HAКIКA TA BIYAR

56. Page

sunaye da siffofin mai samarwa ma'abocin jalala mai tsarki suke nuni zuwa ga lahira, kuma suke ishara zuwa gare ta kuma suke buƙatarta.

 

HAКIКA TA BIYAR

 

Babin Tausayi da Bautatuwar Muhammadu (S.A.W)

 

Wanda shi ne tajallin Sunan Mai amsawa da sunan Mai rahama

 

Shin abu ne mai yiwuwa ga ubangiji mai yawan tausayi da jin-ƙai wanda ba bu ƙarshe ga tausayinSa da jin-ƙansa wanda yake ganin buƙatar mafi ƙanƙantar abin halittarSa, sai ya agaje shi da cikakken tausayi kuma ta inda bai yi tsammani ba, kuma yake jin mafi ƙasa-ƙasan sauti na mafi ɓuyan abin halitta ya kumataimake shi, kuma yake amsawa kowane mai tambaya da harshen hali da na magana, zai yiwu a ce zai ga mafi girman buƙata ta mafi girman bawa[1] kuma mafi soyuwar abin halitta zuwa gare shi a ce ba zai biya masa itaba kuma ba zai agaje shi ba?kuma a ce ya ji mafi girman addu'a kuma mafi ɗaukakarta amma ba zai amsa masa itaba?!

 

Na'am; haƙiƙa tausasawa da sauƙi da suke bayyana cikin abin da ya keɓanci arziƙin dabbobi raunana da ƙananunsu-bisa misali-da rainonsu duk suna nuni ne a kan cewa mamallakin wannan halitta yana tasarrufi ne a cikinta da ubangijintaka da ta kai matuƙa wajen jin ƙai, to shin mai yiwuwa ne ga tausayin mai jin ƙai a cikin ubangijintakarSa irin wannan a ce ba zai amsawa mafificiyar addu'a daga mafificin abin halitta ba?!


[1] Na'am, haƙiƙa wanda ya yi mulki na tsawon shekara ɗari uku da hamsin kuma mulkinsa da hukuncinsa ba su gushe ba suna masu ci gaba, kuma wanda al'umarsa ta kai yawan miliyan ɗari uku da hamsin a mafi yawan zamunna, kuma wanda talakawansa ke sabunta caffa gare shi a kowace rana, kuma suke ba da shaida a game da kamalarsa, kuma suke miƙa wuya ga umarce-umarcensa da cikakkiyar biyayya, kuma wanda rabin duniya da ɗaya daga cikin biyar na bil Adama suka rinu da irin rininsa;ma'ana suka rinu da irin rininsa na ma'ana, kuma shi abin soyuwa ne zuwa ga zukatansu, kuma shi ne mai tarbiyyantar rayukansu, ba shakka cewa shi ne mafi girman bawa na ubangijin da yake tasarrufi a cikin wannan duniya, kuma haƙiƙa mafiya yawan nau'o'i na ababan halitta sun sanya albarka ga aikinsa, da rawar da yake takawa a rayuwa da kuma shugabancinsa ta hanyar ɗaukar ɗan ita ce daga 'ya'yan ita ce na mu'ujizarsa, to ba makawa cewa shi ne mafi soyuwar ababan halitta a wajen mahaliccin wannan duniya, kuma cewa dukkan bil Adama suna da buƙata da suke roƙonta suke kuma suke nemanta da dukkan kintsin halittarsu, domin ita tana ɗaga su daga ƙasan ƙasa zuwa mafi ɗaukakar Illiyyina, haƙiƙa ita ce wanzuwa da dawwama, don haka babu kokwanto cewa waccan buƙatar ita ce mafi girman buƙata kuma mafi matsayinta, kuma babu shakka cewa mafi girman bawa zai nemi biyan waccan buƙata daga wajen mai biyan buƙatun da yawun kowa da kowa.(mawallafi).




57. Page

Za mu bayyana wannan haƙiƙa a nan a karo na biyu kamar yadda muka bayyana ta a "Kalma ta sha tara":

 

Ya kai wannan aboki da yake ji na tare da zuciyata, haƙiƙa mun faɗa a cikin hikayar kwaikwayawa cewa akwai wani taro a wani tsibiri na daban, kuma cewa 

58. Page

akwai wani manzo mai karamci da yake yin jawabi, to haƙiƙar da yake nuni zuwa gare ta ita ce:

 

Taho, mu tsaraita daga zamanin da a ke ciki mu tafi da tunaninmu zuwa zamanin farinciki, mu tafi da saƙe-saƙen ƙwaƙwalwarmu zuwa tsibirin Larabawa, har mu ziyarci Manzo mafi girma S.A.W, kuma mu kalle shi yayin da yake aiwatar da aikinsa cikin bautatuwa cikakkiya.

 

Duba, kamar yadda cewa wannan manzo mafi karamci (S.A.W) shi ne sababin samuwar rabauta da firin ciki na har abada, kuma tsanina saduwa zuwa gare su ta hanyar manzancinsa da shiriyarsa, to haka nan shi ne silar samuwar waccan rabautar, kuma tsanin samar da aljanna ta hanyar bautatuwarsa da kuma addu'arsa.

To Duba; ka ga haƙiƙa wancan manzo mafi karamci S.A.Wyana addu'a a cikin sallah babba, kuma da ibada maɗaukakiya, saboda rabauta ta har abada,kai ka ce wannan tsibiri ko ma a ce duniya baki ɗaya tana yin sallah ne tare da sallarsa kuma tana ahi; domin bautatuwarsa, kamar yadda ta ƙunshi bautatuwar al'umarsa da take bin sa, hakanan ta ƙunshi sirrin bautatuwar dukkanin annabawa ta hanyar sirrin dacewa.

 

Sannan shi yana sallatar wannan sallar babba a cikin wata jama'a mai girma yana ahi, kamar ka ce cikakkun mutane ma'abota haske daga ‘yan’dam tun daga lokacin Annabi Adam zuwa wannan zamani namu kuma har zuwa ranar Alƙiyama suna koyi ne da shi ta hanyar binsa, kuma suna amsa addu'arsa[1].

 


[1] Na'am, haƙiƙa dukkan salloli da al'uma ta ke tsaida su, da dukkan salatai da a ke yi wa manzo mafi karamci (S.A.W) tun lokacin munajatinsa, su amsawa ce madawwamiya ga addu'arsa, kuma tarayya ce magamiya gare shi, har ta kai duk wani salati da za a yi masa amsawa ne ga waccan addu'ar,kuma dukkan salati da taslimi na kowane mutum ɗaya daga alummarsa gare shi a cikin kowace sallah da yake sallatarta da addu'ar Shafi'awa gare shi a bayan iƙama, duk wannan amincewa ce mai ƙarfi ƙwarai ga addu'arsa wadda ta keɓanci rabauta ta har abada, to ta haka ne manzo mafi karamci (S.A.W) yake roƙo yake tambaya a madadin bil adama na wanzuwa da rabauta ta har abada, wadda ‘yan’dam gaba ɗayansu suke fatansu kuma suke roƙon su, da dukkan ƙarfinsu ta harshan ɗabi'ar halitta ta bil adama, sai ma'abota haske a cikin ‘yan’dam su amsa a bayansa, to shin mai yiwuwa ne a ce wannan addu'a ba za ta gamu da karɓuwa da amsawa ba?! (mawallafi).




59. Page

Kuma kalli, haƙiƙa ga shi yana yin addu'a domin tabbatar da wata buƙata magamiya kamar wanzuwa;kai ka ce ba wai mutanan ƙasa ne kawai suke tarayya cikin ahinsa da hurwarsa ba, a'a har ma da ma'abota sammai su ma, kai, dukkan halittu, suna masu cewa:Na'am; ka amsa ya ubangijinmu, ka ba shi abin da yake nema, ka amsa addu'arsa, mu mahaka muna nema muna roƙo kamarsa.

 

Sannan kalli, ga shi yana roƙon rabauta ta har abada roƙon da yake cike da buƙatuwa da damuwa da ƙauna da shauƙantuwa da ahi, ta yadda yake sanya ɗaukacin halitta kuka, kuma take tarayya da shi a cikin addu'arsa.

 


60. Page

Kuma kalli,ga shi yana roƙon rabauta saboda wani maƙasudi da manufa, kuma yana roƙo irin roƙon da yake ɗaukaka bil Adama da dukkan ababan halitta daga faɗawa cikin cikakkiyar ƙarewa da wofinta da rashin amfani, kuma daga gararambar da take ita ce mafi ƙasƙancin ƙasƙanci, zuwa mafi ɗaukakar guri a Illiyyin, ma'ana zuwa ƙima da wanzuwa, kuma zuwa ayyuka maɗaukaka, kuma zuwa matsayin abubuwan rubutawa na ubangiji abin nufi da baƙata.

 

Kuma kalli, ga shi yana roƙo, yana ahi da irin kukan da ya siffanta da kintsuwa da neman agaji, da addu'a ta hurwa mai zaƙi wadda ta ke cike da neman jin ƙai da fata, kamar ka ce shi yana nufin jiyar da shi ga dukkan samammun abubuwa da sammai da Al'arshi kuma ya motsa bege da shi[1], kuma yana sanya su suna faɗa ga addu'arsa: "Amin ya Allah amin"[2].

 

Kuma kalli;ga shi yana roƙo yana neman rabauta da wanzuwa daga mai iko ,mai ji mai karamci, kuma masani mai gani mai jin ƙai, wanda yake ganin mafi ɓuyan buƙata da mafi ɓuyan ahi, ga mafi ƙanƙantar ma'abocin rayuwa tahanyar kallo, kuma yake jin sa kuma yake amsa masa yake jin ƙan-sa; kuma yake ba da abin da yake roƙonsa, ko da kuwa yana roƙon sa ne da harshen yanayi; zai  ba shi bayarwar da ta ke cike da hikima da basira da jin ƙai, kuma ya amsa masa; ta inda ba zai bar wata kafa ta wata shubuha ba a kan cewa wannan raino da wannan gudanarwar sun keɓanta ne da wanda yake shi mai ji ne kuma mai gani, kuma mai karamci mai jin ƙai.


[1] Bege: shauƙi da ɗokantuwa.

[2]Na'am, haƙiƙa dukkan tasrifin mai tasarrufi na wannan duniya sun siffantu da tsinkaye da fahimta da ilimi da hikima kamar yadda a ke gani, don haka ba zai yiwu ta kowace fuska ba a ce wannan mai tasarifin ba shi da masaniya game da motsin mafificin mutum ɗaya daga cikin ababan samarwarsa ba da kuma tsinkaye game da ita,kuma ba zai yiwu ta kowace fuska wannan mai tasarifin masanin a ce ba mai kulawa ba ne kuma ba mai damuwa ba ne da wannan mutum ɗayan mafifici, tare da cewa shi mai tsinkaye ne game da dukkanin motsinsa da addu'o'insa, kuma ba zai yiwu ta kowace fuska ba a ce wannan mai tasarrufin mai iko mai jin ƙai ba zai amsa waxancan addu'o'in tare da tsinkayensa gare su da damuwarsa da su ba.

Na'am,haƙiƙa duniya ta canza da hasken Manzo mafi girma (S.A.W), kuma gundarin haƙinanin ɗan’adam da ma dukkanin duniya ya fayyatu ya bayyana da wannan haske,kumaya bayyana cewa samammun abubuwa a wannan duniya rubuce-rubuce ne na ubangiji abin nufi da buƙata da suke bin ƙididdiga na sunayen ubangiji, kuma su ababan ɗorawa ayyuka ne ababan umarta ne, kuma su samammun abubuwa ne masu ƙima da ,ma'ana da aka zaɓe su domin dawwama, to ba don wannan hasken ya kasance ba, da samammun abubuwa sun ci gaba da zama a cikin duhu na dimuwa, ababan yi wa hukunci da ƙarewa sakakkiya,kuma ba tare da ƙima da ma'ana ba, da kuma sun zama wasa da kara zube abin jagwalgwalawa, kuma abin wasa wanda ke faruwa katsam.

 Daga wannan sirri ne za a ga cewa ɗaukacin samammu tun daga Al'arshi zuwa shinfiɗa, daga ƙasa zuwa tauraran surayya duk suna alfahari da haskensa, kuma suna bayyana alaƙa tare da shi, kamar yadda mutane suke amsawa addu'arsa (S.A.W), alhali haƙiƙar lamarin shi ne cewa ruhin bautatuwar Manzo mafi girma (S.A.W) ita ce addu'a, kai haƙiƙa ma motsin dukkanin samammu da kai kawonsu wani nau'i ne na addu'a, doming a misali, haƙiƙa motsin ƙwallon ɗan itaciya shi ma nau'i ne na addu'a ga mahaliccinsa, domin ya zamo bishiya.(mawallafi)..




61. Page

 Ya jama'a! yanzu mai alfaharin samammu yake nema kuma yake tambaya kuma yake roƙo S.A.Wwanda kuwa shi ne mafi darajar nau'in ɗan’adam, kuma tilo a duniya da zamani, yana mai tsayawa a bayan ƙasa, yana mai tattara dukkanin 

62. Page

‘yan’dam a bayansa, yana mai ɗaga hannayensa, yana mai fuskantar Al'arshi mafi girma,kuma yana mai addu'a cikin haƙiƙar bautatuwar Ahmadiyya wadda ta tattara bautatuwar bil Adama gaba ɗayansu?, to mu saurare shi mu ji shi, dubi, ga shi yana roƙon rabauta ta har abada ga kansa da al'umarsa, kuma yana neman wanzuwa,yana neman aljanna, yana neman haka da dukkan sunayen ubangiji masu tsarki waɗanda suke bayyana kyawunsu a cikin madubban samammu, kuma yana neman ceto ta hanyar waɗancan sunaye,kai kana ganin haka.

 

Haƙiƙa ko da ba a sami wasu sababai marasa iyaka masu wajabta samuwar lahira ba; da dalilan samuwarta, da addu'a ɗaya ta wancan muhimmin mutum ta zama dalili wajen gina waccan aljanna wadda samar da ita mai sauƙi ne ga ikon mahaliccinmu kamar sauƙin samar da lokacin kakarmu[1].

 

Na'am; ta yaya samar da aljanna zai wuyata ga mai cikakken iko wanda yake sanya doron ƙasa a lokacin kaka fage na tashi,kuma a cikinsa akwai ɗaruruwan dubban misalai na tashin Alƙiyama?!

 

Kenan,kamar yadda manzancinsa (S.A.W)ya zama dalilin buɗe wannan gidan jarrabawa, kuma ya sami sirrin "ba don kai ba da ban halicci falakai ba"[2], to haka nan bautatuwarsa, ta zame dalilin buɗe gidan rabautar lahira.

 


[1] Na'am, haƙiƙa bayyana abin da ba ya ƙirguwa kuma ba ya iyakantuwa na misalan abubuwa masu shallake hankali ƙayatattu, da misalin tashin matattu da Alƙiyama a ban ƙasa wanda kamar 'yar takarda ce ƙarama in an kwatanta ta da lahira.kuma rubuta dangogi ababan samarwa tsararru ƙayatattu waxanda suke kamar littafi dubu ɗari uku ne a cikin wannan takarda guda ɗaya, da shigar da su a cikin ta cikin cika da kyautatawa da tsari, babu shakka cewa shi ya fi wahala daga gina aljanna mai ƙayataccen kyau tsararriya a duniyar lahira mai faɗi, na'am za a iya cewa; haƙiƙa halittar lambunan lokacin kaka shi ne mafi wahala daga waccan aljanna in an kwatanta da ɗaukakar aljanna a kan lokacin kakan , kuma mafi yawan motsa ɗimuwa da mamaki.(mawallafi).

[2] Ya zo a cikin Al-asrarul Marfu'a fi al-Akhbar al-maudhu'a na Mulla Aliyu Al-ƙari 295: Assaghani ya ce maudhu'i ne kuma haka yake a cikin al-Khulasa, sai dai ma'anarsa ingantacciya ce, domin Addailami ya rawaito daga Ɗan Abbas Allah ya yarda da su yana mai jingina shi ga Annabi (S.A.W): Jibrilu ya zo mini sai ya ce ya Muhammadu ba don kai ba da ban halicci aljanna ba, kuma ba don kai ba da ban halicci wuta ba,kuma a cikin ruwatar ibn Asakir ba don kai ba da ban halicci duniya ba".




63. Page

Shin mai yiwuwa ne ya jama'a, a ce kyakkyawa mai ƙayatarwa-wanda babu tawaya a cikinsa-kuma kyawu na ubangijintaka wanda ba shi da tamka-waɗanda suke bazama dukkan hankula, kuma suke bayyana su fito ƙarara cikin tsaruwar wannan duniya da rahama mai yalwa, zai yiwu a ce sun yarda da irin wannan rashin tausayi da kara zube da rashin tsari ta hanyar rashin amsa waccan addu'a?ma'ana ya saurari mafi ƙanƙantar buƙata da mafi ƙasa-ƙasan sauti cikin kulawa kuma ya biya su ya tabbatar da su, amma a ce bai damu ko kula da mafi muhimman buƙatu kuma mafi buƙatuwarsu, kuma a ce ba zai ji su ba kuma ba zai san su ba, kuma a ce ba zai biya su ba?!

 


64. Page

Faufau, tsarki ya tabbata a gare shi sau dubu! Domin irin wannan kyawu ba ya zama muni ta hanyar yarda da irin wannan muni[1].

Kenan manzo mafi girma S.A.Wkamar yadda ya buɗe duniya da manzancinsa,zai buɗe ƙofar lahira da bautatuwarsa.


عليه صلوات الرحمن ملء الدنيا ودار الجنان،اللهم صل على عبدك ورسولك ذلك الحبيب الذي هو سيد الكونين و فخر العالمين و حياة الدارين ووسيلة السعادتين و ذو الجناحين و رسول الثقلين ، وعلى آله وصحبه أجمعين وعلى إخوانه من النيين و المرسلين[2] ،آمين.

 


[1] Na'am, haƙiƙa juyewar haƙiƙoƙi abu ne ba mai yiwuwa ba bisa haɗuwar maganar malamai, kuma mafi tsananin abubuwa marasa yiwuwa cikin juyewar haƙiƙoƙi shi ne juyewar kishiya zuwa ɗaya kishiyar, kuma mafi tsananin abubuwa marsa yiwuwa sau dubu wajen juyewar kishiyoyi shi ne a ce kishiya ta zama kishiyarta kwabo da kwabo tare da wanzuwarta a ainihinta, kamar a ce kyau zallansa-bisa misali-ya koma muni zallansa tare da kasancewarsa kyawu na haƙiƙa; don haka kasancewar kyawun ubangijintaka da ake gani kuma tabbatacce a wannan misali na mu a ce ya zama shi ne ainihin muni, tare da kasancewarsa madawwami cikin gundarin kyawu na ubangijintaka shi ne mafi ban mamakin misali daga misalan abubuwa marasa yiwuwa da kuma ƙarya a duniya.(mawallafi).

[2]Tsiran sarki mai rahama ya tabbata a gare shi cikin duniya da gidan aljanna, ya Allah ka yi tsira a bisa bawanka da manzonka wannan masoyin da shi ne shugaban kasantattu biyu (duniya da lahira), kuma alfaharin talikai, kuma rayuwar gidaje biyu, kuma tafarkin rabauta biyu kuma ma'abocin fuka-fukai biyu kuma manzon nauyayyyu biyu (mutum da aljan), da alayensa da sahabbansa baki ɗaya, da kuma 'yan’uwansa annabawa da manzanni, amin




65. Page

HAКIКA TA SHIDA

 

Babin girma da sarmadiyya

 

Wanda shi ne tajallin suna na Mai girma da kuma suna na Wanzajje

 

Shin yanzu mai yiwuwa ne ga girman ubangijintaka wadda ta ke horewa ta gudanar da dukkan samammu farawa daga rana-rana da bishiyoyi, har i zuwa ƙwayoyin zarra a matsayinsu na sojoji da aka girke su, a ce ta tabbata a kan masu ƙarewa miskinai waɗanda suke rayuwa wata rayuwa ta ɗan lokaci a wannan gida na saukar baƙi, kuma a ce ba za ta samar da wani gida na girma na har abada madawwami wanzajje ba,wanda zai zama gurin kai kawo na ubangijintaka ta har abada maɗaukakiya mai matsayi?!

Na'am, haƙiƙa tsare-tsaren aiwatarwa da a ke gani a wannan duniya, kamar caccanzawar lokuta na shekara, da manya manyan motsi, kamar motsin taurari masu kama da motsin jiragen sama, da manya-manyan horewa, kamar sanya ƙasa a matsayin makwancin ɗan’adam, da sanya rana a matsayin fitila ga halitta, da juye-juye masu faɗi kamar rayar da ƙwallon duniya matacce da ƙawata shi; duk wannan yana nuna cewa a bayan hijaban akwai ubangijintaka mai girma da ta ke iko da mamaya da mulki mai girma, domin mulkin ubangijintaka irin wannan yana buƙatar talakawa da suka dace da shi, da wasu alamomi da suka yi daidai da shi.