Saƙo na shida
NAVIGATION
17. Page
SAКO NA SHIDA
Haƙiƙa Manzo mafi girma (S.A.W) ya ce "كل بدعة ضلالة وكل ضلالة في النار"
“Dukkan bidi’a ɓata ce, dukkan ɓata yana cikin wuta[1]”, ai ƙin ƙa’idojin shari’a mai haske da dokokin sunnah mai haske da ƙin ganin girmansu da ƙin ganin kyaunsu da canza su da sababin al’amura bayan sun cika sun kammala da sirrin aya: (اليوم أكملت لكم دينكم) (المائدة: 3)
ko kuma farar da bidi’o’i da suke nuni, kamar mai farar da su yana ganin waɗannan ƙa’idodi da dokoki na Allah da suka zo daga Annabi (S.A.W) masu tawaya ne -Allah ya tsarkaka ga haka-, to wannan shi ne ɓata da wuta.
Haƙiƙa akwai darajoji ga sunna mai haske, wani kashi daga gare ta wajibi ne, ba ya yiwuwa abar shi, kuma wannan kashin haƙiƙa an bayyana shi ƙarara tare da
[1] Wannan hadisin za a same shi a littafin Sunani Annisa’i Alkubra hadisi mai lamba 449 ko Sahih Ibn Khuzaimah mujalladi na uku shafi na 143 ko Mu’ujamul Kabir 9/98.
18. Page
rarrabewa a cikin shari’a mai tarin haske, shi yana daga cikin tabbatattun dokoki waɗannan da ba ya yiwuwa a canja su ta kowacce fuska daga fuskoki .
kashi daga gare ta da yake na nafiloli, ya kasu ya zuwa kaso biyu:
Ɗaya daga ciki shi ne sunnah mai haske, wadda ta keɓanci ibadu, haka nan ma kuma ita an bayyana ta a cikin littattafan shari’a, canza ta bidi’a ne, ɗaya kashin kuwa an ambace shi “da ladubba”, haƙiƙa an ambace shi a cikin littatafan sira mai haske, ba a ambaton saɓa masu a matsayin bidi’a sai dai cewa ita tana kasancewa saɓawa ce ga ladubban Annabi (S.A.W) , kuma bijirewa ga fa’idantuwa daga haskensu kuma daga ladubba na haƙiƙa, wannan kashi shi ne na bibiyan ayyukan Manzo mafi girma (S.A.W) waɗanda suka shafi al’adu da mu’amalar mutuntaka ta fiɗira, waɗanda aka sansu ta hanyoyin mutane da yawa, da yawa akwai daga sunnoni masu haske waɗannan da suke bayyana ladubban zance misali, da dokokin nan na ladubban halaye kamar ci da sha da barchi da abin da ya shafi mu’amala, ana kiran wannan nau’i na sunnoni “Laduba”, duk wanda da yake bin wannan laduba, al’adunsa suna juyawa su koma ibadah kuma yana samun falala mai girma daga waɗannan ladubba; domin cewa kula da mafi ƙarancin laduba tana tunatarwa da Manzo mafi girma (S.A.W) kuma tana kwarara haske a zuciya.
19. Page
Haƙiƙa mafiya muhimmanci da mafiya girman sunnoni a tsakanin sunnoni masu haske su ne waɗannan da suke rataye da manyan alamomin musulunci, alamomin su ne – kamar ibada – na daga nau’in haƙƙoƙi na gaba ɗaya waɗannan da suka keɓanci al’umma, kamar yadda al’umma dukkanta take fa’idantuwa da aikatawar mutum ɗaya daga cikinta, cewa dukkan al’umma kuma tana kasancewa abin tambaya ga barinta, misalin wannan nau’in na daga manyan alamomi ana bayyana su a fili, riya kuma bata shigarsu, suna da muhimmanci sama da farillai na ƙashin kai, har dai ko da waɗannan manyan alamomi sun kasance daga nafiloli.


