Na biyu

121. Page

Na biyu: A dangane da abin da shugaba Ra’afat’ da shugaba Mustapa Arwaj suka rubuta a Istanbul, shi ya kasance a rubuce a gaban goshin gini mai girma na ma’aikatar tsaro da jagoranci na dukkan sojoji – wanda ya gudanar da sojojin musulunci shekaru masu yawa, sannan sai aka juyar da shi i zuwa jami’a-, ayoyin Alƙur’ani masu ma’ana da rubutun irin na Alƙur’aniوَيَنصُرَكَ ٱللَّهُ نَصۡرًا عَزِيزًا da  إِنَّا فَتَحۡنَا لَكَ فَتۡحٗا مُّبِينٗاhaƙiƙa an ɓoye waɗancan ayoyi da duwatsu masu ado na tangaran kuma aka lulluɓe waɗancan hasaken.


122. Page

To yaye rufin wannan ayar ishara ce i zuwa cewa ita za ta zama misali na sake samun dammar rubutu da haruffana Alƙur’ani kuma tsani ne i zuwa tabbatar da manufa da Rasa’il annur take so ta cimma,kuma haƙiƙa jami’ar za ta zama makarantar Nuriyya a nan gaba.

A cikin wani ɓangarorin rubutu wanda Ahmadai biyu waɗanda ɗalibai ne biyuna nur a birnin Danizili suka ciro daga littafin Bisamariƙ malamin nan mashhuri da mafi girman mutane a ƙarni na goma sha tara a wajen hankali, kuma mafi girman ‘yan falsafar rayuwar al’umma, yana cewa Bisamarik mai girma a cikin littafinsa:haƙiƙa ni nayi tsokaci a cikin Alƙur’ani daga kowanne bangare, kuma na ga hikima mai girma a cikin dukkan kalmamominsa, to  ba shi da makamanci, kuma babu wani littafi da zai iya gudanar darayuwar don adam koma bayansa, kuma ba ya yiwuwa a samu.


123. Page

Kuma yana faɗa ga manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi: Ya Muhammad alaihissalam, haƙiƙa ni ina matuƙar baƙin ciki, domin cewa ni ban haɗa zamani tare da kai ba, haƙiƙa ‘yan’dam sun ga ƙayataccen iko kamar kai sau ɗaya tak, da ba za su taɓa ganinsa a wani karin ba, gini a kan haka. ina ruku’u a gabanka tare da cikar girmamawa, sai ya sa hannu a cikin zancensa ya rubuta Bisamarik[1].

Haƙiƙa ni nayi nuni i zuwa ga cewa yana wajaba kada a rubuta waɗancan jumlolin,domin cewa shi yana tauyewa daga sha’anin littattafai saukakku da aka jirkita su waɗanda aka shafe hukuncinsu tawaya mai girma, a cikin wancan zancen nasa na cikin littafinsa.

Haƙiƙa cewa shi yana daga kyaun tsinkaye wannan mutum ya zama shi ne mafi hankalin filosafofi da mafi girmansu a cikin ƙarni na goma sha tara, kuma ɗaya daga cikin mutane mafi muhimmancin mutane a cikin siyasa da zamantakewar ɗan’adam, kuma duniyar musulunci ta samu ‘yan cinta zuwa wata iyaka, kuma hukumomin

[1] Za a iya sa zancen nan na Ahmadain wannan da aka samu daga littafin Bisamarik a cikin wannan saƙon nawa, amma za ku iya cire kalmomin da ba su daceba daga cikinsa.




124. Page

Turawa su dinga kardadon tabbatattun haƙiƙoƙi na Alƙur’ani, kuma ya kasance akwai wata jama’a mai girmaa yamma da arewa maso yamma suna aiki don ci gaban Alƙur’ani.

Hukuncin mista Karliyal[1] wanda shi ne mafi girma da shaharar fulosafofi a Amirka kamar yadda Bisamarik ya ce: (haƙiƙa dukkan wasu littattafai ba su kai Alƙur’ani ba ta kowacce fuska daga fuskoki,faɗinsa kuma shi ne faɗin gaskiya, yana wajaba mu yi sauraro a gare shi) hukunci ne yankakke[2],kuma buɗe-buɗen nan na Rasa’ilul nur a dukkan gurare da yaɗuwarsu,dukkan waɗannan busharori ne na alheri mai girma;dan da sannu za a samu da yawa kamar Bisamarik da mista Karliyal a tsakankanin Turawa , kuma akwai alamomi  a bisa haka, ina mai bijiro da wannan barka da sallah ga masu bin Rasa’il annur, kuma muna aiko zancen Bisamarik tare da wannan saƙon namu.

Ina gaishe da kowa da kowa.

الباقي هو الباقي

Wanzajje shi ne wanzajje

Ɗan’uwanku

Sa’id an-nursi

 


[1] Thomas Karlayal: mashahurin marubucin turanci ne, yana daga mafi muhimmanci littattafansa: (jarumai) ya rubuta a cikinsa babi mai qayatarwa a kan Annabi (S.A.W)

[2] Tafsirin (isharori masu gajiyarwa) na larabci wanda daya ne daga littattafan Rasa’il nur ya yi nuni zuwa ga hukuncinsa mai kima mai neman gaskiya don ya tabbatar da ita tun kafin shekaru talatin




125. Page

 

Bayanin Bisamarik a cikin “Risalar Ahmadai biyu”

Shugaban mu malaminmu mai girma.

Mun bijiro muku, shugabanmu, kuma malaminmu maganganun nan na yarima Bisamarik wanda yana cikin mashahuran masu hikimar ƙasar Jamus, maganganunsa