Saƙo na bakoy

20. Page

SAКO NA BAKWAI

Haƙiƙa sunnah mai haske ladabi ne mai gwaɓi, babu wata mas’ala daga mas’alolinta sai dai akwai haske da ladabi a cikinta, kuma

Manzon Allah tsira da amini su tabba a gare shi ya ce: "أدبني ربي فأحسنى تأديبي"

ubangijina ya tarbiyantar da ni, kuma ya kyautata tarbiya ta[1].

Haka ne haƙiƙa wanda ya kyautata duba a cikin sirar Annabi, kuma ya san sunnoni masu haske, zai sani yana mai yaƙini cewa mai gaskiya maɗaukaki, ya taro dukkan nau’o’in laduba ya bawa masoyinsa (S.A.W), to wanda yake barin sunnarsa, haƙiƙa shi yana barin ladabi, halinsa yana kasancewa mai dacewa da wannan ƙa’idar: "بي أدب محروم باشد أزلطف رب"[2]


[1] Duba hadisi a cikin littafin: Al’imta’i Bil Arba’inal Mutabayyinat Alsima’i Li Ibn Hajar, ya faxa a cikinsa. Al-askari ne ya fitar da shi, amma mai rauni ne. Kuma yi duba i zuwa littafin, Kanzul Ummal 11/186 da kuma cikin Asnal Madalib shafi na 35, a cikin sanadinsa akwai rauni, amma ma’anarsa ingantacciya ce.

[2] - Ibara ce ta Farisanci, tana nufin, mai ƙarancin ladabi an haramta masa falalar Allah da kyautatawarsa. 




21. Page

“haƙiƙa mai ƙarancin ladabi ana haramta masa falalar Allah da kyautatawarsa”, (kamar yadda ya zo da harshen Farisanci a sama, mai mummunan ladabi yana zama ma’abocin hasarori.

Tambaya: yaya ladabi zai kasance tare da masanin abin da yake a ɓoye masani mai ganin dukkan komai, wanda ba a ɓoye masa komai tare da cewa shi ba ya yiwuwa a ɓoye masa halaye waɗanda za su sa jin kunya, haƙiƙa nau’i na daga nau’ukan laduba shi ne suttura da suturcewa da ɓoye halaye da suke wajabta ƙyamatar nan ta zuciya da tsana, shin zai yiwu a suturce su ga masanin abin da yake fake?.


22. Page

Amsa:

 Na farko: kamar yadda haƙiƙa mahalicci jalla yake so ya bayyana ƙirarsa da ƙayatarwarsa da ƙwarewarsa su zama masu kyau tare da cikar kula da muhimmartarwa, da suturce al’amura masu sa ƙyama waɗanda ake guje musu da labulaye, kuma yana ƙawata ni’imominsa, don ya waiwayo da idanuwa i zuwa gare su; domin haka ne ma yake so ya bayyana halittunsa da bayinsa a cikin surori da 

23. Page

halaye masu kyau a gaban ma’abota wayewa da riska; domin bayyanar su a cikin hali munmuna yana kasancewa saɓo ne da wani nau’i na munana ladabi ga sashin sunayensa kamar Aljamil da Almuzayyin da Al-ladifu da Al-hakim, hakanan ladabi wannan da yake cikin sunnah mai haske shi ado ne ga ladubba tsantsa cikin kewayen iyakokin sunayen wannan mahalicci ma’abocin girma.

Na biyu: kamar yadda likita yake kallo i zuwa mafi girman gaɓɓai haramci na matan da suka haramta a gare shi ta wajen buƙatar yin magani, ake buɗe masa su a wajen larurah, ba a cewa wannan munana ladabi ne, bari, sai dai a ce ladabin likitanci yana hukuntar da haka, a lokacin da wannan likita ba ya halatta a gare shi ya yi duba i zuwa matar nesa a gare shi da siffarsa ta namiji ko mai wa’azi ko mai kira, ko malami, ko shaihi ko masani, ladabi ba ya halattawa matan bare su bayyana ta (wannan gaɓar) a gare shi, to bayyanawarta a gare shi, ta wannan fuskar shi rashin ladabi ne da ƙarancin kunya. 


24. Page

Haka nan mahalicci ma’abocin girma yana da sunaye masu yawa, kuma kowanne suna yana da tajalli na musamman keɓaɓɓe, misali kamar yadda sunnan “Al-gaffaru” yana hukuntar da samuwar zunubai, kuma sunan Al-sattaru yana hukuntar da samuwar taƙaitawa, haka nan ma sunan Al-jamil ba ya son ya ga muni, haka nan sunayensa da suka shafi ɓangaren kyau da cika, kamar: Al-laɗif da Al-karim da Alhakim da Al-rahim

suna hukuntar da samammu su kasance a cikin sura mafi kyau da mafificin hali da zai iya samuwa.

Waɗannan sunaye da suka shafi ɓangaren kyau da sunaye da cika, suna so suga kyaunsu ta hanyar ganin nan na mala’iku da rauhanai da aljanu da mutane ta yanayai masu kyau na samanmu da kyaun ladubansu.

Hakanan, laduban da suke cikin sunnah mai haske, nuni ne i zuwa waɗannan laduba maɗaukaka da dokokinsu da misalansu.