Saƙo na hudu

8. Page

Saƙo na Huɗu:

Wata rana na samu kaina a cikin duniya mai ban mamaki, da kuma a cikin halin nan na ruhi da ya faru daga dangantakar mutuwa da kasancewarta da kuma haƙiƙa wadda take cikin ƙariyar (mutuwa gaskiya ce)” da gushewar nan ta duniya da ƙarewar ta, nayi duba sai na gan ni a matsayin jana’iza, ni kuma ina tsaye a kan jana’izozi uku manya muhimmai:

Ta farkonsu: haƙiƙa ni kamar alamar kan kabari ne a kan waɗannan jana’izozi na ma’ana na dukkan halittu ma’abota rayuwa, waɗanda suke da alaƙa da rayuwa ta, kuma waɗanda suka shuɗe a can baya. 


9. Page

Ta biyunsu: haƙiƙa ni ɗigo ne da ake shafe shi da sauri, kuma tururuwa ce da take mutuwa da gaggawa a bisa fuskar wannan zamanin, wanda shi alamar kabari ne a kan maƙabartar ƙwallon duniya a bisa kan jana’iza mai girma wadda aka binneta a cikin ƙabarin lokacin da ya shuɗe, na duka ma’abota rai waɗannan da suke da alaƙa da rayuwar nau’in ɗan’adam.

Na ukunsu: domin cewa haƙiƙa abkuwar mutuwar wannan halittar tabbatacciya ce a lokacin tashin alƙiyama; to haƙiƙa ita a duba na, kamar ta abku ne, sai na ga kaina a cikin ɗimuwa da sababin magagi na wannan jana’iza mai girma, da kuma a cikin rikicewa da ɗimaucewa da sababin mutuwarta, sai ya bayyana a gare ni haƙiƙa mutuwa ta –wacce ita tabbatacciya ce, kuma abkuwarta yankakke ne a nan gaba- tana faruwa yanzu, kuma dukkan samammu da dukkan masoya sun juya min baya a lokacin mutuwa ta, suka bar ni sai na zama ni kaɗai da sirrin  (فإن تولوا)

aka kora raina i zuwa lokacin da zai zo nan gaba wannan da yake a jihar abada, wannan da ya riƙi surar kogi wanda  ba shi da ƙarshe, ya kasance babu makawa daga faɗawa cikin kogin nan anso ko anƙi, muna so ko bama so. 


10. Page

Yayin da na kasance a cikin wancan hali mai ban mamaki mai baƙin ciki ƙwarai; sai ga Aya mai girma: (فإن تولوا فقل حسبى الله لا إله إلا هو عليه توكلت وهو رب العرش العظيم)

(التوبة: 129) Tana taimako na da wani taimako mai zuwa daga imani da Alƙur’ani, sai ta zama kamar jirgin ruwa a cikin matuƙar aminci da zaman lafiya, raina sai ya shiga cikin wannan aya tare da cikar aminci da farin ciki.

Na’am; na fahimta haƙiƙa ma’anah ta nuni ga wannan aya - daɗi a kan ma’anarta ta fili - haƙiƙa wannan fahimtar ta haƙurƙurtar dani, sai na samu nutsuwa, kuma sai ta bani kwanciyar hankali a zuci. 


11. Page

Na’am; kamar yadda ayar take faɗa a ma’anarta ta fili ga Manzo mafi girma tsira da aminci su tabbata a gare shi : ” idan ma’abota ɓata suka juya   bayansu suka bijirewa shari’arka da sunnarka, kuma ba su yi sauraro i zuwa Alƙur’ani ba; kada kasamu damuwa a zuciyarka kada ka yi baƙin ciki, ka ce: “Allah ya isar mini, ina dogara a gare shi, shi ne zai halicci ya reni wanda za su bi shariata da sunnata maimakon ku, kuma gadon sarautarsa ya kewaye komai, masu laifi ba za su iya tsere masa ba, haka masu neman taimako, taimakonsa ba zai yanke a gare su ba” ; haka nan ma take faɗa da ma’anarta, ta nuni: “ya kai mutum, ya shugaban mutane mai shiryar da su, idan dukkan samammu suka barka suka tafi i zuwa rasuwa ta hanyar gushewa, idan ma’abota rayuwa suka rabu da kai suka tafi ta hanyar mutuwarsu, idan mutane suka rabu da kai suka shiga kabari, kuma ko da ma’abota gafala da ɓata ba su saurare ka ba har suka afka cikin duffai; kada ka yi baƙin ciki, kuma kada ka shiga cikin damuwa, ka ce: Allah ya isar min, tun da shi yana nan to komai zai iya zama samanme, saboda haka waɗannan da suka ƙaura[1] basuyi ƙaura i zuwa rashi na (gabaɗaya ba), sai dai cewa su kawai sun ƙaura ne i zuwa wani gidan na ma’abocin al’arshi mai girma, ya girma ya ɗaukaka, haƙiƙa shi zai aiko da wasu a maimakonsu

[1] - Mutuwa.




12. Page

daga rundunarsa waɗanda ba su da iyaka, waɗannan da suke shiga kabari ba ƙarewa suka yi ba, sai dai cewa su suna komawa i zuwa wata rayuwar, haƙiƙa girma da ɗaukaka su tabbata a gare shi zai aiko da wasu ma’aikata a bigirensu, shi mai iko ne a kan aiko bayinsa masu biyayya, waɗannan da suke bin hanyar gaskiya, a maimakon waɗannan da suke afkuwa, a cikin ɓata, tun da al’amarin ya zama haka, to shi mawadaci ne a bisa komai, ba ya yiwuwa komai ya wadata daga fuskanta ɗaya daga gare shi.

Ta hanyar wannan ma’anar ta nuni, waɗannan jana’izozi uku masu tsoratarwa waɗanda suka tsoratar dani, sai suka ɗauki wani yanayi daban. shi ne cewa samanmu suna cancanzawa kamar haka,a cikinsu akwai masu zuwa suna tafiya, a cikin zuwansu da tafiyarsu akwai hikima a cikinta da abin lura, kuma tafiya ce ma’abociyar izna kuma ma’abociyar ayyuka, saboda sallama da ɗaukan aiki ta ƙarƙashin kulawar ubangijintaka mai hikima mai jinƙai, adali mai iko ma’abocin girmame-girmame, duk wannan yana cikin hikimarsa da rahamarsa.