Saƙo na uku
NAVIGATION
5. Page
Saƙo na Uku:
Yayin da Sa’id mai buƙata a wajen Allah ya kasance yana ƙoƙarin fita daga halinsa na Sa’id na da[1], sai hankalinsa da zuciyarsa suka yi kai-komo a tsakankanin haƙiƙoƙi, cikin tashin hankali na ma’ana mai tsoratarwa da sababin rashin samun mai shiryarwa a gare shi, da dalilin ruɗin nan na zuciya mai yawan unmarni da munanan aiyuka, Sun kasance suna kai-kawo wani lokacin daga ƙolin sama, i zuwa turɓaya ta dandagaryar ƙasa, suna hawa daga ƙasa i zuwa ƙolin sama a wani lokacin, hakanan cikin sauka da hawa, a sannan ya ga haƙiƙa mas’alolin sunna mai haske – har da ladubbanta masu sauƙi-kai ka ce hanya ce da take bayyana mafuskantar jiragen ruwa, kuma alamomi ne da suke a bisa hanya mai haɗari mai duhu.
[1] Kafin shekaru arba’in na rayuwarsa, ana kiransa da Sa’id na da, amma bayan shekara arba’in na rayuwarsa ana kiransa da Sa’id sabo, a lokacin ne ya rayu yana mai sake samun sabon juyi na ruhi da tunani da fuskantar mafuskanta sabuwa.
6. Page
Yayin da na ga kaina a cikin wannan tafiya ta ruhi a ƙarƙashin ƙuntace-ƙuntace matsananta da wahalhalu, da nauyaye-nauyaye da suke abkuwa a kan kaina, sai nabi koyarwar sunna mai haske da abubuwan da take koyarwa, waɗannan da suke dacewa da wannan halin; sai na samu sauƙi da hutu, kai ka ce su ne suka ɗaukake dukkan wahalhalu da nesantar da su ga barina,[1] kuma na kasance ina tsira daga shibuhohi da was-wasi da baƙƙan ciki ta hanyar miƙa wuya ga sunnah, misali: ya ku jama’a shin waɗannan aikace-aikace gaskiya ne? shin akwai maslaha a cikin su?
[1] - Tsallake.
7. Page
Daga zarrar na bar wannan biyayya sai na ji ƙunci mai tsanani, sai na ga hanyoyi masu yawa a gabana, waɗanda ba a san mashigar su da mafitarsu ba, ba a san i zuwa ina za su tuƙe ba, sai na ji cewa wahalar mai nauyi ce, ni kuma mai matuƙar gajiyawa ne, kuma ganina taƙaitacce ne, ga hanyar kuma tana da duhu.
Amma da zarar da na komo riƙo da sunnah, sai na ji a wannan halin kamar hanya ta haskaka, sai hanya amintacciya kubutacciya ta bayyana, sai wahala ta sawwaƙa, ƙunci ya gushe, a sannan ne na gasgata hukuncin Imamu Rabbani sai na ganshi a fili ƙuru-ƙuru nasan gaskiya ne.


