TAКAITACCEN TARIHIN IMAM BADI’UZ ZAMAN SA’İD NURSİ

1. Page

TAКAITACCEN TARIHIN IMAM BADI’UZ ZAMAN SA’İD NURSİ

 

An haifi Imam Badi’uzzaman Sa’id Nursi a cikin ƙauyen Nuris a jihar Bitlis, a shekara ta 1293\AH wadda ta yi daidai da 1877\AD, a gabashin Turkiyya.

Ya zauna a wajen iyayensa a cikin gidansu har ya kai ɗan shekara tara a duniya. Ya fara karatunsa na farko ne a hannun babban wansa, Malam Abdullahi. Ya hardace Alƙur’ani a tsakankanin sati biyu; sai hankalin mutane ya karkato kansa, saboda ƙarfin ƙwaƙwalwarsa da kaifin hankalinsa da ƙarfin zuciyarsa, a cikin karatunsa na taƙaitaccen lokaci a wajen manyan malamai, da makarantu daban-daban a gabashin Turkiyya.

Wannan sai ya sanya mutane suka yarda cewa shi ne na farko a wajen ilmi. A yayin da kuma ya gama dukkan darasin zangunan karatu, da kwatankwacin abin da tsarin malaman Usmaniyya na wannan lokacin ya ƙunsa, a taƙaitaccen zamani (wata uku). Ya yi nasara a cikin jarrabobi da malamansa suka yi masa da kuma tattaunawa ta ilimi da aka yi tare da shi.

Haƙiƙa malaminsa ne ya kirawo shi da Badi’uzzamani tun a lokacin ƙuruciyarsa ya kirawo shi da wannan sunan, saboda ƙarfin ƙwaƙwalwarsa da kaifin hankalinsa wanda samun irinsu yake da wahala. Sai wannan laƙabin ya samu karɓuwa a wajen dukkan malaman gabashin Turkiyya.

Bayan lokacin ƙuruciyarsa Imam Badi’uzzaman ya zagaya cikin cibiyoyin ilimi, waɗannan da ya kasance yana aikin harkar ilimi da ibada da horar da ruhi a cikinsu, kamar misalin (Bitlis) da (Siirt) da (Tillo) da (Mardin) da makarantu da suke tabbatattu a cikin wannan lardi. Ya haɗu da mashahuran malamai a zamaninsa kuma ya zauna da su.

Ya hardace mujalladi casa’in na daga ilimai mabambanta a cikin wannan ɗan zamani, kamar irin su Sarfu da Nahwu da Manɗiƙi da Tafsir da Ilmul Kalam[1]. Ya ƙware a harshen Larabci da Farisanci, a ɗaya ɓangaren kuma harshen Turkiyyanci da Kurdiyyanci sun zama kamar harshen uwa ne a wajensa. Ya tsaya a kan ra’ayin ilimin zamani wajibi ne; don isar da musulunci a kan fahimtar zamani.

Кari a kan haka, ya karanci wasu iliman da ƙoƙarin kansa (wato ba tare da ya je gaban malami ba) kamar lissafi da ilimin sanin abin da yake ƙarƙashin ƙasa, Fiziyya da Kimiyya da ilmin Falaki da Tarihi da Ilimin sanin ƙasa (Geography) da Falsafa, duk a cikin taƙaitaccen lokaci.

A iya tsawon lokacin da ya zauna a cikin garin Wan wanda ya kusanci shekaru goma sha biyar, ya shagala ne da koyarwa da wa’azantar da jama’u da shiryar da su, har dai cewa aka san shi da makaranta a nan, wadda ake kiranta Khur-Khur.


2. Page

A lokacin da yake a cikin fadar gwamna, Ɗahiru Basha, ya karanta wani labari a jarida, wanda ya haifar da wani babban canji a cikin rayuwarsa, wato shi ne wazirin ƙasashen da Ingila suke yi wa mulkin mallaka mai suna Gladston, yana mai ba da shawara, ya riƙe Alƙur’ani a hannunsa, yana mai cewa, mutuƙar wannan Alƙur’ani yana hannun musulmi, ba za mu iya mulkar su ba. Lallai-lallai mu je mu karɓe shi daga wajensu, ko mu nesanta su daga gare shi, duk irin kuɗin da za mu kashe.

Haƙiƙa wannan magana ta yi tasiri matuƙar tasiri a cikin zuciyar malam. Sai ya ɗauki alƙawari a kansa, ya ce: (wallahi sai na fito da dalilai, wallahi sai na bayyanawa duniya gabaɗayanta cewa tabbas wannan Alƙur’ani rana ce a wajen haske, wadda ba ta bicewa kuma ba za a iya bice ta ba); wato shafe shi ba ya yiyuwa, haƙiƙa kuwa, ya tsaya a dukkan rayuwarsa saboda tabbatar da wannan al’amari.

Sai ya fara aikin samar da jami’a wadda ake kira (Madrasat Alzahra’a) wadda za a dinga koyar da ilmin addini da na zamani tare a waje ɗaya, sai ya tafi i zuwa babban birnin Usmaniyya, wato Santanbul a lokacin yana ɗan shekara talatin don gabatar da wannan katafaren aiki a wajen sarkin musulunci na Usmaniyya.

Shi da almajiransa sun yaƙi ƙasar Rasha a lokacin yaƙin duniya na biyu, bayan shekaru biyu da wannan yaƙin na Rasha, sai ya faɗa cikin ribatattun yaƙi, bayan shekaru biyu kuma sai ya sake dawowa Santanbul, bayan ya fito daga bursunancin yaƙi.

Amma waɗannan da suke riƙe da mulkin masu gudanar da mulki a cikin sabuwar daula, sun ƙulla wasu alƙawarurruka da Turawa a sirrance, sai suka fara yin zalunci da danniya don su bice hasken musulunci a Turkiyya; domin su mantar da mutane Alƙur’ani, suka rasar da dubunnan mutane, musamman ma malamai a cikin kotu-kotu, waɗanda suka yi su kawai saboda haka. Suka rufe makarantun Islamiyya, suka hana koyar da addini, suka hana amfani da haruffan Larabci, suka tilasta koyar da haruffan boko da yin amfani da su, kai in taƙaice ma zance sai da suka hana kiran sallah, sai dai ka yi kiran sallah da harshen Turkiyyanci, hakanan suka yi ta amfani da kowace hanya don su juyar da kowane gurbi na tsarin musulunci daga rayuwar al’ummar.

Haƙiƙa Imam Nursi ya tabbatar da cewa hanyar da za a fuskanci wannan rusau na musulunci, hanya ɗaya ce, shi ne a fuskanci Alƙur’ani (wato a riƙi Alƙur’ani wajen fuskantar su).

Don haka sai ya wallafa mujalladai goma sha huɗu masu yalwataccen bayani, waɗanda suka ƙunshi risaloli ɗari da talatin, da ya kira su da Rasa’il Nur (wato wasiƙu ko littattafai masu haske), waɗanda sun ƙunshi al’amuran musulunci na wannan zamanin.


3. Page

Waɗannan Rasa’il, sun rusa ra’ayoyin masu adawa da musulunci, sun fatattaki munanan hujjojin masu ilhadi, waɗanda aka fara yaɗa su, a hannun daular ‘yan sakyula, (‘yan ba ruwanmu da addini), sai ya fara baza waɗannan Rasa’il a kowanne loko na Turkiyya. Haƙiƙa ya wallafa waɗannan Rasa’il da ilhama daga ayoyin nan na Alƙur’ani, waɗanda suke rushe kafirci da ɓata, suke tabbatar da tauhidi da lahira.

A lokacin wallafa waɗannan Rasa’il bai zama akwai wani littafi a gurinsa ba, sai Alƙur’ani kawai, ya kasance ana yi masa ilhama daga ma’anonin ayoyinsa masu girma, ya rayu zuciyarsa da ransa suna tsarkakakku da dukkanin sauran sasanninsa.

Shi a cikin Rasa’il nasa yana zance ne da hankulan mutane kuma da fahimtarsu, da matakansu da yanayin shekarunsu. yana ba da muhimmanci da al’amuran kowace jama’a na kowane mataki da kowane shekaru, ba ya barin ɗaya saboda kula da ɗayan.

Ya zo da salo irin na zamani wanda ya kaɗaita da shi, wanda yake magana a kan ainihin batutuwa na musulunci da salon da ya dace da zamani, ya magance matsaloli da ƙadiyyoyi na musulmi kyakkyawar magancewa.

Ya samarwa da mutane wayewa a musulunci da kuma mayar da su i zuwa tushensu na asali.

Haƙiƙa ya yi riƙo da tushe madaidaici, (wannan lokacin, lokaci ne na jama’a). A jihadinsa na ba da ilimi da na gyaran zuciya, ya fara aikinsa da yaɗa ilimi a kowanne lokon garin tare da dubunnan ɗalibai na Rasa’il Nur, waɗanda suke karanta Rasa’il Nur suke rubuta su, suke karanta su a tsakankaninsu tare da kiran junansu i zuwa gidajen juna.

Shi ne farkon wanda ya tsaya a harkar musulunci a sabuwar Turkiyya. Kuma an fassara waɗannan Rasa’iloli i zuwa sama da harsuna talatin na duniya, waɗanda suka yaɗu a da yawa daga ƙasashen duniya.

Haƙiƙa abin da Imam Nursi ya tsaya da shi[2], ya tsayawa maƙiya musulunci a zuciya. Saboda haka ya yi rayuwa irin ta ɗaurin talala wanda ya kai tsawon shekaru talatin da huɗu, ana tsare da shi daga wannan gari i zuwa wannan garin. Mafi yawa da mafi tsawon inda aka tsare shi, shi ne garin Isparta, aka tsare shi a kurkuku aka ba shi guba, an sha kawo masa hari don a kawar da shi daga doron ƙasa, gabaɗaya rayuwarsa ta kasance a ƙarƙashin sa’ido da takunkumi. Sai dai ba wani ƙarfi da ya iya hana shi yin hidima ga musulunci, saboda falalar ƙarfin imaninsa da kuma ikhlasinsa, waɗannan da ake girmama shi don su.

Haƙiƙa ya bayyana don kare kansa a cikin kotu, a wannan ƙudurin aniya na yi wa Islama hidima: (yana mai cewa da a ce ina da kawuka adadin yawan gashin kaina, kowace rana a cire guda ɗaya daga gare su, ba zan rusuna wannan kan ba wanda shi fansa ne ga haƙiƙoƙin nan na Alƙur’ani. A gaban zindiƙanci da kafirci tsantsa, ba zan bar wannan da’awah ta imani mai haske ba, ba zan iya bari ba).

Shi ne farkon wanda ya tsaya da harkar Islamiyya a sabuwar Turkiyya. Shi ne farkon wanda ya fara kawo cikas ga munanan canje-canje na daular Sakyula, bayan faɗuwar Halifancin Islamiyya.

Haƙiƙa Imam Nursi ya bar dubunnan ɗaruruwan ɗalibai tare da Littattafan Rasa’il Nur, waɗanda su ne tafsirin imani ƙayatacce na Alƙur’ani mai girma, wanda irinsa yake da wuyar samu. Sannan sai ya tafi i zuwa rahmar Ubangijinsa mafificiya, a cikin garin Urfa a shekara ta 1960.

Haƙiƙa ya yi ishara a cikin da yawa daga Rasa’ilolinsa, wannan da ya wallafa su ya rubuta su, i zuwa jama’arsa da almajiransa, da su tattaru a nan wajen Ustaz Ahmad Khusrau, kuma ya ce ku yi sani haƙiƙa Khusrau shi gwarzon Rasa’il Nur ne, shi kamar a matsayina yake.

Hukuma ba ta ƙyale shi ba har lokacin da yake numfashinsa na ƙarshe. Bari dai in taƙaice ma bayani, har bayan rasuwarsa ma, da wata uku, sai da suka je suka buɗe kabarinsa suka ɗauke gawarsa suka kai ta wani waje, da ba wanda ya san wajen.