Sako na biyu

4. Page

Saƙo na Biyu:

Limami Rabbani, Ahmad Alfaruƙi[1], Allah ya ƙara yarda a gare shi ya ce: (ni na gani yayin da nake yanke matakai na daraja a cikin tafiyar nan ta ruhi na imani cewa mafi hasken matakai na waliyyai da mafi girmansu da mafi taushinsu da mafi kuɓutarsu, shi ne matakin nan na masu riƙo da bi ga sunnah mai haske a matsayin tushe ga ɗariƙa, har dai waliyyai gama-gari a cikin wannan mataki sukan bayyana a matsayi mafi girma da mafi ƙayatarwa daga keɓantattun waliyyai a cikin sauran matakai).

Lallai haƙiƙa mujaddadi na shekara ta dubu biyu, Limami arrabbani, Allah ya ƙara yarda a gare shi, ya faɗi gaskiya, haƙiƙa wanda ya riƙi sunna mai haske a matsayin tushe a gare shi, zai samu matsayin soyayya a inuwar masoyin Allah, (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi).


[1] Shi ne Sheikh Ahmad xan Abdul’ahad Zainul Abidina Alfaruqi Alsarhandi wanda aka fi sani da mujaddadin shekara ta 2000, ya kasance malami ne masani mai aiki. Yana da littafi mai suna Maktubat da ya rubutu a cikin mujalldai uku. An haife shi a shekara ta 971A.H. a Indiya, ya yi wafati a shekara ta 1034A.H.