HAКIКA TA SHA ƊAYA

98. Page

HAКIКA TA SHA ƊAYA

 

Babin Mutumtaka

 

Wanda tajalli ne na sunan Mai Gaskiya

 

Shin abu ne mai yiwuwa ga sarki na Gaskiya abin bautawa da gaskiya ya sanya mutum-a tsakanin dukkan duniyoyin ababan halitta-mafi girma da muhimmancin bawa ga ubangijintakarSa ta sake babu ƙaidi, da ubangijintakarSa magamiya, kuma abin yi wa magana mafi yin tunani cikin zantuttukanSa na tsarkaka, kuma shi ne madubi mafi tattarawa ga bayyanar sunayenSa mafiya kyawu, kuma mafi kyawun mu’ujizar ƙudura a matakin mafi kyawun zubi da ya sami tajallin suna mafi girma,da bayyanar suna mafi girma da yake a kowane suna, kuma shi ne mai tantancewa mafi mallakar adadin mafi yawa na ma’aunai da na’urori domin ya auna kuma ya san abin da taskokin rahamarSa ta ƙunsa, kuma ya sanya shi mafi yawan buƙatuwa zuwa ni’imarsa mara iyaka, kuma mafi yawan jin raɗaɗi daga ƙarewa da gushewa, kuma mafi shauƙantuwa zuwa wanzuwa, kuma mafi taushi da laushi, kuma mafi buƙatuwa a tsakanin dabbobi, kuma mafi jin raɗaɗi da wahaltuwa a rayuwar duniya,kuma ya halicce shi a matsayin mafi yawan ɗaukaka da matsayi ta ɓangaren tanadin halittarsa, kuma cikin mafificiyar sura da haƙiƙa,(ya halicce shi a bisa dukkan waɗannan kamanni) sannan a ce ba zai aika shi zuwa wani gida na har abada ba,wanda shi a shirye yake don zuwansa can kuma mai shauƙi ne zuwa gare shi mai dacewa da shi,hakan zai sa haƙiƙanin mutumtaka ta ɓaci, kuma a zalunce shi zalunci mai cin karo kwata-kwata da cancantarsa, kuma mai muni a idanun haƙiƙa?

 


99. Page

Kuma shin abu ne mai yiwuwa ga mai hukunci da gaskiya mai jin ƙai na sake ba ƙaidi a ce ya bawa mutum wani tanadi na halitta wanda da shi ne zai iya ɗaukar babbar amanar da ƙasa da sammai da duwatsu suka ji tsoron ɗaukarta,ma’ana ya auna kuma ya ƙiyasta kuma ya sani ta hanyar ma’aunansa ƙananu taƙaitattu, da ƙwarewarsa da ƙirƙire-ƙirƙirensa sauƙaƙa,-shin da waɗannan- zai iya sanin siffofin mahaliccinsa masu kewayewa, da sha’anoninsa matattara, da tajallolinsa marasa ƙarewa,kuma ya sanya shi mafi yawan taushi da laushi da gajiyawa da buƙata a tsakanin halittu, tare da cewa ya sanya shi ta wata fuskar a matsayin ma’aikacin tsara dukkan halittun ƙasa na tsirrai da dabbobi, kuma ya sanya shi yana sanya hannu cikin tasbihinsu da ibadarsu, kuma ya sanya shi ƙaramin misali na tsare-tsaren aiwatarwa na Allahntaka a halitta, kuma ya sanya shi yana shelanta ubangijintakar tsarkakka a halitta a aikace da a faɗe,kuma ya fifita shi a kan mala’ikunsa ya  ba shi matsayin halifanci, sannan a ce ba zai  ba shi rabauta ta har abada ba wadda ita ce manufar duk waɗannan ayyuka kuma sakamakonsu da alfanunsu?

 

Kuma a ce ya jefa shi cikin mafi ƙasƙancin ababan halittarsa gaba ɗaya, kuma ya sanya shi mafi taɓewarsu, mafi rauninsu,mafi gajiyawarsu mafi yawansu a ɗanɗana kuɗa da damuwa da baƙin ciki, kuma ya sanya hankalinsa-wanda shi kyauta ce mai albarka ta haske saboda hikimarsa kuma tafarki ne na rabauta-a ce ya sanya shi ya wata na’ura ce ta yin azaba da ita azzaluma kuma mai shu’umanci ga wannan miskinin,sai ya zama an zalunce shi da hakan zalunci mai saɓawa hikimarSa ta sake babu ƙaidi dukkan saɓawa, kuma mai karo gaba ɗaya da rahamarsa ta sake babu ƙaidi?Tsarki ya tabbabta gare shi ga barin haka faufau!


100. Page

A ƙarshe dai: duk sanda muka dubi haƙiƙanin wancan jami’i da rajistarsa a cikin hikayar kwaikwayo, kuma muka ga cewa matsayinsa da albashinsa da tsarin kai-kawonsa da injinansa za su bayyana mana su fayyace mana cewa wannan jami’i ba yana aiki ba ne saboda wannan fage na ɗan lokaci kawai, maimakon haka zai tafi ne zuwa wata masarauta matabbaciya,don haka shi yana aiki ne saboda waccan masarauta,kuma haka ma’abota yayewa da tabbatarwa sun haɗu a kan cewa abubuwa masu ban ƙaye ɓoyayyu da suke cikin haƙiƙanin zuciyar ɗan’adam, da gaɓoɓin sansana da suke cikin rajistar hankalinsa, da injina da suke cikin tanadin halittarsa, dukkaninsu masu fuskanta ne cikakkiyar fuskanta zuwa rabauta ta har abada, kuma shi an masa kyautarsu ne kuma an masa guzuri da su ne domin haka.

 

Ga misali:Da za a cewa tanadin ƙarfin zana hoton zuci wanda shi ne mai wa hankali hidima kuma shi ne kamar kyamara ta sa, da za a ce da shi, za a  ba ka  tsawon ran shekara miliyan ɗaya tare da iko da mulkin duniya, amma kai za ka zamo ba komai ba tabbas, kuma za ka tafi zuwa hali na babu kai a lahira, lallai dole 

101. Page

zai yi ahi ya yi baƙin ciki ya ji raɗaɗi maimakon ya saki ransa, matuƙar zato na riyawa bai yaudare shi ba, kuma rai da san zuciya ba su shigo ba, domin mafi girman abin da yake ƙarewa ba zai iya biyan buƙatar mafi ƙanƙantar injinda ke aiki a jikin mutum ba, kuma saboda wannan tanadi na halittar mutum burace-buracen mutum suka zama masu miƙuwa ne har zuwa abada, kuma tunaninsa da suka kewaye halitta, da kwaɗaye-kwaɗayensa da suka yaɗu cikin nau’o’in rabautarsa ta har abada suna nuni ne cewa wannan ɗan’adam an halicce shi ne saboda rayuwa ta har abada,kuma shi zai ciru ya zuwa gare ta kuma cewa wannan duniyar gidan saukar baƙi ne, kuma farfajiya ce ta sauraron lahira.

 

HAКIКA TA SHA BIYU

 

Babin Manzanci da Saukar da wahayi

 

Wanda tajalline naDa Sunan Allah mai Rahama mai Jin Ƙai

 

Shin abu ne mai yiwuwa ga zace-zace na riyawa raunana waɗanda ba su da ƙarfi-daidai da ƙarfin fiffiken ƙuda-a ce za su rufe hanyar lahira da ƙofar aljanna waɗanda Manzo Mafi Karamci ya buɗe su (S.A.W) da dukkan ƙarfinsa, yana mai dogaro da ƙarfin mu’ujizozinsa guda dubu waɗanda suka tabbata tabbatattu-wannan manzon da dukkan annabawa suka ƙarfafi maganarsa da zancensa suna masu dogaro da mu’ujizozinsu,kuma dukkan waliyyai sun gasgata kiransa suna masu dogaro da kashafofinsu da karamominsu, kuma dukkan zaɓaɓɓu sun shaida da cancantarsa suna masu dogaro da tabbatarwarsu-kuma waɗanda Alƙur’ani mai hikima ya buɗe ƙofarsu, wanda shi mu’ujiza ne ta fuska arba’in da dukkan tabbatarwarsa da babu kokwanto a cikinta, yana mai dogaro da dubban ayoyinsa tabbatattu da babu kokwanto a cikinsu?