamin ƙudura; ya gurɓata; domin hakan ba ya yiwuwa ta kowacce fuska daga fuskoki.

Wannan zaton ya koru, waɗannan sururin bayanan kamar inkarin samuwar wannan halittar ne.

A ƙarshi dai:Haƙiƙa rukunan imanin nan guda biyar suna shiryarwa da dukkan dalilansu kan samuwar tashin alƙiyama da tashin mutane da abkuwarsu da samuwar gidan lahira da buɗe shi, suna lazamtarsu suna shaidawa da su , suna nemansu.

Don cewa haƙiƙar tashin alƙiyama wannan yana da ginshiƙai da dalilai masu girma da ba sa raurawa, suna da cikakkiyar dacewa da girman tashin alƙiyama,haƙiƙa kashi ɗaya daga kashi uku na Alƙur’ani da bayaninsa yake gajiyarwa yana ƙunshe da zancen tashin alƙiyama da lahira, yana sanya su su zama dutse na tushen dukkan haƙiƙoƙinsa da tushen harsashinsa, ya gina dukkan komai a bisansu.

(Haƙiƙa na samu abar gabatarwa a ƙarshe).