Gabatarwa:

113. Page


بسم الله الرحمن الرحيم

فَسُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ حِينَ تُمۡسُونَوَحِينَ تُصۡبِحُونَ * وَلَهُ ٱلۡحَمۡدُ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِوَعَشِيّٗا وَحِينَ تُظۡهِرُونَ * يُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَيُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّ وَيُحۡيِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۚ وَكَذَٰلِكَ تُخۡرَجُونَ* وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنۡ خَلَقَكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ إِذَآ أَنتُم بَشَرٞ تَنتَشِرُونَ * وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنۡ خَلَقَ لَكُم مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ أَزۡوَٰجٗا لِّتَسۡكُنُوٓاْ إِلَيۡهَا وَجَعَلَ بَيۡنَكُم مَّوَدَّةٗ وَرَحۡمَةًۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ*وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ خَلۡقُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَٰفُ أَلۡسِنَتِكُمۡ وَأَلۡوَٰنِكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّلۡعَٰلِمِينَ * وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ مَنَامُكُم بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَٱبۡتِغَآؤُكُم مِّن فَضۡلِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَلَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَسۡمَعُونَ * وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ يُرِيكُمُ ٱلۡبَرۡقَخَوۡفٗا وَطَمَعٗا وَيُنَزِّلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗفَيُحۡيِۦ بِهِ ٱلۡأَرۡضَبَعۡدَ مَوۡتِهَآۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ *وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَن تَقُومَ ٱلسَّمَآءُ وَٱلۡأَرۡضُ بِأَمۡرِهِۦۚ ثُمَّ إِذَا دَعَاكُمۡ دَعۡوَةٗ مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ إِذَآ أَنتُمۡ تَخۡرُجُونَ * وَلَهُۥ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِوَٱلۡأَرۡضِۖ كُلّٞ لَّهُۥ قَٰنِتُونَ * وَهُوَ ٱلَّذِي يَبۡدَؤُاْ ٱلۡخَلۡقَ ثُمَّيُعِيدُهُۥ وَهُوَ أَهۡوَنُ عَلَيۡهِۚ وَلَهُ ٱلۡمَثَلُ ٱلۡأَعۡلَىٰ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِوَٱلۡأَرۡضِۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

[1]


A cikin wannan haske na tara za a bayyana wata hikaya mai ƙayatarwa babba da hujja babba ta waɗannan ayoyi manya-manya saukakku daga sama, waɗanda suke nuni zuwa wani ginshiƙi daga ginshiƙan imani, da kuma na waɗannan hujjoji manya-manya masu tsarki waɗanda suke tabbatarda tashin Alƙiyama.

 


Wata kulawa ta ubangiji mai ban ƙaye ɓoyayyiya:

Haƙiƙa shekaru talatin da suka wuce Sa’id Na Da ya faɗa cikin Manufa ta biyu daga manufofin Alƙur’ani a ƙarshen littafin “Al-Muhakamat(Kai ƙara da yanke hukunci)

[2]

”, wanda ya rubuta shi a matsayin muƙaddima ga tafsirin: “za a fassara kuma a yi bayanin ayoyi biyu da suke nuni zuwa tashin Alƙiyama”, kuma ya ce: “Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai”, ya tsaya, kuma bai iya ci gaba da rubutun ba,to godiya da yabo su tabbata ga mahaliccina mai jin ƙai adadin dalilai da alamomin tashin Alƙiyama,sai dai ya kyautata mini ya datar da ni bayan shekaru talatin.

 

Na’am, haƙiƙa Shi mai jalala da ɗaukaka ya yi ni’ima gare ni shekaru tara ko goma da suka wuce, da wallafa “Kalma ta goma”, da “Kalmata Ashirin da Tara”waɗanda suka ƙunshi hujjoji masu matuƙar ƙayatarwa da ba da mamaki masu

[1]{Saboda haka tsarkakewa ta tabbabta ga Allah a lokacin da kuke shiga maraice da lokacin da kuke shiga safiya.Kuma godiya tasa ce a cikin sammai da ƙasa da lokacin yammaci da lokacin zawali.Yana fitar da mai rai daga matacce, kuma yana fitar da matacce daga mai rai, kuma yana rayar da ƙasa bayan mutuwarta,kuma kamar haka ake fitar da ku (daga ƙaburburanku).Kuma akwai daga ayoyinSa Ya halicce ku daga turɓaya, sai ga ku kun zama mutum, kuna watsuwa.Kuma akwai daga ayoyinSa Ya halitta muku matan aure daga kanku domin ku nutsu zuwa gare su, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani. kuma akwai daga ayoyinSa.halittar sammai da ƙasa, da saɓawar harsunanku da launukanku.Lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga masu sani.Kuma akwai daga ayoyinSa Barcinku a cikin dare da rana, da nemanku ga falalarSa Lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu saurarawa.Kuma akwai daga ayoyinSa Ya nuna muku walƙiyaa don tsoratarwa da kwaɗaitarwa, kuma Ya dinga saukar da ruwa daga sama, sa’an nan Ya rayar da ƙasa da shi bayan mutuwarta Lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu hankaltuwa.Kuma akwai daga ayoyinSa,tsayuwar sama da ƙasa bisa umarninsa sa’an nan idan Ya kira ku, kira ɗaya, daga ƙasa, sai ga ku kuna fita.Kuma wanda ke cikin sammai da ƙasa Nasa ne, Shi kaɗai.Dukansu masu ƙasƙantar da kai ne gare Shi.Kuma Shi ne wanda Ya fara halitta, sa’an nan ya sake ta, kuma sakewarta ya fi sauƙi a gare Shi,Kuma Yana da misali wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasa, kuma Shi ne Mabuwayi,Mai jin ƙai.}[Ar Rum:17-27].

 

[2]Ɗaya daga cikin littattafan Rasa’il An-Nur.




114. Page

bayyana ƙarara ƙarfafa ƙwarai ga ɗaya daga cikin waɗannan ayoyi biyu dokar ubangiji da tafsirorinta wadda ita ce

فَٱنظُرۡ إِلَىٰٓ ءَاثَٰرِ رَحۡمَتِ ٱللَّهِ كَيۡفَ يُحۡيِ ٱلۡأَرۡض بَعۡدَمَوۡتِهَآۚ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِير


Kuma ya yi mini ni’ima bayan shekaru tara ko goma daga waɗannan sansanoni biyu masu ƙarfiƙwarai na aƙidar tashin Alƙiyama, da wallafa wannan risala a matsayin tafsiri na ayoyi manya-manya da aka ambata a baya, wadda ita ce aya ta biyu.

 Wannan haske na tara yana matsayin maƙamomi ne guda tara maɗaukaka da gabatarwa muhimmiya da a ke yin nuni zuwa gare su a cikin ayoyin da aka ambata.

 

Gabatarwa: Nuƙuɗoɗi biyu da suke a matsayin bayani na fa’idoji na ruhi masu yawa ƙwarai ga aƙidar tashin AlƘiyama, kuma sakamako ne matattari na sakamakonta na rayuwa a taƙaice, da bayyana irin zurfin kasancewarta lalura,da kuma lazimtarta ga rayuwar bil Adama musamman ma rayuwarsa ta zamantakewa, da kuma fayyacewa game da hujja matattariya tsakanin hujjojin aƙidar imani da tashin AlƘiyama masu yawa ƙwarai a dunƙule, da fa’idantar da yadda cewa wannan aƙidar abu ne da kowa ya sani babu shakka.

 

Nuƙuɗa ta Farko: Za mu yi nuni zuwa dalilai huɗu-A matsayin magwadai-a tsakanin ɗaruruwan dalilai da suke nuni cewa haƙiƙa aƙidar Lahira ita ce tushen rayuwa ta zamantakewa da rayuwa ta mutum a kan kansa, kuma cewa ita ce tuwasun rabautarsa da kamalolinsa.

 

Dalili na Farko: Yara waɗanda su ne kusan rabin ‘yan’dam ba za su iya jurewa ba a gaban mace-mace ko mutuwa ba wadda ta ke ɓuɓɓulo musu a matsayin abu mai razanarwa da sa kuka sai da tunanin Aljanna, kuma da wannan tunani za su iya samun ƙarfi na ma’ana a cikin zatinsu mai rauni tattausa ƙwarai,kuma za su iya samun buri da fata da tunanin Aljanna a cikin yanayin ruhinsu rarrauna ƙwarai, kuma mai saurin kuka daga kowane abu mai tasiri, wannan sai ya ba su damar rayuwa cikin farin ciki da sakin rai.

 

Ga misali:Da tunanin Aljanna zai ce: ɗan’uwana ƙarami ko abokina ya rasu, sai ya zama tsuntsu daga tsuntsayen Aljanna, yana kewayawa a cikinta yana rayuwa yana morewa da jin daɗi fiye da mu, in ba haka ba sai mutuwar sakonsa daga yara da ma manya da ke tare da su ta zama abu ne da zai ɗimauta idanun waɗannan miskinan raunana waɗanda ba sa tsayawa guri ɗaya, kuma ta ruguza juriyarsu da ƙarfinsu na ma’ana, kuma bayan idanunsu ma za ta sanya ɓoyayyaun abubuwansu kuka, kamar ruhinsu da zuciyarsu da hankulansu, sai ya zama ko dai su tozarta, ko kuma su zama kamar dabbobi masu shiga uku da wahala da gararamba.