Saƙo na biyar

13. Page

SAКO NA BIYAR

Haƙiƙa aya mai girma (قل إن كنتم تحبون الله فاتبعوني يحببكم الله) (آل عمران: 31) tana bayyanawa da sanarwa, sanarwa yankakkiya a kan matuƙar muhimmancin bin

sunna .

Na’am, haƙiƙa wannan aya mai girma ita ce mafi ƙarfi da mafi tabbatarwa wajen ƙiyasi daga nau’in “ƙiyasin nan na togacewa[1]” na daga ƙiyasosin manɗiƙi, shi ne kamar haka:

Kamar yadda ake cewa a cikin manɗiƙi ga ƙiyasin togacewa, misali:

"إن كانت الشمس طالعة فالنهار موجود".


[1] Kiyasin nan na togacewa, shi ne kiyasin da ake ambato a cikin farkonsa wannan natijar ko akasinta, ai savaninta. Kamar yadda yake a cikin misali da aka ambata, yi duba a cikin ma’anarsa a littafin ‘Mausu’atu Musxalihat Ilmul Manxik Indal Arab’. Shafi na 683.




14. Page

“in dai rana ta fito to lalle wuni yana nan”. kuma ana faɗa misali, a kan natijar nan mai tabbatarwa:

"لكن الشمس طالعة فالنتيجة إن النهار موجود"

Tunda dai rana ta fito sakamakon haka, lallai yini zai zama samanme. Ana kuma faɗa a cikin sakamakon nan mai korewa:

"لكن النهار ليس موجود فالشمس ليست بطالعة".

Tun da dai yini ba ya nan to rana bata fito ba.

Waɗannan sakamako guda biyu mai tabbatarwa da mai korewa, yankakku ne gwargwadon ilminnan na manɗiƙi.

Kamar yadda yake a cikin wannan ƙiyasin cikakke, Ayar nan ta sama tana faɗi: “idan kun kasance masu son Allah, ya wajaba a kanku bin masoyin Allah, Idan ba ku bi shi ba, sakamakon shi ne ba ku son Allah, idan dai akwai son Allah a gare ku, to haƙiƙa wannan soyayyar za ta haifar da bin sunnah mai haske ta masoyin Allah”. 


15. Page

Hakayake; haƙiƙa wanda ya yi imani da Allah babu kokwanto cewa shi zai bishi, kuma babu kokwanto cewa mafi kyaun hanya da mafi taƙaitarta da mafi daidaituwarta a tsakan kanin hanyoyin biyayya, ita ce wannan hanyar da masoyin Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi wanda ya shiryar i zuwa gare ta kuma ya bita.

Na’am, haƙiƙa karimi ma’abocin kyau -wannan da ya cika wannan duniya da gwargwadon waɗannan ni’imomin -, babu makawa cewa zai nemi godiya daga ma’abota wayewa da fahimta kwatankwacin waɗannan ni’imomin.

Haƙiƙa karimi jalla -wanda ya ƙawata wannan duniyar da wannan gwargwado na daga mu’ujizozin ƙirƙirarsa-, babu kokwanto cewa shi zai riƙi mafificin mutum a tsakankanin ma’abota wayewa da fahimta da zai dinga Magana da yawunsa da kuma mai yi masa tarjama, da zai bayyana abin da yake nufi mai isarwa da kuma shugaba ga bayinsa.


16. Page

Haƙiƙa wannan kyakkyawa ma’abocin cika - wanda ya sanya wannan halitta mabayyanar abin da  ba shi da iyaka na tajallin kyaunsa da cikarsa- , zai bayar ba da kokwanto ba kuma a bayyane ,mafificin hali na bauta ga wanda shi ne mafi tarowa da ƙayatarwar abin ƙiyasi, da tushen abin da yake sonsa da son bayyanarsa na daga kyau da cika da sunaye da ƙayatarwa, da sannu zai sa halayensa su zama koyi da kwaikwayo ga sauran (jama’a), kuma ya zaburar gaba ya kwaɗaitar da kowa  a bisa binsa, har dai halayensa kyawawa su haskaka  a bisa sauran mutane. 

A ƙarshe:

Haƙiƙa son Allah yana lazamtar da bin sunnah mai haske, farin ciki ya tabbata ga wanda rabonsa ya zama yalwatacce ne ga bin sunnah mai haske, baƙin ciki da taɓewa sun tabbata ga wanda ba ya ƙimanta sunnah mai haske kuma yake kutsawa cikin bidi’a.