HAКIКA TA BAKWAI

74. Page

Tushe na Takwas:Kuma za ka fahimci cewa mai samarwa na har abada ga wannan duniya mai ƙarewa yana da wata duniyar daban wanzajjiya, kuma shi yana kora bayinsa zuwa can kuma ya ɗokantar da su zuwa gare ta.

 

Tushe na Tara:Kuma za ka fahimci cewa wancan Mai jin ƙan zai girmama waɗannan bayin nasa makeɓanta a waccan duniyar, kuma zai yi ni'ima a gare su da karramawa da ni'imtawar da idanu ba su taɓa ganin irinsu ba, kuma kunnuwa ba su taɓa jin irinsu ba, kuma ba su taɓa ɗarsuwa a zuciyar wani bil Adama daga cikinmu ba.

 

 

HAКIКA TA BAKWAI

 

Babin kiyayewa da Siffar kiyayewa

 

Wanda shi ne tajallinSunan Mai kiyayewada Mai sa ido

 

Shin Abu ne mai yiwuwa ga wani mai kiyayewa da yake kiyaye kowane abu cikin cikakken tsari da ma'auni, daga ɗanyan abu ko busasshe, ko ƙarami ko babba,sababbe maɗaukaki a sama da ƙasa, da tudu da kogi, kuma ya keƙididdige sakamakonsa, cikin yanayi mai kama da hisabi,a ce ba zai kiyaye ayyukan mutum ba-wanda yake da ɗabi'ar halitta mai girma maɗaukakiya, wanda kuma yake a matakin halifanci babba, wanda yake yana da aiki mai matsayi kamar ɗaukar amana babba-da ayyukansa waɗanda suka shafi ubangijintaka magamiya?! Kuma a ce ba zai tankaɗe su ba da rariyar hisabi?! Kuma a ce ba za a auna ayyukansa ba da ma'aunin adalci?! Kuma a ce shi wannan mutumin ba zai sami kyakkyawan sakamako ba kuma ba zai gamu da uƙuba mai dacewa da ayyukansa ba?! Faufau har abada.


75. Page

Na'am, haƙiƙa wanda yake gudanar da wannan duniya yana kiyaye kowane abu cikin tsari da ma'auni, su kuwa tsari da ma'auni su tajallin ƙudura da sani da hikima da nufi ne; domin mu muna ganin cewa duk wani jikin wani abin samarwa ana halittar sa ne da tsari da ma'auni sakakku babu ƙaidi, kuma kamar yadda kowace sura da tsawon rayuwarsa ke canza ta tsararriya ce ƙayatacciya,don haka kamanninsa su ma suna cikin tsaruwa ƙayatacciya; domin mu muna gani kuma muna kallon cewa mai kiyayewa ma'abocin jalala yana kare da yawa daga surorin kowane abu da rayuwarsa ta ƙare da ƙarewar aikinsa, kuma ya ƙaura ya bar wannan duniya duniyar bayyane,yana kiyaye su a cikin ƙwaƙwale waɗanda suke kamar alluna ne ababan kiyayewa[1], kuma cikin abin da ya yi kama da madubai na misali, kuma yana rubuta mafi yawan tarihin rayuwarsa a cikin ƙwallonsa, kuma yana sanya shi wanzajje a cikin madubai na fili da na ɓoye.


[1]Duba hashiyar misali na bakwai.(mawallafi).




76. Page

Ga misali; ƙwaƙwalwar mutum, da 'ya'yan itaciya na bishiya, da ƙwallon ɗan itace, da irin fure, duk suna nuni bisa girman kewayewa da dokar kiyayewa, yanzu ba ka ganin cewa dukkan samammu masu yin furanni masu fitar da 'ya'ya a cikin lokacin kaka mai girma ɗingimeme, da takardun ayyukansu da suka keɓanta da su,da dokokin samuwarsu da kamantuwarsu da surorinsu, ana rubuta su ne a kiyaye su a cikin wasu 'ya'yan iri masu taƙaitaccen adadi, kuma ayaɗa takardun ayyukansu a cikin wani lissafi da ya keɓanta da su a cikin kaka ta biyu, kuma-mai kiyayewa ma'abocin jalala-yana fitar da kamannin wata duniya ta wata kakar da ban mai girma ɗingimemiya cikin cikakken tsari da hikima, ta haka ne irin zurfin faruwar siffar kiyayewa cikin kewayewa ƙaƙƙarfa ke bayyana,to ya jama'a idan kiyayewa tana faruwa a cikin abubuwa na ɗan taƙaitaccen lokaci sababbu masu ƙarewa wofintattu irin wannan, to yanzu shin yana daga cikin abubuwa masu yiwuwa a ce ba za a rubuta kuma a adana ayyukan ‘yan’dam ba-waɗanda suke samar da amfani mai muhimmanci a duniyar fake da duniyar lahira, da duniyar rayuka, da kuma cikin ubangijintaka magamiya-rubutawa cikin himmatuwa ƙarƙashin kiyayewa?faufau faufau (Hakan ba zai yiwu ba) .


77. Page

Na'am, ana fahimta daga tajallin wannan siffa ta kiyayewa da wannan kamanni nata;cewa mamallakin waɗannan samammun abubuwa yana da damuwa ƙwarai da tantance da kuma kiyaye duk abin da yake gudana kuma yake faruwa a masarautarSa, kuma yana da tsananin takatsantsan cikin siffarsa ta mai mulki, kuma yana da matuƙar damuwa cikin masarautar ubangijintakarsa inda har ta kai yana rubutawa kuma yana adana mafi ƙanƙantar abu mai faruwa da mafi ƙanƙantar aiki, kuma ya sanya ma'aikatanta -masarautar- su adana su,kuma yana kiyaye surorin kowane abu da yake faruwa a mulkinSa cikin abubuwa mabambanta, to wannan siffa ta kiyayewa tana nuni zuwa cewa da sannu za a buɗe takardar ayyukan hisabi muhimmiya mai matuƙar haɗari, musamman ma ayyuka manya-manya, da ayyuka muhimmai na ɗan’adam – wanda shi ne mafi girma kuma mafi karamci kuma mafi darajar abin halitta ta ɓangaren haƙiƙa-waɗanda waɗannan ayyukan za su shiga ƙarƙashin hisabi da ma'auni muhimmai masu haɗari, kuma da sannu za a yaɗa takardun ayyukansa:to ya jama'a shin yana daga abu mai yiwuwa a ce an girmama ɗan’adam da halifanci da amana, kuma ya hau matsayin mai kiyayewa kuma mai kallo ta hanyar shigarsa cikin ibadun mafi yawancin samammun abubuwa da tasbihohinsu ta hanyar shelantawarsa da ɗayantakar Allahntaka cikin gungun 'yan yawaitaka ta hanyar kallonsa ga sha'anoni matattara 

78. Page

na ubangijintaka, sannan a ce ya shiga ƙabari ya kwanta cikin hutawa kuma ba za a farkar da shi ba,kuma ba za a tambaye shi game da ayyukansa ba ƙananansu da manyansu, kuma a ce ba zai tafi filin taron Alƙiyama ba kuma ba zai samu babbar kotu ba?!faufau har abada.

 

Kuma ta yaya zai yiwu wannan mutum ya tafi zuwa rashi ya gudu daga mai ƙaddarawa ma'abocin jalala wanda ayyukansa-waɗanda su ne mu'ujizozin ikonsa-suke shaidawa cikin dukkan zamunnan da suka wuce cewa shi mai iko ne a bisa halittar dukkan abubuwa masu yiwuwa da za su faru a nan gaba gaba ɗayansa[1],kuma wanda yake samar da lokacin sanyi da lokacin kaka da ake ganinsu, kuma waɗanda suke yin kama da tashin Alƙiyama da tashinta sosai, ta yaya zai yiwu gare shi -mutum- ya guje masa ya shiga turɓaya ya ɓuya?

 

Kuma tun da shi ba a yi wa mutum hisabi a cikin wannan duniyar irin hisabin da ya dace da shi, kenan babu makawa cewa shi mai tafiya ne zuwa wata kotu babba da rabauta babba.

 

 

HAКIКA TA TAKWAS

 


[1]Na'am, haƙiƙa shuɗaɗɗan zamani-wanda yake farawa daga yanzu zuwa fara halittar duniya-dukkaninsa da abubuwa masu faruwa da abubuwa masu aukuwa, kuma kowace rana da kowace shekara da kowane ƙarni daga cikinsa da ya bayyana a samuwa kamar wata saɗara ce da takarda da littafi da aka rubuta shi da alƙalamin ƙaddara, kuma hannun ƙudura ya rubuta mu'ujizozin ayoyinsa da cikakkiyar hikima da tsaruwa,shi kuwa zamani mai zuwa da yake farawa daga zamanin yanzu kuma yake ci gaba har zuwa ranar Alƙiyama, zuwa Aljanna da kuma har abada to dukkaninsa abubuwa ne masu yiwuwa, ma'ana lokacin da ya wuce abubuwa ne masu faruwa da suka faru, shi ko lokaci mai zuwa abubuwa ne masu yiwuwa, to idan aka sanya sarƙoƙin waɗannan zamunna ɗaya na fuskantar ɗayan, kuma babu shakka har abada cewa wanda ya halicci jiya kuma ya samar da samammun abubuwansa waɗanda suka keɓanta da shi mai iko ne bisa halittar gobe da ababan halittarsa, kuma babu shakka cewa samammun abubuwa da abubuwa masu shallake hankali na wannan zamani da ya wuce wanda shi ne fage na abubuwan mamaki su ne mu'ujizozi na mai iko ma'abocin jalala, kuma suna shaidawa shaidawa ɗoɗar cewa wancan mai ikon mai iko ne a bisa samar da lokacin nan gaba dukkaninsa, da kuma samar da dukkan abubuwa masu yiwuwa dukkaninsu, da bayyana dukkan abubuwan mamakinsa, Na'am, kamar yadda wanda zai halicci tuffa ɗaya, lallai ne ya zama mai iko bisa halittar dukkan tuffa din duniya, kuma mai iko ne bisa samar da lokacin kaka dukkaninsa, kuma wanda ba ya samar da lokacin kaka, ba zai iya samar da tuffa ɗaya ba, domin cewa waccan tuffar ana saƙa ta ne a cikin waccar masaƙar, don haka wanda zai iya samar da tuffa zai iya samar da lokacin kaka, domin tuffa ɗaya ƙaramin samfuri ne na bishiya, ko ma a ce na lambu, ko kuma ma na duniya baki ɗaya, ita kuwa halitta ce mai shallake hankali ta fuskar kasancewar ƙwallonta yana ɗauke da dukkan tarihin rayuwar bishiyar gundumemiya, domin wanda ya halicce ta bisa wannan surar ba zai gaza ba wajen halittar kowane abu,hakanan kuma wanda yake halittar wannan yini zai iya halittar ranar Alƙiyama, kuma wanda zai samar da lokacin kaka ya kamata ya kasance mai iko bisa halittar tashin Alƙiyama, kuma wanda ya rataya dukkan duniyoyi na lokacin da ya wuce bisa turba ta zamani cikin hikima da tsaruwa kuma yake bayyana su, babu shakka shi zai iya rataya wasu duniyoyi da ban a kan turabar zamani mai zuwa kuma ya bayyana ta, kai tabbas ma zai bayyana ta.

 Kuma haƙiƙa mun tabbatar a cikin da yawa daga cikin "kalmomi"Musamman ma kalma ta ashirn da biyu"tabbatarwa kai tsaye; cewa wanda ba shi da iko bisa halittar kowane abu, ba shi da iko bisa halittar wani abu komai ƙanƙantarsa, kuma wanda yake da iko bisa halittar wani abu ɗaya yana da iko bisa halittar dukkanin abubuwa, sannan kuma idan aka jingina samar da abubuwa zuwa abu ɗaya to halittar dukkanin abubuwa za ta zama mai sauƙi kamar sauƙin halittar abu ɗaya, kuma za ta zama sassauƙa, amma idan aka jingina ta zuwa abubuwa masu yawa kuma zuwa yawa to samar da abu ɗaya zai zama mai wahala mai matsala kamar wahalar samar da dukkan abubuwa, kuma zai zama mai wahalar da ta kai matakin abin da ba zai yiwu ba (mawallafi).