Bayanin Bisamarik a cikin “Risalar Ahmadai biyu
NAVIGATION
125. Page
Bayanin Bisamarik a cikin “Risalar Ahmadai biyu”
Shugaban mu malaminmu mai girma.
Mun bijiro muku, shugabanmu, kuma malaminmu maganganun nan na yarima Bisamarik wanda yana cikin mashahuran masu hikimar ƙasar Jamus, maganganunsa
126. Page
da ya faɗe su kan addinai mabambanta musamman a kan musulunci, maganganunsa suna nuni i zuwa matuƙar da musulunci zai iya isa a cikin ƙasashen turai.
(Haiƙa ni na samu bayanin marigayi yarima Bisamarik ga addinai waɗanda aka shafe hukuncinsu gwargwadon tsokacina ga rayuwar al’umma, kuma da karatu na na abubuwanda aka rubuta aka yaɗa a cikin ƙarni na goma sha tara).
(Haƙiƙa nayi tsokaci mai zurfi a cikin dukkan littattafai da aka saukar daga sama waɗannan da ake yin da’awar cewa sun zo daga nan wajen Ubangiji don gudanar da al’amuran ‘yan’dam a cikin zamuna mabambanta,amma ban samu ba a cikin kowanne ɗaya daga cikinsu, wannanhikimar da nake nema ya faru ne, saboda canje-canje da karkatarwada ta gudana a cikinsu).
127. Page
Haƙiƙa waɗannan dokokin sun yi nisa dukkan nisa ga yalwatar da farin ciki da jin da-ɗi ga ‘yan’dam, koma-bayan Alƙur’anin mabiyaMuhammad alaihis salam. Haƙiƙa ni nayi tsokaci mai zurfi a cikin Alƙur’ani ta kowanne ɓangare da kowanne lungu; sai na ga a cikin kowacce kalma daga kalmominsa a kwai hikima mai girma.
Haƙiƙa maƙiyan Muhammad tsira da aminci su tabbata a gare shi, suna da’awar cewa wannan littafin yana daga abin da ya wallafa, sai dai haƙiƙa da’awar samuwar abu mai ƙayatarwa kamar wannan daga cikakken hankaliyana nufin ya zama mutum abin ƙullacewa ne da ƙi ko da an rufe ido daga haƙiƙoƙinsa, wannan yana saɓawa ilimi da hikima, haƙiƙa ni ina da’awar cewaAnnabi Muhammad tsira da aminci su tabbata a gare shi iko ne mai ƙayatarwa, kuma zaton hannun ƙudura ya ba da wani kamarsa zato ne manisanci.
Ya Muhammad S.A.W haƙiƙa ni ina mai baƙin ciki cewa ban sadu da kaiba, kuma littafin da kake yaɗawa ba yinka ba ne, kuma inkarin cewa wannan littafin na ubangiji ne, lamari ne mai ba da dariya kuma wasa ne kamar yarda ne da butulcewa haƙiƙoƙin ilmi, kuma haƙiƙa mutane sun ga ƙudura maiƙayatarwa kamarka sau ɗaya
128. Page
tak a rayurwarsu, kuma ba za su ga haka ba a karo na biyu, gini a bisa haka ni ina durƙusawa a gare ka tare da cikakken girmamawa.
Bisamarik.
129. Page
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
يا الله يا رحمنيارحيميافردياحي
يا قيوم يا حكم يا عدل يا قدوس[1]
Da haƙƙin sunan Allah mafi girma da alfarmar Alƙur’ani da bayanansa suke gajiyarwa,da girma daɗaukakar manzon mafi girma alaihis salamka azurta Khusrau wannan da ya rubuta kofi ɗari biyar da alƙalami ɗaya, kuma ka shigar da mataimakansa masu albarka da waɗanda suke tare da shi da abokansa ɗaliban nur arziki da jin-daɗi na har abada a cikin aljannar Firdausi amin,ka datar da su a cikin hidimar imani da Alƙur’ani kodayaushe, amin, kuma ka rubuta a cikin littafin kyawawan ayyukansu lada dubu ga kowanne harafi daga haruffan littafin mai shiryar da matasa, amin, ka yi kyautayi i zuwa gare su da tabbata da dawwama da ikhlasi, a cikin yaɗa hasaken”Rasa’il annur”, amin.
Ya Mafi jin-ƙai masu jin-ƙai, ka arzurta ka faranta cikin dukkan ɗaliban Nur a duniya da lahira, ka sanya su su zama masu arziƙi da farin ciki, amin.
Ka kiyaye su ka tsare su sharrin shaiɗanun aljanu da mutane, amin.
Ka kau da ido daga taƙaitawar wannan bawa gajiyayye miskini, Sa’id, amin.
Da sunan dukkan ɗaliban Nur
Sa’id annursi
Amin
يا نور يا نور النور يا منور النور يا مقدر النور
يا مدبر النور يا خالق النور
Da haƙƙin sunan Allah mafi girma da alfarmar Alƙur’ani da bayanansa suke gajiyarwa,da girma da ɗaukakar manzon mafi girma alaihis salam ka azurta
[1]Ya Allahu ya Rahmanu ya Rahimu ya Fardu ya Hayyu
130. Page
.............[1] wanda ya kofin wannan littafin, kuma ka shigar da mataimakansa masu albarka da waɗanda suke tare da shi da abokansa ɗaliban nur arziki da jin-daɗi na har abada a cikin aljannar Firdausi amin, ka datar da su a cikin hidimar imani da Alƙur’ani kodayaushe, amin, kuma ka rubuta a cikin shafin kyawawan ayyukansu, lada dubu ga kowanne harafi daga haruffan littafin Mai shiryar da matasa, amin, ka yi kyautayi gare su da tabbata da dawwama da ikhlasi, a cikin yaɗa hasaken” Rasa’il annur”, amin.
Ya mafi jin-ƙai masu jin-ƙai, ka arzurta ka faranta cikin dukkan ɗaliban Nur a duniya da lahira, ka sanya su su zama masu arziƙi da farin ciki, amin.
Ka kiyaye su ka tsare su daga sharrin shaiɗanun aljanu da na mutane, amin.
Da haƙƙin da alfarmar da dalilin halittar kasantattu, aminci ya tabbata a gare shi don haƙƙi da alfarmar sunanka mafi girma da Alƙur’aninka mafi hikima.
[1]A wajen wannan dige-digen ana rubuta sunan wanda ya yi kofin Rasa’il Annur sai ya zama addu’a ce keɓantacciya a gare shi.


