HAКIКA TA BIYU

42. Page

HAКIКA TA BIYU

 

Babin Karamci da Rahama

 

Wanda shi ne tajallin suna na Mai karamci da Mai rahama

 

Shin zai yiwu ga Ubangijin wannan duniya-wanda shi ne ma'abocin karamcin da ba shi da iyaka, da rahamar da ba ta da tiƙewa, da buwayar da ba ta da iyaka, da kishi da ba shi da iyaka da dalilan ayoyinsa waɗannan da ya bayyana su- a ce ba zai yi sakamako irin sakamakon da ya dace da karamcinsa da rahamarsa ba, kuma a ce ba zai yi uƙuba ba irin uƙubar da ta dace da buwayarsa da kishinsa ba?

 

Na'am; idan da mutum zai yi tsai ya yi nazari cikin gudanar lamura a cikin wannan duniya da ya ga cewa rayayyu dukkaninsu, farawa daga mafi gazawarsu kuma mafi rauninsu, da tuƙewa da mafi ƙarfinsu ana ba su arziƙi ne da ya dace da su[1], kuma cewa shi ana bawa mafi rauninsu kuma mafi gazawarsu arziƙi mafifici, kuma cewa duk wani da aka jarrabe shi da masifa to maganinsa da warakarsa na zuwar masa ta inda bai za ta ba,kuma cewa ana shirya kaɓakai a ba da kyaututtuka cikin karamci maɗaukaki abin da ke nuna cewa lallai wani hannu na karamci mara iyaka ne ke aiki a cikinta kuma yake tafiyar da lamura, domin ga misali:

Da za a zurfafa nazari cikin yadda a ke lulluɓawa dukkan bishiyoyi tufafi masu kama da sundusu kamar Hurul Ini, da yadda ake ƙawata su da furanni da 'ya'yan itatuwa waɗanda aka daje su, kuma aka hore su don su yi mana hidima,kuma su ba da mafi ƙayatarwar 'ya'yan itatuwa mabambanta, kuma mafiya zaƙinsu, mafi ƙayatarwarsu garemu ta hanyar rassansu da suke su ne hannayansu masu taushi a lokacin kaka, kuma da ciyar da mu mafi zaƙin zuma wanda yake a cikinsa akwai waraka ta hannun wani ƙuda mai ɗauke da dafi, da tufatar da mu da mafi kyawun tufafi mafi laushinsu

[1] Haƙiƙa dalili yankakke da yake nuna cewa arziƙi na halak ba ana ba da shi ba ne gwargwadon ƙarfi, sai dai gwargwadon buƙata, shi ne irin rayuwar lagwada da yara ƙanana da ba su da wani ƙarfi ko iko suke morewa, yayin da dabbobi mafaɗata ƙarfafa masu iko ke rayuwa cikin ƙuncin rayuwa, da ƙibar kifaye waxandaba su da wani wayo, kuma ga ramar dilaye da birirrika wanda suke da kaifin hankali da wayo saboda baƙƙan cikin rayuwa, kenan alakar da take tsakanin arziƙi tare da iko da zaɓi ita ce alakar kishiyantar juna, ma'ana duk sanda halitta ta dogara da ikonta da zaɓinta sai a ƙara jarrabeta da damuwa cikin abin masarufin rayuwa da kuma ƙuncinta.(mawallafi). 




43. Page

da taushinsu ta hanyar wani ƙwaro da ba shi da hannu, da ajiye mana wata taska ta rahama mai girma garemu cikin wani ƙwallon ɗan ita ce ƙarami; da za a zurfafa tunani cikin duk waɗannan lamuran da ya bayyana kai tsaye cewa su alamu ne na karamci cikin matuƙar kyawu da jin ƙai cikin matuƙar tausasawa.

 

Kuma kai kawon dukkanin abubuwa-in ban da ɗan’adam da wasu daga mabangazan dabbobin dawa-don aiwatar da ayyukansu cikin kamala da himmatuwa da kyautatawa, tun daga rana da wata da ƙasa, zuwa mafi ƙanƙantar abin halitta, da kuma rashin tsallake iyakokinsu daidai da misalin gaɓar yatsa, da samuwar biyayya magamiya ƙarƙashin wani kwarjini mai girma,duk waɗannan suna nuna cewa kowane abu yana motsawa ne kawai da umarnin wanda yake da jalala da buwaya da girma.

 

Kuma haƙiƙa rainon dukkanin iyaye mata[1], tsirrai ne su ko dabbobi ko mutane-ga 'ya'yayensu raunana masu gazawa cikin tausayi da jin ƙai, da mafi taushin abinci kamar nono; yana bayyanawa kai tsaye cewa bayyanar wata rahama mayalwaciya ce ta ke aiki cikin wannan al'amari da kuma sarrafa shi,kuma tun da mai tasrifi a cikin wannan duniya yana da irin wannan karamci wandaba shi da iyaka, da irin wannan rahama wadda ba ta da matuƙa, da irin wannan jalala da waccan buwaya waɗanda ba su da iyaka; to haƙiƙa jalala da buwaya da ba su da iyaka suna lazimta hukunta mai munana ladabi, hakanan karamcin da ba shi da iyaka yana buƙatar yin karamci wanda ba shi da iyaka,kuma rahamar da ba ta da iyaka tana wajabta wani irin kyautayi da ya dace da ita, sai dai babu abin da zai tabbata kuma ya bayyana daga cikin waɗannan lamura a cikin wannan duniya mai ƙarewa da wannan rayuwa gajeriya face yanki ɗaya daga miliyoyin yankuna kamar dai ɗigo ɗaya daga kogi, kenan ba makawa cewa akwai wani gidan na rabauta da ya dace da wancan karamci da waccan rahamar, idan ba haka ba kuwa to ya wajaba kenan a yi inkarin samuwar wannan rahamar wanda a ke gani, kamar dai inkarin samuwar rana wadda ta ke cika yini da haskenta; domin kuwa gushewa ba tare da komowa ba na wajabta koruwar haƙiƙar rahamar,ta hanyar juya tausayin zuwa masifa, da sauyawarsa na soyayya zuwa ƙonuwa, ko ni'ima zuwa uƙuba, ko hankali zuwa wata na'ura mai shu'umanci, ko jin daɗi zuwa raɗaɗi.


[1]Na'am, haƙiƙa fifitawar da mayunwacin zaki yake yi wa yaronsa rarrauna a kan kansa, da ƙin cinsa ga gutsuren naman da ya kama, ya ba shi shi, da afkawar da matsoraciyar kaza ta ke yi ga kare domin ba da kariya ga 'yan 'ya'yanta, da ƙoton da bishiyar ɓaure kan yi daga taɓo ta shayar da 'ya'yan itacenta waɗanda su ne 'ya'yanta daga tataccen nono, lallai yana bayyanawa kai tsaye ga wandaba makaho ba cewa su suna motsawa ne da umarnin mai rahama mai karamci mai tausayi wanda babu iyaka ga rahamarsa da karamcinsa da tausayinsa (mawallafi).

Na'am,haƙiƙa aikatawar wanda ba shi da ji na zuci ko fahimta daga cikin ababan halitta kamar tsairrai da dabbobi, na wasu ayyuka da suka kai matuƙa wajen alaƙa da ji na zuci da fahimta da hikima na nuni bisa lazimta cewa akwai wani masani mai hikima wanda babu ƙarewa ga iliminsa da hikimarsa,wanda yake amfani da su kuma yake hore su, kuma cewa su kawai suna aiki ne da sunansa da umarninsa shi kansa.(mawallafi).




44. Page

Kuma babu makawa a samu wani gida na uƙuba da ya dace da waccan jalalar da kuma waccan buwayar; domin da yawa azzalumi kan zarce cikin buwayarsa, kuma abin zalunta ya dawwama cikin ƙasƙancinsa, kuma su ƙaura daga wannan duniya bisa wannan halin, kenan ana jinkirta lamarin zuwa wata kotu babba kuma a sarara masa,amma fa ba a wasarairai da shi, kai wani lokacin ma ana yin uƙuba a kansa har a duniya, domin nau'o'in azabobin da suka sami mutane masu saɓo masu tawaye a ƙarnonin da suka shuɗe suna bayyana cewa ɗan’adam dai ba sakakke ba ne mai gararamba da yake aikata abin da ya ga dama, face shi a ko yaushe yana gamuwa da mangari na jalala da kishin -ubangiji-.

 

Na'am, haƙiƙa wannan mutum wanda yake da ayyuka muhimmai da tanade-tanade muhimmai tsakanin gaba ɗayan samammu, idan bai san ubangijinsa ta hanyar imani ba, bayan ubangijinsa ya sanar da shi kansa da irin waɗannan ababan samarwa ƙayatattu masu tsari irin wannan, kuma idan bai soyantar da kansa zuwa ubangijinsa ta hanyar ibada ba bayan ubangijinsa ya soyantar da kansa zuwa gare shi da amfanin rahamarsa abar ƙawatawa tattausa irin wannan, kuma idan bai girmama shi ya kambama shi ba bayan ubangijinsa ya bayyana soyayyarsa da rahamarsa a gare shi ta hanyar ni'imominsa mabambanta ta hanyar godiya da yabo;muna cewa Shin zai yiwu a ce ba za a yi uƙuba ga wannan mutum ba, kuma a bar shi sakaka yana gararamba a sake? Kuma shin zai yiwu ga sarki na gaskiya maɗaukaki ma'abocin jalala da buwaya da kishi a ce ba zai tanadi gidan uƙuba ba?

45. Page

Kuma shin zai yiwuga mai rahama mai jin ƙai a ce ba zai tanadi gidan yin kyakkyawan sakamako ba, kuma ya ba da rabauta ta har abada ga muminai ba waɗanda suka sakawa sanar da su kansa da ya yi ta hanyar saninsu gare shi ta hanyar yin imani da shi, kuma suke sakawa soyantar da kansa gare su da sonsu gare shi ta hanyar bauta da ma sanya sonsa a zukatan wasu, kuma suke sakawa rahamarsa gare su ta hanyar girmamawa da godiya?

 

HAКIКA TA UKU

 

Babin Hikima da Adalci

 

Wanda shi ne tajallin suna na Mai Hikima da Mai Adalci

 

Shin mai yiwuwa ne[1] ga sarki na gaskiya maɗaukaki ma'abocin jalala wanda ya bayyana masarauta ta ubangijintaka da hikima da tsaruwa da adalci, da ma'auni mai

[1] Na'am,haƙiƙa jumlar "Shin mai yiwuwa ne" tana yawan maimaituwa; saboda ita tana ba da fa'idar wani sirri mai girma kuma muhimmi, wanda shi ne:Haƙiƙa mafi yawan kafirci da ɓata suna faruwa ne daga nesanta yiwuwar abu, ma'ana dai su ma'abota kafirci da ɓata suna ganin cewa abu ba mai yiwuwa ba ne kuma manesanci ne daga hankali, sai su yi inkarinsa, don haka ne ma a cikin "saƙo na tashin Alƙiyama" aka bayyana wannan da bayani fayyatacce yanke cewa, nesantawa ta haƙiƙa, dakoruwa ta haƙiƙa, da nisanta daga hankali, da wahalta ta haƙiƙa, kai har ma mushkiloli da suka kai matakin rashin yiwuwa, duk waɗannan suna cikin tafarkin kafirci ne da turbar ɓata, kuma cewa yiwuwa ta haƙiƙa, da karɓar hankali ga abu ta haƙiƙa,kai har ma sauƙin yiwuwar abu da ya kai matakin wajabci, duk waɗannan suna kan tafarkin imani ne, da turbar Musulunci.

A ƙarshe dai:Haƙiƙa ma'abota falsafa suna jawuwa ne zuwa inkari ta hanyar ƙaimin nisantuwa, kuma "batu na goma" yana bayyana maɓoyar nisantuwar, kuma ya yi musu ɓarin makauniya.(mawallafi).