HAКIКA TA GOMA
NAVIGATION
88. Page
HAКIКA TA GOMA
Babin hikima da kulawa da jin ƙai da adalci
Waɗanda su ne tajallin sunan Mai hikima da Mai karamcida Mai Adalcida Mai rahama
Shin yanzu mai yiwuwa ne ga mamallakin mulki ma’abocin jalala wanda ya bayyana guraban hikima mai ƙayatarwa irin wannan, da guraban kulawa mabayyaniya irin haka, da guraban adalci marinjayi irin wannan, da guraban rahama mai yalwa irin wannan, a wannan gidan saukar baƙi na duniya, wanda babu wanzuwa gare shi, kuma a wannan fagen jarrabawa wanda babu dawwama gare shi, kuma a wannan filin baje koli na doron ƙasa wanda babu tabbata gare shi, shin zai yiwu a ce a cikin da’irar masarautarSa da duniyar mulkinSa da sarautarSa babu masaukai madawwama, da mazauna na dindindin da mazaunai wanzazzu, da ababan halitta masu zama,don haka sai matsayin haƙiƙoƙin wannan hikima da kulawa da adalci da jin ƙai waɗanda a ke ganinsu su saraya; su zama ba komai ba.
89. Page
Sannan shin abu ne mai yiwuwa ga mai hikima maɗaukakin sarki ya sanya wannan ɗan’adam abin yin Magana gare shi matattari, kuma madubi magami gare shi tsakanin dukkan ababan halittarSa, kuma ya ɗanɗana masa duk abubuwan da taskokin jin-ƙansa suka ƙunsa, ya sanya shi mai ƙiyasta su da auna su, ya sanar da shi su,ya sanar da kansa gare shi da dukkan sunayensa, ya sanya wasu su so shi, sannan a ce ba zai aika wannan mutum miskini zuwa masarautarSa madawwamiya ba, kuma a ce ba zai kira shi ba zuwa gidan rabauta madawwami,kuma a ce ba zai rabautar da shi ba?!
Sannan shin mai yiwuwa ne a hankalce a ce ya ɗorawa kowane samammen abu-ko da daidai da girman ƙwallon ɗan ita ce ne-nauyin wasu ayyuka gwargwadon bishiya, kuma ya sanya masa hikimomi adadin ‘ya’yan itatuwanta, ya rataya masa maslahohi adadin ‘ya’yan itatuwanta, sannan a ce ba zai sanyawa waɗannan ayyuka da hikimomi da maslahohi komai ba face wata manufa daidai da girman wani ɗan ƙwallon ɗan ita ce wadda take fuskantarduniya, kuma ya sanya wanzuwarsa ta duniya ce wadda ba ta da muhimmanci ko da daidai da ƙwayar komayya ita ce manufarsa, kuma a ce ba zai sanya waɗancan samammun abubuwa a matsayin ƙwallon iri na duniyar ma’ana da gonar duniyar lahira, har dai su samar da manufofinsu na haƙiƙa da suka dace da su su ba da sakamakonsu, kuma a ce ya bar waɗannan bukukuwa muhimmai masu girma irin haka su zama don wasa sakaka ba tare da manufa ba,kuma a ce ba zai juyar da fuskokinsu zuwa duniyar ma’ana da duniyar lahira ba, har manufofinsu na asali su bayyana, kuma su samar da amfanoninsu da suka dace da su.?!
90. Page
To shin mai yiwuwa ne ya aikata waɗannan abubuwa bisa saɓanin haƙiƙa kamar haka,kuma ya bayyana kansa a matsayin mai siffantuwa da kishiyoyin hikima da karamci da adalci, da jin ƙai waɗanda su su ne siffofin zatinSa na haƙiƙa-tsarki ya tabbata a gare shi kuma tsarki ya tabbata gare shi ga barin haka-sai ya zama ya ƙaryata dukkan haƙiƙoƙin halitta da suke nuna hikimarsa da karamcinSa da adalcinSa da jin ƙanSa, kuma ya mai da duk irin shaidu da dukkan samammu suka yi masa mai girma da ɗaukaka, kuma ya ɓata dalilan dukkan ababan samarwa?!
Kuma shin hankali zai karɓa cewa a ɗorawa kan mutum da abin da ke cikin galɓaninsa na sansana, a ɗora musu ayyuka daidai da adadin gasussukan kansa, sannan ya ba shi lada na duniya kamar girman silin gashi, sai ya zama ya yi tasarrafi tasarrafin wasa yana mai saɓawa adalcinSa na haƙiƙa, kuma mai cin karo da hikimarSa ta haƙiƙa.
91. Page
Kuma shin mai yiwuwa ne a ɗorawa duk wani mai rai, ko ma duk wata gaɓa daga gaɓɓansa kamar harshe, ko ma duk wani abin samarwa adadin sakamako da ‘ya’yan itatuwa da ya rataya su a kan bishiya ɗaya, ya ɗora musu wannan adadin na hikimomi da maslahohi, don ya tabbatar cewa Shi mai hikima ne mai cikakkiyar hikima, sannan a ce an bar shi ba za a ba shi wanzuwa da gamuwa da rabauta ta har abada ba, waɗanda su ne mafi girman hikimomi kacokan, kuma mafi muhimmancin maslahohi dukkaninsu, waɗanda suke sanya hikima ta zama hikima, suke sanya ni’ima ta zama ni’ima, suke sanya rahama ta zama rahama, waɗanda su ne maɓuɓɓuga kuma su ne matuƙar dukkanin hikimomi da ni’imomi da rahamomi da maslahohi, sai ya sarayar da dukkanin ayyukanSa zuwa matakin wasa cikakke, sai ya kamanta kanSa da wanda ya gina fada, kuma ya sanya dubban zane-zane a cikin kowane dutse daga duwatsunta, kuma cikin kowane sashi daga sassanta ya sanya dubban ƙawace-ƙawace, kuma cikin kowane ɗaki daga ɗakunanta ya sanya dubban na’urori da kayayyakin gida masu tsada, sannan a ce ba zai sanyawa wannan fada rufi ba, sai ta tsofe kuma duk abin da ke cikinta ya tsufa, sai ta ɓaci ta tsufa bisa wasa ba da wata ma’ana ba?Tsarki ya tabbata a gare shi faufau!
92. Page
Daga alheri na sake babu ƙaidi alheri yake zuwa, kuma daga kyakkwawa na sake babu ƙaidi kyawu yake zuwa, kuma daga cikakken mai hikima wasa ba ya zuwa.
Na’am; haƙiƙa duk wanda yake karanta tarihi da tunaninsa, kuma ya tafi zuwa lokacin da ya wuce, zai ga masaukai da fagage da filayen baje koli, da duniyoyi matattu gwargwadon yawan shekaru, kamar dai wannan gidan duniyar, da fagen jarrabawar, da filin baje kolin abubuwa da mu ke ganinsu, kuma mu ke ganin su a lokacin yanzu, to tare da cewa su sashinsu yana sassaɓawa daga sashi ta fuskar sura da yanayi, to haƙiƙa kuma su suna kama da juna ta fuskar tsaruwa da ƙirƙira da bayyana ikon mai samarwa da hikimarSa, hakanan kuma a cikin waɗancan gidajen waɗanda ba su da tabbata, da kuma waɗancan fagagen da babu dawwama gare su, da waɗancan filayen baje koli da babu wanzuwa gare su zai ga ƙirƙira da tsaruwa da hikima mai matuƙar ƙayatar da hankula, da isharori na kulawa mabayyana, da alamomi na adalci marinjayi, da amfanoni na rahama mai yalwa har ta kai tare da ita zai san tabbas cewa-matuƙar dai ba mara basira ba ne-cewa ba zai yiwu a sami wata hikima ta zama mafi cika daga waccan hikimar ba, kuma ba zai yiwu a sami wata kulawa mafi kyawu daga waccan kulawar da muke ganin gurabanta ba, kuma babu wani adalci mafi girma daga wancan adalcin da mu ke ganin alamominsa, kuma ba zai yiwu a iya tunanin wata rahama mafi gamewa daga waccan rahamar da a ke ganin alfanunta ba, to a bisa mu ƙaddara yiwuwar abin da ba zai yiwu ba-idan da a ce sarki na dindindin wanda yake gudanar da waɗannan lamura, kuma yake tsara su, yake caccanza waɗannan baƙin da kuma waɗannan gidaje saukar baƙin, idan da a ce a cikin da’irar mulkinsa ba shi da
93. Page
masaukai na dindindin da gurare maɗaukaka, da mazaunai tabbabtattu, da gidaje wanzazzu, da ‘yan gari mazauna, da masu bauta masu rabauta, to ya wajaba a kore haƙiƙoƙin hikima da adalci da kulawa da jin ƙai waɗanda su ne sinadarai huɗu na ma’ana ƙarfafa masu gamewa irin ƙarfi da gamewar haske da iska da ruwa da turɓaya, da inkarin samarwarsu waɗanda a ke ganinsu a bayyane kamar bayyanar waɗancan sinadarai,domin sanannen abu ne cewa wannan duniyar mai ƙarewa ce, tare da duk abin da ke cikinta, ba za ta iya zama bigiren bayyanar haƙiƙoƙin waɗancan lamura da gaske ba, to idan da babu wani guri daban da zai iya zama gurbin bayyanar haƙiƙoƙin waɗancan haƙiƙoƙin da gaske a wani gidan da ban ba, to sannan kenan ya wajaba a yi inkarin ɓoyayyiyar hikima da ke tsaye a cikin kowane abu da muke gani a gabanmu, da inkarin wannan kulawa da muke ganinta a kan kanmu ko yaushe, kuma a cikin mafi yawan abubuwa, da inkarin wannan adalci[1] da yake bayyana kuma a ke ganin alamominsa masu ƙarfi ƙwarai, da kuma inkarin wannan jin ƙai da muke ganinsa kuma muke kallonsa a kowanne guri, ya wajaba yin inkarin duk waɗannan inkarin da ya kai haukan wanda yake inkarin samuwar rana tare da cewa yana ganin haskenta da yake gauraye yini, hakanan ya wajaba a karɓi cewa ma’abocin waɗannan tsare-tsare na gudanarwa masu hikima da ayyuka masu karamci, da kyautayi da ni’imtawa mai cike da jin ƙai da muke ganinsu da kallonsu a duniya-ya tsarkaka kuma ya tsarkaka ga barin haka-a ce ya zama mai wasa ne wawa ne, azzalumi ne mai yaudara ne, duk wannan na nufin juyewar haƙiƙoƙi zuwa kishiyoyinsu wannan abu ne mara yiwuwa da ba sama da shi, kai har Sufasɗawa wawaye waɗanda suke inkarin samuwar kowane abu da ma samuwar su kansu,ba za su iya kusanta daga tunanin haka ba, cikin sauƙi.
[1] Na’am; haƙiƙa wannan adalci kashi biyu ne, ɗayansu na fuskar daɗi ne, ɗayan kuma na rashin daɗi ne, shi dai na fuskar daɗin shi ne bawa kowane mai haƙƙi haƙƙinsa, wannan kaso na adalci ya kewaye lamura a duniya ƙarara, domin kamar ya tabbata a “Haƙiƙa ta uku” (daga wannan talifi) cewa maƙagi ma’abocin jalala yana bayarwa kamar yadda a ke gani cikin ma’aunai masu tsananin tantancewa,da magwadai na musamman, yana ba da duk abin da komai yake buƙata cikin yare na kintsi, ko yaren buƙatuwa ta zubin halitta, ko da yaren matsuwa, yana ba da dukkan haƙƙoƙinsa da suka zama tilas ga samuwarsa da rayuwarsa, kenan samuwar wannan kaso na adalci tabbatacce ne yanke kamar dai tabbatar samuwa da rayuwa.Kashi na biyu na rashin daɗi ne wanda shi ne yin uƙuba ga azzalumai, ma’ana tabbatar da haƙƙi da azaba da uƙuba, kuma tare da cewa wannan kaso ba ya bayyana a wannan duniya bayyana cikakkiya, sai dai akwai nuni da alamominsa marasa iyaka da suke nuna samuwar wannan haƙiƙa, daga ciki akwai mangare-mangaren ladabtarwa, da bulalun azaba da suka sauka a kan Adawa da Samudawa har zuwa mutane masu tawaye a wannan zamani, duk suna nuni kai tsaye bisa mamayar adalci mai matuƙar ɗaukaka.(Mawallafi).
94. Page
A taƙaice dai:babu wata alaƙa ko ta sisin kwabo tsakanin abin da muke gani na sha’anonin duniya na haɗuwa mai yalwa na rayuwa, da rabuwa mai gaggawa ta mutuwa, da tarurruka manya-manya, da rabuwa mai gaggawa da tarurrukan bukukuwa manya-manya, da tajallolin masu girma,da kuma abin da yake sananne a wajanmu na sakamakonsu taƙaitacce da manufofinsu wofintattu na ɗan lokaci waɗanda suke komowa zuwa wannan duniya mai ƙarewa, kuma alaƙa tsakaninsu tana kama da ɗorawa wani ɗan dutse ƙarami hikimomi da manufofi manya-manya da suka dace da girman dutse babba, da kuma ɗorawa dutse babba manufofi
95. Page
taƙaitattu na ɗan lokaci daidai da girman dutse ƙarami, wannan haƙiƙa ba zai saje da kowane hankali ko kowace hikima ba, kenan rasar da alaƙa tsakanin waɗannan samammu da sha’anoni da kuma manufofinsu na duniya irin haka yana shaidawa shaida mai yanke shakkucewa fuskokin waɗannan ababan halitta masu fuskanta ne zuwa duniyar ma’ana -duniyar da ba a gani wato lahira-, kuma za su ba da sakamakonsu ne da ya dace da su a can, kuma idanunsu suna ƙara kallonsu ne zuwa sunaye masu tsarki kuma suna shauƙantuwa zuwa gare su, kuma manufofinsu suna fuskantar waccan duniyar ne kuma suna komawa gare ta ne,gundarinsu da ainihinsu yana cikin turɓaya ne sai dai zangarniyoyinsu za su bubbuɗe ne su bayyana a duniyar surori, don haka mutum yana shuka ne a nan kuma yana shuka ne gwargwadon tanadin halittarsa, kuma ya girba a lahira.
Na’am, haƙiƙa kai idan ka dubi fuskokin da suke fuskanta zuwa sunayen Allahntaka da duniyar lahira na waɗannan abubuwa za ka ga cewa kowane ƙwallo-wanda shi a kansa mu’ujiza ce ta ƙudura-yana da manufofi masu girma kamar dai bishiya, kuma cewa kowane fure[1]-wanda shi kalma ce mai hikima-yana da ma’anoni masu yawa daidai da adadin furannin bishiya, kuma kowane ɗan itaciya-wanda shi wata ƙirƙira ce da ta shallake hankali kuma ƙasida ce tsararriya ta rahama-yana da hikima gwargwadon ‘ya’yan ita ce na bishiya, shi kuwa kasancewarta arziƙi da abinci garemu to hikima ɗaya ce daga cikin dubban waɗancan hikimomi, inda ta ke ƙare aikinta kuma ta bayyana ma’anoninta, sannan ta mutu a binne ta a cikin tumbunanmu.
[1] Tambaya: Idan aka ce:me ya sa kake kawo misalan fure da ƙwallo da ɗan itace?
Amsa:domin su mu’ujizozi ne mafiya ƙayatarwa da ban mamaki da ɓuyan sirri, kuma masu aƙidar ɗabi’a da ma’abota ɓata da falsafa sun nutse a cikinsu saboda rashin karantawarsu ga rubutu mai tsananin ƙanƙanta da alƙalamin ƙaddara da ƙudura ya yi rubutu a kansu, don haka suka faɗa cikin dabgar imani da ɗabi’a(wato cewa ɗabi’a ita ta halicci komai.(Mawallafi).
96. Page
Kuma tun da waɗannan abubuwa masu ƙarewa suna samar da amfanoni masu wanzuwa ne a wani gurin, kuma su bar surori wanzazzu, kuma su bayyana ma’anoni na har abada ta wata fuskar,kuma su yi tasbihi tasbihi na har abada, kuma tun da mutum ba ya zama mutum na haƙiƙa sai in ya kalli fuskokinsu da suke fuskantar wannan fuska, kuma ya sami hanyar daga mai ƙarewa zuwa wanzajje, kenan lallai akwai wata manufa cikin waɗannan samammun abubuwa da suke jujjuyawa tsakanin rayuwa da mutuwa,kuma suke haɗuwa su rabu.
Don haka waɗannan halaye suna kama da halayen da a ke tsara su a jera su a samar da su saboda kwaikwayo, kuma babu saɓani cikin buga wannan misali, kamar yadda tarurruka da rabuwa gajeru suke faruwa ta hanyar ɗawainiya mai girma, har ta kai an ɗaɗɗauki hotuna sannan a tattara su, a haska su a sinima haskawa madawwamiya, hakanan manufar rayuwar mutum ta kan kansa ko a cikin al’uma a
97. Page
lokaci gajere a cikin wannan duniya, ita ma ɗaukar hotuna ce da tattara su da harhaɗa su, da ɗaukar sakamakon ayyukan mutum da adana su, domin a yi masa hisabi a wani taro mafi girma, kuma a bijiro da su a mabijira mafi girma, kuma a bayyana kintsawarsa domin samun rabo mafi girma, kenan hikimar nan da ta ke cewa “Duniya gonar Lahira ce”tana bayyana wannan haƙiƙa ne.
Kuma tun da duniya samammiya ce, kuma a cikinta akwai hikima da kulawa da rahama da adalci da gurabansu da muke gani, to ba makawa cewa ita ma lahira samammiya ce yanke kamar samuwar duniya, kuma tun da kowane abu a duniya yana fuskantuwa ne ta wata fuska zuwa waccan duniya, kenan tafiyar da a ke zuwa can ne, kuma inkarin samuwar lahira inkari ne ga samuwar duniya da duk abin da ke cikinta, kenan kamar yadda ajali da ƙabari suke jiran mutum, haka nan ma aljanna da wuta suke jiransa da fakonsa.


