Hanya ta biyu
NAVIGATION
2. Page
Hanya ta farko: Haƙiƙa wannan kabari ya tabbata ga ma’abota imani a matsayin kofa ce ta wata rayuwar, wadda ta fi wannan duniyar.
Hanya ta biyu: Haƙiƙa shi kofa ce ta kurkuku na har abada ga waɗannan da suke gasgata lahira, sai dai cewa su suna ci gabacikin wauta da ɓata, shi kofar kurkukuce, kurkuku na kaɗaitaka gare su ,za a tsiraitar da su daga dukkan masoyansu kuma za a tsaresu a cikinsa su kaɗai, haƙiƙa da sannu za a yi mu’amala da su, da irin wannan mu’amular don su suna gani suna ƙudurewa da wannan ƙudurin, amma ba sa aiki da abin da suke ƙudurta da shi.
Hanya ta uku:Haƙiƙashi ƙofa ce ta rasarwa ta har abada ga ma’abota inkari da ɓata waɗannan da ba sa imani da ranar lahira,ai shi: haƙiƙa igiyar rataya ce ta kisa, wadda za a halakar da shi da dukkan masoyansa, domin shi haƙiƙa yana ƙudurce wannan ƙudirin, da sannu za a yimasa irin wannan mu’amalar don uƙuba a gare shi.[1]
[1] - Yin tunanin haka ukuba ce a wajensa.


