Saƙo na goma

33. Page

SAƘO NA GOMA

Haƙiƙa a cikin ayar: (قل إن كنتم تحبون الله فاتبعوني يحببكم الله) (آل عمران: 31)

akwai taƙaita magana mai gajiyarwa[1] ; domin jumloli masu yawa an shigar da su a cikin waɗannan jumlolin guda uku kamar yadda ya zo a nan:

Wannan ayar tana faɗa; idan kun kasance kunyi imani da Allah; to babu shakka ku za ku soshi, tun da cewa ku kuna son Allah to haƙiƙa ku za ku yi ayyuka, kamar yadda yake so shi mai girma da buwaya, shi ne ku yi koyi da wanda yake sonsa, kuma koyi da wanda yake so yana nufin binsa, a duk sanda kuka bi shi Allah zai so ku, ku kuna son Allah don Allah ya so ku.


[1] - Na mu’ujiza. 




34. Page

Dukkan waɗannan jumloli ba wani abu ba ne sai dai taƙaitacciyar fassarar dunƙulalliyar ga waccan ayar, abin da take nufi shi ne: haƙiƙa mafi muhimmanci da mafi ɗaukakar manufa ga mutum shi ne ya samu tsantsan soyayyar Allah maɗaukaki, kuma Nassin wannan aya yana nuni i zuwa hanyar da take samar da wancan abin neman mafi ɗaukaka ita ce bin masoyin Allah tsarki ya tabbata a gare shi, da koyi da sunnar sa, kuma idan an tabbatar a wannan matsayinNuƙuɗoɗi uku suna bayyana wannan haƙiƙar abar Ambato, wadda take ƙarara a bayyane.

Nuƙuɗa ta farko: Haƙiƙa an halicci mutum kuma an ɗabi’ance shi a bisa soyayya da bata da iyaka ga mahallicin wannan halitta, domin cewa a cikin zubin halittar mutum akwai soyayya ga kyau da tsananin son cika, da so ga kyautatawa, 

35. Page

wannan soyayya tana ƙaruwa gwargwadon darajojin kyau da cika da kyautatawa, takan isa i zuwa mafi nisan darajoji na tsananin bege.

Haƙiƙa a cikin ƙaramar zuciya ta wannan mutum ƙarami ƙwarai an sa soyayya da za ta yalwaci dukkan halitta.

 Hakayake, haƙiƙa rubuta ababan rubutawa da gwargwadon dubunnan littattafai da suke a matsayin ɗakin littattafai a cikin ƙwaƙwalwa wadda take a matsayin ɗan akwati ƙarami ƙwarai gwargwadon ƙwayar waken soya idan ka kamanta ta da zuciya, yana nuni a bisa cewa wannan zuciyar ƙarama za ta iya tare dukkan halittu gabaɗayansu, za ta iya ɗaukar soyayya da gwargwadon yalwar nan ta halitta. 


36. Page

Hakayake, haƙiƙa rubuta ababan rubutawa da gwargwadon dubunnan littattafai da suke a matsayin ɗakin littattafai a cikin ƙwaƙwalwa wadda take a matsayin ɗan akwati ƙarami ƙwarai gwargwadon ƙwayar waken soya idan ka kamanta ta da zuciya, yana nuni a bisa cewa wannan zuciyar ƙarama za ta iya tare dukkan halittu gabaɗayansu, za ta iya ɗaukar soyayya da gwargwadon yalwar nan ta halitta.

Tare da cewa a cikin wannan zubin halitta ta mutum, an yi tanadin abubuwan da za su sa shi ya so kyautatawa da kyau da cika soyayya da bata da iyaka, tun da cewa wannan mahaliccin na kasantattu, yana da” kyau” mai tsarki da  ba shi da iyaka, wanda tabbatarsa, ta zama tilas saboda ƙawatattun zane da take bayyanashi kai tsaye ta hanyar gurabansa masu bayyana a cikin kasantattu, da kuma “cika” mai tsarki da bata da iyaka, wadda samuwarta tabbatacciya ce tilas da sababin zanen ƙirƙirarsa mai bayyana  a bisa waɗannan samanmu, da kuma “kyautatawa” da bata da iyaka wanda samuwarta tabbatacciya ce da yaƙini, bari dai da ganin ƙuru-ƙuru ga abubuwan da ba su da iyaka na daga nau’o’in kyautatawarsa da ni’imtarwarsa waɗanda suke tajalli a bisa dukkan ma’abota rayuwa; babu makawa haƙiƙa wannan -kyau, da cika da kyautatawa-, -suna hukuntawa ya kasance a gurin mutum-, wanda shi ne mafi tattarewa dukkan ma’abota wayewa da riska, shiri da mafi yawansu buƙata, da mafi yawansu tunani, da mafi tsanantar su bege- soyayya da bata da iyaka. 


37. Page

Haka yake, kamar yadda ga kowanne mutum akwai shiri na soyayya da bata da iyaka, ga wannan mahaliccin ma’abocin girmame-girmame, haƙiƙa wannan mahaliccin mai girma da ɗaukaka shi ne yake cancanta ya kasance abin so fiye da kowa a madadin kyaunsa da cikarsa da kyautatawarsa, har dai abin da yake wajen mutum mumini na daga soyayya nau’i-nau’i da alaƙa mai ƙarfi dangane da rayuwarsa da wanzuwarsa da jikinsa da duniyarsa da kansa da kuma dangane da samanmu, ba komai ba ne sai dai wani ɗan yayyafi ne ƙanƙani ga tanadin soyayyar ubangiji, bari har ji ( na jiki) na mutum nau’i-nau’i matsananci, ba komai ba ne sai jujjuyawa ga wannan shiri na soyayya da ‘yan yayyafai da suka riƙi surori mabambanta. 


38. Page

Yana daga abin da aka sani cewa: mutum yana jin daɗi da kasancewarsa a cikin farinciki da yalwa; haka nan ma yana jin daɗi da kasancewar duk waɗannan da yake da alaƙa da su a cikin farinciki da yalwa, kamar yadda cewa shi yana son wanda yake tsamo shi daga bala’o’i; haka nan yana son wanda yake tsamo masoyansa daga bala’o’i.

Haƙiƙa mutum idan ya yi tunani - gini  a bisa wannan hali na ruhi- , a cikin ni’ima ɗaya kawai daga tsakankanin nau’o’i na kyautatawa na ubangiji waɗanda ake zubo su  a bisa kowanne mutum da sannu zai ce: “kamar yadda mahaliccina ya tsamo ni daga rashi wannan da shi ne duffai na har abada, kuma ya bani wannan duniya mai kyau a cikin wannan alam; haka nan ma da sannu zai tsamo ni daga rashi da ƙarewa, waɗannan da su biyu rashi ne na har abada, idan ajali na yazo, kuma da sannu zai bani rayuwa ta har abada ƙayatacciya a cikin alam na wanzuwa dawwamanme, da sannu zaiyi ni’ima a gare ni da jiye-jiye na jiki na bayyane da na baɗini da za su fa’idantu daga dukan nau’uka na daɗin wancan alam da jin daɗinsa da kyaunsa, za su yi kaiwa da komowa da shaƙatawa a cikinsa; haka nan da sannu zai zubo  a bisa dukkan makusantana da masoyana da ’ya’yan jinsina -waɗannan da nake sonsu so matsananci da shaƙuwa da su, shaƙuwa mai ƙarfi- ni’imomi da yalwa wanɗanda ba su da iyaka, wannan ni’imtarwar da kyautatawa suna komowa i zuwa gare ni ni daga wata fuska; domin cewa ni ina samun farin ciki kuma ina jin-daɗi farin cikn waɗannan masoyan nawa. 


39. Page

Domin cewa a cikin kowanne mutum a kwai son kyautatawa wanda zai iya isa har i zuwa matsayin bauta da sirrin “mutum bawan kyautatawa ne “ babu kokwanto cewa shi a madadin wannan kyautatawa ta har abada da bata da iyaka, zai ce: “da ina da zuciya da ta kai yalwar kasantattu, da ya zamar min dole in cika ta da soyayya ga wannan kyautatawar, kuma da na so in cikata da ita; ko da ban iya yin wannan soyayyar ba a aikace, to ni da zan iya yinta ta hanyar shiri da imani da niyya da yarda da girmamawa da bege da lazamta da nufi” 

40. Page

Kamar haka kowa ya auna soyayya wadda mutum yake bayyanata ga kyau da cika da wannan soyayya da yake bayyanata ga kyautatawa, wadda da muka yi nuni i zuwa gare ta a dunƙule.

Amma kafiri haƙiƙa shi yana ɗauke da ƙiyayya da bata da iyaka da sababin kafircinsa, bari dai har yana ɗauke da adawa a cikin zalunci da wulaƙanci da tozartawa ga samanmu.

 

Nuƙda ta biyu: haƙiƙa son Allah yana lazamtar da bin sunnah Muhammadiyyah  a bisa ma’abocinta tsira da aminci su tabbata a gare shi; saboda soyayyar Allah ita ce yin abin da yake yardar da shi, abubuwan da suke yardar da shi suna bayyana ne  a bisa mafi cikar sura ta Manzon Allah (S.A.W). 


41. Page

Amma kamantuwa da shaksiyyar nan ta Ahmadiyya  a bisa ma’abocinta tsira da aminci su tabbata a gare shi, a cikin motsinta da ayyukanta, to ya kasu i zuwa fuska biyu.

Na farkon su: bangaren son Allah maɗaukaki; ta yadda cewa bin umarninsa da motsi da tasarrufi cikin kewayen ababan yardarsa suna hukuntar da wannan biyayyar; domin cewa mafificin limami a cikin wannan sha’ani shi ne shaksiyyar muhammadiyya a bisa ma’abocin ta tsira da aminci su tabbata a gare shi.

Ta biyun su: matuƙar cewa shaksiyya Ahmadiyya  a bisa ma’abocinta tsira da aminci su tabbata a gare shi, ita ce mafi muhimmancin wasila ga ni’imomin nan na ubangiji da ba su da iyaka, da ake kwararosu  a bisa mutane, babu makawa cewa shi (S.A.W) ya cancanci soyayya da bata da iyaka da sunan mai gaskiya maɗaukaki, 

42. Page

to mutum a irin zubin halittarsa yana so ya yi kwaikwayo da wanda yake so, idan haka zai yiwu, to waɗannan da suke son masoyin Allah, ya wajaba akansu su tafi -lallai- i zuwa kwaikwayonsa (S.A.W) da bin sunnarsa.

Nuƙɗa ta uku: Kamar yadda Allah yake da rahma da bata da iyaka hakanan ma yana da soyayya da bata da iyaka, kuma kamar yadda yake soyar da kansa soyarwar da bata da iyaka ta hanyar kyauwawan dukkan abubuwan da ya ƙera, waɗannan da suka kasance a cikin kasantattu, tare da ƙawatarwarsa wannan abubuwan da ya ƙera, hakanan haƙiƙa shi yana son ma’abota wayewa da riska daga abubuwan da ya halitta, waɗannan da suke son abubuwan da ya ƙera balle a cema waɗannan da suke fuskantar abubuwan da za su sa a so shi da soyayya, a saboda haka kowa zai fahimta a bayyane girma da ɗaukakan nufin fizgo kallon son ubangiji wanda dukkan tausashe-tausashen aljanna da ababan kyawunta daɗaɗe-daɗaɗenta da ni’imominta ba su zama ba, sai tajalli daga tajalliyoyin rahmarsa.

Tunda da cewa haƙiƙa samun soyayyarsa bata samuwa saida bin sunnah ahmadiyya da nassin zancensa maɗaukaki, to babu makawa bin sunnah Ahmadiyya shi ne mafi girman manufa ta mutum. Kuma mafi muhimmanci aikin mutuntaka.