HAКIКA TA HUƊU
NAVIGATION
50. Page
sai dai daidai da girman laifinsa da nauyinsa, da kuma muhimmancin zatinsa, da girman aikin da aka ɗora masa.
Kuma tun da yake wannan duniya mai ƙarewa ta ɗan lokaci nesa ta ke ƙwarai daga kasancewa guri na bayyanar irin wannan adalci, da wannan hikima game da mutum wanda aka halitta saboda rayuwa ta har abada; to ke nan ba makawa cewa wannan mai ɗaukakar ma'abocin kyawu mai adalci, kuma kyakkyawa ma'abocin jalala da hikimazai samar da wata Jahannama madawwamiya da wata aljanna madawwamiya.
51. Page
HAКIКA TA HUƊU
Babin Kyauta da Kyawu
Wanda shi ne tajallin suna na Mai Kyauta da suna na Kyakkyawa
Shin abu ne mai yiwuwa ga kyauta da baiwa marasa ƙarewa, da kuma wata dukiya da ba ta ƙafewa, da taskoki waɗanda ba sa ƙarewa, da kyawu na har abada wanda ba shi da tamka, da kamala ta har abada wadda babu tawaya a cikinta a ce ba sa lazimtar samun masu godiya mabuƙata zuwa gare su, da samuwar wasu masu shauƙi zuwa gare su da suke yin aiki irin na madubi, da masu kallo masu ƙayatuwa da su da za su dawwama a cikin gidan rabauta da bigiren saukar baƙi ba.?
Na'am, haƙiƙa ƙawata doron ƙasa da ababan samarwa masu ado irin haka, da sanya wata da rana a matsayin fitilu, da sanya bayan ƙasa a matsayin wani kaɓaki na ni'ima, da cika shi da mafi daɗin dangogin kayan ciye-ciye, da sanya bishiyoyi masu 'ya'ya a matsayin su ne ƙorai, da sabunta su a karo daban-daban a kowane lokaci na shekara; wannan yana nuni ne zuwa ga kyauta da baiwa na sake-babu-ƙaidi, to kuwa irin wannan kyauta da baiwa waɗanda ba su da iyaka, da irin waɗannan taskoki da rahama waɗanda ba sa ƙarewa suna buƙatar samuwar wani gida na saukar baƙi, da bigire na rabauta madawwamiya, kuma a cikinsa akwai duk wani abu da ake sha'awa, kuma babu shakka suna buƙatar masu ni'imtuwa masu morewa a cikin wannan gida na saukar baƙi su rayu rayuwa madawwamiya a cikin wannan bigire na rabauta, kuma su dawwama a cikinsa,ta yadda ba za su ji raɗaɗin gushewa ko rabuwa ba; domin gushewar jin daɗi raɗaɗi ne kamar yadda gushewar raɗaɗi jin daɗi ne, kuma irin wannan baiwa ba ta yarda da cutarwa da sanya raɗaɗi, kenan wannan yana wajabta samuwar wata aljanna ta har abada madawwamiya da samuwar masu buƙata madawwama a cikinta; domin kyauta da baiwa marasa ƙarewa suna lazimta cewa su kyautata kuma su ni'imtar ba tare da ƙarewa ba; su kuwa kyautatawa da ni'imtawa marasa ƙarewa suna wajabta godewa da morewa waɗanda ba sa ƙarewa,
52. Page
wannan kuwa yana buƙatar dawwamar samuwar mutumin da zai sami kyautatawar har dai ya bayyana ta hanyar ni'imtuwar madawwamiyar godiyarsa da yabawarsa sakamakon wannan ni'imtarwar dawwamammiya,domin kuwa jin daɗin da yake taƙaitacce yake kuma gurɓata da gushewa cikin ɗan lokaci gajere ƙwarai ba ya dacewa da abin da irin wannan kyauta da baiwa ke buƙata.
Sannan ka kalli guraren baje koli na sassan duniya waɗanda su gurin baje koli ne na ƙayatattun abubuwan samarwa na Allahntaka, kuma ka zurfafa kallo cikin allunan sanarwa na ubangijintaka[1]waɗanda suke a hannun tsirrai da dabbobi a bayan ƙasa, kuma ka saurari annabawa da waliyyai waɗanda su ne masu kira zuwa kyawawan abubuwa na ubangijintaka kuma masu bayyana su, dubi yadda cikin haɗuwar kalmarsu suke bayyanawa da fayyace kamalolin mai samarwa ma'abocin jalala, waɗanda babu tawaya a cikinsu ta hanyar baje kolin ƙayatattun ababan samawarsa, kuma suke janyo hankalin masu tsinkaye zuwa waɗancan kamalolin, kenan haƙiƙa wanda ya samar da wannan duniya yana da ɓoyayyun kamaloli waɗanda babu tawaya a cikinsu, waɗanda kuma suke buƙatar baje kolinsu da tallata su a idon masu ƙimantawa masu ganin kyawu, masu ƙayatuwa masu kallo ma su cewa ما شاء الله,su kuwa kamaloli madawwama to suna buƙatar tajalli ne madawwami, wannan kuwa yana wajabta dawwamar masu ƙimantawa masu ganin kyawun; domin masu ganin kyawu masu gushewa ƙimar kamaloli na saraya daga idanunsu[2].
[1] Na'am, haƙiƙa furen da yake da matuƙar ado da kyawu, da ɗan itacen da ke da matuƙar tsaruwa da jeruwa waɗanda aka rataya su a ƙarshen wani reshe siriri ƙwarai kamar sirantar zare siriri a jikin wata bishiya busasshiya kamar ƙashi, ba shakka su allo ne na sanarwa da suke jan duk wani ma'abocin ji a zuciya zuwa karanta kyawawan ƙirƙire-ƙirƙiren mai samarwa gagara-badau mai hikima da yake son ƙirƙira, kuma ka kwatanta sauran dabbobi da tsirran da aka yi kwatance da su a nan.(mawallafi).
[2] Na'am, haƙiƙa ya zama misali gama gari cewa wata kyakkyawar mace wadda ba ta buƙatar ado saboda kyawunta, wata rana ta kori wani mutum gama gari da ya ƙaunace ta daga majalisarta, sai mutumin ya ce yana mai fanshe haushinsa:tir da ita ta fiye muni, ya musa kyawun wannan kyakkyawar mata, wata rana kuma wata dabbar dubbu ta tsaya ƙarƙashin wata bishiyar inibi mai ɗan karan zaƙi, tana so ta ci 'ya'yan inibin, amma hannunta ya kasa kaiwa ya tsinko, kuma ta kasa hawa, sai ta ce-da yare irin nata-tana mai huce haushinta:ai tsami ma ke gare shi, ta juya ta tafi tana bubbuɗawa cikin fushi.(mawallafi).
53. Page
Haƙiƙa waɗannan samammun abubuwa da aka ba za su kyawawa masu ban sha'awa ƙayatattu waɗanda aka yi wa ado a sararin wannan duniya suna ba da labari ne game da kyawawan abubuwa na kyawu na ma'ana wanda ba shi da tamka, kamar yadda hasken rana ke ba da labari game da rana, kuma suna sanyawa zukata jin samuwar wasu ɓoyayyun abubuwa ƙayatattu na wani kyawu ɓoyayye wanda ba shi da tamka[1], kuma waɗannan ababan halitta suna nuni zuwa samuwar wasu ɓoyayyun taskoki daga wancan kyawu abin tsarkakewa,cikin sunaye mafiya kyawu, ko ma a cikin kowane suna daga cikinsu,kuma haƙiƙa kyawu ɓoyayye wanda ba shi da tamka, maɗaukaki mai daraja irin wannan, kamar yadda yake so a ga kyawawan
[1] Haƙiƙa samammun abubuwa da su ka yi kama da madubi tare da cewa su suna ƙarewa su gushe bi da bi, domin tajallin kyawu da kansa,a kan abubuwan da za su zo bayansu na daga abubuwan halitta, na nuna cewa kyawun banasu ba ne a kan kansu, sai dai shi alamomi ne ga wani kyawu abin tsarkakewa kuma alamomi ne nasa.(mawallafi).
54. Page
abubuwa nasa a cikin madubi, kuma yana so a kalli darajojin kyawunsa da kuma magwadan kyawunsa a cikin wani madubi ma'abocin ji a zuci mai shauƙantuwa zuwa gare shi, kuma yana dai so a ganshi kuma a kalle shi domin shi ma ya ga kyawunsa abin so ta hanyar ganin wasu.
Kenan shi yana so a ga kyawunsa ta fuskoki guda biyu:
Ta farkonsu: Ya ga kyawunsa shi kansa a cikin madubai masu launi-launi daban-daban.
Ɗayar kuwa:A gan shi ta hanyar masu kallo masu shauƙantuwa masu ganin kyawu masu ƙayatuwa da shi.
Ke nan haƙiƙa kyawun na son ya ga kansa kuma a gan shi,kuma bayyana da bayyanawa na wajabta samuwar masu kallo masu shauƙantuwa masu ganin kyawu masu ƙayatuwa, kuma tun da kyawun na har abada ne madawwami, to shi yana buƙatar dawwamar samuwar masu shauƙantuwa da tabbatar su dindindin; domin kyawu madawwami ba ya gamsuwa da mai shauƙantuwa mai gushewa,domin mai kallo wanda aka tabbatar masa da gushewa ba tare da komowa ba soyayyarsa tana juyewa ne zuwa ƙiyayya da zarar ya yi tunanin gushewar, kuma ƙayatuwarsa tana karkata zuwa rashin girmamawarsa kuma ta koma wulaƙantawa; domin mutum mai ruɗuwa mai son kansa yana saɓawa abin da ba zai iya kaiwa gare shi ba kamar yadda yake gaba da abin da ya jahilta; don haka sai a dunƙule ya fuskanci kyawun da ya cancanci soyayya mara iyaka da shauƙi da ganin kyawu waɗanda ba su da iyaka, ya fuskance su da gaba da ƙullata da inkari, ta nan ne sirrin kasancewar kafiri maƙiyin Allah ne maɗaukakin sarki ke bayyana.
55. Page
Kuma tun da waccan kyauta da waccan baiwa na sake babu ƙaidi, da wancan kyawu wanda ba shi da tamka, da kamala wadda babu tawaya a cikinta, suna buƙatar samuwar masu godiya da masu shauƙantuwa da masu ganin kyawu madawwama, kuma yayin da a wannan gida na saukar baƙi na duniya muke ganin cewa kowane mutum yana ƙaura ya faku da sauri, kuma yana ɗanɗanar wani abu na kyautayin wannan kyauta, sai su tsokano sha'awarsa, sai dai shi yana ƙaura ne ba tare da ya ci ba, kuma yana ganin wata 'yar ƙyallawa ta hasken wancan kyawu da kamala, ko ma a ce wata 'yar inuwa rarrauna tasa a ɗan taƙin lokaci mai walƙawa, kuma ya ƙaura ba tare da ya ƙoshi ba; kenan tafiyar da ƙauran suna kasancewa ne zuwa wasu lambuna na shaƙatawa na har abada madawwama.
A ƙarshe dai: kamar yadda wannan duniya da dukkan samammun abubuwanta suke nuni nuni na yankan shakku zuwa ga mai samar da su ma'abocin jalala; to haka
56. Page
sunaye da siffofin mai samarwa ma'abocin jalala mai tsarki suke nuni zuwa ga lahira, kuma suke ishara zuwa gare ta kuma suke buƙatarta.
HAКIКA TA BIYAR
Babin Tausayi da Bautatuwar Muhammadu (S.A.W)
Wanda shi ne tajallin Sunan Mai amsawa da sunan Mai rahama
Shin abu ne mai yiwuwa ga ubangiji mai yawan tausayi da jin-ƙai wanda ba bu ƙarshe ga tausayinSa da jin-ƙansa wanda yake ganin buƙatar mafi ƙanƙantar abin halittarSa, sai ya agaje shi da cikakken tausayi kuma ta inda bai yi tsammani ba, kuma yake jin mafi ƙasa-ƙasan sauti na mafi ɓuyan abin halitta ya kumataimake shi, kuma yake amsawa kowane mai tambaya da harshen hali da na magana, zai yiwu a ce zai ga mafi girman buƙata ta mafi girman bawa[1] kuma mafi soyuwar abin halitta zuwa gare shi a ce ba zai biya masa itaba kuma ba zai agaje shi ba?kuma a ce ya ji mafi girman addu'a kuma mafi ɗaukakarta amma ba zai amsa masa itaba?!
Na'am; haƙiƙa tausasawa da sauƙi da suke bayyana cikin abin da ya keɓanci arziƙin dabbobi raunana da ƙananunsu-bisa misali-da rainonsu duk suna nuni ne a kan cewa mamallakin wannan halitta yana tasarrufi ne a cikinta da ubangijintaka da ta kai matuƙa wajen jin ƙai, to shin mai yiwuwa ne ga tausayin mai jin ƙai a cikin ubangijintakarSa irin wannan a ce ba zai amsawa mafificiyar addu'a daga mafificin abin halitta ba?!
[1] Na'am, haƙiƙa wanda ya yi mulki na tsawon shekara ɗari uku da hamsin kuma mulkinsa da hukuncinsa ba su gushe ba suna masu ci gaba, kuma wanda al'umarsa ta kai yawan miliyan ɗari uku da hamsin a mafi yawan zamunna, kuma wanda talakawansa ke sabunta caffa gare shi a kowace rana, kuma suke ba da shaida a game da kamalarsa, kuma suke miƙa wuya ga umarce-umarcensa da cikakkiyar biyayya, kuma wanda rabin duniya da ɗaya daga cikin biyar na bil Adama suka rinu da irin rininsa;ma'ana suka rinu da irin rininsa na ma'ana, kuma shi abin soyuwa ne zuwa ga zukatansu, kuma shi ne mai tarbiyyantar rayukansu, ba shakka cewa shi ne mafi girman bawa na ubangijin da yake tasarrufi a cikin wannan duniya, kuma haƙiƙa mafiya yawan nau'o'i na ababan halitta sun sanya albarka ga aikinsa, da rawar da yake takawa a rayuwa da kuma shugabancinsa ta hanyar ɗaukar ɗan ita ce daga 'ya'yan ita ce na mu'ujizarsa, to ba makawa cewa shi ne mafi soyuwar ababan halitta a wajen mahaliccin wannan duniya, kuma cewa dukkan bil Adama suna da buƙata da suke roƙonta suke kuma suke nemanta da dukkan kintsin halittarsu, domin ita tana ɗaga su daga ƙasan ƙasa zuwa mafi ɗaukakar Illiyyina, haƙiƙa ita ce wanzuwa da dawwama, don haka babu kokwanto cewa waccan buƙatar ita ce mafi girman buƙata kuma mafi matsayinta, kuma babu shakka cewa mafi girman bawa zai nemi biyan waccan buƙata daga wajen mai biyan buƙatun da yawun kowa da kowa.(mawallafi).


