Saƙo na Farko

2. Page

Saƙo na Farko:                            

Manzo mafi girma tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ce: (wanda ya yi riƙo da sunnata a lokacin da rayuwa ta gurɓace yana da ladan shahidai ɗari).

قال الرسول الأكرم صلى الله عليه وسلم "من تمسك بسنتي عند فساد أمتي فله أجر مائة شهيد"[1]

Haka yake; yana daga abin da babu kokwanto a cikinsa, haƙiƙa bin sunna mai haske yana da matuƙar muhimmanci musamman a lokacin mamayar bidi’o’i da yaɗuwar su, a wannan lokacin ne darajar bin ta zai kasance mafi girma mafi ɗaukaka, haƙiƙa kiyaye mafi ƙarancin laduba na sunna mai haske musamman a lokacin da rayuwar al’umma ta gurɓace yana nuna tsoron Allah mai girma da imani tabbatacce.

Haƙiƙa bin sunna yana tunatarwa kai tsaye da Manzo mafi girma tsira da aminci su tabbata a gare shi. Wannan tunatarwa tana juyawa ta koma i zuwa jin halarto da ubangiji a zuciya, ka ga wanda yake kiyaye sunnah mai haske, har a cikin mafi sauƙin mu’amaloli har a cikin ladubba na ci da sha da barci; duk ayyukansa da

[1] Yi duba ga hadisin da aka karvo shi daga Xon Abbas a cikin littafin Zuhudul-Kabir na Imam Baihaqi mai lamba (118), da kuma a cikin Targib da Tarhib na Munzir sifili na xaya shafi na 62. Haka nan a cikin Mu’ujamil al’ausax na Xabarani da aka karvo daga Aba Hurairat (R A) da ruwayar “mai riqo da sunnata a lokacin gurvatar al’ummata yana da ladan shahidi”. A sifili na 5, shafi na 315. 




3. Page

yake yi na al’ada da ayyukansa na fiɗira sai su juye su zama ibada, da za a  ba shi lada a kan su, kuma su zama aiki ne na shari’a; domin cewa shi aikinsa na al’ada zai kasance tunaninsa yana zama a cikin biyayyar Manzo mai girma, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, yana surantawa cewa shi yana yin wasu ladubba na daga ladubban shari’a, sai ya zo masa a cikin zuciyarsa cewa shi tsira da aminci su tabbata a gare shi, shi ne ma’abocin shari’a, daga nan kuma sai zuciyarsa ta fuskanta i zuwa mai gaskiya maɗaukaki,[1] wanda shi ne mai shar’antarwa na haƙiƙa, sai ya rabauta da halartowar nan ta ubangiji, da yin wani nau’i na ibada.

Gini a bisa wannan sirri; haƙiƙa duk wanda ya yi riƙo da bin sunna mai haske ya mayar da ita al’ada a gare shi, haƙiƙa zai zama ya juyar da al’adunsa i zuwa ibadoji, zai iya yiyuwa a gare shi ya mayar da rayuwarsa duk ta zama mai amfani da samun lada a gare shi.


[1] - Allah mai girma.