TAКAITACCEN TARIHIN SHAIK AHMAD KHUSRAU AFANDI
NAVIGATION
4. Page
TAКAITACCEN TARIHIN SHAIK AHMAD KHUSRAU AFANDI
Shi ne marubucin Mus’hafin Tawafuƙat, mai yaɗa Rasa’il Nur, kuma khalifan Imam Nursi. Nauyin yaɗa littattafan Rasa’il Nur, bayan Imam Nursi, ya koma kan Ahmad Khusrau, shi ɗalibinsa ne mai ikhlasi, wato Shaik Ahmad Khusrau Afandi. Ya tafi a kan wannan tafarki tare da cewa duk bala’o’in da suka faru tun a lokacin rayuwar Imam Nursi, ba su tsaya ba har bayan rasuwarsa.
An haifi Shaik Ahmad Khusrau Afandi a cikin garin Sanniraja wadda take a ƙarƙashin jihar Isparta, a shekara ta 1315\AH ko 1899\AD. Haƙiƙa shi jika ne daga cikin jikokin Ibn Sayyid Alhaji Adham, wanda ɗaya ne daga cikin gwamnonin Isparta. A cikin ƙarshen mulkin daula Usmaniyya. Babansa shi ne; Sayyid Muhammad, babarsa ita ce Sayyida A’isha.
Haƙiƙa, tushen nan na nasabar babansa, waɗannan da aka san su da (ma’abota korayen rawuna) waɗanda su ne mafi ɗaukakar jama’a a Isparta, wadda wannan nasabar tasu take saduwa i zuwa Sayyidina Abubakar, Allah ya ƙara yarda a gare shi. Amma asalin babarsa, Sayyida A’isha, ta fito ne daga jikokin Manzon Allah (S.A.W), daga Sayyidina Husaini, Allah ya ƙara yarda a gare shi. Кarin daɗawa kuma tana da dangantaka i zuwa gidan ilimi, kakanninta sanannu ne, domin cewa su makaranta ne kuma mahaddata.
Bayan ya kammala karatunsa na sakandare a bisa tsarin Usmaniyya a lokacin daular Usmaniyya, sai ya shiga yaƙin duniya na farko. Bayansa ne kuma sai ya shiga yaƙin nemo ‘yanci, suna masu yaƙar daular Yunan. Sai ya faɗa hannunsu a matsayin ribataccen yaƙi, ya yi rayuwa irin rayuwar nan ta bursunonin yaƙi, ta tsawon shekaru biyu, bayan ya fito daga bursunancin yaƙi sai ya zama ma’aikaci na tsawon shekaru takwas.
A cikin shekara ta 1931\AD a cikin garin Isparta, wannan da ya rayu a cikinsa, a nan ne ya san Imam Badi’uzzaman Sa’id Nursi, wanda a nan garin ne aka yi masa ɗaurin talala (wato shi Imam Nursi). Shi kuma Shaik Ahmad Khusrau Afandi, wanda ya kasance yana neman mai shiryarwa cikakke, wanda zai sadar da shi i zuwa ga Ubangiji mai girma da ɗaukaka, tun wani zamani mai tsawo. Sai ya tafi ya ziyarci Imam Badi’uzzaman Sa’id Nursi, ya zauna da shi bayan ya karɓi wasiƙar gayyata daga wajensa. A wannan haɗuwar ya fahimci, shi ya sadu da mai shiryar da shi, wanda ya kasance yana nemansa.
5. Page
Sannan sai ya bar aikinsa sai ya fara hidimar nan ta Rasa’il Nur da ƙoƙari da ƙudurin aniya, wadda ta zama cikakkiya, a ƙarƙashin kulawa da umarnin Imam Badi’uzzaman Sa’id Nursi.
Haƙiƙa Shaik Ahmad Khusrau Afandi ya kasance shi ne mafi kusancin ɗalibi ga Imam Badi’uzzaman Sa’id Nursi. Bayan ya kasance mai ikhlasi ne da cikakkiyar kamala, kuma ga shi da ƙoshin lafiya, (komai da komai ya ji). Sai aka fara kiransa da babban malami na biyu. Sannan sai ɗaliban Rasa’il Nur, suka ɗauke shi a matsayin babban malaminsu na biyu. Sai suka fara kiransa da babban malaminmu na biyu a cikin rubuce-rubucensu.
Shaik Ahmad Khusrau Afandi shi ya assasa Waƙful Khairat a shekara ta 1974\AD shi ne ya ba da damar bugawa da yaɗa Mus’hafi-Tawafuƙat, wanda shi ne ya wallafa shi ga Waƙful Khairat. A dai cikin wannan lokacin ne, ya fara gudanar da hidimar Annur ta ƙarƙashin wannan ƙungiya. Sannan sai ya koma i zuwa rahamar Ubangijinsa, a cikin shekara ta 1977\AD, a cikin watan Agusta, bayan rayuwa mai cike da haske wadda ta kai shekaru 77. Rayuwar tana cike da wahaloli, a cikin hanyar hidimar imani da Alƙur’ani da Rasa’il Nur, har tsawon shekara 46.
Waɗanda suka zo bayansa sun gaji Mus’hafin Tawafuƙat, wannan da yake yana ƙayatar da idanuwa da bayyana mu’ujizar Alƙur’ani da karamar wannan bawan Allah da ya rubuta shi, da irin tsarinsa da ya saɓawa al’ada, wanda yake a cikin rubutunsa. Da dubunnan kwafi na Rasa’il Nur, abar dogara, wadda ta kai matuƙa a wajen kyau. Da dubunnan ɗaruruwan ɗalibai masu shauƙi ga hidimar Musulunci, har a can zurfin ƙarƙashin zukatansu.
A bayansa an jiɓintar da amanar Rasa’il Nur i zuwa ɗaya daga cikin maɗaukaka a yanzu, Shaik Gwani Sa’id Nuri, shi ma yana daga cikin ɗaliban Imam Nursi.
Haƙiƙa Ustaz Ahmad Khusrau ya samu soyayyar Imam Nursi da girmamawarsa, saboda abin da ya tsaya da shi na daga yaɗa Rasa’il Nur har tsawon shekaru talatin a Turkiyya. Da kuma ƙoƙarin da ya shimfiɗa na kira i zuwa ga addini. Haƙiƙa Imam Nursi ya yi magana a kansa.
Haƙiƙa Khusrau, gwarzo ne ga mutanen Turkiyya, (wanda ba kamarsa) kuma mai tsamo wannan ƙasa ne daga halaka. Mai gaskiyar sadaukantar da kai ne ga al’ummar Turkiyya, suna alfahari da shi. Imam Sa’id Nursi ya ƙara da cewa da ina da rayuka guda arba’in da na fanshe ka da su.Haƙiƙa maƙiyan musulunci sun fahimci cewa, Haƙiƙa Sayyid Khusrau shi ne mafi kusanci a ɗaliban Imam Nursi, wanda zai iya zama halifansa. Sai suka fara farautarsa, suna tuhumarsa. Har dai almajiran Rasa’il Nur suka fara baya-baya da shi. Yayin da Imam Nursi ya fara jin haka, sai ya yi magana a kansa.
Haƙiƙa ni ina jin tsoro na ɗauki matsayi na ƙiyayya a gare shi ko da yana da kurakurai guda dubu, domin cewa ɗaukar matsayi na ƙiyayya a gare shi a yanzu, kamar na ɗauki wuƙa ne na daɓawa kaina da kuma ƙin Rasa’il Nur kai tsaye, ha’inci ne mai girma, kuma maslaha ce ga waɗannan da suke zaluntar mu.
6. Page
TAКAITACCEN TARIHIN SHAIK SA’ID NURI, JAGORAN ƊALIBAN RASA’IL NUR NA UKU
An haifi Shaik Sa’id Nuri a shekara ta 1937\AD a nahiyar Kule-onu, wadda take a ƙarƙashin jihar Isparta. Mahaifinsa Gwani Mustapha, ya kasance ɗaya daga makusantan ɗaliban Imam Nursi, su shida ne, waɗanda Imam yake kiransu da (rukunai shida). Haƙiƙa nahiyar Kule-onu ta kasance ɗaya daga mafi girman cibiyoyi, wadda ta kasance ta taka rawa sosai a cikin fitar da kwafi-kwafi na Rasa’il Nur. Wannan da Imam Badi’uzzaman Sa’id Nursi ya wallafa shi, sannan ya yaɗa su a lokunan Turkiyya. Ya rayu tun daga ƙuruciyarsa a cikin wannan yanayi, na irin wannan cibiya ta Rasa’il Nur, da ake aiki tuƙuru a cikinta na da’awar Rasa’il Nur.
A lokacin da aka haifi Ustaz Sa’id Nuri, babansa ya yi nufin ya sa masa sunan (Sa’id Nursi) saboda neman albarkar malaminsa. Sai dai cewa Ustaz Imam Nursi, sai ya canza sunan i zuwa (Sa’id Nuri). Haƙiƙa ya ambaci haka a cikin littafin (Mulhaƙ Amir Ɗag) da faɗinsa “Gwani Mustapha wanda ya kasance a cikin masu ƙwazo da ake girmama su ya yi aiki da yawa wajen yaɗa Rasa’il Nur, ya kamata ya ambaci ɗansa mai albarka abin kiyayewa, wanda ya rubuta, Risalat (Shu’a’u Sadis) da sunan (Sa’id Nuri) har dai alaƙarsu ta kasance mai ƙarfi da hasken nan na Rasa’il Nur”.
Ya fara ɗaukar ilimi kuma ya haddace Alƙur’ani yana yaro a hannun mahaifinsa, a ƙarƙashin kulawar mahaifinsa tun da farko, sannan kuma ya koma hannun wasu shaihunnai. A yayin da ya kasance ɗan shekara goma sha biyu sun halarci kotu, a sanda ake shari’ar Imam Nursi a garin Afyon. A shekara 1949\AD, inda yake tsare a kurkuku. Ya samu nasarar sumbantar hannun Imam Nursi da samun addu’arsa da ya yi masa, a yayin da yake tafiya i zuwa ɗakin shari’a a ƙarƙashin matsanancin tsaro.
Haƙiƙa shi ya taso a gidan da ya ɗamfaru da da’awar Rasa’il Nur, ya kasance tun yana yaro mai ƙwazo ne a wajen kwafar Rasa’il Nur, ya yi haƙuri a bisa rashin uba da yake a cikin kurkuku a ɗaure saboda Rasa’il Nur. Mahaifiyarsa ma’abociyar falala ta kasance abar ba da misali a cikin mataye a wajen riƙe alƙawari, uwa ce mai haƙuri, wadda take tsayawa tare da mijinta a kan duk halin da ya shiga, kuma take ƙoƙarin tarbiyyantar da ɗanta a bisa tafarkin Rasa’il Nur, kuma take tabbatar da shi a kan haka.
Babansa Gwani Mustapha ya rasu a shekara ta 1950\AD tare da haka ya ci gaba da riƙo da aikin da’awa na Rasa’il Nur tare da dukkan ƙarfinsa. Ya kasance yana ziyartar Imam Nursi sau da yawa, a lokacin da Imam ya kasance yana Isparta. Yana sumbantar hannayensa yana sauraron nasihohinsa da wasiyyoyinsa da hore-horensa da kyawawan ayyuka.
Haƙiƙa ya ziyarci Imam Nursi tun kafin ya tafi ya haɗu da masu aikin ɗamara, saboda sauke nauyinsa na aikin bautar ƙasa, a shekara ta 1958\AD. Ta kasance ita ce ƙarshen ziyararsa gare shi. Sai Imam Nursi ya ce da shi a cikin wannan ziyarar, yana mai bayyana masa ƙauna da ba shi muhimmanci,
“ya kai Gwani Sa’id, bayan ka dawo daga hidimar aikin bautar ƙasa, zan kusanto da kai i zuwa gare ni a cikin wannan da’awar.” Bayan dawowarsa daga hidimar bautar ƙasa, saboda rasuwar Imam Nursi a shekara ta 1960\AD sai ya wuce Santanbul, ya samu karatuttuka a cikin harshen Larabci da kuma karatun Alƙur’ani mai girma.
Haƙiƙa Imam Nursi ya nuna Shaik Ahmad Khusrau ya zama matsayin Khalifansa a bayansa a bisa shugabancin da’awar Rasa’il Nur.
Bayan haka lokaci mai tsawo bai shuɗe ba, sai Shaik Ahmad Khusrau ya kirawo shi i zuwa gidansa don ya ba shi jagorancin da’awa a Rasa’il Nur a Isparta. Haƙiƙa fuskar Shaik Ahmad Khusrau ta yi kama da fuskar Imam Nursi, hakanan ma muryarsa. Tun tsawon zamani duk lokacin da yake yi wa Shaik Sa’id Nuri magana, wannan kamannin yana yin tasiri a zuciyarsa matuƙar tasiri. Kuma yana ƙara masa ƙwarin guiwa sosai a aikin da’awa. Ya ba da muhadarori da darussa a cikin Alƙur’ani mai girma da Rasa’il Nur, zamani mai tsawo a garin Isparta da kuma cibiyoyi waɗanda aka bubbuɗe su a nahiyar Kule-onu. Ya tarbiyyantar da ɗalibai da yawa, a tsakankanin shekaru goma sha biyar da ya yi tare da Shaik Ahmad Khusrau yana aikin da’awa a ƙarƙashin umarninsa. Ya kasance ɗalibi mafi tsarkake niyya a wajensa, mafi yi masa biyayya. Mafificin abokin shawararsa, kai ka ce ɗansa ne mafi soyuwa a gare shi.
Tabbas Shaik Ahmad Khusrau da Shaik Sa’id Nuri sun sha azaba na watanni shida a zaman kurkuku da suka yi a shekara ta 1964 a Isparta, sannan shekara uku daga shekara ta 1971 har shekarar 1974 a garin Askishahri, tare da wasu da suke wannan tafiya tare, kamar irin su Sayyid Mustapha Nuri.
Bayan fitar Shaik Ahmad Khusrau a shekara ta 1974 daga kurkuku, sai ya sa harsashin ginin Waƙful Khairat tare da abokan tafiyarsa a cikin da’awa, saboda bugawa da yaɗa (Mus’hafil Tawafuƙat) wanda Imam Nursi ya fito da shi, kuma Shaik Ahmad Khusrau ya rubuta shi. Wanda Imam Nursi ya wasafta shi da faɗinsa: “ba wanda ya taɓa rubuta irin wannan mus’hafin tun fiyayyun ƙarnuka har i zuwa yau”. Sannan aka kafa maɗaba’a ta musamman, saboda buga wannan mus’hafin.
Haƙiƙa Shaik Sa’id Nuri tare da abokan tafiyarsa da kuma Shaik Ahmad Khusrau sun yi jihadi mai girma a cikin yanayi na wannan lokaci mai wahala, bayan shekaru uku na aiki da da’awa a tare, a wannan cibiya ta Waƙful Khairat a Santanbul, sai Shaik Ahmad Khusrau ya yi ƙaura i zuwa rahmar Allah, a shekara ta 1977.
Haƙiƙa Shaik Ahmad Khusrau yana ganin Shaik Sa’id Nuri mafifici a ɗalibansa wajen tsarkin niyya da gaskiya da kiyayewa, a saboda haka sai ya jiɓinta masa al’amarin waƙafi, daga nan kuma sai aka jiɓinta masa jagoranci da’awa, bayan Khusrau da wasiyya rubutacciya da ya rubuta kafin rasuwarsa.
To gini a kan haka an jiɓintawa Sa’id Nuri kula da Da’awar Rasa’il Nur da kuma Waƙful Khairat da ɗaliban Rasa’il Nur tun shekarar 1977 har i zuwa yanzu.
Haƙiƙa Shaik Sa’id Nuri ya ba da muhimmanci matuƙa game da kiyaye abubuwan da’awar Rasa’il Nur ta keɓanta da su na daga ɗauko komai daga asalinsa na daga tsarkakewa a farkon bayyanarta.
Yana aikin da’awa da waɗanda suke tare da shi daga ɗaliban Rasa’il Nur, da cikakken taimakon juna. Ba tare da kasala ba, da aiki tuƙuru tare da ƙoƙari har i zuwa yau. An bubbuɗe cibiyoyin Rasa’il Nur, waɗanda suka riƙi haruffan Alƙur’ani a matsayin tushe a gare su a dukkan nahiyoyin Turkiyya don samar da tsareku sababbi, waɗanda suke a shirye da ɗaukar nauyin hidimar Musulunci da ta Alƙur’ani.
An yi masa baiwa da haƙuri da ƙwazo da juriya da ƙasƙantar da kai matsananci. Ba ya son shuhura, ya fi so ya yi aiki a sirrance. Ya ci gaba da da’awar Rasa’il Nur tare da jan girmansa duk da cewar akwai bala’o’i da tsanance-tsanance. Ya kiyaye tuwasun Rasa’il Nur ba tare da ya karkata ga barin su ba. A saboda haka ne ɗaliban Rasa’il Nur suke alfahari da babban malaminsu kuma jagoransu.
Haƙiƙa a lokacinsa ne aka buɗe babbar maɗaba’ar buga littattafai ta zamani a Santanbul da Isparta, saboda kwafin mus’hafin Alƙur’an na Tawafuƙat da kwafin nan na asali na Rasail Nur da haruffan Musulunci.
Sai ta fara da aikin yaɗa kwafi-kwafin nan na Mus’hafi – Tawafuƙat da Rasa’il Nur a cikin dukkan duniya. Sannan kuma cibiyoyin Rasa’il Nur sun yalwata har i zuwa wasu ƙasashe. Domin an cigaba da buɗewa a Sudan da Misra da Niger da Nigeria da Saudi Arabia da Malesiya da Indunisiya da makamantansu daga ƙasashen musulmi na duniya. Akwai ƙasar Amurka da Ingila da Jamus da Faransa da Holanda da wasunsu daga ƙasashen Turai. Saboda mutane su fa’idantu daga wannan da’awa, mai haske ta hanyar tarjama Rasa’il Nur, i zuwa harsunan mutanen waɗannan ƙasashe.
Musamman tarjama Rasa’il Nur i zuwa harshen Larabci a ɗan lokaci ƙanƙani ta samu karɓuwa a wajen mutane don abin da ta keɓanta da shi na daga sauƙi da dacewarta da nafsi na asali, idan aka kwatanta da watarta na daga tarjama. Haƙiƙa Shaik Sa’id Nuri ya riƙi birnin Isparta da Santanbul cibiyoyi a gare shi. Daga su ne yake cigaba da da’awarsa tare da dubunnan abokanan tafiyarsa a wannan tafarkin, da abin da yake kwaranyo musu, daga hidimar Alƙur’ani da imani na daga ƙoƙari da nishaɗi, a dukkanin garuruwan da suke Turkiyya da wajen Turkiyya.


