Jawabi a kan tambayar da ta zo daga wajen ɗaliban Rasa’il annur:

31. Page

Jawabi a kan tambayar da ta zo daga wajen ɗaliban Rasa’il annur:

Mun tambayi malaminmu cewa: Haƙiƙa kai  ba ka  tambayemua tsakankanin shekaru biyu ba -yanzu an kusanci shekaru goma-[1]sannan  ba ka  tambaya ko da sau ɗaya ba Amini wannan da yake yi ma hidima a kowacce rana a kan wannan yaƙi na duniya wanda yake da alaƙa ƙaƙƙarfa da abubuwan nan da duniyar musulunci ta mallaka har dai a cikin matsanantan kwanukansa wajen firgici da razani, kuma  ba ka  damu da shi ba,ko kana gani! Shin akwai wata haƙiƙa mafi girma daga wannan yaƙin mai girma da take shagaltar da kai har kake ƙasƙantar da muhimmancinsa?ko kuma shagala da shi zai zama mai cutarwa ne?

Sai ya amsa cewa: Na’am; tabbas! Cewa akwai haƙiƙa mafi girma daga wannan yaƙin duniya, da mas’ala mafi girma daga gare shitana shagaltar da tunanina, yaƙin duniya  ba shi da muhimmanci ƙwarai danga ne da ita.


[1] Shekara biyu, da shekara goma, ana nuni da su a kan lokacin da aka wallafa wannan risalar ba lokacin mu ba ne na yanzu 




32. Page

Domin cewa shi, an ɗaga mas’alar ƙara na sulhu a tsakankanin addinai biyu manya a cikin kotun sulhu da maslaha a lokacin mas’alar hukuma biyu ga ƙariyar mamaya a bisa duniya a cikin wannan yaƙin na duniya, kuma an ɗaukaka ƙara a babbar kotu a tsakanin jama’arnan tagurguzu da jama’ar nan ta masu kuɗi ta mutane a tsakankanin farkon rigimar jama’ar ta masu ra’ayin musun samuwar Allah Ta’ala mai tsoratarwa tare da addinai da aka saukar da su daga sammai, sai dai cewa mas’alar mafi muhimmanci da yawa tsakankanin ɗabaƙoƙin nan guda biyu daga mas’ala mai girma da aka ɗaukakata, da haƙiƙa mai girma da ta bayyana; ta yadda, gwargwadon abin da zai sami mutun ɗaya daga gare ta shi ne mafi girma daga wannan yaƙin duniyar.

Wannan mas’ala itace,cewa an ɗaga a gaban dukkan mumini, bari a gaban kowanne mutun a cikin wannan zamani mas’alar rabauta ko hasarar gona wanzajjiya da faɗinta ya kai faɗin duniya, ai mas’alar rabauta ko hasarar mulki nan na har abada wanda aka ƙawatashi da lambuna da fadoji. 


33. Page

Ai cewa an ɗaga mas’alar a gaban kowa, ta yadda da a ce yana da dukiya da ƙarfi da gwargwadon dukiyada ƙarfi irin na England da Jamus, kuma yana da hankali; da ya ba da su dukkansu don rabauta da wannan mas’alar ita kaɗai.

Babu shakka wandayake damuwa da wasu al’amurakafin ya rabauta da wannan mas’alarwawane mahaukaci, bari hardai wannan mas’alar takasance a matsayi mai wahala; domin mutum ɗaya ne kawai ya rabauta da ita- da kallon ɗaya daga cikin ma’abota kashfi-[1] daga tsakankanin mutane arba’in da suka karɓi katin sallama daga hannun ajali a cikin wani gari kuma mutane talatin da tarane suka rasata.

Idan ya kasance a kwai lawyer da zai sa a rabauta da wannan mas’ala mai haɗari mai girma, bari da gaske, da tajjaruba yana sa mas’alar ta ƙare da rabautar mutane takwas daga goma kuma wannan abin yana faruwa tun shekaru ishirin da suka wuce haryanzu; to babu shakka duk wanda yake da lafiyayyen hankali ya wajabaa kansa da ya ba da muhimanci mafi yawa daga ba da muhimmancinsa ga dukkan wani abu daban ga ƙoƙarin da zai samar da mai aiki, misalin wannan lauyan, wanda zai sa ya rabauta da wannan mas’ala.


[1] - Waxanda ake yayewa waxansu sirrika. 




34. Page

Dubunnai daga waɗanda suka rabauta da wannan mas’ala ta hanyar Rasa’il nur suna shaida cewa ɗaya daga cikin lauyoyin na farkonsu shi ne Rasa’il annur mai ɓuɓɓugowa daga iyjaz na ma’ana na Alƙur’ani da bayaninsa yake gajiyarwa.

Hakayake; haƙiƙa cewa an tabbatar tabbatarwa mai ƙarfi kowanne mutum cewa an aiko shi ne zuwawannan Duniyaa matsayin ma’aikaci abin ba wa umarni, shi baƙo ne kuma mai barin ta ne, kuma ainihinsa mai fuskantar wanzajjiyar rayuwa ne.

Haƙiƙa kowane mutum zai bar wannan duniyar tasa da dukkan masoyansa, waɗannan da ya shaƙu da su ya ƙullu da su a cikinta zai bar su bari na har abada da sababin raurawa da rauni na dukkan sansanoni masu ƙarfi waɗannan da suke tseratar da rayuwar mutum ta har abada a cikin wannan zamanin, tare da haka haƙiƙa an ɗaga 

35. Page

a gaban kowanne mutum mas’ala hasarar ko rabautar mulki wanzajje mafi ƙayatarwa mafi kyau daga wannan duniyar sau dubunnai.

Idan bai kasance ba yana da wasiƙar imani ba, kuma bai samu ƙudurin niyya wannan da yake shi ne kuɓutarsa da shaidarsa ba; to shi zai yi hasarar wannan mas’ala, to! Ya jama’a! Wane abu ne zai iya warkar masa da hasararsa.

Gini  a bisa wannan haƙiƙar da hankalina da hankulan ‘yan’uwana za su ƙaru sau daraja ɗari ba ya kusata su isa sai dai don hidimar wannan aiki mai tsarki mai girma, kuma sai ya zama ba da muhimmanci ga wasu al’amuran daban ƙari ne da kuma abubuwan da suke bana dole ba, sai dai cewa haƙiƙa wanisashi daga ɗaliban Rasa’il Nur ba tare da son zuciyarsu ba sun ba waɗannan al’amuran muhimmanci da gwargwadon larura, don kasancewarsu a cikin wasu mas’aloli, ko yayin wautar ta wawaye da kawowar harinsu zuwa garemu ba tare da lalura ba ko wani daliliba. 


36. Page

Sannan yin shisshigi -tare da bawa tunani da hankali muhimmanci - a cikin mas’aloli da rigingimu koma bayan wannan mas’ala ta haƙiƙa mai girma ƙwarai mai cutarwa ne; domin wannan da ya damu da kewayoyin siyasa mai fizga mayalwaciya -misalin wannan- kuma yana shagaltada ita, zai yi jinkiri ga yin hidimominsa da ayyukansa muhinmaiwaɗannanda aka ɗora masanauyin yinsu a cikin ƙaramin kewaye ko hamasarsa take samun rauni, kuma shauƙinsa sai ya karye.

Sannan wannan da ya damu da kewayoyin siyasa da rigingimu mayalwata masu fizga, wanilokacin zai shagalta da su, kuma ba ya iya tsayuwa ya yi ayyukansa , zai yiwu ya wanzu cikin tuhuma, cewa shi ya rasa amincin zuciyarsa da kyaun niyyarsa da daidaituwar tunaninsa da tsarkinsa a cikin da’awarsa, ko da bai rasa suba.

 Kuma nima nace yayin da suka tuhumeni agaban kotua wannan batu: Cewa shi kamar yadda haƙiƙar imani da haƙiƙar Alƙur’ani waɗanda su kamar rana ce bata kasance mai bicewa ba ko kuma na’ura da take fizgar hasake waɗanda aka sa musu lokaci zuwa ƙasa, haka nan wandaya san waccan haƙiƙa sani na haƙiƙa ba zai iya sata ta zama na’ura ko sinadari ga abubuwa fararru a cikin ƙasa ba, bari harma ga dukkan samanmu, sai nasa su suka yi shiru, haƙiƙa a nan ne jawabin malamin mu ya tuƙe, mu haƙiƙa mun gasgata da dukkan ƙarfinmu.

Ɗaliban Rasa’il nur.