Saƙo na takos
NAVIGATION
25. Page
SAƘO NA TAKWAS:
Haƙiƙa ayar: (لقد جاءكم رسول) I zuwa ƙarshen ayar (wacce ta zo
kafin ayar) (فإن تولو فقل حسبى الله)
tana bayyana cikar tsausayin Manzon mai girma (S.A.W) da ƙarshen tausayawarsa ga al’umarsa, sannan wannan ayar tana cewa:) (فإن تولوا
yaku mutane ya ku musulmi! to fa ku sani, da yawa akwai zalunci da tsabar zalunci da yawa akwai wauta da shashancin a cikin bijirewarku ga sunnah da hukunce-hukunce, waɗanda wannan mutum mai tausasawa da jin-ƙai ya isar da ita, wanda ya shiryar da ku ta hanya tausayawa da bata da iyaka, kuma ya ba da dukkan ƙoƙarinsa da ƙarfinsa da abin da yake cikin yalwarsa, saboda maslahar ku, kuma da matuƙar jin-ƙan shi ya magance waɗannan raunukan naku na ma’ana da wannan hukunce-hukuncen da ya taho da su da kuma sunnah mai haske, kai ka ce ku kuna musanta wannan tausayawa mabayyaniya, kuma kuna tuhumar tausayawa mabayyani ta zahiri!.
26. Page
Ya kai wannan Manzo mai jin-ƙai kuma ya kai wannan Annabi mai tausasawa, idan waɗannan ba su san tausasawarka mai girma ba, da jin-ƙanka mai girmaba, kuma ba su girmama su ba, kuma Idan suka bijire suka juya baya ga barinka ba su saurare ka ba saboda shashancinsu da wautarsu, kada ka samu damuwa kada ka yi baƙin ciki, haƙiƙa mai gaskiya maɗaukaki ma’abocin girma, wannan da rundunar ƙasa da sama suke a ƙarƙashin umarninsa, wannan da masarautar ubangijintakarsa ta mamaye a bisa al’arshi mai girma wanda ya kewaye dukkan komai, shi ya isar maka, kuma shi ne zai tattaro jama’a masu biyayya a gefenka da gaskiya, ya sanya su suna sauraro i zuwa gare ka suke karɓar hukunce-hukuncen ka.
27. Page
Tabbas; babu wata mas’ala a cikin Shari’ar Muhammadiyya da Sunnar Ahmadiyya – a bisa ma’abocinta tsira da aminci su tabbata a gare shi -, sai dai tana da wata hikimomi masu yawa, kuma ni talaka ina wannan da’awar tare da dukkan gajiyawata da taƙaitawata, ina mai shiri don tabbatar da wannan da’awa, sannan cewa har yanzu abin da aka rubuta, kuma aka wallafa abin da yake isuwa na daga wasiƙa saba’in ko tamanin na daga wasiƙun nan na Rasa’il al-nur, suna matsayin shaidu saba’in ko tamanin masu gaskiya a bisa cewa haƙiƙa mas’alolin sunnah ta Ahmadiyya da Shari’ar Muhammadiyya, tabbas su ma’abota hikima da haƙiƙa ne, da za a samu ikon rubutu a kan waɗannan hikimomi da saƙonni saba’in ba za su ɗauke ta ba, kai bari saƙonni dubu ɗari bakwai ma ba za su iya Ƙididdige waɗannan hikimomin ba.
28. Page
Haƙiƙa ni tabbas ina sanarwa haƙiƙa ni na sani da kaina ta hanyar gani da ɗanɗano, bari da dubunnan na gogayya, haƙiƙa mas’alolin shari’a da dokokin nan na sunnah mai haske, magani ne mai amfani ƙwarai ga cutukan nan na rayuka da hankula da zuciya, musamman ma cutukan nan na al’umma, haƙiƙa ni na ji da kaina hanyar dubawa, da sa wasu su ji i zuwa wata iyaka, a cikin Rasa’il annur, haƙiƙa mas’alolin nan na falsafa da na hikima ba ya yiwuwa su tsaya a matsayin waɗannan dokoki ko su maye bigirensu, to waɗannan da suke kokwanto a wannan da’awar tawa, ya wajaba a gare su da su koma juzu’an Rasa’il annur su yi duba a cikin su.
To a auna matuƙar ribar da yake cikin bin sunna mai haske ta wannan mutum daidai gwargwadon iko, da matuƙar arzikin nan da jin daɗi na rayuwar ta har abada, da matuƙar abin da yake cikin binta na daga amfani da maslaha ga rayuwar duniya.


