MASA’ALA TA SHIDA
NAVIGATION
53. Page
MASA’ALA TA SHIDA
Daga saƙon amfanin kurkukun Dinizili
Ishara ce taƙaitacciya ga dalili ɗaya na daga dubunnan dalilai cikakku ga rukunni na imani da Allah wanda yake da bayanai da hujjoji yankakku da ba su da iyaka a cikin wajaje da yawa daga Rasa’il annur.
Wani adadi daga ɗaliban makarantun sakandare sun ziyarce ni a birnin Ƙasdamoni, sai suka ce dani, ka sanar damu mahaliccinmu; domin malamanmu ba sa zance a kan Allah Ta’ala.
Da irin taka rawata kuma ni sai nace musu: haƙiƙa dukkan ilimi na daga ilman da kuke karanta su yana magana a kan Allah kodayaushe da harshensakeɓantacce kuma yana sanar da shi, ku yi sauraro i zuwa gare su, ba i zuwa ga malamai ba.
Gamisali: kamar yadda kyamis[1] ƙayatacce wanda yake ɗauke da kwalabe, a cikin kowacce kwalaba akwai kayan kimiyya da ake haɗa magunguna da su kumada haƙƙaƙaƙƙun magunguna waɗanda aka haɗasu da ma’aunan nan rantsattsu masu keta al’ada, babu shakka cewa shi yana shiryarwa a bisa ƙwararren mai haɗa magani da ƙwararren ɗan kimiyya da ƙwararren likita; haka nan kyamis ɗin nan na Duniya yana nunawa -harga idanuwa makafi-mai hikimada ɗaukaka wannan da shi ne mai haɗa magungunansa, kuma yana sawa a sanshi a bisa ilimin likitanci wannan da kuke karanta shi da gwargwadon ƙayatarwarsa da girmansa fiye da wannan kyamis da yake cikin kasuwa don shi yana ɗauke da nau’i dubu ɗari huɗu daga kayan da ake haɗa magunguna da su kuma da magunguna haƙƙaƙaƙƙu waɗanda ake samunsu a cikin jijiyoyin tsirrai da bishiyoyi da dabbobi.
[1]Wajen hada magani da sayarwa.
54. Page
Misali: kamar yadda masana’anta, mai keta al’ada mai ƙayatarwa, da take saƙa nau’o’i dubunnai nayaduna daga wani sinadari sassauƙatana nunawa tana sanarwa ba tare da kokwanton ba ma’abocinta da ƙwararren ba ka niken nan nata;hakanan ma wannan injin mai tafiya na Ubangiji da ake ambatonsa ƙwallon ƙasa wandayake da dubunnan ɗaruruwa na kawuka, a kowanne kai daga kawukansa akwai dubunnan ɗaruruwa namasana’antu masu keta al’ada masu ƙayatarwa;yana nunawa yana sanarwa wanene maƙerinsa da mamallakinsa da gwargwadon girmansa da ƙayatarwarsa da cikarsa fiye da masana’antar nan ta ɗan’adam a tsarin ilmin injina wannan da kuke karantasu.
55. Page
Misali:Kamar yadda cikakkiyar ma’ajiyar abinci da taskarshi da kantinsa wanda aka jerashi a cikinsu da tsari a bisa dubbunan nau’o’i da nau’i na daga abinci bayan an kawo su daga wajaje daban-daban yana sanar da mamallakin abincin da ma’abocinsada mai aikinsa ba tare da kokwanto ba; haka nan wannan wajen ajiyar kayayyakin abinci da arziki na al rahman,
da wannan jirgin ruwan na subhana wanda yake tafiya cikin tsari a cikin shekara ɗaya a cikin kewayen da ake tafiya a cikinsa tsawon shekaru dubu ashirin da huɗu, wannan da ya tattaro ɗaruruwan dubbai na daga jama’u waɗanda kowacce jama’a daga cikinsumasu buƙata nei zuwa arziki da ya keɓanta da su, wannan da yake tafiya tare da yanayai, yake cika yanayin kaka kamar tarragon jirgin ƙasa mai girma da dubunnan abubuwan ci mabambanta nau’i-nau’i, kuma ya taho da su i zuwa ma’abota rayuwa talakawa miskinai waɗannan da arzikinsu ya ƙare a cikin lokacin sanyi, kuma wannan wajen ajiya da kanti na ubangiji wannan da yake ɗauke da dubbunan nau’o’ina dagakayayyaki da dukiyoyi da kwalaye da gwangwanaye na abubuwanci tatattu, yananunawa yana sanarwa kuma yana sawa a so da yanayin nan na girmansa da ƙayatawarsa fiye da kantin da aka ambata a cikin misalin mamallaki da mai sarrafawa da mai gudanar dama’ajiyin nan na duniya da ƙiyasi da ma’aunai ilimin abinci wannan da kuke karanta shi ko kuma nan gaba za ku karanta shi.
56. Page
Kuma da kamarcewa akwai wata runduna wadda ta ƙunshi al’ummatai dubu ɗari huɗu, kowacce al’umma tana da keɓantaccen arzikinta, da keɓantattun makamanta, da keɓantattun tufafinta,da keɓantattun horar da ita, da keɓantattun sallamar ta, kuma a kwai wani shugaba mai abubuwa masu keta al’ada da suke kama da mu’ujizozi ga wannan runduna yana bayarwa shi kaɗai ga dukkan al’umma daga wannan al’ummomi arzikokinta mabambanta, keɓantattu, da makamanta da tufofinta da kayan aikin ta nau’i nau’i masu adadi da yawa ba tare da ya manta ɗaya daga cikin su ba, kuma ba tare da wani abu ya cakuɗa a gare shi ba...ina faɗa babu ko kwanto haƙiƙa wannan runduna da wannan cibiya ta sojoji tana nunawa da shiryarwa a bisa wannan shugaban mai girma kai tsaye,tana sa waninsa ya soshi ya girmamashi.
Kamar yadda yake a cikin wannan misali kwabo-da kwabo haƙiƙa cewa shi ana bayarwa ana tsarawa daga wajen shugaba mai girma ga dukkan al’umma, na daga nau’in dangi ɗari huɗu na tsirrai da dabbobi a cikin rundunar nan ta subhana, waɗannan da ake tarosu da sake mayar da su a cikin tutar nan ta sojoji ta duniya, a cikin dukkan lokacin kaka tufafin ta da arzikinta da makamanta da horarwarta da sallamar ta nau’i-nau’i mabambanta a cikin matuƙar kyautacewa da cika da tsari ba tare da manta ko ɗaya ba, ba tare da cakuɗawa ko cuɗanyawa ba.
57. Page
Haƙiƙa wannan tuta ta sojoji ta duniya dadarajar cikarta da girmanta na daga rundunar nan ta mutane dakuma tutar sojoji ta mutane tana sanarwa ga faɗakakku da masu hankali a gwargwadon ilmin aikinsoja wannan da za ku karantashi mai hukuncin duniyar da mai jijjuyata da renonta, da jagoranta mafi tsarki da shugabanta mai tsarki za ta sa waninsa ya soshida godiya da tsarkakewa.
Kamar yadda cewa idan da ya kasance akwai miliyoyin fitilu nalantarki a birni mai keta al’ada, suna masu kekkewayawa a cikin kowanne waje a cikin wannan birnin, abin da ake rura su ba ya ƙare wa; to babu shakka haƙiƙa fitilun nan na lantarki kamar waɗannan da wajen ƙera wannan fitilun suna sanarwa kai tsaye-da ban mamaki- suna sa a sani kuma kai tsaye a sowannanmaƙerin ma’abocin umarni masu keta al’ada masu kama da mu’u jizozi,da ma’aikacin lantarkin mai girman iko, ikon da yake keta al’ada da yake gudanar da lantarkin kumayake ƙera fitilunnanmasu
58. Page
tafiya kuma ya assasa ma’aikatar kuma yake zuwa da abin hurasu, kuma a yi masa kirari, kamar haka, Allah ya rayaka,Allah ya rayaka.
Kamar yaddayake a cikin wannan misali kwabo-da-kwabo, haƙiƙa fitilun nan na taurari a cikin birnin nan na wannan halittar a cikin rufin fadar nan ta duniya, tare da cewa wani yanki daga cikinsuyafi duniya girmasau dubu, kuma sunamotsawa da sauri da ya fi majaujawa sauri sau saɓa’in a gwargwadon fadin nan na masu ilimin falaƙi; haƙiƙa su ba sa wofantar da tsarinsu sashin su ba ya karo da sashi kuma ba sa bicewa, abin rura su ba ya ƙarewa.
A bisa gwargwadon faɗin nan na masu ilimin falaƙi wannan da kuke karanta shi haƙiƙa cewa zarcewar rura ranarmu yinsa yana lazamtuwa ne kowacce rana-wannan da ita ce mafi girma daga Duniya sau milliyan, wannan da take a raye sama da shekaru miliyan, wannan da ita fitilace da kuma abin ɗumama waje a cikin gidan saukar baƙinamai jin ƙai- abin rurawa da gwargwadon kogunan duniya, da gawayi da gwargwadon duwatsunan ta, da tarin ƙirare da gwargwadon ƙwallon ƙasa sau dubu, har dai kar ta bice.
59. Page
Haƙiƙa fitilun nan na lantarki na fadar nan ta duniya a cikin birnin nan na kasantattu mai girma wannan wacce suke nunawa da ‘yanyatsun nan na haske iko da mulki waɗanda ba sa ƙarewa, ana rura rana da makamantan ta na taurari maɗaukaka ba tare da mai ba, ba da ƙirare ba, ba da gawayi ba, kuma baa barin su su bice, ana tafiyar da su tare da sauribaa barin sashi ya yi karo da sashi- gudanar da waɗancan fitilu; yana sanarwa da darajar girman nan nasu da ƙayatarwarsu ga fitilun nan na misalin nan da aka ambata cikin misali-suna masu riƙe da taurarin nan na haske shaidu-sarki mahallicin kasantattu mai girma mai haskakasu mai gudanar da su maƙerinsu a gwargwadon ma’aunan nan na ilimin lantarki wannan da kuke karatanshi ko kuma za ku karanta shi, za su soyar da shi i zuwa waninsa da tasbihohi da tsarkake tsarkake har zuwa ga darajar nan ta bauta.
60. Page
Misali:Da a ce akwai wani littafi; da aka rubuta a cikin akowacce saɗararsa wani littafin cikakke da rubutu ingantacce, a cikin kowacce kalma daga gare shi akwai surar Alƙur’ani da aka rubuta da alƙalami ingantacce,to ba makawa wannan littafin mai abin mamaki kamar haka -wannan da yake fa’idantar da ma’ana mai yawa, kuma dukkan mas’alolinsa suna ingantasashin junansu kuma yana bayyana marubucinsa da mawallafinsa ma’abocin ƙwarewa ne da iko maɗaukaki-yana sanarwa ba tare da kokwanto ba kamar rana,marubucinsa da mawallafinsa da cikarsa da ƙwarewarsa kuma yana nuni i zuwa gare shi, kuma yana jawowa mawallafinsa girmamawa, da jumlolina madalla Allah ya yi albarka.
Kamar yadda yake a cikin wannan misalikwabo-da-kwabo , haƙiƙa mu muna gani da idanuwanmu haƙiƙa alƙalami yana aiki a cikin babban littafin nan na kasantattu, yana rubutawa a cikin fuskar ƙasa, wadda ita shafi ɗaya ne daga cikinsa, da a cikin lokacin kaka wanda shi wani ɗan ɓangare ne ɗaya daga cikinsa dubu ɗari uku na dangi tsirrai da dabbobi,waɗanda su suna matsayin littafi dubu ɗari uku a tsakaninsu akwai banbance-banbance baki ɗaya da suke shiga juna batare da rafkanuwa ba, ko kuskure ko cakuɗawa ko cuɗanyawa ba, tare da kyautacewa da tsarawa, wani lokaci yana rubuta ƙasida a cikin kalma ɗaya kamar bishiya da firasar littafi cikakke a cikin nuƙuda ɗaya kamar kwayar iri.
61. Page
Ina faɗin haƙiƙa wannan littafi na kasantattu da wannan halitta maigirma da Alƙur’ani mai siffa irin ta jiki wannan da yake fa’idantar ma’anoni waɗanda ba sa ƙarewa, wannan da yake ɗauke da hikimomi masu yawa a cikin kowacce kalma daga kalmominsa masu girma, yana sanar da girman darajarsa da girmansa da ƙayatarwarsa da yawan ma’anoninsa da hikimominsa littafi wanda aka ambata a cikin misali; mai zanennan na wannan littafin na kasantattu da mai rubutunsa tare da cikarsa wadda bata da iyaka a gwargwadon ma’aunai yalwatattu, da idanuwa wannan da suke kamar tabaron likita na ilimin hikimomin abubuwa wanda kuke karanta shi da fannin karatu da fannin rubutu waɗannan su biyun da kuke yinsu
62. Page
a aikace a cikin makaranta, kuma yana sanarwada shi da tsarkakewa سُبۡحَٰنَ ٱللَّه tsarki ya tabbata ga Allah Ta’ala kuma yana sa aso shi kuma a yabe shi da godewa ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِgodiya ta tabbata ga Allah.
To ƙiyasi a bisa waɗannan ilimai, haƙiƙa kowanne ilimi daga ɗaruruwan ilimai, yana koyar da sanin mahalicci mai girma na wannan kasantattun da sunayen sa, kuma yanasanar da siffofinsa da cikarsa ta hanyar nan ta ma’aunansa mayalwata da madubinsa wanda ya keɓanta da shi, da idanunsa da suke kama da tabaron likita, da dubansa mai lura.
Sai na faɗa ga waɗannan matasa ɗalibai: haƙiƙa Alƙur’ani da bayaninsa yake gajiyarwa, yana sanar da mu mahaliccinmu a maimaice a cikin mafi yawan lokuta da ayoyinsa.
63. Page
رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِdaخَلَقَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ
ubangiji sammai da ƙasa da mahallicin sammai da ƙasadon ya karantar wannan hujja da aka ambata, wadda ita ce dalilan ƙaɗaitaka mai girma mabayyaniya.
Waɗannan tare da rawar da suke takawa, sai suka karɓa suka gasgata cikakkiyar karɓa da gasgatawa, sai suka ce: muna godewa ubangijinmu ba tare daiyaka ba,a bisa cewa mumun samudarasi tsarkakakke da tsantsar haƙiƙa,Allah ya yarda da kai.
Ni kuma sai nace musu:
Haƙiƙa mutum ya kasance wani inji mai rayuwa, zai iya jin raɗadi da dubunnan nau’o’i na raɗaɗi haka nan ma zai iya jin daɗi da dubunnan nau’o’i na jin daɗi,Shi abin halitta ne miskini, yana da maƙiya na zahiri da na ma’ana da ba su da iyaka tare da gajiyawarsa ta saki ba ƙaidi, yana da buƙatu na fili da na boye, da ba su da iyaka tare da talaucinsa na saki ba ƙaidi, kuma abin halitta ne miskini yana haɗuwa da zafin saran nan na gushewa da rabuwa;amma idan ya danganta kansa i zuwa sarki ma’abocin girma ta hanyar imani da bauta sai ya sami ginshiƙi na jingina da zai
64. Page
fuskanci dukkan maƙiyansa, da kuma ginshiƙina madadida zai tabbatar da dukkan buƙatunsa.
Sau da yawa yana zama mai farinciki da godiya, sau da yawa zai yi alfahari a cikin godiya - kamar yadda kowa yake alfahari da ɗaukaka ta shugabansa wanda yake danganta kansa i zuwa gare shi- idan ya danganta kansa da ibada i zuwa sarki mai ƙudura da rahma ta saki ba ƙaidin ta hanyar imani,yayi masa hidima ta hanyar bauta, ya juyar da sanarwar nan ta rasuwa na ajali i zuwa tikitin nan na sallama a haƙƙinsa, sai ku yi ƙiyasi.
65. Page
Kamar yadda na faɗa ga waɗannan ɗalibai, ina faɗi ga tsararru waɗanda aka jarrabesu, tun daga farko: wanda ya san Allah S.W.T. kuma ya yi masa biyayya mai arziki ne mai jin daɗi ko da ya kasance a cikin kurkuku, kuma wanda ya manta shi a cikin kurkuku yake da wahala ko da ya kasance a cikin fadoji.
Har dai cewa abin zalunta, mai arziki da rabauta, ya faɗa ga azzalumai masu ƙeƙasassun zuciyoya a sanda za a rasarda shi: “ haƙiƙa ni ba za a rasar dani ba, bari dai, zanyi ƙaura ne i zuwa arziki da jin daɗi na har abada ta hanyar sallama,Sai dai cewa ni zan ɗauki fansa yayin da na ganku an yi hukunci akanku da rasuwa ta har abada” sai ya miƙa ransa a cikin farin ciki yana mai faɗin Kalmar shahada
لَآ إِلَٰهَ إِلا ٱللَّهُ ّ
سُبۡحَٰنَكَ لَا عِلۡمَ لَنَآ إِلَّا مَا عَلَّمۡتَنَآۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡحَكِيمُ


