Saƙo na sha daya

43. Page

SAƘO NA GOMA SHA ƊAYA:

 Wanda ya ƙunshi mas’aloli uku:

Mas’ala ta farko: haƙiƙa sunnah mai haske ta manzo mafi girma alaihis salam tana da maɓuɓɓugai uku, su ne: zantukansa da ayyukansa da halayensa, waɗannan kashe-kashen uku, kowanne ɗaya daga cikinsu kashi uku ne, su ne: farillai, nafiloli da al’adunsa alaihis salam kyawawa.

Biyayya a cikin kashin farillah da wajibi dole ne, a cikin barinsa akwai azaba da uƙuba, to dukkan kowa an wajabta masa binsa da lazamtarsa.

Amma kashin nafiloli, ma’abota imani su aka wajabtawa biyayyarsa wajabcin mustahabbanci, sai dai babu azaba ko uƙuba a cikin barin su, sai dai aikatasu da bibiyarsu akwai lada mai girma a cikinsa, amma canjasu, bidi’a ne da ɓata da kuskure mai girma babba. 


44. Page

Amma al’adunsa masu haske (S.A.W) da ayyukansa kyawawa, koyi da su da bibiyarsu abune mai kyau kwarai ta fuskar hikima da mas’laha a wajen rayuwa ta mutum da ta iyali da ta al’umma; domin cewa dukkan motsi na daga motsukansa na al’ada alaihis salam nada amfani mai yawa a rayuwa, to da binsu ne waɗannan laduban da al’adun suke zama a hukuncin ibada. 


45. Page

Haka yake; tun da cewa haƙiƙa manzo mafi karamci tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya samu mafi ɗaukakar matakin daraja na kyawawan ɗabi’u da haɗuwar masoya da maƙiya, tun da cewa an yi ittifaƙi manzo shi ne mafi shahara da mafi girman mutum a tsakanin mutane , kuma tun da cewa shi ne mafi cikar mutane wajen kamala da mafificin mai shiryarwa da dubun dalilai na mu’ujizozinsa, tare da shaidar nan na cikar duniyar musulunci wannan da ya tsara ta, kuma da gasgatawan nan ta tabbatatattun bayanan Alƙur’ani mai hikima, wanda shi ne mai isarwa mai fassara a gare shi, tun da cewa miliyoyi na daga ma’abota cika haƙiƙa sun ɗaukaka a cikin matakan cika, kuma sun samu arzikin gidaje biyu sakamakon yi masa biyayya; to babu kokwanto, haƙiƙa sunnar wannan mai karamci da ayyukansa su ne mafiya kyawun ababan kwaikwayo ga mai koyi, kuma mafi kuɓuta mafi ƙarfin mai shiryarwa da ya fi cancanta a bishi, mafi hikima da ƙarfin dokoki da suka cancanta a ɗaukesu dokoki na rayuwa. 


46. Page

Haka yake; tun da cewa haƙiƙa manzo mafi karamci tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya samu mafi ɗaukakar matakin daraja na kyawawan ɗabi’u da haɗuwar masoya da maƙiya, tun da cewa an yi ittifaƙi manzo shi ne mafi shahara da mafi girman mutum a tsakanin mutane , kuma tun da cewa shi ne mafi cikar mutane wajen kamala da mafificin mai shiryarwa da dubun dalilai na mu’ujizozinsa, tare da shaidar nan na cikar duniyar musulunci wannan da ya tsara ta, kuma da gasgatawan nan ta tabbatatattun bayanan Alƙur’ani mai hikima, wanda shi ne mai isarwa mai fassara a gare shi, tun da cewa miliyoyi na daga ma’abota cika haƙiƙa sun ɗaukaka a cikin matakan cika, kuma sun samu arzikin gidaje biyu sakamakon yi masa biyayya; to babu kokwanto, haƙiƙa sunnar wannan mai karamci da ayyukansa su ne mafiya kyawun ababan kwaikwayo ga mai koyi, kuma mafi kuɓuta mafi ƙarfin mai shiryarwa da ya fi cancanta a bishi, mafi hikima da ƙarfin dokoki da suka cancanta a ɗaukesu dokoki na rayuwa. 


47. Page

Mas’ala ta biyu: haƙiƙa mai gaskiya maɗaukaki yana faɗa a cikin Alƙur’ani mai hikima وإنك لعلى خلق عظيم)) haƙiƙa ya zo a cikin ruwaya ingantacciya haƙiƙa sahabiya mai girma, Aisha Siddiƙa- haka nan dukkan sahabbai- ta kasance idan za ta siffanta Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, tana siffantashi tana mai faɗin: “Alƙur’ani ne halayensa[1]” ai misali iri na zakaran gwajin dafi na kyawawan halaye waɗannan da Alƙur’ani ya bayyana su, shi ne Muhammad tsira da aminci su tabbata a gare shi, kuma shi ne farkon wanda ya kamanta waɗannan kyawawan halaye, haƙiƙa an halicce shi kuma an sa waɗannan kyawawan halayen a zubin halittarsa.

Kuma idan ya zama dukkan aiki na daga ayyukan irin wannan shaksiyyar alaihis salam da dukkan zance na daga zantukan ta, da dukkan motsi daga mammotsawarta abin koyi ne da misali ga nau’in nan na mutum, to a auna a gani irin girman shaƙiyanci da ta’asa na waɗanda ba su damu da sunnar shi ba ko kuma suke neman canza ta daga muminai marabkana daga al’ummarsa! har dai mahaukata za su iya fahimtar haka


[1] Yi duba i zuwa littafin Musnad na imam Ahmad ibn Hambal 91/7 da Mu’ujamul Ausax 31/1 da kuma Al’adabul Mufrad shafi na 115.




48. Page

Mas’ala ta uku: haƙiƙa Manzo mafi karamci alaihis salam an halicce shi a cikin mafi daidaituwar zubi, da mafi cikar sura kuma mafificiyarta; to haƙiƙa dukkan motsinsa da kawaicinsa sun tafi a bisa daidaituwa, sirarsa mai haske tana nuni nuni yankakke cewa shi ya tafi a cikin dukkan harkoki daga harkokinsa  a bisa daidaito da istiƙama, kuma ya nisanci taƙaitawa da zurfafawa.

Hakayake; haƙiƙa Manzo mai girma tsira da aminci su tabbata a gare shi tabbas ya bi umarnin wannan ayar(فاستقم كما أمرت) biyayya cikakkiya; saboda haka daidaituwa take bayyana a cikin dukkan ayyukansa da zantukansa da halayansa bayyana ta sarari.


49. Page

misali: kamar yadda haƙiƙa “Ƙarfin hankalinsa” yana tafiya koyaushe mai dacewa daidai da “hikima” wannan da ita ce iyaka matsakaiciya da matattarar daidaituwa abar kuɓutarwa daga abin da yake shi ne matsayin nan na ɓacin karfin hankali da duhunsa kamar” jarbaza”[1], wannan da ita ce wuce gona da iri, da” wawanci” wannan da shi ne sakaci, hakanan ya zama” ƙarfin fushinsa” a koyaushe yana tafiya daidai da “jarumtaka” mai tsarki, wannan da ita ce matattarar daidaituwar ƙarfin fushi, da kuma matsakaiciyar iyakarta, abar tsarkakewa daga duk wani abu da yake matsayin ɓacin ƙarfin fushi kamar ta’”addanci” wanda shi fice gona da iri ne na jarumtaka da” ragwanci” wanda shi ne kamar sakacin jarumtaka, haƙiƙa“ƙarfin sha’awarsa” a koyaushe yana kan kamewa mai girma mai shiriyarwa a gare shi har ya kai i zuwa darajar rashin saɓo, wajen kamewar kai, wannan da ita ce matattara daidatuwa ta wannan ƙarfin, tatacciya ce daga duk abin da yake a matsayin ɓacin ƙarfin sha’awa, na daga “bicewa” wannan da yake shi ne sakaci da kuma “fajirci” wanda shi ne wuce gona da iri.

[1] Munanan halaye.




50. Page

Hakanan, haƙiƙa ya zaɓi iyaka ta daidaituwa a cikin dukkan sunnoninsa masu haske, da halayansa na zubin halitta da hukunce-hukuncensa na shari’a, kuma ya nisanci wuce gona da iri da sakaci da ɓarna da almubazzaranci, wanɗannan da su ne zalunci da duffai, haƙiƙa ya riƙi tsakaitawa mai shiryar a gare shi har dai a cikin zantukansa da cinsa da shansa, ya kuma nisanci ɓarna samsam.

Tabbas an wallafa don bayyana wannan haƙiƙa dubunnai mujalladai, to sai mu wadatu da ɗigo ɗaya na daga wannan kogi mutaƙaita magana; domin cewa “masani” nuni ta ishe shi.

اللهم صل على جامع مكارم الأخلاق ومظهر سر. آمين.

(وإنك لعلى خلق عظيم) الذي قال:

"من تمسك بسنتي عند فساد أمتي فله أجر مائة شهيد" وقالوا الحمد لله الذي هدانا لهذا وما كنا لنهتدي لولا أن هدانا الله لقد جاءت رسل ربنا بالحق).

 (سبحانك لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم).

 


51. Page

HASKE NA GOMA SHA TARA

RISALAR TATTALIN ARZIƘI

A KAN

TATTALI DA WADATAR ZUCI DA ƁARNA DA ALMUBAZZARANCI

Muna farawa da sunan Allah mai rahma mai jin-ƙai:

(كلوا واشربوا ولا تسرفوا) (الأعراف:31 )

Haƙiƙa wannan aya mai girma tana koyar da darasi na hikima muhimmi ƙwarai da umarninta a kan tattali umarni tabbatacce, da haninta ga ɓarna hani na ƙarara, a cikin wannan mas’ala, akwai bayanai guda bakwai.

 Bayani na Farko: haƙiƙa mahalicci mai jin-ƙai, yana son godiya sakamakon ni’imomi waɗannan da ya bayar da su ga ‘yan’dam, ɓarna mai korewa ce ga godiya, kuma ƙasƙantar da ni’imomi ce mai hasarori, amma tattali shi girmama ni’imomi ne mai riba. 


52. Page

HASKE NA GOMA SHA TARA

RISALAR TATTALIN ARZIƘI

A KAN

TATTALI DA WADATAR ZUCI DA ƁARNA DA ALMUBAZZARANCI

Muna farawa da sunan Allah mai rahma mai jin-ƙai:

(كلوا واشربوا ولا تسرفوا) (الأعراف:31 )

Haƙiƙa wannan aya mai girma tana koyar da darasi na hikima muhimmi ƙwarai da umarninta a kan tattali umarni tabbatacce, da haninta ga ɓarna hani na ƙarara, a cikin wannan mas’ala, akwai bayanai guda bakwai.

 Bayani na Farko: haƙiƙa mahalicci mai jin-ƙai, yana son godiya sakamakon ni’imomi waɗannan da ya bayar da su ga ‘yan’dam, ɓarna mai korewa ce ga godiya, kuma ƙasƙantar da ni’imomi ce mai hasarori, amma tattali shi girmama ni’imomi ne mai riba. 


53. Page

Bayani na Biyu: haƙiƙa mahaliccin halitta mai hikima, ya halicci jikin mutum, kamar wata fada ƙayatacciya da birni tsararre, ƙarfin nan na ɗanɗano wanda yake a cikin baki mai kula da ƙofa ne ga wannan birnin, hanyoyin jini ƙanana da jijiyoyi kamar wasu hanyoyi ne na ba da saƙo kamar wayoyi, (mai aika saƙo) tsakanin ƙarfin nan na ɗanɗano da uwar hanji wadda ta kasance a cikin cibiyar jiki, kamar hanyoyin tarho da wayoyin jiki da suke sadar da magana, kuma ƙarfin nan na ɗanɗano sai ya ba da labarin abubuwan da suka shigo cikin baki ta hanyar jijiyoyi, idan ba su zama lallai ba ne ga jiki da uwar hanji, sai ya ce: ba zai yiwu a shiga ba sai ya watso su i zuwa waje, amma idan sun kasance masu cutarwa ne masu ɗaci ne tare da cewa ba su da amfani ga jiki a wani lokaci, to shi zai watso su, ya tofar da su da gaggawa i zuwa waje kuma dayin kaki a fuskarsu. 


54. Page

Tunda cewa ƙarfin ɗanɗanon nan da ke cikin baki ya kasance mai kula da ƙofa ne, uwar hanji kuma shugaba ce mai hukunci a cikin gudanar da jiki, idan ƙimar kyautar wadda take zuwa wannan fadar ko wannan garin ake kuma gabatar da ita ga sarkin wannan birnin tana daidaituwa da abin da yake daidai da daraja ɗari, ba ya dacewa ya zama kyauta ga mai kula da ƙofa sai dai darajoji biyar daga gare ta kaɗai ba zaifi haka ba, har dai kada mai kula da ƙofa ya ruɗu sai ya ɓata, ya manta aikinsa, kuma ya shigar da waɗanda suka  ba shi cin-hanci mafi yawa a cikin fadar. 


55. Page

Gini a bisa wannan sirrin, mu ƙaddara misali yanzu a gabanmu a kwai nau’i buyu na abinci, abinci na farko ya ƙunshi abubuwan ci kamar cukui da ƙwai, kuɗinsu ƙirshi[1] arba’in ne, ɗayan kuwa yana daga mafi alfaharin nau’o’in bagalawa (kayan daɗi) kuɗinsu ƙirshi ɗari huɗu, waɗannan abinciccika guda biyu madaidaitane babu banbanci a tsakaninsu dangane da jiki, kafin shigarsu baki, kuma su madaidaitane a wajen amfanar da jiki bayan shuɗewarsu ta maƙogoro, bari, cukui na ƙirshi arba’in zai iya ba da amfani ga jiki fiye da amfanin waɗancan, babu wani banbanci a nan sai dai na ɗan wani lokaci na rabin minti kawai a cikin tausasawar nan na ƙarfin ɗanɗano wadda take a cikin baki; ka auna ka gani yawan ɓarnar mai cutarwa ba tare da ma’ana ba, shi ne ba da ƙirshi ɗari huɗu a maimakon ƙirshi arba’in, saboda ɗan jindaɗi na rabin minti!


[1] - Kuxin qarfe da ake amfani da su a qasashen Larabawa. 




56. Page

Duk da cewa wannan kyautar da take zuwa ga sarki kuɗinta, ƙirshi arba’in; to haƙiƙa bawa wannan mai kula da ƙofa ninki wannan kyautar sau tara kamar wata kyauta ce za ta ruɗe shi ta kora shi i zuwa ya ce: ni ni ne sarkin.

To wanda ya  ba shi kyauta da jin daɗi mafiyawa zai  ba shi damar shiga, sai ya yi sababin ɓacin fadar da tashin gobara a cikinta, har ya buƙatar ga mai ita ya ce taimako-taimako likita ya zo ya sassautar da hawan zafina kuma ya bice shi.

Amma tattali da wadatar zuci jujjuyawa ce mai dacewa da hikimar Allantaka; domin cewa su suna mu’a’mala tare da karfin nan na ɗanɗano,  a bisa cewa shi mai kula da ƙofa ne, gini  a bisa haka sun  ba shi wani alheri, amma ɓarna domin ita tana jujjuyawa saɓanin waccan hikimar to ita za ta haɗu da mari da gaggawa kuma uwar hanji ta ɓaci, kuma tana kaiwa i zuwa rashin sha’awar abinci ta haƙiƙa, kuma tana sanya mutum ya dinga ci da sha’awa abinci ta ƙarya mai samuwa daga mabambantan abubuwanci, kuma ya rikicewar ciki da lalacewarsa, kuma yake kaiwa i zuwa ciwo. 


57. Page

Bayani na Uku: haƙiƙa mun faɗa a cikin saƙo na biyu da ya gabata, cewa ƙarfin nan na ɗanɗano mai kula da ƙofa[1] , hakayake; haƙiƙa shi yana matsayin mai kula da ƙofa a wajen ma’abota gafala, da waɗannan da ba su samu ɗaukaka ba a ruhi, kuma ba su samu cigaba a matafiyar nan ta godiya ba, yana wajaba abar ɓarna, yana wajaba kada farashin kuɗin ya wuce daga ɗaya daga cikin goma,[2] saboda jin daɗin wannan mai kula da ƙofar, sai dai shi ƙarfin ɗanɗano a wajen ma’abota godiya na gaskiya da ma’abota haƙiƙa da ma’abota zuciya shi ne -kamar yadda aka bayyana a cikin kamanceceniya wannan da aka ƙullata a cikin “kalma ta shida” - , a matsayin mai kula kuma mai bincike,  a bisa madafar nan ta rahmar Allantaka, aikinsa shi ne aunawa da sanin nau’o’in ni’imomin nan na Allantaka da ma’aunai rantsasstsu masu ƙananan siffa da adadin abubuwan ci da suke cikin ƙarfin nan na ɗanɗano, kuma su isar da waɗannan abubuwan cin ga jiki da uwar hanji, kamar godiya ce ta ma’ana,

[1] - Qofar baki.

[2] - Abin lira xaya a saye shi lira goma. 




58. Page

ƙarfin nan na ɗanɗano da wannan sura ba ya fuskanta i zuwa jiki na zahiri kawai; bari, sai dai shi yana fuskanta i zuwa zuciya da ruhi da hankali, a saboda haka; yana da iko da matsayi sama da uwar hanji.

Zai iya yiwuwa mutum yakula da jiye-jiyen daɗinsa, da sharaɗin kada ya yi ɓarna, sai don ya yi godiya kaɗai, domin ya ji ya san nau’o’in ni’imomi na ubangiji, kuma ya kasance jin-ɗaɗinsa, jin-ɗaɗi ne na shari’a, kuma kada ya kasance hanya ce ta ƙasƙanci da roƙo, kuma zai yiwu ya fifita abubuwan ci, masu daɗi a saboda ya iya aikatar da wannan harshen dake ɗauke da ƙarfin nan na ɗanɗano ga godiya


59. Page

Abubuwan da ya faru da karamar shugabanmu Abdulƙadir Jilani, (Allah ya tsarkake sirrinsa), suna nuni i zuwa wannan haƙiƙa:

Wata mata tsohuwa mai yaushi ta kasance tana da ɗanta ɗaya tilo kawai a cikin tarbiyar gausu mai girma,[1] shugaban mu Abdulƙadir Jilani, Allah ya tsarkake sirrinsa, wannan tsohuwa abar girmamawa wata rana sai ta tafi i zuwa ɗakin ɗanta sai ta same shi yana cin gutsiran gurasa busasshiya ɓaƙa, ya kasance haƙiƙa har ya rame daga wannan tarbiyya, sai halin nan nasa ya motsa tausayin mahaifiyarsa, sai taji tausayinsa, sannan sai ta tafi i zuwa halarar gausu don kai ƙara, sai ta sami shugaba gausu yana cin soyayyun kaza, sai ta faɗa sanadiyar tausasawarta: ya shehu ɗana ya kusa mutuwa, saboda yunwa, amma ga shi kai kana cin kaza, sai halarar shehu ya faɗa ga wannan kazar: “Tashi da izinin Allah” sai ƙasusuwan wannan kaza dafaffiya da aka cinye suka tattaru har suka zama kaza cikakkiya, sai ta yi tsalle i zuwa wajen kwano.


[1] - Almajiransa. 




60. Page

Wannan abin da ya faru an karɓo shi daga mazaje da yawa amintattu, ababan dogara a matsayin ɗaya daga karamomin halarar gausu wannan da ya shahara a cikin duniya da samunsa karamomi masu keta al’ada.

 Sai halarar gausu ya faɗa ga tsohuwar nan: to yayin da ɗanki ya kai wannan martaba, shi ma zai ci kaza.

Ma’anar faɗin nan ta halarar gausu shi ne lokacin da ruhin ɗanki ya yi rinjaye  a bisa gangar jikinsa, zuciyarsa  a bisa kansa, hankalinsa  a bisa uwar hanjinsa, yake neman jin daɗi don godiya; to a lokacin ne zai iya cin abubuwan ci masu daɗi.

Bayani na Huɗu: mai tattali ba ya shan mafi yawa daga wahalar nan ta talauci, a cikin rayuwa da sirrin hadisin nan maɗaukaki

"لا يعول من اقتصد"


61. Page

“wanda ya yi tattali[1] ba ya talauci”, abin nufi mai tattali ba ya shan wahalar talauci a cikin rayuwa.

Haka yake; haƙiƙa akwai abin da ba zai ƙididdugu ba ba zai ƙirgu ba na daga dalilai masu yawa da suke shiryarwa a bisa cewa tattali dalili ne mai ƙarfi na albarka da yalwar rayuwa.

Kuma ina ambaton sashi daga gare ta da shaidar abin da na ganshi a cikin kaina da shaidar waɗanda suka yi min hidima suka abokance ni ina faɗin:

haƙiƙa ni da wasu abokaina a wani lokaci mun samu ninki goma na albarkoki ta hanyar tattali, har dai cewa kafin shekaru tara, sashin shugabannin wasu ƙabiloli wanda aka koresu, tare dani a ƙasar bordor sun so su sanya ni i zuwa karbar zakkarsu, domin kar na abka cikin ƙasƙanci da talauci da takaici na rashin kuɗi, sai na ce ga waɗannan shugabanni mawadata: haƙiƙa kuɗina kaɗan ne ƙwarai, sai dai cewa ni ina yin tattali, kuma nayi sabo da wadatar zuci, saboda haka ni nafiku wadata, sai naƙi karɓar abin bijirowa da suka bijiro shi a gare ni tare da nannacewa a maimaice, yana daga abin jan-hankali, cewa sashin waɗanda suka bijiromin zakkarsu, sun ci  ba shi bayan shekara biyu, saboda da rashin tattali, godiya ta tabbata ga Allah, haƙiƙa kuɗaɗen nan kaɗan sun wadatar dani har i zuwa shekaru bakwai, saboda albarkar

[1] -Wajen buƙata. Yi duba ga hadisi a cikin littafin: Mu’ujamul Kabir na Xabarani 108/10.




62. Page

tattali, ruwan fuskata bai tsotse ba, ban bijiro da buƙatata ba i zuwa mutane ba, ban bar ƙa’idata ba wadda” ita ce wadatuwa ga roƙon mutane wani abu”, wanda ta zama doka ce daga dokokin rayuwata.

Hakayake; ka ga wannan da ba ya tattali mai shiri ne ga afkawa cikin ƙasƙanci da cikin roƙo na ma’ana, da talauci da wahala, haƙiƙa kuɗi wannan da suke haifar da ɓarna, su dukiya ne masu tsada ƙwarai a cikin wannan zamanin; domin wani lokaci ana rasa mutunci da girma don saboda samunsu, haka ana rasa abubuwa masu tsarki na addini, don samun waccan dukiyar mara albarka, ake hasarar lira ɗari ta ma’ana sakamakon salwantar ƙirshi biyu na zahiri, da dai mutum zai wadatu  a bisa buƙatu na lalura ya isu da su da tsare su, da zai samu arzikinsa mai isa ga rayuwarsa ta lalura daga inda ba ya zato da sirrin: (إن الله هو الرزاق ذو القوة المتين) (الذاريات- 58).

haka nan kuma da ƙarin bayyanawar: (وما من دابة في الأرض إلا على الله رزقها) (هود: 6)


63. Page

waɗannan ayoyin sun yi masa alƙawari da haka.

Haka yake; haƙiƙa arziki nau’i biyu ne:

Na farko: shi ne arziki na haƙiƙa wannan da mutum yake iya rayuwa da shi, wannan arziki yana ƙarƙashin alƙawarin nan na ubangiji da hukuncin wannan ayar, idan mutum bai shigar da munmunan zaɓinsa ba zai iya samun wancan arzikin na lalura a kowanne hali, ba zai buƙatu ya sadaukantar da addininsa ba ko da mutuncinsa ko da girmansa ba.

Na biyu: shi ne arziki na aro; domin buƙatu waɗanda bana laluraba, sun zama buƙata na lalura sanadiyar munana amfani, kuma haƙiƙa sai mutum ya zama mai dawwama da ita, saboda musifar nan ta kwaikwayo a makance, ba zai iya barinta ba.

Wannan arzikin domin cewa shi bai kasance a ƙarƙashin alƙawarin ubangiji ba, samun sa yana ɗora mutum abubuwa da yawa, musamman a wannan zamanin, har dai shi cewa zai samu wannan dukiya wadda babu albarka a cikinta ta hanyar 

64. Page

sadaukantar da izzarsa, da kuma yarda da ƙasƙanci a wani lokaci , da saryowarsa a matsayin nan na mabarata; ta yadda zai sumbaci ƙafafun wasu ƙasƙantattun mutane, a wani lokacin kuma da sadaukantarwarsa tsarkakan ayyukansa na addini waɗanda su ne hasken rayuwarsa na har abada.

 Sannan abin da yake samun ma’abota mutunci na daga jin raɗaɗi mai tasowa daga raɗaɗin nan na mayunwata masu buƙata, da dalilan tausayawa ga ɗan jinsi ɗaya, a cikin wannan zamani- zamanin talauci da buƙatu-, yana sanya jin daɗin wanda ya samo shi ta hanyar dukiyar da ya tsururuce ta ta hanyar daba ta shari’a ba, Mai ɗaci idan ya kasance yana da mutunci, yana wajaba wadatuwa da gwargwadon lalura na dukiyoyin da suke da rikitarwa a cikin wannan zamani mai ban mamaki; domin cewa shi yana yiwuwa a yi amfani daga dukiyar haram a iyakar larura, saboda matsuwa da sirrin “Ana gwada larura da gwargwadonta” ba ya yiyuwa ya yi riƙo da fiye daga hakan. 


65. Page

Hakayake, haƙiƙa mai matsananciyar buƙata ba ya halatta a gare shi, ya yi ta cin naman mushe har ya ƙoshi bari zai iya ci i zuwa iyakar da ba zai mutu ba.

Sannan cin abinci da yawa da cikakken jin daɗi a gaban mutum ɗari daga masu jin yunwa ba ya dacewa.

Abin da ya abku wanda yake nuni a bisa haƙiƙa cewa tattali dalili ne na ɗaukaka da cika:

Hatimu Atta’i wanda ya shahara wajen karamci da kyauta a cikin duniya, wata rana sai ya shirya wata walima ta alfarma ya gabatar da kyaututtuka mai yawa ga baƙinsa, ya fita don kewayawa a cikin sahara, sai ya ga wani mutum tsoho talaka yana ɗauke ƙiraruwa masu ƙaya da ciyawa  a bisa bayansa suna shiga cikin jikinsa har jininsa na fitowa, sai Hatimu Atta’i ya ce da shi: Hatimu yana yin kaɓaki na alfahari yana rarraba kyaututtuka, kai ma tafi i zuwa gare shi, domin ka sami ƙirshi ɗari biyar, a maimakon wannan ƙiraren, wanda kuɗinsu baifi ƙirshi biyar ba, sai wannan tsoho mai tattali ya ce yana mai mayar da amsa a gare shi: haƙiƙa ni ina 

66. Page

ɗauke da ƙirare a cikin ‘yancina, bana iya yarda da ƙasƙanci na zuwa wajen Hatimu Atta’i .

Sannan sai aka tambayi Hatimu Atta’i:

Shin ka taɓa samun wanda ya fi ka karamci da buwaya?

Sai ya ce na samu wannan tsohon mai tattali, wanda na gamu da shi a cikin sahara ya fi ni buwaya da ɗaukaka da karamci.

 

 Bayani na Biyar: haƙiƙa mai gaskiya maɗaukaki yana daga cikar karamcinsa jiyar da mutum mafi talauci daɗin ni’imarsa, kai ka ce shi mafi wadatar mutane ne, talaka kai ka ce shi sarki ne.

Haka yake, haƙiƙa daɗin da talaka mai jin yunwa yake samu a cikin gutsuren gurasa busasshiya baƙa ta hanyar tattali, ya fi daɗin da sarki ko mai kuɗi yake samu a cikin dangogin kayan marmari na alfarma, waɗannan da yake cinsu da ginsa, da rashin sha’awa mai faruwa daga ɓarna. 


67. Page

Yana daga abin da yake jawo hankali, cewa sashi daga mutane masu ɓarna masu almubazzaranci suna tuhumar irin waɗannan masu tattalin da rowa, bahaka ba ne fau-fau, tattali buwaya ce da yalwa, amma rowa da ƙasƙanci su a haƙiƙarsu karamci ne na zahiri da ma’abota ɓarna da almubazzaranci suke da’awarsa.

Akwai wani abin da ya faru ya gudana a gidana a wannan shekarar, da yake ƙarfafa wannan haƙiƙar, shi ne: ɗaya daga ɗalibaina ya yi naci a gare ni domin na karɓi kyautar uƙiya biyu da rabi na zuma saɓanin abin da na riƙe shi ƙa’ida da doka, duk da cewa na tsananta bayyanawata a gare shi abin da yake cikin wannan ƙa’ida na daga muhimmanci; amma shi bai gamsu ba, sai dole na ce ga ‘yan’uwa uku da suke tare da ni ku karɓe ta don ku ci daga wannan zumar a tsawon kwana talatin ko arba’in, tare da tattali a cikin watannin Sha’aban da Ramadan masu albarka, don wanda ya kawo ta ya samu lada, domin kada su wanzu ba tare da zuma ba, kuma ya kasance a waje na akwai uƙiya ta zuma, duk da cewa ‘yan’uwana uku sun kasance a 

68. Page

kan daidaituwa, kuma suna daga waɗanda suke girmama tattali sai dai cewa sun manta shi, saboda wata ɗabi’a maɗaukakiya daga wata fuska, wadda ita ce sashinsu yana girmama sashi, sashinsu yana tausasawa da ji-najikin ɗaya sashin, da fifita zaɓin wani a bisa kansa, sai suka shanye uƙiya biyu da rabi na zuma dukanta, kuma suka ƙarar da ita a cikin kwana uku, sai na faɗa ina mai murmushi:” haƙiƙa na kasance zan ciyar daku, tsakanin kwana talatin ko arba’in, sai kuka sanya kwana talatin ɗin nan suka zama kwana uku, ku ci ku yi hani’an”, sai dai ni na yi amfani da zuma, wadda take a wajena, tare da tattali, sai ni na sha daga ita a tsawon watan sha’aban da Ramadan, godiya ta tabbata ga Allah na gabatarwa kowanne ɗaya daga ‘yan’uwana waɗancan cokalin shayi babba daga zuma a lokacin buɗa baki, sai ya kasance dalili na samun lada mai girma, zai iya yiyuwa waɗanda suka ga halina wannan su zaci rowa ce, haƙiƙa kuma za su iya zaton halin ‘yan’uwana a wannan kwana ukun, karamci ne, sai dai mu mun dube shi ta mahanga ta haƙiƙa, haƙiƙa abin da yake ƙarƙashin wannan rowar ta zahiri ɗaukakace da albarka mayalwaciya da lada mai girma, domin cewa idan ba a bar wannan karamci ba da ɓarnatar da dukiya ba, da ya kasance sun haifar da wani halin mafi koma-baya da yawa daga rowa misalin jiran tsammani da kwaɗayin cikin abin da yake hannun waɗansu. 

69. Page

Bayani na Shida: haƙiƙa akwai bambanci mai girma tsakanin tattali da rowa, kamar yadda tawadhu’u ɗabi’ace ta yabo mai banbancin a ma’anance daga wulaƙanta kai, wanda shi yana daga munanan halaye da suke kama da juna da shi a sura, kuma haƙiƙa nutsuwa ɗabi’ace abar yabo mai saɓawa a ma’anance daga girman kai, wanda shi yana daga munanan ɗabi’u da suka yi kama da juna da shi a sura, kuma haƙiƙa tattali yana daga kyawawan ɗabi’u maɗaukaka na Annabi (S.A.W), bari dai ma, tsarin hikimar Allantaka yana tafiyar da halittarsa a kansa ( shi tattali )  ba shi da alaƙa da rowa, wannan da ita ce mai cuɗanya da ƙasƙanci da kwaɗayi, ba abin da yake tsakaninsu sai dai kamanceceniya a bayyane.


70. Page

Wani abin da ya afku da yake ƙarfafa wannan haƙiƙar. 

 Sahabi mai girma Abdullahi ɗan Umar Allah ya ƙara yarda da su, shi yana daga mafi girma da mafi ɗaukakar ’ya’yan Faruk Al’a’azam halifan Manzon Allah (S.A.W) yana ɗaya daga cikin Abdullahi su bakwai mashahurai yana daga cikin fitattun malaman sahabbai, ya kasance a cikin wata tattaunawa mai zafi a wata rana a wajen saye da sayarwa a cikin kasuwa, a kan abin da bai fi ’yan ƙirshina ba[1], don saboda tattali da kuma kiyaye amana da daidaituwa waɗanda su ne kasuwanci yake tsayuwa da su, sai ɗayan sahabbai ya ganshi, Allah ya ƙara yarda a gare su, sai ya yi zaton cewa tattaunawar ɗan halifa Umar mai girma khalifa na ƙasa, a kan abin da bai fi wasu ’yan ƙirshina ba rowa ce mai ban mamaki, sai ya bi wannan shugaba don ya fahimci alamarinsa, sai ya ga shugaba Abdullahi yana shiga gidansa mai albarka sai ya samu a nan bakin kofa wani mutumi talaka, sai ya ɗan tsaya i zuwa wani lokaci tare da shi sannan ya juya ya tafi, sannan ya fita ta ɗaya ƙofar daga gidansa, sai ya ga wani mutumin talaka anan, sai ya ɗan tsaya tare da shi, i zuwa wani lokaci, sannan ya juya, sai wannan abin ya sa wannan sahabin ya yi tsinkaye a kan abin da ake ciki, dama ya kasance yana biye da shi daga nesa sai ya tafi i zuwa talakawan nan guda biyu ya tambaye su, me shugaba ya yi a sanda ya tsaya a wajenku?


[1] - Kwabbai.




71. Page

 kowanne a cikinsu, sai ya ce ya bani wani yanki na zinare ne, sai wannan sahabi ya ce yana mai tunani:’subhanallah’ tsarki ya tabbata ga Allah, shi ya shiga cikin wannan tattaunawar a kasuwa a kan abin da bai wuce ƙirshi ɗaya ba, sannan ya bayar da ƙirshi ɗari biyu a gidansa tare da cikakkiyar yardar zuciyarsa kuma ba tare da wani ma ya sani ba, sai ya tafi i zuwa shugabanmu Abdullahi ɗan Umar, Allah ya ƙara yarda a gare su, ya ce da shi: shin za ka iya warwaremin wannan ƙullin ? a kasuwa ka yi haka ka yi haka, sannan na ji kuma a gidanka ka yi wannan da wannan? Sai ya mayar a gare shi yana mai ba da amsa da faɗarsa: haƙiƙa abin da ya 

72. Page

gudana a kasuwa ya gudana ne, saboda tattali da cikar hankali, kuma saboda kiyaye amana da gaskiya waɗanda su ne tushen saye da sayarwa da kuma ruhinsu, ba rowa bace, amma abin da ya gudana a gida na, ya faru ne daga tausayin zuciya da cikar ruhi, wancan ba rowa ba ne wannan kuma ba ɓarnar dukiya ce ba.

Haƙiƙa shugaba mai girma ya faɗa (Abu Hanifa) Allah ya ƙara yadda a gare shi, yana mai nuni i zuwa wannan sirrin “babu ɓarna a cikin alkhairi kamar yadda babu alkhairi a cikin ɓarna” ai babu ɓarna a cikin yin alkhairi da kyautatawa, amma ga wanda ya cancanta sannan kuma babu alkhairi a cikin ɓarnar kai tsaye. 


73. Page

 Bayanin na Bakwai: haƙiƙa ɓarna tana haifar da kwaɗayi, kwaɗayi yana haifar da sakamako uku:

Na farkonsu: rashin wadatar zuci, rashin wadatar zuci yana karya begen tafiya wajen sana’a da aiki, kum ya na kora mutum i zuwa kai ƙara a maimakon godiya, ya jefa mutum cikin kasala, ya bar dukiya kaɗan ta halal[1] wadda shari’a ta yarda da ita, ya dinga neman dukiya wadda shari’a bata yarda da ita ba, da babu wahala a samunta ya zubar da girmansa a cikin wannan hanya, bari ma, ko ma ɗaukakarsa.


[1] Da sababin rashin tattali ‘yan cima-zaune suna qaruwa, masu aikin yi suna raguwa kowa zai dinga sauraron gwamnati ta ba shi, a wannan lokacin ne, sana’a da kasuwanci da noma za su ragu waxannan da rayuwar al’umma ta dogara a kansu; kuma mutane za su samu ci baya, kuma su zama matalauta. Wannan maganar mawallafin littafin ne.




74. Page

Na biyun su: taɓewa da hasara da rashin samun abin nufi da gujewar mutane a gare shi don kada ya ɗora musu nauyi, da haramta samun sauƙi da taimakekeniya, halin mai kwaɗayi zai dace da wannan Karin-maganar” mai kwaɗayi mai taɓewa ne mai hasara ne”.

Haƙiƙa tasirin nan na kwaɗayi da wadatar zuci yana gudanawa ne a cikin duniyar rayayyu a gwargadon kundin dokoki mai gamewa mai yalwa ƙwarai, a bisa misali kamar yadda wadatar zuci ta zubin halitta tana gudanar da arziki i zuwa bishiyoyi masu buƙatarsa; gudun dabbobi da kwaɗayi don neman arziki a cikin 

75. Page

tawaya da wahala wannan yana shiryarwa  a bisa cutarwa mai girma ga kwaɗayi, hakanan kuma  a bisa amfani mai girma ga wadatar zuci, sannan kwararar abinci mai tabshi, kamar nono i zuwa dukkan ƙanana raunana, ta inda ba sa zatonsa, sanadiyar wadatarsu ta zuci ta harshen halayensu, da kuma afkowar nan ta dabbobin daji da kwaɗayi i zuwa arziƙinsu tauyayye gurbatacce tana tabbatar da da’awarmu tabbatarwa mabayyaniya, sannan halin nan na wadatar zuci ga kifaye ƙosassu dalilinsa saduwar arzikinsu kyakkyawa i zuwa gare su, kuma raunin dabbobi masu wayo kamar dila da birrai da ramewarsu don rashin samun abin da zai ishesu na arziki tare da cewa suna ƙoƙarin samo arziki da kwaɗayi, lallai wannan yana shiryarwa  a bisa cewa kwaɗayi sau da yawa shi sababi ne na wahala, da  a bisa cewa kuma wadatar zuci sau da yawa ita dalili ce ta hutu, sannan haƙiƙa samun jama’ar yahudawa arzikinsu wanda ba ya yiwuwa ya isa sai dai don lalurar rayuwarsu kaɗai ta hanya wadda ba a yarda da ita ba, da ƙasƙanci da koma baya da sababin mu’amalarsu da riba da yaudara sakamakon kwaɗayinsu, ita kuma wadatar zuci ta mazauna sahara (ai mutanen ƙauye) da rayuwarsu cikin ɗaukaka, da samunsu ga arzikinsu isasshe; lalle shi ma yana tabbatar da da’awarmu wadda muka ambata yankakkiyar tabbatarwa. 


76. Page

Sannan haƙiƙa, abkawar yawanci malamai[1] da masanan Adab[2] a cikin halin talauci da sababin kwadayin su mai faruwa daga wayonsu, da wadatar da yawa daga wawaye da gajiyayyu da dalilin wadatar zuciyarsu ta zubin halitta, yana tabbatarwa, tabbatarwa yankakkiya cewa haƙiƙa arziki na halal yana zuwa daidai gajiyawa da

[1] An tambayi Buzurjumhur, malami ne wanda ya shahara da kaifin hankali da hikima kuma shi wazirin Anushirwan mai adalci ne, xaya daga cikin masu mulkin qasar Iran masu adalci, me ya sa ake ganin malamai a qofofin sarakuna kuma ba a ganin sarakuna a qofofin malamai tare da cewa ilimi yana saman sarauta? Sai ya ce yana mai ba da amsa, wannan yana daga ilmin malamai tare da jahilcin sarakuna, domin cewa sarakuna ba sa girmama ilimi da sababin jahilcinsu, balle su je qofofin malamai su nemi ilmi. Amma su malamai sun san qimar dukiyar sarakuna a saboda haka suke nemanta a qofofin sarakuna. Da shi Buzurjumhur ya ba da amsa mai tabshi. A bisa amsa ta farko ya yi ta’awili mai kyau na kwaxayin malamai wanda yake kaiwa i zuwa talaucin da qasqancinsu. Wanda ya zama sakamakon kaifin hankalinsu; wannan zancen; Ahmad khusrau ne.

[2] Abin da yake qarfafa wannan haqiqar a Faransa ana ba wa malaman Adab wata wasiqa don yin bara don su sun iya yin bara, wannan zance Suleman Rushdi ne.




77. Page

buƙatuwa, ba daidai iko da zaɓi ba, bari, haƙiƙa wannan arziƙin na halal yana da dangantaka da iko da zaɓi dangantaka ta aksi. Domin cewa shi duk sanda ikon yaro da nufinsa ya ƙaru samun arzikinsa (ta sauƙi) yakan ƙaranta da yi masa nisa, ya zama samunsa a gare shi mai wahala, kuma haƙiƙa wadatar zuci taskace ta wadatar rayuwa da hutun rayuwa da sirrin hadisi maɗaukaki “wadatar zuci taskace da bata ƙarewa[1]”, amma kwaɗayi taskace ta hasara da talauci.

 Na ukunsu, haƙiƙa kwaɗayi yana gurɓata Ikhlasi, yana yi wa aikin lahira rauni; domin cewa da kwaɗayi ya kasance ga wani mutum daga masu tsoron Allah da ya nemi fiskantowar jama’a i zuwa gare shi, ka ga wannan da yake kwaɗayin fuskantowar mutane i zuwa gare shi ba ya iya samun Ikhlasi cikakke, wannan sakamako yana da muhimmanci mai girma ƙwarai, kuma mai jawo hankali ne kuma ya cancanci a yi tsokaci a cikinsa.


[1][1][1] Ya zo a cikin littafin Mu’ujamul Ausax daga Yusuf ibn Muhammad ibn Munkadir daga babansa daga Jabir ya ce Manzon Allah (S.A.W) ya ce, ina umartar ku da wadatar zuci, don wadatar zuci dukiya ce da ba ta qarewa. Yi duba i zuwa Mu’ujamul Ausax 84/7. Hadisi mai lamba 6922.




78. Page

A ƙarshe: haƙiƙa ɓarna tana haifar da rashin wadatar zuci, rashin wadatar zuci yana karya bege i zuwa aiki yana kuma jefa mutum cikin kasala, kuma yana ɓuɗe ƙofofin kai-ƙara a rayuwarsa, sai ya sanya shi yana kai-ƙara koyaushe, yana gurɓata Ikhlasi ya ɓuɗe kofar riya, ya karya girmansa ya nuna masa hanyar roƙe-roƙe.

Amma tattali yana haifar da wadatar zuci, ita kuma wadatar zuci tana haifar da buwaya da sirrin hadisi maɗaukaki “wanda ya yi wadatar zuci ya ɗaukaka, wanda ya yi kwaɗayi ya ƙasƙanta, yana kwaɗaitar da mutum  a bisa tafiya ga aiki, kuma yana ƙara masa himmarsa da shauƙinsa, ya iza shi i zuwa ga aiki,

domin mutum idan ya yi aiki misali a yau, to a gobe zai yi aiki da sirrin nan na wadatar zuci da wani yanki na lada da ya same shi a jiya. 


79. Page

Amma mai ɓarna ba ya aiki a ranar da take biye, saboda rashin wadatar zuciyarsa, ko da da ya yi aiki, to shi zai yi aiki ne ba tare da bege ko kwaɗayi ba.

Sannan ita wadatar zuci wadda take faruwa daga tattali tana buɗe kofar godiya kuma tana rufe ƙofar kai ƙara, sai mutum ya zama mai dawwamar godiya ne a cikin rayuwarsa, sannan shi ba ya kwaɗayin fuskantowar mutane i zuwa gare shi domin wadatuwarsa ga barinsu da dalilin wadatar zuci, sai ƙofar Ikhlasi ta buɗe ƙofar riya ta rufe. 


80. Page

Haƙiƙa na ga cututtuka masu girma, na rashin tattali da ɓarna a cikin fage mai girma kamar yadda zai zo:

Na gabato i zuwa wani birni mai albarka kafin shekaru tara ya kuma kasance lokacin sanyi ne, sai na kasa ganin maɓuɓɓugar dukiyar wannan birnin, mai ba da fatawar birnin ya faɗa sau da yawa Allah ya yi masa rahma: haƙiƙa ma’abota wannan garin namu talakawa ne, wannan magana sai ta motsa zuciyata, sai na kasance ina tausayi,  a bisa ma’abota wannan birni kusan shekaru shida bayan haka, a bayan shekaru takwas na sake gabata i zuwa wannan birni a cikin lokacin zafi sai nayi duba i zuwa bishiyoyin inibinta, sai na tuna faɗin mufti, Allah ya yi masa rahma, sai nace tsarki ya tabbata ga Allah! haƙiƙa amfanin wannan inibin ya wuce buƙatar wannan garin sosai, ya kamata a ce mutanen garin mawadata ne kwarai, sai nayi mamaki, na riski haƙiƙanin abin da ya ɗarsu a zuciyarta -ita mai shiryar da nice don riskar tabbatatattun abubuwa bata yaudara ta- haƙiƙa an ɗaukake albarka da sababin ɓarna da rashin tattali, mufti ya kasance ya na faɗa Allah ya ji-ƙansa haƙiƙa mutane na talakawa ne, duk da cewa ga wannan gwargwadon na daga maɓuɓɓugar dukiya.


81. Page

Haka yake; haƙiƙa akwai abubuwan da suka abku, waɗanda ba su da iyaka da suke shiryarwa a bisa cewa tattali da ba da zakka dalili ne na albarka a cikin dukiya an jarraba haka, haƙiƙa ɓarna da rashin ba da zakka kuwa sababi ne na ɗauke albarka.

Haƙiƙa ibn Sina, Abu Ali Al-abƙari, wanda akafi saninsa da -Pluton, ’yan falsafan musulmi- shaihin malamin likitoci, babban malamin filosafofi ya fassarawa ayar:

(كلوا واشربوا ولا تسرفوا).

Ta fuskar ilmin likitanci kawai kamar yadda zaizo:

1-   Na taro duk likitanci a cikin baitina biyu Tarowa.

2-   Kyawun magana yana cikin taƙaice zance.

3-   Idan za ka ci ka ƙaranta ci, bayan ci kuma.

4-   Ka nisanci ƙari, waraka tana cikin niƙan nan na uwar hanji.

5-   Babu, halin da ya fi tsananta  a bisa rai.

6-   Fiye da shigar da abinci a kan abinci.

سبحانك لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.


82. Page

Dacewa mai jawo hankali, da kuma abin lura

Haƙiƙa marubuta biyar ko shida sun rubuta Risalar – tattali -uku daga cikinsu ba su ƙware a rubutu ba- , dukkan aliffa hamsin da ɗaya suka dace a cikin kowanne kofi idan an fitar da addu’a, ko kuma dukka alif hamsin da uku tare da addu’a, duk da saɓanin guraren waɗannan marubutan, da banbancin abin suka rubuto daga gare shi, da nisan gurarensu daga sashi i zuwa sashi, da banbancin rubutunsu, tare da rashin tunaninsu a kan waɗancan alif-alif ko kaɗan, haƙiƙa daidaituwar adadin alif-alif tare da tarihin rubuta risala ta tattali wanda shi ne da tarihin Rumawa hamsin da ɗaya da tarihin hijira hamsin da uku, wannan daidaituwar bazai yiwu ba, ta zo haka kaitsaye ba sam-sam, bari shi nuni ne i zuwa ɗaukakar albarka a tattali i zuwa matsayin karama, bari ya cancata a kira wannan shekara shekarar tattali. 

83. Page

Hakayake, haƙiƙa zamani ya tabbatar da wannan karamar ta tattali -bayan shekara biyu- a cikin yaƙin duniya na biyu, ta hanyar yunwa da rugurguzau, da nau’i-nau’i na ɓarna mai yaɗuwa a cikin kowanne waje, da tsananin buƙatun nan na ɗan’adam da dukkan sauran abubuwa i zuwa yin tattali. 


84. Page

DAGA TSANGAYAR

RASA’IL ANNUR

HIJABI

 

WANDA YA WALLAFA

IMAM

BADI’UZZAMAN SA’ID ANNURSI

 

WANDA ya yi TARJAMA

: Cibiyar fassara da binciken ilimi ta

HAYRAT NEŞRIYAT

 

 

WAƊANDA SUKA DUBA

PROF ATTAHIR MUHAMMAD DAWOOD

DA

PROF RABI’U SA’AD


85. Page

HASKE NA ASHIRIN DA HUDU

 GAME DA ABIN DA YA SHAFI HIJABI

Wannan haske ya kasance mas’ala ta biyu da “mas’ala ta uku” daga “muzakkira ta goma sha biyar” sai dai cewa ita ta zama “haske na ishirin da huɗu” don muhimmancin ta.

بسم الله الر حمن الرحيم

(يأيها النبى قل لازواجك وبناتك ونساء المؤمنين يدنين عليهن من جلابيبهن) الخ (الأحزاب:- 59).

Wannan aya mai girma tana umarni da hijabi. Amma wayewa ta ‘yan birni ta wauta ta tafi i zuwa saɓanin wannan hukunci na Alƙur’ani, kuma bata ganin hijabi wani abu ne da ya dace da zubin halittar mutum,bari ita tana ganinsa rashin ’yanci ne ko ƙaidin bautane.


86. Page

Amsa: Da sannu zan bayyana, hikimomi huɗu a tsakankanin hikimomi masu yawa da suke shiryarwa  a bisa haƙiƙa wannan hukuncin Alƙur’ani ya dace da zubin halittar ɗan’adam cikakkiyar da cewa, kuma haƙiƙa abin da ya saɓa masa shi ne bai dace da zubin halittar ɗan’adam ba.

HIKIMA TA FARKO:

Haƙiƙa hijabi ya dace da zubin halittar mata kuma zubin halittar tasu yana hukuntar da shi; domin cewa mata raunana ne masu raunin halitta, suna buƙatar kariya da taimakon namiji da zai kare su ya kare ‘ya’yansu, waɗannan da suke son su fiye da rayuwarsu, kuma suna taimakonsu, suna da karkata ta zubin halitta i zuwa sa a so su, da kuma ƙin wasu su ƙisu, da ƙin bijiro da kansu don kada a kyamacesu.

Sannan shida daga goma ko bakwai daga goma na mata, ko dai tsofaffi ko kuma munana ba sa so tsufansu ko muninsu ya bayyana ga dukkan mutane, ko kuma suna jin tsoron idan aka kwatantasu da waɗanda suka fisu kyau, za a ɗauke su munana, ko kuma suke tsoron aci zarafinsu ko su faɗa cikin zargi, sai suso su suturtar da kansu a zubin halitta don tsoron kada aci zarafinsu a tuhume su da ha’inci a cikin 

87. Page

idon mazajensu, bari har dai da za a kyautata duba da za’asamu cewa mafi yawan waɗanda suke ɓoye kawukansu don kada a gansu su ne mata tsofaffi.

Haƙiƙa yana kasancewa biyu ko uku ne daga cikin dukkan mata goma matasa da kyawawa, ba sa ƙuntata daga buɗe jikinsu domin yana daga abin da aka sani, haƙiƙa mutum yana takura daga duban waɗanda ba ya son su kuma yana jin nauyinsu yana tasirantuwa da kallonsu, babu kokwanto cewa mace mai kyau mai tabarruji mai tsiraici, in takasance tana son mutane biyu su ganta ko uku daga dukkan goma na mazaje, waɗanda ba muharramanta ba, haƙiƙa ita za ta ƙi bakwai ko takwas daga cikinsu, mace mai kyau wadda ba mai ɓatattun al’aduba ko gurɓatattu ba, domin cewa ita mai rauni ce mai saurin tasirantuwa cewa ita da sannu za ta ƙuntata daga kallon nan mai guba gurɓatacce, da aka jarraba tasirinsa na fili, bari haƙiƙa mu muna ji[1] a turai wadda ita ce ƙasar tsiraici da yawa daga mata suna ƙuntata daga kallon nan wanda ke fakonsu, suna kai ƙara i zuwa ’yan sanda suna cewa; waɗannan ƙasƙantattun, suna fakon mu, fako matsananci, suna damunmu.




88. Page

Wato cewa jefarwar da wayewa tayiwa hijabi mai korewa ne ga zubin halitta, haƙiƙa umarnin Alƙur’ani da yin hijabi, ƙari a kan cewa shi ya dace da zubin halitta, haƙiƙa shi yana tsamo mata, waɗannan da suke su taskace ta tausayi da waɗannan da za su iya zama abokai ƙawaye masu girma ga mazajensu, i zuwa har abada, da suke tseratar da su daga faɗuwa cikin ƙasƙanci da ribacewa ta ma’ana da wulaƙanci.

Sannan mata suna da tsoro na irin zubin halittarsu daga maza waɗanda bana jikinsu ba, saboda haka wannan tsoron yana hukunta hijabi a a cikin zubin halitta; domin akwai wahalar ɗaukar ciki mai nauyi na ɗa a tsawon wata takwas ko tara, da yake gurɓatawa mata jin daɗin minti takwas ko tara, bugu da ƙari a kan ɗaukar wahalar tsayuwa da tarbiyar yaron da babu me kula da shi, kuma za ta ɗauki wahalar tsawon shekaru takwas ko tara sakamakon jin daɗi wanda bana sharia ba, wanda ya 

89. Page

ɗauki minti takwas ko tara, Saboda faruwar irin waɗannan al’amura sau da yawa mata suna tsorata a –a irin zubin halittarsu- daga maza waɗanda bana jikiba, ɗabi’arsu tana hukunta nesantar su, ɗabi’ar halittar su mai rauni tana tilasta ta hanyar sa hijabi rashin motsa sha’awar wanda bana jikinsu ba, da rashin buɗe musu damar a abka musu, da faɗakar da su da ƙarfi i zuwa haka, tana bayyanar da cewa katangar su da makarinsu shi ne hijabinsu.

Kamar yadda ya zo a kunne na cewa wani mai gyaran takalmi ƙasƙantacce a tsakiyar rana a gaban mutane cikin babban birni na turkiyya ya latsa matar wani mutum mai girma da daraja wadda ƙwaurukan ta a waje suke, a cikin haka akwai mari a fuskokin waɗanda suke inkarin hijabi. 


90. Page

HIKIMA TA BIYU:

Haƙiƙa alaƙa mai ƙarfi da haɗuwa amintacciya da soyayya matsananciya mai zurfi tsakanin mace da namiji bata zuwa daga buƙatun duniya kawai.

Hakayake, haƙiƙa mace bata zama abokiyar zaman mijinta a cikin rayuwar duniya kawai ba, bari ita abokiyar rayuwarsa ce a cikin rayuwarsa ta har abada, mutuƙar cewa ita da sannu za ta zama abokiyar rayuwar mijinta har a cikin rayuwa ta har abada; to yana wajaba akanta, kada ta jawo duban wani, ba mijinta ba i zuwa kyaunta, wannan mijinnata wanda shi ne abokinta badaɗinta na har abada, kada ta motsa fushinsa da kishinsa, matuƙar cewa haƙiƙa alaƙar mijinta mumini tare da ita -da sirrin imani- bata zama mai taƙaituwa ba a cikin rayuwa ta duniya, kuma bata zamo soyayya ta dabbantaka ba ta ɗan wani lokaci kuma taƙaitacciya a bisa lokacin kyaunta kawai ba, bari ita alaƙace ta soyayya da girmamawa matabbata, don kasancewarta abokiyar rayuwa ta har abada a cikin rayuwa ta har abada, kuma shi ma yana nunawa a gare ta wannan soyayya da wannan girmamawar masu ƙarfi ba a lokacin ƙuruciyarta da kyaunta kaɗai ba, bari harma a cikin lokacin tsufanta da takwarkwashewarta da muninta; a sakamakon haka babu makawa ta taƙaita adonta  

91. Page

a bisa iya duban mijinta, kuma ta tsare soyayyarta a gare shi, domin haka shi ne manufar mutuntaka, idan ba haka ba sai ta samu amfani kaɗan kuma ta yi hasara mai yawa.

Sannan miji ya wajaba ya kasance daidai da matarsa a shari’a, ai kowanne ɗaya ya kasance ya dace da ɗayan, mafi muhimmancin sharaɗi a cikin daidaito shi ne addini.

Farin ciki ya tabbata ga mijin da yake duba i zuwa addinin matarsa da tsoron Allahnta sai yake koyi da ita, kuma ya yi riƙo da addini domin kada ya rasa abokiyarsa a rayuwa ta har abada, mamakin arzikin waccan matar wadda take duban addinin mijinta da tsoron Allahnsa sai ta yi riƙo da tsoron Allah har dai kada ta rasa abokin zamanta na har abada!


92. Page

Kuma taɓewa ta tabbata ga wannan mutumin da yake al’amuran na wauta da za su rasar da shi matarsa ta gari rashi na har abada, mamakin rashin arzikin wannan matar da bata koyi da mijinta mai tsoron Allah, sai ta rasa abokin zamanta mai albarka!

Dubun Taɓewa da azaba su tabbata ga waɗannan ma’aurata marasa arziki ɗayansu yana koyi da ɗaya a cikin fasiƙanci da sharholiya ɗayansu yana taimakon ɗayan  a bisa ingiza shi i zuwa wuta!


93. Page

HIKIMA TA UKU

Haƙiƙa jin-daɗin iyali a cikin rayuwa yana dawwamane ta hanyar aminci da ikhlasi da girmamawa da soyayya da ake musanyansu a tsakanin ma’aurata biyu.

Amma tabarruji da yaye jiki da rashin hijabi yana gurbata wannan amintaka yana ɓata wannan girmamawa, ya gurɓata tsarkin wannan soyayya da ake yi wa juna; domin cewa mace ɗaya ce kawai daga cikin mataye goma masu tabarruji masu yaye jiki bata ganin namijin da ya fi mijinta kyau, sannan bata ƙoƙarin ta soyar da kanta ga manesanta,


94. Page

sauran taran suna samun wanda shi ne ya fi mazajensu alheri, kuma ba ya gani sai namiji ɗaya a tsakanin mazaje ashirin cewa ga wata mata can da ta fi matarsa kyau, a yayin ne Ikhlasi yake gushewa da soyayya da girmamawa da su keyi a tsakaninsu, ƙari a kan haka cewa shi yana haifar da motsa ji na-jiki na fajirci mai muni maƙasƙanci, saboda haka mutum ba zai iya ɗauka –da irin zubin halittarsa ba- motsin sha’awa ga makusantansa kamar shaƙiƙiyarsa; domin cewa fuskokin nan na makusantansa suna sashi jin tausayi da soyayya da shari’a ta yadda da ita saboda dalilin kusanci da muharramanci, sai ta yanke karkatar nan ta zuciya da sha’awa, sai dai yaye sashin wasu wajaje wannan da ba ya halatta yaye su a shari’a, kamar ƙwaurika biyu har a gaban makusanta zai yiwu ya sabbaba motsa wulaƙantaccen jin nan ƙasƙantacce a cikin zukata maƙasƙanta; domin fuskar muharrami tana tunatar da kai muharramanci, bata kama da wanda muharraminka ba, sai dai ƙwauruka buɗaɗɗu -misali- muharrami da wanda ba muharrami ba suna daidaita, babu wata alama mai rabewa da take ba da labari a kan muharramanci; to domin haka zai iya yiwuwa su motsar a cikin maƙasƙantan zuciyoyi kwaɗayin duba kamar irin na dabba, duba irin wannan, faɗuwar mutuntaka ce wanda jiki yake ƙyanƙyamin ta. 


95. Page

HIKIMA TA HUƊU

Yana daga abin da aka sani, cewa yawan zuriya abin nema ne a wajen kowa, babu wata al’umma ko wata hukuma sai dai tana ƙarfafa gwiwa a wajen yawan dangi da zuriya, har dai Manzo mafi girma tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ce:

(تناكحوا تكاثروا فإني أباهي بكم الأمم) أو كما قال

Ku yi auratayya don ku yawaita, “haƙiƙa ni zan alfahari daku ga al’ummatai” ko kamar yadda ya faɗa:

Sai dai ɗauke hijabi ba ya ƙara yawan auratayya, bari dai, yana rage shi ne sosai; domin cewa matashin da ya fi ɓarna a cikin matasa da fasiƙanci da ƙuruciya yana son abokiyar rayawarsa ta zama kamanmiya ce tsarkakakkiya, ba ya so ta zama ’yar zamani kamarsa mai tabarruji mai yaye jikinta, sai ya tabbata a gwagwarci, bari wataƙila ma sai ya shiga alfasha (zina), amma mace bata zama kamar haka; domin ita bata iya hukunci a kan mijinta i zuwa wata iyaka babba, wannan domin mace abar umarni ce da kiyayewa  a bisa dukan dukiyoyin mijinta da ’ya’yansa da dukkan abin da ya keɓance shi don kasancewarta mai gudanarwa da sha’anonin cikin gida a rayuwar iyalai, a saboda haka mafi tabbatar ɗabi’o’inta su ne ikhlasi da cika alƙawari da aminci, amma tabarruji da yaye jiki yana wofantar da ikhlasi da cika alƙawari, da rasar da ita aminci a duban mijinta, ta sanya shi ya dinga jin raɗaɗi na lamirin zuciyarsa. 


96. Page

Hardai cewa jarumta da kyauta waɗanda su ɗabi’u ne ababan godewa a wajen mazaje da za su kasance a wajen mata da sai su kasance daga ɗabi’u munana; domin cewa su za su cutar kuma su wofantar da wannan amincin da cika alƙawari da ikhlasi, da sai a ƙirgasu daga ɗabi’u munana na zargi, sai dai aikin mijinta bai kasance taƙaitacce ba a bisa kiyayewa a kan dukiyoyinta da ikhlasi a gare ta, bari ya tattare kiyayeta da jin ƙanta da girmamata, kuma a saboda haka ba a sa namiji a ƙarƙashin wani tsaro da ƙayyadewa ba, bari yana iya yiwuwa ya auri wasu matayen. Haƙiƙa garuruwanmu ba a kwatanta su da turai; domin kamewa a can ana kiyayeta ne i zuwa wata iyaka, a tsakanin tabarruji da yaye jiki da hanyoyi masu tsanani kamar fito na fito, wannan da yake kallo kallo munmuna i zuwa matar mutum mai kwarjini babban mutum to ya sanya likkafaninsa a bisa wuyansa sannan sai ya kalla, sannan ɗabi’o’i a turai wadda take gari ne mai sanyi, sandararriya mai sanyi kamar waɗancan garuruwa, amma Asiya -ai yankin duniyar musulunci- ita mai zafi ce idan za a kwantanta da waɗancan garuruwan masu sanyi, yana daga abin da aka sani cewa, yanayi yana da tasiri  a bisa ɗabi’o’in mutum, amma tabarruji da yaye jiki, saboda 

97. Page

motsar da kwaɗayi irin na dabbanci da tada sha’awa nan ga waɗannan mutanen da suke a (ƙasar) sanyi, wataƙila bazai iya zama kira ne i zuwa aikata munanan ayyuka da ɓarna ba, amma tabarruji da yaye jiki wanda yake kodayaushe yana tada kwaɗayi da shauƙin nan ga mutane masu tsananin ji da tasirantuwa a cikin ƙasashen nan masu zafi lallaine zai bayu i zuwa aikata ayyuka munana da ɓarna da raunin haihuwa da zuriya da raunin ƙarfi da rushewarsa, sai namiji ya zama mai tsananin buƙata i zuwa ɓarna a kowanne kwanuka uku ko huɗu a lokacin da ya zama biyan buƙata ta zubin halitta ta zama sau ɗaya a kowanne wata ko a kwana ishirin; haƙiƙa biyan buƙata ta zubin halitta yana kasancewa ne sau ɗaya a kowanne wata ko kwana ishirin, a yayin da shi yake zama dole ya nisanta daga matarsa a tsawon kwana goma sha biyar a kowanne wata da sababin abubuwa masu bijirowa kamar haila, cewa shi zai iya karkata i zuwa alfasha, idan ya kasance kansa ya rinjaye shi. 


98. Page

Sannan ma’abota birane ba ya yiwuwa su ɗauke hijabi kamar ‘yan ƙauye, domin wahalar rayuwa tana shagaltar da mutanen alƙarya da ƙauyuka da suke buƙatuwa i zuwa aikin ƙarfi na jiki suke wahala, ƙaramin abu ba ya motsa sha’awar zuciya na daga mataye ma’aikata kuɓutattu masu kaushin jiki waɗannan da ba sa iya jawo kallon kowa, idan aka kwatantasu da matayen birane, ba a samun mazaje wawaye marasa aiki a ƙauye sai dai kaɗan; a saboda haka ba a samun kashi goma na daga abin da ake samu na ɓarna a birane, domin haka ba a kwatanta birni da ƙauye. 


99. Page

mas’ala muhimmiya da aka yimin ilhamarta katsahan.

Za a fahimta daga ruwayoyin hadisai cewa waɗanda za su taka rawa mafi haɗari a cikin fitinar ƙarshen zamani su ne jama’ar mata da fitinarsu. [1]


[1] Ya zo a cikin littafin Sahihu Muslim 4/2098 Hadisi mai lamba 2742 “Muhammad bn Musanna da Muhammad bn Bashar sun ce Muhammad bn Jafar ya yi mana Hadisi Shu’uba daga Abi Salmata ya ce na ji Aba Nadhara yana yin Hadisi daga Abi Sa’idil Khuduri daga Annabi (s.a,w.) ya ce: haqiqa duniya kamar riga ce mai kyau koriya, haqiqa Allah ya halifantar da ku a cikinta don ya ga me za ku aikata, ku ji tsoron duniya ku ji tsoron mata; haqiqa farkon fitinar ‘yan Bani Isra’ila ta kasance a mata, a cikin Hadisin Bashar, domin ya ga me za ku aikata”.

 




100. Page

Na’am, kamar yadda aka ruwaito shi a cikin tarihi, cewa yakasance a cikin zamuna da suka wuce wani kaso ne na sojoji da aka yi su na mata ƙwararru wajen amfani da makami matuƙar ƙwarewa, da ake ambatonsu da matan amazon[1], sun yi yaƙi yaƙoƙi ƙazamai; hakanan mataye masu tufafi matsiraita a cikin yaƙi na ɓatan zindiƙanci[2] wanda aka fuskanci musulunci da shi a cikin wannan zamanin, su ne mafi haɗarin kashi wanda aka miƙa jagorancinsu ga shaiɗan da shirin nan na zuciya mai yawan umarni da saɓo; domin suna kai hari ga ma’abota imani da ƙwaurukansu matsiraita, kai ka ce su wuƙaƙene masu kaifi, sai su ribace zukata masu yawa a cikin ƙiftawar ido. Kuma su soki zuciyoyinsu da rayukansu da manyan zunubai, masu tafiya ne don kulle ƙofar aure da yalwata hanyoyin gidajen fasiƙanci da alfasha,bari ma dai suna kashe sashin waɗannan zukatan; a saboda haka ne waɗannan ƙwauruka masu kama da wuƙaƙe za su zama ƙiraren jahannama, waɗanda za a ƙona da farko kafin dukkan komai, sakamako mai dacewa  a bisa bayyana waɗannan ƙwauruka a gaban waɗanda ba muharramai ba shekaru masu yawa, kuma ba za su samu namiji wanda ya dace da su ba wanda suke nufin su rabauta sosai da shi, da suke buƙatarsa buƙatuwa matsananciya da irin zubin halittarsu; saboda dalilin tozartawarsu aminci da gaskiya da ikhlasi a duniya har da dai za su same shi da sai ya zama musiba a gare su.


[1] Mace mayaqiya a cikin labarukan Rumawa ta shahara da sunan Amazon, an ruwaito cewa ya kasance akwai wata jama’a ta mayaqa mata ana kiranta da matan Amazon sun kasance suna amfani da makamai mabambanta a yaqinsu, labaran yaqunan Rumawa suna cike da ambaton waxannan jama’a ta mata da yaqunansu tare da Girkawa, wasu sashi daga masu bincike suna danganta qoramar Amazon ga waxancan matan

[2]Mai wasa da addini.

تم بحمد الله