HAКIКA TA SHA BIYU
NAVIGATION
101. Page
zai yi ahi ya yi baƙin ciki ya ji raɗaɗi maimakon ya saki ransa, matuƙar zato na riyawa bai yaudare shi ba, kuma rai da san zuciya ba su shigo ba, domin mafi girman abin da yake ƙarewa ba zai iya biyan buƙatar mafi ƙanƙantar injinda ke aiki a jikin mutum ba, kuma saboda wannan tanadi na halittar mutum burace-buracen mutum suka zama masu miƙuwa ne har zuwa abada, kuma tunaninsa da suka kewaye halitta, da kwaɗaye-kwaɗayensa da suka yaɗu cikin nau’o’in rabautarsa ta har abada suna nuni ne cewa wannan ɗan’adam an halicce shi ne saboda rayuwa ta har abada,kuma shi zai ciru ya zuwa gare ta kuma cewa wannan duniyar gidan saukar baƙi ne, kuma farfajiya ce ta sauraron lahira.
HAКIКA TA SHA BIYU
Babin Manzanci da Saukar da wahayi
Wanda tajalline naDa Sunan Allah mai Rahama mai Jin Ƙai
Shin abu ne mai yiwuwa ga zace-zace na riyawa raunana waɗanda ba su da ƙarfi-daidai da ƙarfin fiffiken ƙuda-a ce za su rufe hanyar lahira da ƙofar aljanna waɗanda Manzo Mafi Karamci ya buɗe su (S.A.W) da dukkan ƙarfinsa, yana mai dogaro da ƙarfin mu’ujizozinsa guda dubu waɗanda suka tabbata tabbatattu-wannan manzon da dukkan annabawa suka ƙarfafi maganarsa da zancensa suna masu dogaro da mu’ujizozinsu,kuma dukkan waliyyai sun gasgata kiransa suna masu dogaro da kashafofinsu da karamominsu, kuma dukkan zaɓaɓɓu sun shaida da cancantarsa suna masu dogaro da tabbatarwarsu-kuma waɗanda Alƙur’ani mai hikima ya buɗe ƙofarsu, wanda shi mu’ujiza ne ta fuska arba’in da dukkan tabbatarwarsa da babu kokwanto a cikinta, yana mai dogaro da dubban ayoyinsa tabbatattu da babu kokwanto a cikinsu?
102. Page
Haƙiƙa ya bayyana daga haƙiƙoƙin da suka gabata kuma ya fito fili cewa batun tashin alƙiyama haƙiƙa ce tabbatacciya da wani ƙarfi mai ikon ya ɗaga ƙwallon duniya daga gurbinsa ya gusar da shi ba zai iya girgiza wannan batu ba, domin wannan haƙiƙa Sarki na gaskiya shi ya tabbatar da ita, ya kafa ta, da abin da dukkan sunayensa kyawawa da siffofinSa maɗaukaka suke buƙata, kuma manzo mafi karamci ya gasgata ta (S.A.W) da dukkan mu’ujizozinsa da hujjojinsa, kuma Alƙur’ani mai hikima ya tabbatar da ita da dukkan haƙiƙoƙinsa da ayoyinsa, kuma wannan halittar ta ke shaidawa da ita, da dukkan ayoyinta na samar da ita da kuma sha’anoninta masu hikima, to shin abu ne mai yiwuwa ya jama’a bayan dukkanin samammun abubuwa sun haɗu-in ban da kafirai-a kan cewa batun tashin alƙiyama wajibin samuwa ne, shin bayan duk wannan wasu shubhohi raunana da wasuwasin shaiɗan waɗanda ba su da ƙarfi – daidai da gwargwadon gashi - a ce za su girgiza
103. Page
wannan haƙiƙa kafaffiya maɗaukakiya mai daraja da ta kafu kamar kafuwar dutse kuma ta ɗaukaka kamar ɗaukakarsa, a ce kuma za su ɗaga ta daga gurbinta su gusar da ita, tsarki ya tabbata ga Allah ga barin haka faufau!
Ka da ka taɓa tunanin cewa hujjojin tashin Alƙiyama sun taƙaita ne ga waɗannan haƙiƙoƙi goma sha biyu da muka ambata ko sun iyakantu a cikinsu ne, a a maimakon haka haƙiƙa Alƙur’ani mai hikima kamar yadda shi ya koya mana waɗannan haƙiƙoƙi da suka gabata goma sha biyu, hakanan yana nuni zuwa dubban fuskoki, kuma kowace fuska alama ce ƙaƙƙarfa da ta ke nuni zuwa cewa mahaliccinmu zai ɗauke mu daga wannan gida mai ƙarewa zuwa wani gidan wanzajje.
104. Page
Kuma kada ka taɓa zaton cewa sunayan Allahntaka waɗanda suke wajabta tashin Alƙiyama sun taƙaita ne ga sunayen da muka ambata kawai waɗanda su neالحكيمMai hikima,daالكريم Mai Karamci,daالرحيم Mai jin ƙai, العادلdaMai adalci,daالحفيظ Mai kiyayewa, faufau,sai dai dukkan sunayen Allahntaka da suke bayyana cikin gudanar da halitta suna wajabta lahira, kai suna ma lazimta ta.
Kuma kada ka taɓa zaton cewa ayoyin samarwa na halitta da suke nuni ga tashin Alƙiyama sun taƙaita ne cikin abin da muka ambata, kuma sun iyakantu ne gare su, faufau,maimakon haka suna cikin mafi yawancin samammu ta ɓangaren fuskokinsu da yanaye-yanayensu, kamar dai hijaban da ake buɗe su ta dama da hagu, ta yadda ta ɗaya daga fuskokin nasa yana nuni ga mahalicci, ta biyun kuma tana nuna tashin alƙiyama ne.
Ga misali: Kamar yadda kyawun halittar mutum wanda yake a cikin mafi kyawun diri, yake nuni ga mahalicci, to haka ma gushewarsa a lokaci taƙaitacce tare da siffarsa ta karɓar abubuwa matattariya wadda ita ma ta ke a cikin mafi kyawun diri ta na nuni zuwa tashin alƙiyama, kuma da zai yi kallo wani lokacin da fuska ɗaya amma kallo biyu mabambanta to da ya ga cewa abubuwa suna nuni ne ga mahaliccinsu da kuma tashin Alƙiyama a lokaci guda.
105. Page
Ga misali: Kamar yadda idan ya zurfafa kallonsa cikin haƙiƙanin abin da yake bayyana a cikin mafi yawan abubuwa na daga tsarin hikima, da ƙawatawar kulawa, da awo na adalci, da tausasawa na rahama, da ya ga cewa su suna nuni ne bisa cewa ita ta samo tushe ne daga hannun ikon mahalicci mai hikima mai karamci mai adalci da jin ƙai, to hakanan idan ya zurfafa kallo cikin ƙarfin waɗannan sunaye da siffofi da rashin iyakantuwarsu, kuma ya yi nazari game da wofintar samammu masu ƙarewa da rayuwarsu gajeriya wadda ita ce bayyanar waɗancan sunaye da siffofi da anga lahira, kenan kowane abu yana karantawa kuma yana karantarwa da harshen yanayinsa yana cewa: “Na yi imani da Allah da ranar lahira”.
106. Page
KAMMALAWA
Haƙiƙa haƙiƙoƙi goma sha biyu da suka gabata sashinsu yana goyon bayan sashi ne,kuma sashinsu yana cikasa da ƙarfafa sashi, kuma dukkaninsu sun bayyana sakamako ta hanyar haɗewar sashinsu da sashi, to wane zato ne na riyawa zai iya keta waɗannan ganuwoyi goma sha biyu masu kauri da ƙarfi kamar ƙarfe, ko kamar daiman, kuma ya huda su har ya girgiza imani da tashin alƙiyama wanda shi Katanga ce mai katangewa, kuma fadace da ba a iya keta ta, domin aya mai girma tana cewa:مَّاخَلۡقُكُم وَلَا بَعۡثُكُمۡ إِلَّا كَنَفۡسٖ وَٰحِدَةٍۚ[1]
tana fa’idantar da cewa halittar dukkan ‘yan’dam da tashinsu mai sauƙi ne kuma mara wahala ne ga ƙudurar Allahntaka kamar sauƙin halittar mutum ɗaya da tashinsa.
Na’am; Haka ne,kuma haƙiƙa na yi rubutu a game da mabincikar tashin alƙiyama a cikin Risalar“Al-Nuƙɗah” dalla-dalla game da haƙiƙar da wannan aya ta yi bayani game da ita, sai dai mu a nan za mu yi nuni zuwa taƙaitacciyar ma’anar ta tare da misalai, in ka so ka koma zuwa waccan risalar ta “Al-Nuƙɗa”, ga misali:kuma misali mafi ɗaukaka na Allah ne,kuma babu ja-in-ja cikin misali, kamar yadda da tajallin rana da zaɓinta ne da nufinta, da ita kamar yadda ta ke tajalli game da ƙwayar zarra ɗaya cikin sauƙi, tana tajjalli haka ma a bisa abubuwa masu garai-garai waɗanda ba su da iyaka da irin wannan sauƙin da sirrin haskakuwa.
[1]القمان:28”Kuma halittarku da tashinku ba komai ba ne face kamar rai ɗaya”


