TATACCEN BAYANI NA “SHI”
NAVIGATION
109. Page
TATACCEN BAYANI NA “SHI”
Da sunansa tsarki ya tabbata a gare shi babu wani abu sai yana tasbihi da godiyarsa, amincin Allah da rahmarsa da albarkakatunsa na har abada madawwama su tabbata a gare ku.
السلام عليكم ورحمة الله و بركاته أبدا دائما
‘Yan’uwana, masu girma masu gaskiya:
‘Yan’uwana na gani a cikin nuƙɗa na tauhidi mai taushi an nunamin shi a wani ɗan lokaci ta hanyar tsinkaye a cikin shafin iska[1], a cikin jihar abubuwan zahiri kawai, a lokacin tsattsakin tafiya na saƙe-saƙen zuciya da tunani a cikin lafaziهوshi da yake cikinلَآ إِلَٰهَ إِلَّاٱللَّهُ
َda wanda yake cikinقُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ; haƙiƙa hanyar imani mai sauƙi ce a matuƙar sauƙi da sassauci, mai sauƙi ceda darajar nan ta wajabci,kuma haƙiƙa hanyar nan ta shirka da ɓata a cikinta akwai dubunnan korarrun abubuwa waɗanda ba za su faru ba, masu matsaloli, zan bayyana wancan nuƙɗa mayalwaciya mai tsawo a cikin ishara taƙaitacciya.
Na’am, kamar yadda cikin tafin hannu na ƙasa a cikin ƙwarya yake zama wajen raino na ɗaruruwan nau’o’i na furanni -fure bayan fure- da an jingina al’amuransa i zuwa ɗabi’a da sababbai da ya lazamta ya zama a cikin waccan ƙwarya ko dai ɗaruruwan injina da ma’aikatu ƙanana na ma’ana da adadin furanni, ko dai kowacce ɗaya na daga ƙwayoyin zarrorin nan ƙanana na cikinwannan cikintafin na turɓaya tasan yin
[1]Da take filfilawa a sararin subhana.
110. Page
ƙirar dukkan furanni mababanta manau’anta da keɓance-ƙeɓancensu masu sassaɓawa tare da gaɓoɓinsu na sassa, kai ka ce su ubangiji ne da ke ɗauke da wani ilimi wadda ba ya tiƙewa, da iko wanda ba shi da ƙarshe.
Hakanan yake, wajaba ya zama a cikin kowanne yanki na iska da guguwa waɗanda su biyun su ne -shimfiɗar umarni da nufi- kuma da a cikin iskar nan da take a cikin lafazinهوshi-wacce ita ce a gwargwadon numfasawa da gwargwadon gaɓa ɗaya na ɗan-yatsa- cibiyoyi masu karɓa da masu miƙawa na dukkan wayoyin hannu da talgirafofi da rediyoyi da zantuttukamababanta waɗanda ba su da iyaka waɗanda suke samanmu a cikin dukkan wannan duniya har dai ta tsaya da yin dukkan waɗannan al’amura gaba ɗaya a lokaci ɗaya.
Ko yana kamata ya kasance ga dukkan ƙwayar zarra na daga ƙwayoyin zarrorin yanki-yankin iska na lafazin هوshi kai! dukkan ƙwayar zarra na daga ƙwayoyin zarrorin yanki-yankin iska jikkuna na ma’ana, kuma shiri da adadin dukkan ma’aikatan wayar hannu, da kuma adadin ma’aikatan tarho, da adadin waɗannan da suke magana cikin rediyoyi ya kamata ya san harshensu gaba ɗaya, ya sansu ya yaɗa su a cikin lokaci ɗaya i zuwa wasu ƙwayoyin zarrorin don cewa wannan abin da muka ambata ana ganinsa a cikin iska a aikace, kumadukkan yanki na daga yankunan iska yana ɗauke da wannan shirin.
111. Page
To a cikin hanyar nan ta ma’abota kafirci da ‘yan ɗabi’a da ma’abota zahiri ba a ganin abin da ba ya yiwuwa ɗaya kawai, bari za a gani a fili ƙuru-ƙuru abubuwa marasa yiwuwa da hanannu da matsaloli da adadin ƙwayoyin zarrori.
Kuma idan aka jingina -al’amarin iska- i zuwa maƙeri ma’abocin girmame - girmame sai iska ta kasance da dukkan ƙwayoyin zarrarta soja ne mai shiri ne ga bin umarninsa mai girma da ɗaukaka sai ya iya tsayawa da ayyukansa dukka waɗanda ba su da iyaka - kamar misalin aiki ɗaya tsararre na ƙwayar zarra ɗaya-da sauki tare da izini da ƙarfin mahaliccinsa, tare da dangantaka da jingina i zuwa gare shi,da tajallin ikon maƙerinsa a cikin ƙibtawar ido da irin saurin walƙiya da irin sauƙin,
112. Page
furta lafazinهوshi da irin juyawar nan ta iska, ai ta zama -iska-shafi ne na rubuce-rubuce da ba su da iyaka ƙayatattu tsararru na alƙalamin nan na ƙudura, sai ƙwayoyin zarrarta su kasance kawukan wancan alƙalaminne, kuma ayyukan nan na ƙwayoyin zarrori sai su kasance ɗige-ɗigenalƙalamin ƙudurasai ya yi aiki tare da sauƙi kamar irin sauƙin nan na motsawar zarra ɗaya.
Yayin da na kasance ina tsokaci ga alam na iska kuma ina karanta shafin nan na dangin iska a cikin wannan tsokacin nan nawa na tunani a cikin kalmar shahada da ƙul Huwal Lahu Ahad لَآ إِلَٰهَ إِلَّاٱللَّهُ
َ da قُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ na ga wannan haƙiƙa dunƙulalliya afili firi-falo da rarrabewarta da kallo na yaƙini.
Kamar yadda yake a lafazin هو shi kadaitakarsa kamar wannan dalilin mabayyani, da kamar wannan hasken na kaɗaitaka, hakanan ma a cikin ma’anarsa da isharorinsa ɗayantaka maihaske ƙwarai take bayyana, da hujjar tauhidi mai ƙarfi ƙwarai, sai nayi sani, sani na yaƙini, kumaAlƙur’ani mai girma da ma’abota zikiri, sunamaimaitawannan kalmar da yawa a muƙamin tauhidi don akwai mahaɗa ayyananniya a cikin waccan hujjar ga wannan tambayar: gawa take fuskanta wannan ishara ta saki ba ƙaidi da wadda take a ɓoye ta lamirinهوshi?
113. Page
Na’am; duk da cewa shi idan aka sanya nuƙoɗoɗi biyu ko uku a bisa farar takarda a cikin kewayen nan na nuƙuɗa ɗaya to haƙiƙa dukkansu za su cakuɗe, kumaidan mutum ɗaya ya yi ayyuka mabambanta masu yawa haƙiƙa al’amura za su cakuɗe masa,kuma idan aka ɗora nauyaye-nauyaye masu yawa a bisa ƙaramin ma’abocin rayuwa toshi zai sha wahala ya yi rauni a ƙarƙashin su, kumaidan kalmomi masu yawa suka fita daga harshe ɗaya suka shiga cikin kunne ɗaya tare a cikin lokaci ɗaya to haƙiƙa shi tsarin zai ɓaci saicaƙuɗeɗeniya ta abku, duk da haka;haƙiƙani ni na gani da ido na yaƙini haƙiƙa shi an sanya -ko zai yiwu a sanya - dubunnai na daga nuƙoɗoɗi da haruffa da kalmomi mabambanta a cikin dukkan yanki na daga yanki-yanki na dangin iska wadda take kekkewayawa a cikinsa ta hanyar tunani da
114. Page
mabuɗin lafazinهوshida kamfas ɗinsa,[1]kai har a cikin dukkan ƙwayar zarra daga ƙwayoyin zarrorinsa, ba tare da ya cakuɗa ko tsarinsa ya lalace ba.
Kuma duk da cewa kowanne yanki da ƙwayar zarra yana tsayawa da ayyuka masu yawa ƙwarai to shi yana yinsu ba tare da kuskure ba ko rafkanuwa ba, kuma duk da ana ɗorawa wancan yankin da waccan ƙwayar zarra nauyaye-nauyaye masu nauyi da yawa sai dai su suna ɗaukansu a cikin tsari tare da kyautatawa ba tare da nunarauni da gajiyawa ba, ba tare danuna jinkiri ƙin dauka ba.
Kuma tare dacewa dubunnan kalmomi suna shiga waɗancan kunnuwa ƙanana,kumasuna fitowadaga waɗancan harasa ƙanana sirara tare da cikar tsari, tare da kamanni da ma’anoni masu tsereneniya ba tare da cuɗanya ko ɓaci ba,kuma duk da cewa dukka waɗancan ƙwayoyin zarrorin da yanki -yanki ƙanana suna tsayuwa da wannan ayyukan masu ban mamaki kuma suna kewayawa tare da cikar ‘yanci suna masu faɗi a cikin nishaɗi da jazba[2]da harshen hali da harshen haƙiƙa wadda akaambata da shaidar ta
[1] - Alama nuna jihohi, arewa, yamma da kudu.
[2] - Fita daga hayyaci, saboda shauƙi.
115. Page
لَآ إِلَٰهَ إِلَّاٱللَّهُ
َdaقُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌkalmar shahada da ƙul Hul Lahu Ahad ; cewa tsarinsu ba ya ɓaci, rashin tsari ba ya shafar ayyukansu har abada duk da guguwar nan da walƙiya da tsawa da jujjuyawar iska waɗannan da suke sanya iska ta zama mai hargitsewa, kuma yin aiki ba ya hana su aikata wani aikin,hakannan na ga waɗannan al’amura da gani na yaƙini.
To wannan yana nufin cewa shi yana kamata ya kasance a cikin dukkan ƙwayar zarra daga ƙwayoyin zarrorin iska, kuma a cikin kowanne yanki na yankunanta hikima da bata da ƙarshe, da ilimi da nufi waɗanda ba su da ƙarshe, da ƙarfi da iko da ba su da iyakada keɓanta da take hukunci kan dukkan ƙwayoyin zarra hukunci na saki-ba-ƙaidi, domin su zama masu yin waɗannan al’amuran ne, towannan mara yiwuwa ne kuma batacce ne da adadin ƙwayoyin zarrori, kaihar dai shaiɗan ma ba zai iya tunani a kansa ba.
116. Page
A saboda haka haƙiƙa shafin nan naiska wanda shi ne – kai tsaye darajar gaskiyar yaƙini da ainihin yaƙini da ilmin yaƙini-shafi ne abin canjawa na alƙalamin ƙudura da ƙaddara wannan da maƙeri Ma’abocin girmame-girmame yake aiwatar da shi a cikin ilimi da hikima waɗanda ba su da ƙarshe,kuma yana matsayin ’’allon shafewa da tabbatarwa ’’na lauhil mahafuz a cikin alam na canjawa, da kuma a cikin sha’anonin nan ababan canjawa.
Kamar yadda iska take bayyanawa a cikin aikinta na ɗaukar murya da isar da sautuka,tajallinɗayantaka wadda aka ambata kuma da ababanbada mamakai waɗanda aka ambata, kuma tana bayyana koruwar ɓata mara iyaka a cikin ɗaya daga ayyuka muhimmai na iska haka nan, su ne tsayuwa da wasuayyukan waɗanda su ne: tsayawa da aikin ɗaukowa da isar da dukkan tausasa[1], kamar lantarki da fizga da ijewa da haske ba tare da kuskure ba, tare da kyautacewa da tsari,kamar yadda yake a cikin lokacin kansa tana tsayuwa da dukkan abubuwan da suka wajaba akanta na ɗaukowa da isar da sautuka tare da waɗannan abubuwa wajibabbu tana taimako da gaggawa da cikakken tsari da waɗannan abubuwan waɗanda suke na lalle ga rayuwar dukkan tsirrai da dabbobi kamar numfashi da kilili ko baye, kuma tana tabbatarwa ba da kokwanto ba, cewa ita gadon mulki ce na al’amarin ubangiji da nufinsa.
[1] Abubuwan da ba su da jiki kuma ba a iya tabasu ko ganinsu.


