Saƙo na tara

29. Page

Saƙo na Tara:

Ba ya zama mai sauƙi bin kowanne nau’i na daga nau’o’in sunnah mai haske biyayya cikakkiya a aikace sai dai kawai ga keɓantaccen keɓantattu,

saidai kowa zai iya neman wannan bibiyar da niyya da nufi da karkata i zuwa gare shi da lazamtuwa da shi, ko da bai samu ikon binsa ba, biyayya cikakkiya.

 bin nau’o’in farilla da wajibi na daga sunnah mai haske dole ne tun asali, amma sunnoni mustahabai a cikin ibadu, to a cikin barinsu akwai tozarta lada mai girma, idan ma bai zama da zunubi a cikin sa ba, a cikin kuma canzasu akwai kuskure mai girma. 


30. Page

Amma sunnoni masu haske a cikin al’adu da mu’amaloli, anason maƙalewa da nacewa a bisa bibiyarsu har waɗannan al’adu su juye su koma ibadu, idan mutum bai bisu ba, babu zargi a gare shi, sai dai fa’idantarsa daga hasken laduban nan na rayuwar masoyin Allah (S.A.W), tana ƙaranta.

Haƙiƙa farar da al’amura a cikin hukunce-hukuncen ibada, bidi’o’i ne, su ko bidi’o’i ababan juyarwa ne; domin cewa su suna kore sirrin (اليوم أكملت لكم دينكم) sai dai cewa ita idan ta kasance daga nau’ukan wuridai da zikirai da mashayai -kamar yadda yake a cikin hanyoyin sufaye-, ita bata kasance bidi’a ce ba, da Sharaɗin ta kasance tushensu ya samu asali daga Alƙur’ani da sunnah, da sharaɗin lallai kada ta saɓawa tushen sunnah maihaske, wadda aka tabbatar da ita, kuma lallai kada ta canja ta ko da ta kasance  a bisa kamanni mabambanta da surori da nau’o’i mabambanta. 


31. Page

Sai dai sashin wasu daga ma’abota ilimi sun ɗauki sashin waɗannansu daga cikin waɗannan al’amura a matsayin bidi’o’i, sai dai cewa su, sun ambace su da “bidi’o’i masu kyau”; yayin da mujaddadin shekara ta 2000, imam arrabbani yana faɗa:na kasance ina gani a cikin tsakatsakin tafiya ta ruhi, haƙiƙa kalmomi da aka ruwaito daga manzo mai girma tsira da aminci su tabbata a gare shi masu haske ne suna ƙyalƙyali da hasken sunnah mai haske, kuma yayin da na kasance ina ganin wurudai da halaye masu haskakawa masu ƙarfi waɗanda ba a ruwaito daga gare shi ba (S.A.W) wannan hasken bai kasance a gare su ba, abin da ya fi haske da yake cikin wannan kashi bai kasance yana isuwa i zuwa mafi ƙaranci daga abin da yake kashi na farko ba, sai na riski daga wannan, haƙiƙa hasken sunnah mai haske iksir ne(wani sinadari ne da magabata suke riyawa cewa yana maida ƙarfe i zuwa zinare), haƙiƙa sunnah mai isuwa ce ga waɗannda suke neman haske, babu buƙatar binciken haske a wajen kewayenta. 


32. Page

Wannan hukuncin na gwarzo daga gwarazan haƙiƙa da shari’a yana bayyana haƙiƙa, ita sunnah mai haske ita ce bulo na farko na harsashin arziki da jin daɗi na gidaje biyu[1], da ma’adanin nan na kamaloli da maɓuɓɓugar su.

Ya Allah ka arzurtamu da bin sunnah mai haske, amin.

(ربنا آمنا بما أنزلت واتبعنا الرسول فاكتبنا مع الشاهدين).


[1] - Duniya da lahira.