ƊAN ITACIYA NA BAКAR BISHIYAR TUT

117. Page

 

Ɗan’uwanku

Sa’idu Nursi.

 

 ƊAN ITACIYA NA BAКAR BISHIYAR TUT[1]:

Haƙiƙa Sa’id na da ya faɗida harshen Sa’id na yanzu a kanbishiyar Tut mai albarka.

Ba Dhiya Basha nake nufi dazance na ba,ina nufin waɗanda suka fitinantu da Turai ne.

Bani nake Magana ba, a a zuciya tacea matsayin ɗalibin Alƙur’ani mai girma.

Kalmomin da suka gabata haƙiƙa ce don haka kar ka ɗimautu sam-sam, ina yimaka kashedi kada ka ƙetare iyakokinsu.

Kada ka karkata i zuwa tunanin Turawan mulkin mallaka; domin ɓata ne, zai sanya ka ka zama mai nadama har abada kada ka  ba shi muhimmanci, sam!

Za ka ga wanda yake mafi yawan haske, wanda shi wata ƙusa ce cikin kaifin hankali, yana faɗa saboda waccan ɗimuwar: kash,wazan kaiwa kuka na? ni na ɗimauce.

Alƙur’ani yana sani yin magana ni kuma ina faɗa bana jin nauyi har abada.

Ina kai ƙara daga gare shi, i zuwa gare shi, bana ɗimauta kamarka.


[1] Bishiya ce mai girma da kaurin rassa da yawan ganyaye ana samunta a turai da china.




118. Page

Ina kururuwa daga haƙƙi da gaskiya bana fice gona da iri kamarka.

Ina kai ƙara daga ƙasa i zuwa sama, bana guduwa kamar ka.

 A cikin Alƙur’ani: akwai kira daga haske zuwa haske a kodayaushe , bana komawa ba ya kamar ka.

A cikin Alƙur’ani akwai gaskiya da hikima,ina tabbatar da su, kuma falsafa ba ta daidaita da kwabo ɗaya a wajena.

A cikin Alƙur’ani: zinaren gaskiya, ina fansarta da raina da zuciyata, bana sayar da ita kamarka.

Ina tafiya daga abubuwan halitta i zuwa mahallici, bana ɓata kamarka.

Ina tashi a cikin hanya mai sarƙaƙiya, bana naɗeta kamarka.

Ina godiya daga ƙasa i zuwa al’arshi, bana butulcewa kamarka.

Kuma ina ganin mutuwa da ajali kamar abokai, bana tsoro kamarka.

Ina shiga kabari ina mai dariya ana yimin bushara, bana tsoro bana firgita kamarka.

 Bana ganin kabari kamar bakin kububuwa da mashinfiɗin kaɗaici da maƙogaron rashi kamar yadda kake ganinsa.


119. Page

To shi yana sadar dani i zuwa masoya, bana ƙin kabari kuma bana jin haushi kamarka.

Shi ƙofar rahama ce, da haske da gaskiya, bana ƙuntata da shi kuma bana koma baya.

 Ina ƙwanƙwasa ƙofarsa ina mai faɗin: bismillah, ba na juyawa i zuwa bayana ba na firgita.

Zan kwanta a cikinsa ina mai faɗin: godiya ta tabbata ga Allah, kuma na huta ba zan wahala ba ba zan zaman kewa ba.

Zan tashi yayin kiran tashin alƙiyama ina mai cewa: Allahu akbar, bana jin tsoro taron mahashar babba, bana fita daga masallaci mafi girma.

Bana baƙin ciki har abada da falalar luɗufin ubangiji, da hasken Alƙur’ani, da kwararowar nan ta imani. 

Zan yi gudu ba da tsayuwa ba, zan tashi i zuwa inuwar al’arshin mai rahma, bana ɗimauce kamarka in sha’Allah.

 

Sa’id Nursi