Mas’ala muhimmiya da aka yimin ilhamarta katsahan

18. Page

Sannanhaƙiƙa hankalinka da ruhinka da zuciyarka da jinka na zuciya suna tattaruwa a cikin al’amura munana na maƙasƙanciyar zuciyya da na soye-soyen zuciya mai muni daƙazanta, da suke taimakonta suna barin ayyukansu maɗaukaka,a saboda haka kai kana ɗaukaka a bisa masuimani a cikin duniya, kumakana bayyana da kamar nan da aka fi so fiye da su a zahiri; domin cewa hankalinka da zuciyarka da ruhinka, sun ƙasƙanta sun koma baya sun faɗa mafi ƙasƙanciyar daraja, sai suka juya i zuwa kwaɗayi mai muni da ƙazanta, da rai maƙasƙanci wulaƙantacce munmuna sai aka shafesu; to babu shakka, ta haka za ka sami wata ‘yar ɗaukaka tawani ɗan lokaci wanda zai kaika jahannama, kuma masu imani waɗanda aka zalunta za su rabauta da shiga Aljanna.

Mas’ala muhimmiya da aka yimin ilhamarta katsahan

Za a fahimta daga ruwayoyin hadisai cewa waɗanda za su taka rawa mafi haɗari a cikin fitinar ƙarshen zamani su ne mata da fitinarsu[1].


[1] ya zo a cikin littafin sahihul muslim 4/2098 Hadidi mai lamba 2742 “muhd bn musanna da muhd bn Bashar sun ce muhd bn Jafar ya yi mana Hadisi Shu’uba daga Abi salmata ya ce na ji Aba nadhara yana yin Hadisi daga Abi sa’id khuduri daga Annabi (S.A.W) ya ce: haqiqa duniya kamar wanni abuce mai zaƙi koriya, haqiqa Allah ya halifantar daku a cikinta don ya ga me za ku aikata, ku ji tsoron Allah ku ji tsoron mata; haqiqa farkon fitinar ‘yan bani Isra’ila ta kasance a mata, a cikin Hadisin Bashar, domin ya ga me za ku aikata”.

 




19. Page

Na’am; kamar yadda aka ruwaito shi a cikin tarihi, cewa yakasance a cikin zamuna da suka wuce wani kaso ne na sojoji da aka yi su na mata ƙwararru wajen amfani da makami matuƙar ƙwarewa, da ake ambatonsu da matan amazon[1] sun yi yaƙi mai tsanani;hakanan mataye masu tufafi matsiraita a cikin yaƙi na ɓatan zindiƙanci wanda aka fuskanci musulunci da shi a cikin wannan zamanin, su ne mafi haɗarin kashi wanda aka sallama jagorancinsa ga shaiɗan da shirin nan na zuciya mai yawan umarni da saɓo; domin suna kai hari kan masu imani da ƙwaurukansu matsiraita kai ka ce su wuƙaƙene masu kaifi, sai su ribace zukata masu yawa a cikin ƙiftawar ido, kuma su soki zuciyoyinsu da rawukansu da manyan zunubai, suna masu tafiya ne don kulle ƙofar aure da yalwata hanyoyin gidajen fasiƙanci da sharholiya,bari ma dai suna kashe wani sashin na waɗannan zukatan; a saboda haka ne waɗannan ƙwauruka masu kama da wuƙaƙe suke zama ƙiraren jahannama, waɗanda za a ƙona da farko kafin dukkan komai, sakamako maidacewa da bayyana waɗannan ƙwauruka a gaban waɗanda ba muharramai ba shekaru masu yawa,kuma ba za su samu namiji wanda ya dace da su ba, wanda suke nufin su rabauta sosai da shi, da suke buƙatarsa buƙata matsananciya da irin zubin halittarsu; saboda sababin tozarta mutuncinsu da gaskiya da ikhlasi a duniya,har dai da za su same shi da sai ya zama musiba a gare su.


[1] Mace mayakiya a cikin labarukan Rumawa ta shahara da sunan Amazon, an ruwaito cewa ya kasance akwai wata jama’a ta mayaka mata ana kiranta da matan amazon sun kasance suna amfani da makamai mabambanta a yakinsu, labaran yakunan rumawa suna cike da ambaton waxannan jama’a ta mata da yakunansu tare girkawa, wasu sashi daga masu bincike suna danganta koramar amazon ga waxancan matan 




20. Page

An fahimto daga ruwayoyin hadisai cewa sakamakon wannan halin na matan za su kasance ba su da muhimmanci,ba mai karesu ba mai abokantakar su babu daraja a gare su har zai kai a ƙarshen zamani zai kasance kula da mata arba’in a ƙarƙashin mutum ɗaya a wasu guraren domin rashin kwaɗayin aure, da rashin ba shi muhimmanci[1].


[1]Ya zo a cikin littafin Sahihul Bukhari 1/43 babin dauke ilimi da bayyanar jahilci Rabiat ya ce ba ya kamata ga xaya da yake da wani abu na ilimi ya tozartar da kansa: “Musaddad ya zantar mana ya ce Yahya ya zantar mana daga Shu’uba da Utada daga Anas ya ce lallai zan zantar da ku hadisi wanda wani a bayana ba zai zantar da ku shi ba na ji Manzon Allah (S.A.W) yana cewa”yana daga alamomin tashin alƙiyama: ilimi zai qaranta jahilci zai bayyana, zina za ta bayyana, mata za su yi yawa maza su yi qaranci har dai ya zamana namiji xaya ne zai kula da mata hamsin”.

 




21. Page

Tare da cewa haƙiƙa haka yake,kuma cewa dukkan mai kyau yana son kyaunsa, yana aiki don kiyayeshi gwargwadon iyawarsa ba ya son narkewarsa, duk da cewa kyau ni’ima ce, to ni’ima tana ƙaruwa, a ma’ana mutuƙar akwai godiya, kuma tana jirkita ta munana idan babu godiya.

To idan mai kyau ta kasance mai hankali ce; toba makawa za ta gudu da dukkan ƙarfinta domin kar ta yi amfani da wannan kyaun a cikin hanyar samun zunubai, ko ta sanya wasu su sami wannan zunuban, ko ta sa wannan kyaun ya zama mummuna mai guba, ko kuma ta canza shi, ya zama sabbabin azaba a gare ta, saboda butulcewa ni’ima,saidai da sannu za ta yi godiya a kan wannan ni’ima ta hanyar aiwatar da wannan kyaun mai gushewa wanda yake dawwama shekara biyar ko goma kaɗai. A irin aiwatarwar da sharia ta yarda daitacekawaiharta sanya kyau ya zama mai wanzuwa, idan bahaka ba sai ta sa mutane duk su kyamace ta zamani mai tsawo a tsufanta, sai ta yi kuka irin kuka na masuɗeɓe ƙauna.

Amma idan aka ƙawata wannan kyaun da kwalliyar nan ta laduban Alƙur’ani a cikin da’irar tarbiyar musulunci sai ya zama a -ma’anan ce-wannan kyau ƙararre wanzajje ne, wanda za a ba wa ma’abociyarsa a cikin aljanna, kyau mai taushi wanda ya fi kyaun matan aljanna, wannan tabbatacce ne tabbata yankakkiya a cikin hadisai maɗaukaka.

Idan dai akwai gwargwadon ƙwayar zarra na hankali a wajen wannan mai kyaun; da ba ta tozarta wannan falalar mai kyau mai haske mai taushi na har abada a hannunta ba.