Hanya ta uku
NAVIGATION
2. Page
Hanya ta farko: Haƙiƙa wannan kabari ya tabbata ga ma’abota imani a matsayin kofa ce ta wata rayuwar, wadda ta fi wannan duniyar.
Hanya ta biyu: Haƙiƙa shi kofa ce ta kurkuku na har abada ga waɗannan da suke gasgata lahira, sai dai cewa su suna ci gabacikin wauta da ɓata, shi kofar kurkukuce, kurkuku na kaɗaitaka gare su ,za a tsiraitar da su daga dukkan masoyansu kuma za a tsaresu a cikinsa su kaɗai, haƙiƙa da sannu za a yi mu’amala da su, da irin wannan mu’amular don su suna gani suna ƙudurewa da wannan ƙudurin, amma ba sa aiki da abin da suke ƙudurta da shi.
Hanya ta uku:Haƙiƙashi ƙofa ce ta rasarwa ta har abada ga ma’abota inkari da ɓata waɗannan da ba sa imani da ranar lahira,ai shi: haƙiƙa igiyar rataya ce ta kisa, wadda za a halakar da shi da dukkan masoyansa, domin shi haƙiƙa yana ƙudurce wannan ƙudirin, da sannu za a yimasa irin wannan mu’amalar don uƙuba a gare shi.[1]
[1] - Yin tunanin haka ukuba ce a wajensa.
3. Page
Waɗannan kaso biyun bayyanannu ne, ba sa buƙatar dalilai za a gansu da gani na ƙuru-ƙuru.
Kuma tare da cewa ajali ɓoyayye ne, mutuwa ta kasance za ta iya zuwa a kowanne lokaci, don ta sare wuyan ɗan’adam, bata banbancewa tsakanin yaro da tsoho;babu shakka wannan babbar mas’ala ce kamar girman duniya a wajen ɗan’adam abin-tausayi, wannan da ba shi dawata dabara a gare shi dangane da mas’ala mai girma, wadda take tsaye a gabansa, a kowanne lokaci kamar wannan; ita ce mutum ya nemi hanya ɗan tsira daga rasuwa ta har abada, da kurkukun nan na kaɗaitaka wanda ba shi da ƙarshe, da juyar da ƙofar kabarinsa i zuwa ƙofar da take buɗewa a rayuwa ta har abada, da arziki da jin daɗi na har abada da duniyar haske.
4. Page
Suna bamu labari -da haɗuwar masu ba da labarai - masu gaskiya dubu ɗari da dubu ashirin da dubuhuɗu,- wato Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su-waɗannan da suke ɗauke da mu’ujizozi a hannayensu, waɗannda su ne alamomin gaskiyarsu- suna ba mu labarai;tabbas wannan haƙiƙar yankakkiya tana faruwa da waɗannan hanyoyi guda uku, haƙiƙa waɗannanhanyoyi guda uku suna tabbata da haƙiƙoƙi uku waɗanda aka ambata, waliyai da salihai miliyan dubu ɗari da dubu ashirin da dubu huɗu sunashaidawa da haka waɗannan da suke gasgatawa ta hanyar yayewa da ɗanɗano da gani, abin da waɗannan Annabawa suka ba da labarinsa na labarai, suke tabbatar da wannan haƙiƙar ita kanta, malamai daba za su kidanyu ba kuma ba za su lissafu ba suna tabbatarwa da dalilai yankakku[1] na hankali da ilimi na yaƙini, abin da waɗannan Annabawa da waliyyai suka ba da labarinsa, shi ne kuɓuta daga rasarwa da kurkuku na har abada, kuɓuta tabbatacciya da gwargwadon tasa’in da tara cikin ɗari hakanan juyar da wannan hanya i zuwa arziki da jin-daɗi na har abada, yana kasancewa da imani da biyayya kawai.
[1]Daya daga cikin waxannan masu tabbatarwar su ne littattafan Rasa’il annur.
5. Page
Ya jama’a!tare da cewa shi ana sanyawa ga al ’ada zancen nan na mai ba da labari guda ɗaya ana sa rai gaskiya ne, kumabaa bin hanya mai haɗari, wanda ake zaton haɗari ɗaya ne a cikin ɗari zai afku, kuma raɗaɗin nan na ma’ana mai tasowa daga tsoron halaka yana yanke daɗin abinci ga wannan da ba ya sauraro i zuwa ga abin da mai ba da labari ya labarta da haka, sai ya bi wannan hanyar,tare da cewa dubu ɗaruruwa na masu ba da labari masu gaskiya ababan gasgatawa sun ba da labari da kyautata zato ɗari bisa ɗari haƙiƙa ɓata da wauta suna kora mutum tilas i zuwa abin ratayar nan na kabari wanda yake tsaye a gaban ido, kumai zuwa kurkuku na kaɗaita na har abada, daɗi a kan hakasun ba da labari da cewa imani da ibada suna gushe wannan rataya ta kisa, tare da kyautata tsammani ɗari bisa ɗari,kuma dai suna rufe wannan kurkuku na kaɗaici,sannan suna juyar da wannan kabarin da yake a gaban kowa i zuwa ga ƙofa wadda take buɗewa a bisa taskokin nan na har abada da fadar nan ta arziki da jin-daɗi, kuma sun bayyana alamominta da gurabanta; tare da dukkan haka ni ina tambayar ku:
6. Page
da an ba da mulkin duniya tare da dukkan jiye-jiyen daɗinta ga mutum ɗaya,shin wannan mulkin da wannan jin-daɗin za su iya gushe wannan raɗaɗin matsananci, wanda yake tasowa daga damuwar nan ta mutum, wanda yake jiran lokacinsa a kowanne ƙiftawar ido, don shiga cikin kabari wanda yake tsaye agaban ido?, idan baizama ba ga wannan gajiyayyen mutun -balle ma musulmi- wandayake fuskantar wannanmas’ala mai mamaki da al’ajabi mai tsoratarwa mai girma; imani da bauta?
Tare da cewa tsufa da cututtuka da musibu da mace–mace, a cikin kowanne waje, suna famewancan raɗaɗin mai tsoratarwa suna tunatar da shi; tobabu kokwanto jahannamar nan ta ma’ana tana ruruwa a cikin zuciyar ma’abota ɓata da wauta tana ƙona ta, ko da sun kasance suna jin daɗi da misalin dubunnan ɗaruruwa na jin daɗi da ɗanɗane-ɗanɗane, sai dai cewa mayen nan na gafala matsananci ya hana su jin ɗanɗanon nan na wannan jahannama a wani ɗanlokaci yankakke.
7. Page
Duk da cewa ma’abota imani da biyayya sun san haƙiƙa kabari wannan da suke ganinsa a gabansu, shi a wajensu ƙoface i zuwa taskar nan ta har abada da arziƙi da jin daɗi da ba sa gushewa, kuma suna sani cewa su da wasiƙar nan ta imani, suka rabauta da tiket, tiket na Alyanasib[1] na abubuwan da aka ƙaddarana tunfil’azalwaɗannan da suke sasu su rabautada miliyoyin zinare da gwal; sannan su kuma da irin taka rawarsu suna sauraro a kowanne lokacin kira” kuzo ku riƙi wannan tiket ɗin naku “ wannan jin daɗin na gaskiya,kuma wannan jin daɗi na ma’anamai zuwa daga wannan sauraro, shi jin daɗi ne da ake kwatanta shi da ƙwayar iri, wadda da za ta samu jiki da saita wayi gari ta zama bishiya, za ta iyazama aljanna makeɓanciya a gare su.
Tare da sani da wannan haƙiƙa wanda yake barin wannan ɗanɗanon da wannan ɗaɗi mai girma, kuma da ƙuruciyarsa yake zaɓar jin daɗi na ɗan lokaci wanda yake bana shari’a ba wanda yakekama da zuma mai guba,wandayake cakuɗe da raɗaɗi mara iyaka; zai faɗo daga darajarsa i zuwa mafi koma-baya daga dabba da kimanin daraja ɗari.
[1]Wani wasa ne mai kamar caca.
8. Page
Bari shi ba zai iya zama ba kamar misalin mulhidai Turawa ba, domin cewa su ko da sun yi inkarin Manzon (alaihi salam), haƙiƙa suna yarda da koma bayannsa na daga Annabawa, idan ma ba su yarda da Annabawa ba haƙiƙa za su yarda da Allah, ko da ba su yarda Allah ba to haƙiƙa zai iya kasancewa a gare su a kwai ɗabi’u masu kyau da za su kai su i zuwa wani ɓangare na kamala.
Amma musulmi; ya san Annabawa da Ubangijinsa ta hanyar Annabi Muhammadu -tsira da aminci Allah su tabbata a gare shi- wanda yake kaucewa koyi da koyarwar Annabi-tsira da aminci su tabbata a gare shi- kuma yake kwance akalar wuyansa[1]ba zai yarda da kowanne Annabi wani daban ba haka ma ba zai san ubangijinsa ba, ba ya zama cikin ruhinsa kowanne irin tushe wanda yake kiyaye cika; domin cewa
[1] Ma’ana yabar bin manzo.
9. Page
wanda ya bar tarbiyya ta asali da tushen addini waɗanda cikamakin Annabawa ya zo da su, wanda shi ne shugaban su wanda yake a sama da kowa ta wajen mu’ujizozi da addini - domin addininsa da da’awarsa sun tattarodukkan mutane- wannan da ya zama malami ga dukkan mutane a cikin dukan tabbatattun abubuwa, da kuma tabbatar da su da kamanni maiƙayatarwa a cikin tsakankkanin ƙarni goma sha huɗu,kuma shi ne ginshiƙin alfaharin ɗan-adam; Mun faɗa wanda yabar wannan;tabbas shi ta kowacce fuska daga fuskoki ba zai iya samun haske da cika ba har abada, kuma zai zamo cikin ƙasƙancin kai tsaye.
Ya ku waɗannan miskinai waɗanda ba su da wata dabara, waɗanda aka fitincesu da ɗan jin daɗin rayuwar duniya, ya ku masu damuwa da abin da zai faru a nan gaba ga rayuwar ku, don haka kuke wahala wajen nemanta;To idan kuna son jin daɗe–daɗenduniya da ɗan shaƙatawarta da arzkinta da hutunta, to ku wadatu da shaƙatawa dajindaɗe–daɗe na cikin kewayen da shari’a ta yarda da su, su masu isarku ne jin-daɗi.
10. Page
Haƙiƙa kun sani cewa; – babu shakka daga bayanai da suka gabata – cewajin daɗi ɗaya wanda shari’a ba ta halattaba; sakamakonsa akwai dubunnan raɗaɗi, da jin-zafi.
Da za a bijiro dahalin gaba na ma’abota fasiƙanci da son zuciya da wauta–wato halin da za su kasance ciki bayan shekaru hamsin nan gaba- a hasko a kan allon sinima a yanzu, kamar yadda ake hasko mana da abin da ya wuce a sinima yanzu; da fasiƙai da masu bin son zuciya da wauta sun yi kuka da yawa a kan dariyarsu a yanzu, suna la’anta kuma suna masu ƙin abin da suke tafkawa na saɓo yanzu.
Wanda yake son farin ciki na har abada dawwamanme a cikin duniya da lahira; ya wajaba a gare shi ya riƙi abin da yake cikin da’irar imani na daga tarbiyya Muhammadiyya – a bisa ma’abocinta tsira da aminci su tabbata a gare shi-a matsayin abin shiriya a gare shi.
Nakasance ina zaune wata rana a bakin tagar kurkukun Aski Shahir:
11. Page
Nakasance ina zaune watarana a gaban tagar kurkukun Aski shahir,a yayin nan ‘yan mata manya sun kasance a cikin makaranta “secondary” wadda take fuskantar kurkukun suna rawa a cikin filinta suna dariya, na kalle su a surar ‘yan matan wutar Jahannama a cikin aljannar nan ta duniya,sai dai katsahan sai aka nuna min halinsu da za su kasance a cikinsa bayan shekaru hamsin, haƙiƙa saidariyar nan ta su ta komakuka mai raɗaɗi da ɗaci, to daga nan ne sai haƙiƙa mai zuwa ta bayyana a gare ni:
Tabbas ni na ga halayensuda za su kasance bayan shekaru hamsin ta hanyar sinima ta ma’ana ta sassaƙawa nan ta zuciya;su ne haƙiƙa hamsin daga matan nan sittin da suke dariya ana yi musu azaba a kabari, sun juya sun koma ƙasa, ragowar guda goma da ga gare su sun kai shekaru saba’in a rayuwar su, sun zama munanakowa yana gudunsu, sai nayi kuka a bisa halayensu.
12. Page
Haƙiƙa an nunamin kamanni ainihin fitintunun ƙarshen zamani , su ne cewa mafi tsananin fitintunun ƙarshen zamani da mafi yawansuruɗi suna faruwa da sababin mata marasa kunya, domin suna sace tunanin mazaje suna jefa su a cikin wutar fasiƙanci dawauta kamar ƙwaro faɗa-wuta, suna sanya mazaje suna fifita daƙiƙa ɗaya ta rayuwar duniya a bisa shekaru na rayuwar wanzuwa, a wani lokaci yayin da na kallititi sai na ga misali mai tasiri daga misalan wannan fitinar, sai natausayawa matasa tausayawa mai yawa, sai na ce a cikin raina: haƙiƙa waɗannan ababan tausayin ba za su iya tsamo kansu daga wutar wannan fitinar mai fizga ba, kamar mayen-ƙarfe.
Yayin da na kasance na nitse a cikin tunani a wannan batun; sai na ga ina ganin mutum na ma’ana, mai bijirewa, wanda yake rura wutar wannan fitina kuma yake ɗaiɗaitata, ga shi kamar jiki a gabana, sai na ce da shi da ‘yan-ba-ruwan-mu da addini waɗannanda suke ɗaukar darasi daga wajensa:
Ya kai shaƙiyi mai ta’asa wanda yake sadaukar da addininsa adalilin ɗan jin-daɗi da ‘yan matan jahannamar duniya, yanaaikata laifi na ɓata da wauta da sonsa, kuma ya
13. Page
yarda da rashinaddini da inkarin samuwar Allah, saboda son zuciya da kwaɗaice–kwaɗaicen son kansa, yana son rayuwa da darajar da ta kai darajar bauta, yana tsoron mutuwa matsanancin tsoro, wannan da ba ya so ya dinga tuna kabari, wannan da yake ya kusa bijirewa addini, ka sani, sani na yaƙini, haƙiƙa duniyar nan taka dukkanta, da dukkan aalamɗin da kake cikinsa da dukkan abin da ya wuce naka, da abin da yake gabato maka,da nau’inka da jinsinka wanda ya shuɗe, da dukkan halitta da tsarori na nan gaba, da duniyoyida jama’u da suka wuce, da mutane da jama’u masu zuwa nan gaba; rasassu ne matattune dukkansu a cikin dubannan na masu inkarin samuwar Allah.
To dukkan waɗannan duniyoyin da sauran halittu masu kwarara waɗanda kake da alaƙa da su ta ɓangaren mutuntaka da hankali-koyaushe suna zubo maka raɗadi mai tsanani mara iyaka, sabodaɓatanka dawwamanme raɗaɗin ya kai cikin ƙasa, -– kamar irin wannan mace-mace masu tsoratarwa, kuma suke ƙona zuciyarka idan kana da shu’uri da ji irin na riskar gaɓoɓi, kuma suke ƙona ruhunka, idan ka kasance kana daruhi, kuma suna nitsar da hankalinka a cikin baƙƙan ciki da ɓace-ɓacen rai, in har ran bai mace ba.
14. Page
Idan wautarka ta kasance a cikn maye, da jin daɗin ka munmuna wannan da yake dawwama ɗan-lokaci za su iya maye gurbin waɗannan damuwar da baƙƙan cikida raɗaɗɗuka waɗannan da ba su da iyaka; toka wanzu a cikin wancan wautar, idan bahaka ba, to ka komo i zuwa shiriyarka, ka yi saurare i zuwa darasin Alƙur’ani mai girma, don ka kuɓuta daga jahannama ta ma’ana, don ka shiga Aljanna ta ma’ana wannan da imani yake tabbatar da itahar a cikin wannan duniyar, kuma don ka ɗanɗana ɗaɗin nan na rayuwa, ka canja ɗan jin-daɗi nan mai ƙarewa wannan da yake dawwama minti ɗaya kaɗai da jin daɗi na imani mai wanzuwa madawwami.[1]
[1] Na’am; haqiqa imani zai iya yiwuwa ya haifar da jiye-jiyen dadi na aljanna na ma’ana har a cikin wannan duniya, yi duba i zuwa fa’ida daya daga daruruwa na daga hasakensa masu dadi: kamar yadda yake a lokacin da kake gani a cikinsa mutumin dakake so matsananci so, yana mutuwa a cikin hatsari, sai ga likita ya zo kamar Lukman alhakim ko halliru, wanda kake son nan sai ya tashi kai tsaye sai ya samu sauki, to za ka ji dadi matsananci; hakananma imani yana ba ka farin ciki da murna da adadin matattu waxanda kake son su kuma kake shaquwa da su; domin miliyoyi waxanda su masoyanka ne waxanda suke cikin makabarta data shude ana tashinsu a gabanka ana kubutar da su daga halaka da rasuwa kai tsaye ta hanyar hasken imani, kuma suna samun rayuwa suna masu cewa:” mu bamu rasu ba kuma ba za mu rasu ba”. Samuwar wannan farin cikin da wannan jiye-jiyen dadin da ba su da karshe-waxanda suke tasowa daga shu’urinsu na saduwa da rayuwa maimakon radadduku da ba su da iyaka waxanda suke tasowa daga rabuwa da bata da iyaka- daga imani har a cikin wannan duniyar; yana shiryarwa a bisa cewa imani kwayar iri ne da take haifarwa kuma za ta haifar da zangarnan Aljanna da dukkan jiye-jiyen dadinta da dukkan qayace-qayacenta ga ma’abota imani.
15. Page
Kada ka ce: Ni zan aiwatar da rayuwata kamar irin ta dabbobi; domin cewa abin da ya shuɗe da abin da zai zo a wajen dabba yana matsayin nan na gaibu, tomai hikima mai jin ƙai, ya ɗauke daga kanta abin da ba shi da iyaka na raɗaɗi, domin ba a yaye mata gaibu ba,har dai cewa kaza wadda ake kwantar da ita kanƙasa dona yankata bata jin wani raɗaɗi koɓacin rai ko kaɗan tana so tajishi a lokacin yankan wuƙar amma jin yana gushewa a gare ta, sai ta kuɓuta daga wannan jin raɗaɗin.
To kenan Allah maɗaukaƙi yana da rahma mai girma cikakkiya da jin-ƙai da tausayi da suka kai matuƙa kuma suke tabbatuwa a rashin yaye gaibu,kuma su nemafi cika musamman a cikin haƙƙin dabbobi kuɓutattu.
To kenan kai ba za ka iya kaiwa dabbobi ba wajen jin-daɗi da wauta,bari, kai kana faɗowa i zuwa ƙasa da su da dubbunan darajoji; domin hankalikayana ganin abubuwa wanda a wajen dabbobi suna matsayin gaibu,kuma yana jin raɗaɗin waɗancan abubuwan, to kenan kai abin haramtawa hutu cikakke ne gaba ɗaya, wannan da yake cikin suturcewar nan ta gaibu.
16. Page
Sannankyawawan ɗabi’unka kamar ‘yan ‘uwantaka da girmamawa da mutuntawa da ɗaukaka, wannan da suka zama abin alfahari ne a gare ka, suna killacewa ne a cikin zamani ƙanƙani ƙwarai, kai ka ce suna killacewa ne awaje misalin gwargwadon ɗan yatsa daga sahara mai girma, suna keɓantar awa kaɗai daga awoyin da ba su da iyaka,dan haka su suna zamagaibuna ɗan wani lokaci, jabu ba na asali ba, guntayeƙwarai, mutuntakarka da kamalarka suna ƙasƙanta da gwargwadon haka, sannan bata kai komai ba kuma za ta rasa ƙimarta dukka.
Amma abokantakar masuimani da girmamawarsu da soyayyarsu da ɗaukakarsu sun kewaye lokacin da ya wuce da lokacin da zaizo waɗanda suke samanmu ne da sirrin
17. Page
imani; to domin haka ne mutuntakarsu da kamalarsu suke ɗaukakagwargwadon haka.
Sannan kai ana datar da kai a cikin al’amuran duniya; domin cewa kai kana ba wa zamani da rayuwamasu ƙunci taƙaitattu farashin da yadaceda rayuwa mayalwaciya dawwamanmiya mai tsayi, kamar yadda bayahude attajirin zinare mahaukaci wanda yake sayen guntayen gilasai da farashin zinare; babu shakka, haƙiƙa kai kana fifita a wancan faggen, sannan kai kana fuskantar daƙiƙa ɗaya da abin da ake fuskanta shekara cikakkiya da shi, kamar ƙwaɗayi da soyayya da kamu mai tsanani; a saboda haka haƙiƙa kai ana datar da kai fiye da ma’abota addini datarwa ta ɗan lokaci.
18. Page
Sannanhaƙiƙa hankalinka da ruhinka da zuciyarka da jinka na zuciya suna tattaruwa a cikin al’amura munana na maƙasƙanciyar zuciyya da na soye-soyen zuciya mai muni daƙazanta, da suke taimakonta suna barin ayyukansu maɗaukaka,a saboda haka kai kana ɗaukaka a bisa masuimani a cikin duniya, kumakana bayyana da kamar nan da aka fi so fiye da su a zahiri; domin cewa hankalinka da zuciyarka da ruhinka, sun ƙasƙanta sun koma baya sun faɗa mafi ƙasƙanciyar daraja, sai suka juya i zuwa kwaɗayi mai muni da ƙazanta, da rai maƙasƙanci wulaƙantacce munmuna sai aka shafesu; to babu shakka, ta haka za ka sami wata ‘yar ɗaukaka tawani ɗan lokaci wanda zai kaika jahannama, kuma masu imani waɗanda aka zalunta za su rabauta da shiga Aljanna.
Mas’ala muhimmiya da aka yimin ilhamarta katsahan
Za a fahimta daga ruwayoyin hadisai cewa waɗanda za su taka rawa mafi haɗari a cikin fitinar ƙarshen zamani su ne mata da fitinarsu[1].
[1] ya zo a cikin littafin sahihul muslim 4/2098 Hadidi mai lamba 2742 “muhd bn musanna da muhd bn Bashar sun ce muhd bn Jafar ya yi mana Hadisi Shu’uba daga Abi salmata ya ce na ji Aba nadhara yana yin Hadisi daga Abi sa’id khuduri daga Annabi (S.A.W) ya ce: haqiqa duniya kamar wanni abuce mai zaƙi koriya, haqiqa Allah ya halifantar daku a cikinta don ya ga me za ku aikata, ku ji tsoron Allah ku ji tsoron mata; haqiqa farkon fitinar ‘yan bani Isra’ila ta kasance a mata, a cikin Hadisin Bashar, domin ya ga me za ku aikata”.


