HAКIКA TA SHIDA

65. Page

HAКIКA TA SHIDA

 

Babin girma da sarmadiyya

 

Wanda shi ne tajallin suna na Mai girma da kuma suna na Wanzajje

 

Shin yanzu mai yiwuwa ne ga girman ubangijintaka wadda ta ke horewa ta gudanar da dukkan samammu farawa daga rana-rana da bishiyoyi, har i zuwa ƙwayoyin zarra a matsayinsu na sojoji da aka girke su, a ce ta tabbata a kan masu ƙarewa miskinai waɗanda suke rayuwa wata rayuwa ta ɗan lokaci a wannan gida na saukar baƙi, kuma a ce ba za ta samar da wani gida na girma na har abada madawwami wanzajje ba,wanda zai zama gurin kai kawo na ubangijintaka ta har abada maɗaukakiya mai matsayi?!

Na'am, haƙiƙa tsare-tsaren aiwatarwa da a ke gani a wannan duniya, kamar caccanzawar lokuta na shekara, da manya manyan motsi, kamar motsin taurari masu kama da motsin jiragen sama, da manya-manyan horewa, kamar sanya ƙasa a matsayin makwancin ɗan’adam, da sanya rana a matsayin fitila ga halitta, da juye-juye masu faɗi kamar rayar da ƙwallon duniya matacce da ƙawata shi; duk wannan yana nuna cewa a bayan hijaban akwai ubangijintaka mai girma da ta ke iko da mamaya da mulki mai girma, domin mulkin ubangijintaka irin wannan yana buƙatar talakawa da suka dace da shi, da wasu alamomi da suka yi daidai da shi.


66. Page

 Sai dai kai kana gani cewa haƙiƙa mafi muhimmanci kuma mafi tattarewar talakawansa da bayinsa ta fuskar haƙiƙa sun tarutaruwa ta ɗan lokaci suna miskinai masu rayuwar ƙunci a wannan gidan saukar baƙi, shi kuwa gidan saukar baƙin a na cika shi ana yashe shi a kowace rana; kuma dukkan talakawan suna zama ne na ɗan lokaci a wannan fagen na jarrabawa saboda a jarraba hidimominsu da ayyukansu.

Shi kuwa fagen ana musanya shi ne kowace sa'a, kuma dukkanin waɗannan talakawan suna zama ne na 'yan sakwankuna a wannan fage na baje koli domin kallon samfura na kala-kalan kyautatawa na mai samarwa ma'abocin jalala masu ƙima, da ƙayatattun halittunsa masu shallake hankali, a filayen baje koli na kasuwar duniya ta mahanga ta kasuwanci, sannan su ɓuya, shi kuwa wannan filin baje koli yana canjawa kowane sakan, don haka mai tafiya ba ya komowa, mai zuwa kuwa mai tafiya ne ya bar shi, wannan hali da wannan yanayi suna nunawa babu kokwanto cewa a bayan wannan gurin saukar baƙi da wannan fage da wannan baje koli akwai wasu fadoji madawwama da masaukai masu zarcewa da suka dace da waccan masarauta ta dindindin, da kuma wasu lambuna da taskoki waɗanda suke cike da mafi tsarkaka kuma mafi ɗaukakar asalin samfura da surorin da muke ganin su kuma muke kallonsu, kenan kai komo da wahala a nan ana yinsa ne domin waɗannan lamura, sai Sarki mai girma da ɗaukaka ya sanya mu mu yi faɗi tashi mu yi aiki a 

67. Page

Sai dai kai kana gani cewa haƙiƙa mafi muhimmanci kuma mafi tattarewar talakawansa da bayinsa ta fuskar haƙiƙa sun tarutaruwa ta ɗan lokaci suna miskinai masu rayuwar ƙunci a wannan gidan saukar baƙi, shi kuwa gidan saukar baƙin a na cika shi ana yashe shi a kowace rana; kuma dukkan talakawan suna zama ne na ɗan lokaci a wannan fagen na jarrabawa saboda a jarraba hidimominsu da ayyukansu.

Shi kuwa fagen ana musanya shi ne kowace sa'a, kuma dukkanin waɗannan talakawan suna zama ne na 'yan sakwankuna a wannan fage na baje koli domin kallon samfura na kala-kalan kyautatawa na mai samarwa ma'abocin jalala masu ƙima, da ƙayatattun halittunsa masu shallake hankali, a filayen baje koli na kasuwar duniya ta mahanga ta kasuwanci, sannan su ɓuya, shi kuwa wannan filin baje koli yana canjawa kowane sakan, don haka mai tafiya ba ya komowa, mai zuwa kuwa mai tafiya ne ya bar shi, wannan hali da wannan yanayi suna nunawa babu kokwanto cewa a bayan wannan gurin saukar baƙi da wannan fage da wannan baje koli akwai wasu fadoji madawwama da masaukai masu zarcewa da suka dace da waccan masarauta ta dindindin, da kuma wasu lambuna da taskoki waɗanda suke cike da mafi tsarkaka kuma mafi ɗaukakar asalin samfura da surorin da muke ganin su kuma muke kallonsu, kenan kai komo da wahala a nan ana yinsa ne domin waɗannan lamura, sai Sarki mai girma da ɗaukaka ya sanya mu mu yi faɗi tashi mu yi aiki a nan Shi kuma ya ba da ladan a can, don haka kowa yana da rabauta a can gwargwadon kintsinsa, idan dai bai rasar da ita ba ko ya tozartar da ita ba.


68. Page

Na'am; abu ne ba mai yiwuwa ba ga masarauta ta dindindin irin wannan ta tabbata a bisa waɗannan masu ƙarewa maƙasƙanta masu gushewa.

 

Dubi wannan haƙiƙa da madubin wannan miali:

 

Haƙiƙa kai kana tafiya a kan hanya, kuma kana ganin otal a kanta wanda wani mutum babba ya gina shi saboda baƙinsa waɗanda za su sauka a wajansa, kuma ya kashe miliyoyin Lirori na zinare wajen ƙawata shi saboda shaƙatawar baƙin nasa, da tunaninsu cikin abin da ya ƙunsa na daga fasahohi da ƙawace-ƙawace domin dare ɗaya kawai, sai dai fa su baƙin suna ganin ɗan kaɗan ne ƙwarai daga waɗancan ƙawace-ƙawacen a ɗan lokaci ƙanƙani, kuma su ɗanɗani kaɗan daga cikin waɗancan ni'imomi a lokaci ƙanƙani ƙwarai, kuma su ƙaura ba tare da sun ƙoshi ba, sai dai kowane baƙo yana ɗaukar hotunan abubuwanda ke cikin wannan otal da kyamararsa ta musamman,a ɗaya gefen kuma ma'aikatan wannan babban mutum mamallakin wannan otal suna sa ido ga yadda waɗannan baƙin suke kai kawonsu sosai kuma suna rubuta su daki-daki,kai dai kana ganin cewa wannan mamallakin wannan otal ɗin yana rusa da ruguza mafi yawan waɗannan ƙawace-ƙawace masu ƙima kowace rana, kuma yana samar da ƙawace-ƙawace sababbi ga wasu baƙin sababbi masu zuwa, to bayan ka ga waɗannan lamura shin har yanzu kana da shubha game da cewa wannan mamallaki wanda ya gina wannan otal ɗin a wannan hanya yana da wasu gidaje madawwama maɗaukaka zubin ya yi ƙwarai, da wasu taskoki masu tsada da ba sa ƙarewa, da baiwa mai girma mai zarcewa, shi yana motsa sha'awar baƙinsa zuwa ga abin da ke wajensa na daga abubuwa da ni'imomi ta hanyar yin karamcin da yake bayyana shi a cikin wannan otal, kuma ya tsokano kwaɗayinsu game da kyaututtukan da ya tanadar musu.


69. Page

Kuma kamar yadda yake a cikin wannan misali, da za ka zurfafa nazari ka yi zurfin tunani ba tare da maye ba, game da yanayin wannan gidan saukar baƙin na duniya da ka fahimci wasu "tuwasu tara":

 

Tushe na Farko: Za ka fahimci cewa ita wannan duniyar kamar dai wancan otal ɗin ce, ba an yi ta ne ba domin kanta, kuma abu ne ba mai yiwuwa ba ta siffantu da wannan yanayi ga kanta domin kanta, sai dai ita gidan saukar baƙi ne da aka gina shi da hikima, kuma a ke cika shi a kuma yashe shi saboda saukar ayarin ababan halitta a cikinta, da kuma ƙaurarsu su bar ta.


70. Page

Tushe na Biyu: Kuma za ka fahimta dai cewa su waɗannan masu zama a cikin wannan otal su baƙi ne, kuma cewa ubangijinsu yana kiransu ne zuwa gida na aminci.

 

Tushe na Uku: Kuma za ka fahimci cewa waɗannan ƙawace-ƙawace a cikin wannan duniya ba wai domin jin daɗi da morewa da ita ba ne ko shaƙatawa a cikinta kawai, domin ita idan ta ɗanɗanawa mutum daɗi na lokaci mai tsawo to za ta gadar da raɗaɗi na rabuwa da ita a mafi yawancin lokaci, domin haƙiƙa ita tana ɗanɗana maka kuma ta motsa sha'awarka, sai dai kuma ba ta ƙosar da kai, domin ko dai rayuwarta gajeriya ce,ko kuma kai rayuwarka gajeriya ce, don haka ita ba za ta isa ta ƙosar ba, kenan duk waɗannan ƙawace-ƙawace maɗaukaka masu ƙima masu gajeren kwana da lokaci su kawai domin izina ne da kuma godiya[1], kuma domin motsa kwaɗayi cikin tuwasunsu madawwama; kuma saboda wasu muradan daban maɗaukaka ƙwarai.

 

Tushe na Huɗu: Kuma za ka fahimta cewa waɗannan ƙawace-ƙawacen da suke a cikin wannan duniya, su suna matsayin surori ne da samfura na ni'imomin da aka tanada a aljanna da rahamar mai rahama ga ma'abota imani.


[1]Na'am, haƙiƙa, tun da lokacin kowane abu da rayuwarsa gajeriya ce, tare da irin ƙimar da yake da ita da tsantsaruwar ƙirarsa cikin matuƙar kyawu, to haƙiƙa waɗannan abubuwa samfura ne, kuma suna matsayin hotuna na wasu abubuwan, kuma tun da yana bayyana cewa waɗannan samfura da hotuna suna janyen hankulan masu zuwa kallonsu zuwa tuwasunsu da maɓuɓɓugansu, kenan babu shakka za a iya cewa haƙiƙa wannan nau'i na ƙawace-ƙawace a cikin wannan duniya su samfura ne na aljanna wadda mai rahama mai jin ƙai ya tanade ta da rahamarsa ga bayinsa waɗanda yake son su, kai haka ma ta ke a haƙiƙa.(mawallafi).




71. Page

Tushe na Biyar: Za ka fahimci cewa waɗannan ababan ƙerawa masu ƙarewa ba an halicce su ba ne saboda ƙarewa, kuma ba an halicce su ba ne domin su bayyana na lokaci gajere, kuma su mutu a hallakar da su bayan haka, sai dai domin a tattara su a cikin samuwa na lokaci gajere, kuma su daidaitu a yanayin da ake so har a ɗauki hotunansu, a adana kamanninsu, a san ma'anoninsu a kiyaye sakamakonsu, kuma domin su saƙa ababan kallo na dindindin ga ma'abota abada da dawwama, kuma su zama magewayai ne ga wasu muradan da ban a duniyar dawwama.

 

Kuma daga bayani mai zuwa za a fahimci cewa abubuwa an halicce su ne domin wanzuwa kuma ba a halicce su ba domin ƙarewa, kuma ko da suna ƙarewa a zahiri yadda a ke gani, to ƙarewar ta su ba komai ba ne face ƙare aiki ne da kuma ba da hutu gare su; haƙiƙa abu mai ƙarewa yana ƙarewa ne ta fuska ɗaya kuma ya wanzu ta fuskoki da dama,misali-dubi wannan furen wanda yake kalma ne daga kalmomin ƙudura, haƙiƙa ga shi yana murmushi kuma yana kallonmu na ɗan wani lokaci, sannan ya ɓace bayan haka a bayan shamaki na ƙarewa, kuma ya tafi kamar yadda Kalmar da take fitowa daga bakinka ta ke tafiya, sai dai kuma ita tana ban 

72. Page

kwana da dubbai irinta a cikin kunnuwa, kuma ma'anoninta su wanzu cikin hankula adadin hankulan da suka ji ta; domin ita tana ƙaura ne bayan ta gama aikinta wanda shi ne bayani game da wata ma'ana, sai dai shi yana ƙaura ne bayan ya bar surorinsa na zahiri a cikin ƙwaƙwalwar duk wanda ya gan shi, kuma bayan ya bar ainihin haƙiƙarsa ta ma'ana a cikin duk wani ɗan iri, kamar dai ka ce kowace ƙwaƙwalwa da kowane ɗan iri yana matsayin hoto ne na kwafi don adana adonta, kuma gida ne domin dawwamar wanzuwarta,to in dai ko abin samarwar da yake a matakin mafi ƙasƙancin darajar rayuwa haka lamarinsa ya ke, to ina ga alaƙar mutum da wanzuwa, wanda shi ne a mafi ƙololuwar matakin rayuwa, kuma ma'abocin ruhi wanzajje?!

 

Kuma zurfin ɗamfaruwa da alaƙar ruhin ɗan’adam da wanzuwa-wanda shi ruhin ƙa'ida na umarni kuma ma'abocin ji a zuciya, kuma mai samo asaline daga haske wanda ya mallaki haƙiƙa matattariya maɗaukakiya, wanda kuma aka lulluɓawa samuwa ta waje, zurfin wannan alaƙartasa da wanzuwa tana bayyana ta fito ƙuru-ƙuru ta hanyar kiyayewa da wanzar da tsarin samuwa-wanda yake kama da ruhi ƙwarai-da kuma surar kowa ne ɗaya daga cikin tsirrai masu furanni da 'ya'ya cikin 'ya'yan iri masu kama da ƙwayar zarra, da cikakken tsari cikin sassauyawa mai jujjuyawa.

 


73. Page

Tushe na Shida:Kuma za ka fahimci cewa shi ɗan’adam ba a bar shi sakaka ba, kuma ba a bar shi yana gararamba ba, ya yi karakaina duk inda ya so, a'a ana ɗaukan hoton dukkanin ayyukansa kuma ana taskace su ana rubuta su, kuma ana kiyaye sakamakon dukkanin ayyukansa saboda hisabi.

 

Tushe na Bakwai: Kuma za ka fahinci cewa mutuwar ababan halitta kyawawa a lokacin duniyar yanayin zafi da kaka, da ƙarewarsu a lokacin damina ba wai rasarwa ba ne, sai dai ba su hutu ne daga ayyukansu cikakken ba da hutu[1], ta hanyar ƙarewarsu, da ba da wuri ga wasu halittun masu zuwa a lokacin kaka sabuwa, har sababbin ma'aikata su zo su kama aiki, kamar yadda kuma yake shiri ne da kintsi, da shirya guri domin zuwan halittu, da farkarwa daga ubangiji mai tsarki ga dukkan ma'abota ji a zuci, daga gafalar da take mantar da su ayyukansu, da kuma maye da yake mantar da su, godiyarsu ga Allah maɗaukakin sarki.

 


[1]Na'am, ya wajaba 'ya'yan itatuwa da furanni da ganyaye waxanda suke a ƙarshan rassan bishiyoyi, kuma suke a matsayin ma'ajiyar abinci da arzika da rahama, ya wajaba su tafi, lokacin da suka tsufa kuma ayyukansu suka ƙare, domin kada a rufe ƙofa ga waɗanda suke zuwa bayansu, in ba haka ba sai su zama sun hana yalwar rahamar da ke zuwa daga hidimomin 'yan’uwansu, kuma su zama ƙasƙantattu miskinai bayan gushewar ƙuruciyarsu da ɗanyantakarsu.




74. Page

Tushe na Takwas:Kuma za ka fahimci cewa mai samarwa na har abada ga wannan duniya mai ƙarewa yana da wata duniyar daban wanzajjiya, kuma shi yana kora bayinsa zuwa can kuma ya ɗokantar da su zuwa gare ta.

 

Tushe na Tara:Kuma za ka fahimci cewa wancan Mai jin ƙan zai girmama waɗannan bayin nasa makeɓanta a waccan duniyar, kuma zai yi ni'ima a gare su da karramawa da ni'imtawar da idanu ba su taɓa ganin irinsu ba, kuma kunnuwa ba su taɓa jin irinsu ba, kuma ba su taɓa ɗarsuwa a zuciyar wani bil Adama daga cikinmu ba.

 

 

HAКIКA TA BAKWAI

 

Babin kiyayewa da Siffar kiyayewa

 

Wanda shi ne tajallinSunan Mai kiyayewada Mai sa ido

 

Shin Abu ne mai yiwuwa ga wani mai kiyayewa da yake kiyaye kowane abu cikin cikakken tsari da ma'auni, daga ɗanyan abu ko busasshe, ko ƙarami ko babba,sababbe maɗaukaki a sama da ƙasa, da tudu da kogi, kuma ya keƙididdige sakamakonsa, cikin yanayi mai kama da hisabi,a ce ba zai kiyaye ayyukan mutum ba-wanda yake da ɗabi'ar halitta mai girma maɗaukakiya, wanda kuma yake a matakin halifanci babba, wanda yake yana da aiki mai matsayi kamar ɗaukar amana babba-da ayyukansa waɗanda suka shafi ubangijintaka magamiya?! Kuma a ce ba zai tankaɗe su ba da rariyar hisabi?! Kuma a ce ba za a auna ayyukansa ba da ma'aunin adalci?! Kuma a ce shi wannan mutumin ba zai sami kyakkyawan sakamako ba kuma ba zai gamu da uƙuba mai dacewa da ayyukansa ba?! Faufau har abada.