Faɗakarwa da darasi da sanarwa da aka yi wa wani sashin matasa miskinai
NAVIGATION
22. Page
Faɗakarwa da darasi da sanarwa da aka yi wa wani sashin matasa miskinai
Wata rana wasumatasa masu haske faɗakakku, suka nema in yi musu nasiha mai motsa zuciya domin su samu kuɓuta daga haɗarurrukan rayuwa da na ƙuruciya da na son zuciya da na sha’awance-sha’awance.
Sai na faɗa musu kamar yadda na faɗawa waɗancan matasan, waɗanda suka nemi madadi daga Rasa’il-nur a lokacin da ya wuce: haƙiƙa ƙuruciyarku lalle za ta gushe, idan ba ku zama a da’irar da shari’a ta lamince ba, da sannu ƙuruciyar ku za ku tozarta ta, kuma ta zo muku da bala’o’’i da raɗaɗi da suka fi daɗinta yawa a cikin duniya da kabari da lahira,Idan kuka aiwatar da wannan ƙuruciyar a cikin kamewa da kunya da biyayya don godiya a bisa ni’imar ƙuruciya da sannu za ta zama wanzajjiya ta -ma’ana- da sannu za ta zama sababin samun ƙuruciya ta har abada.
Amma rayuwa in dai ba imani a cikinta,ko kuma imani bai yi tasiri a cikinta ba da sababin saɓo to ita tare da abin da take gadarwa na jin daɗi a zahiri taƙaitacce ƙwarai, da sannu za ta gadar da raɗaɗi da baƙƙan ciki da damuwamafi yawa daga wannan jin daɗin da dubunnan darajoji; domin cewa mutum –saɓanin dabbane–da irin zubin halittarsa yana da alaƙa da zamanin da ya wuce da mai zuwa ƙari da zamanin da ake ciki; domin cewa shi yana ɗauke da hankali da tunani, kumazai iya jin raɗadi ya ji daɗi har a waɗancan zamuna.
23. Page
Amma dabba bata da tunani;a saboda haka baƙƙan cikin lokutan da suka wuce da kuma tsoron abin da zai zo nan gaba da damuwa, ba za su ɓata mata jin daɗinta na yanzu ba.
Amma mutum idanya kasance ya abka cikin ɓarna da gafala, haƙiƙa baƙin cikin abubuwan da suka wuce,tsoro da fargabar abubuwan da za su faru nan gaba suna sa ɗan jin daɗin nan na yanzu ya zama mai ɗaci ƙwarai kuma su ɓata jin daɗin, balle ma a ce idan ya kasance -jin daɗin-bana shari’a bane, shi misaline cikakke na zuma mai guba, wannan yana nufin cewa shi yana faɗowa da daraja ɗari ƙasa daga dabba
24. Page
ta wajen jinɗaɗin rayuwar, baridai haƙiƙa rayuwar ma’abota ɓata da ma’abota gafalabari samuwar su bari dukkan duniyarsu da Alam-Alam nasu su ne ranarsu da suke rayuwa a cikinta,dukkan lokuta da duniyoyi da alam – alam da suka shuɗe rasassu ne matattu ne da irin kallon gafalarsu; domin suna gadar musu duhunnai masu tsanani da sababin alaƙarsu da su ta hanyar hankali, amma abin da yake nan gaba shi ma dai rasasshe ne da sababin rashin ƙudurin aniyar su, kuma nau’o’in rabuwa ta har abada, wannan da take faruwa da sababin rashi suna gadar musu duhunnai a kowanne lokaci a cikin rayuwar su ta hanyar nan ta tunani.
Idan imani ya zama shi ne ruhin rayuwa a yayin ne abin da ya wuce da wanda zaizo za su haskaka da hasken nan na imani kuma su zama samanmu, kuma sugadar -da sirrin imani- ɗanɗane-danɗane na ma’anamasu ɗaukaka da hasaken
25. Page
samuwa ga ruhin ɗan’adam da zuciyar sa, kamar yadda wannan zamanin na yanzu yake gadar da su, kuma bayyanin wannan haƙiƙa an bayyana shi a cikin “raja’i na bakwai” daga “Risalar nan ta dattijai” ya kamata a kanku ku yi nazari a cikinta.
Kuma hakanan rayuwa, idan kun kasance kuna son ku ji daɗi da abubuwan jin daɗin rayuwa da ɗanɗane-ɗanɗanenta ku yi rayuwar cikin imani, ku ƙawata ta da farillai, ku kiyaye ta da nisantar zunubai.
Amma haƙiƙar mutuwa mai tsoratarwa wannan da mace-mace suke bayyanata a kowacce rana, a kowanne waje a kowanne zamani zan bayyana muku ita da misali kamar yadda na bayyana ta ga wasu matasa:
Misali: Haƙiƙa an sanya abin rataye mutane a nan gaban idanuwanmu, kuma a gefensa akwai wajen wasan yanasib[1] sai dai shiyana samar da tikiti na ladaddaƙi masu girma ƙwarai, kuma muma gomannan da muke ananbabu makawa munaso ko munaƙi sai an kirawo mu zuwa can a cikin kowanne hali sai sun kirawomu.
[1] Wasa ne wanda ake ba wa wanda ya rabauta qudaden jama’a.
26. Page
Kuma yayin da muka zama munajira a cikin kowanne daƙiƙa -da sababin suturce mana lokacin kiran mu- domin suce: zo ka karɓi katin rasuwa, hau abin ratayar mutane, ko kuma ka rabauta da katin kyauta da zai samar maka miliyoyin lira na dinare, kazo ka karɓeshi, sai ga mutum biyu sun taho daga wajen ƙofa,ɗaya a cikinsu mai kyauce mai kamanni na kusan tsiraici mayaudariya, a hannunta a kwai kayan ƙwalan da maƙwalashe masu zaƙi da daɗi ƙwarai a zahirinsu, amma su masu guba ne a cikinsu tana nufin ta ciyar mu su, ɗayan kuma namiji ne nutsattse ba ya ha’inci ba ya yaudara, wannan matar tana shigowa ya shigo a bayanta, sai ya ce: nazo muku da wani sirri da wani karatu, idan kun karanta shi sannan ba ku ci wannan maƙwalashan ba za ku kuɓuta daga wannan abin rataye mutanen, kuma za ku samu katin karɓar kyauta wacce ba ta kwatantuwa, ku kuna gani da idanuwanku wannan abin ratayar mutanen duk wanda ya ci daga kayan ƙwalan-da-maƙwalashen yana
27. Page
hawa kai a rataye shi, kuma har ya hau i zuwa gare shi zai wahala da ciwon ciki matsananci da sababin tasirin guban da yake ciki,tare da cewa waɗannan da suka rabauta da katin kyauta mai girma wannan daba a ganinsu,suma suna hauhawa ga abin rataye mutane a zahiri;amma acan a kwai miliyoyin masu shaida suna ba da labari cewa su ba a a rataye suba, bari ma daisu sun riƙi abin rataya ,darajojine don hauhawa a cikin sauƙi zuwa ga wajen nan na samun kyauta, ku duba ku gani ta waɗannan tagogin,haƙiƙa manya–manyan ma’aikata da waɗanda suke da alaƙa da wannan al’amari daga mutane manya suna bayyanawa suna ba da labari da sautuka maɗaukaka ku sani sani da yaƙini ba da shakka bako shubuha kamar bayyanar hasken rana -kamar yadda kuke ganin, waɗannan da suke tafiya i zuwa abin ratayar mutane da idanuwanku gani na ƙuru- ƙuru -waɗannan haƙiƙawaɗanda suke samun wannan katin na kyauta su ne waɗanda suka mallaki wannan sirrin.
28. Page
Kamar yadda yake a cikin wannan misalin, abin da yake cikin kewayen abubuwan da aka haramta na jin daɗin ƙuruciya mai muni waɗannan da suke kamar zuman nan mai guba,domin cewa su suna rasar da imani, wanda ya zama shi ne wannan katin da tikiti na taskarnan ta har abada da arziki da jin daɗi dawwamanme; haƙiƙa su suna faɗarwa cikin musibar mutuwa mai kama da abin rataye mutane, da cikin kabari wanda shi ne ƙofar duffai na har abada, kamar yadda ake ganin hakan ƙuru-ƙuru.
Domin cewa ajali ɓoyayye ne; to zai iya yiwuwa, mai ɗaukan rai ya zo a kowanne lokaci saboda yanke kawuna, ba ya rabewa tsakanin matashi da dattijo; wanɗanda ba sa ƙidayuwa ba sa lissafuwa daga waliyai da ma’abota haƙiƙa sun yi ittifaƙi taredubu ɗari da dubu ishirin da dubu huɗu na daga Annabawa tsira da aminci su tabbata a gare su, suna ba da labari cewa idan mutum yabar soye-soyen zuciyarsa da kwaɗaice-kwaɗaice na abin da ba na shari’a ba waɗannan da su ne kamar zumar nan mai guba,kuma ya rabauta da imani da farillai -waɗanda su ne sirruka na Alƙur’ani,- da sannu zai samu tiket na taskar arziki da jin-daɗi ta har abada, wannan da zai kasance a cikin wasan alyanasib, na abin da aka ƙaddarawa mutum da yanayi mai ban mamaki daba kamarsa, suna ba da labari a kan haka zai faru kuma suna shiryarwa i zuwa gare shi kuma suna bayyana gurabansa.
29. Page
A ƙarshe: Haƙiƙa ƙuruciya mai wucewace babu makawa, idan kun so ku riski kuma ku fahimci cewa idan ƙuruciya ta wuce a cikin hanyar wauta da sannu za ta gadarwa mai ita dubunnan bala’o’i da raɗaɗi a cikin duniya da lahira,haƙiƙa mafi yawan waɗannan matasa da sannu za su shiga asibitoci saboda cututtuka ma’abota wahamce-wahamce waɗanda suke samuwa saboda yin munanan ɗabi’u da ɓarnace-ɓarnace, ko kurkuku da gidan wahala da tsiya da sababin kaucewar su, ko guraren shan giya da sababin matsaloli da baƙƙan ciki masu tasowa daga raɗaɗɗukan nan na ma’ana,idan kunaso kusan wannan kuma ku fahimta ku tambayi asibitoci da kurkuku-kurkuku da maƙarbartu; to babu shakka ku da sannu za ku ji, a cikin da yawa daga harashen nan na hali na asibitoci nishe-nishe[1] da nadamomi, waɗanda
[1]Nishin mara lafiya saboda tsananin ciwo.
30. Page
yawa daga harashen nan na hali na asibitoci nishe-nishe[1] da nadamomi, waɗanda suke tasowa daga cututtukan da suka faru da sababin ɓarnace-ɓarnace da mummunar aiwatarwar da matasa suke yi wa ƙuruciyarsu da giggiwar nan ta ƙuruciya, ƙari a kan haka za ku ji kuma daga kurkuku a cikin mafi yawa nadamomi da kaico na matasa hallakakku waɗannan da suka gamu da sakamakon ayyukansu wanda shari’a bata yarda da suba da sababin giggiwar nan ta barin hanya irin na ƙuruciya,da sannu za ku sani cewa mafi yawan azabar cikin kabari da cikin wannan duniyar ta barzahu, wannan da koyaushe yake ɓuɗewa yake rufe ƙofifinsa kodayaushe a bisa masu shiga a cikinsa wannan shi ne sakamakon munmunar aiwatarwa ta ƙuruciya, wannan shi ne irin duban da ma’abota kashfi suka yiwakabarurruka da gasgatawa da shaidar dukkan ma’abota haƙiƙa.
Sannan ku tambayi tsofaffi da masu cuta waɗanda su ne mafi yawa a cikinnau’in mutane,babu makawa mafi rinjayensu kai tsaye za su faɗa da cikin takaici da nadama; ya takaicinmu ya hasararmu!! Haƙiƙa mu mun tozartar da ƙuruciyarmu ba da wata fa’idaba. Kai! mu mun tozartar da ita da hasara da cututtuka, muna yi muku kashedi da kada ku aikata misalin abin da muka aikata;haƙiƙa mutun yana wahaltuwa- saboda ɗan jin daɗi na ƙuruciya daba na shari’a ba da yake tabbata shekaru biyar ko goma- da baƙin ciki da gurɓata a duniya, da azaba da cutuwa a barzahu[2]da bala’in jahannama da wutar saƙara a lahira; ba ya yiwuwa ya kasance mai cancantar rahamane har abada da sirrin “mai yarda da cuta ba a tausayamasa” tare da cewa shi, yana cikin mafi tsananin hali na buƙatar a yi masa rahma da tausayamasa; domin cewa ba a tausayi ba a jin-ƙan wanda ya cutar da kansa a bisa yardarsa, ba ya cancantar rahama.
Allah maɗaukaki ya tsaremu tare daku daga fitinar wannan zamani mai fizga amin.
[1]Nishin mara lafiya saboda tsananin ciwo.
[2] Kabari.


