HAКIКA TA TAKWAS
NAVIGATION
78. Page
na ubangijintaka, sannan a ce ya shiga ƙabari ya kwanta cikin hutawa kuma ba za a farkar da shi ba,kuma ba za a tambaye shi game da ayyukansa ba ƙananansu da manyansu, kuma a ce ba zai tafi filin taron Alƙiyama ba kuma ba zai samu babbar kotu ba?!faufau har abada.
Kuma ta yaya zai yiwu wannan mutum ya tafi zuwa rashi ya gudu daga mai ƙaddarawa ma'abocin jalala wanda ayyukansa-waɗanda su ne mu'ujizozin ikonsa-suke shaidawa cikin dukkan zamunnan da suka wuce cewa shi mai iko ne a bisa halittar dukkan abubuwa masu yiwuwa da za su faru a nan gaba gaba ɗayansa[1],kuma wanda yake samar da lokacin sanyi da lokacin kaka da ake ganinsu, kuma waɗanda suke yin kama da tashin Alƙiyama da tashinta sosai, ta yaya zai yiwu gare shi -mutum- ya guje masa ya shiga turɓaya ya ɓuya?
Kuma tun da shi ba a yi wa mutum hisabi a cikin wannan duniyar irin hisabin da ya dace da shi, kenan babu makawa cewa shi mai tafiya ne zuwa wata kotu babba da rabauta babba.
HAКIКA TA TAKWAS
[1]Na'am, haƙiƙa shuɗaɗɗan zamani-wanda yake farawa daga yanzu zuwa fara halittar duniya-dukkaninsa da abubuwa masu faruwa da abubuwa masu aukuwa, kuma kowace rana da kowace shekara da kowane ƙarni daga cikinsa da ya bayyana a samuwa kamar wata saɗara ce da takarda da littafi da aka rubuta shi da alƙalamin ƙaddara, kuma hannun ƙudura ya rubuta mu'ujizozin ayoyinsa da cikakkiyar hikima da tsaruwa,shi kuwa zamani mai zuwa da yake farawa daga zamanin yanzu kuma yake ci gaba har zuwa ranar Alƙiyama, zuwa Aljanna da kuma har abada to dukkaninsa abubuwa ne masu yiwuwa, ma'ana lokacin da ya wuce abubuwa ne masu faruwa da suka faru, shi ko lokaci mai zuwa abubuwa ne masu yiwuwa, to idan aka sanya sarƙoƙin waɗannan zamunna ɗaya na fuskantar ɗayan, kuma babu shakka har abada cewa wanda ya halicci jiya kuma ya samar da samammun abubuwansa waɗanda suka keɓanta da shi mai iko ne bisa halittar gobe da ababan halittarsa, kuma babu shakka cewa samammun abubuwa da abubuwa masu shallake hankali na wannan zamani da ya wuce wanda shi ne fage na abubuwan mamaki su ne mu'ujizozi na mai iko ma'abocin jalala, kuma suna shaidawa shaidawa ɗoɗar cewa wancan mai ikon mai iko ne a bisa samar da lokacin nan gaba dukkaninsa, da kuma samar da dukkan abubuwa masu yiwuwa dukkaninsu, da bayyana dukkan abubuwan mamakinsa, Na'am, kamar yadda wanda zai halicci tuffa ɗaya, lallai ne ya zama mai iko bisa halittar dukkan tuffa din duniya, kuma mai iko ne bisa samar da lokacin kaka dukkaninsa, kuma wanda ba ya samar da lokacin kaka, ba zai iya samar da tuffa ɗaya ba, domin cewa waccan tuffar ana saƙa ta ne a cikin waccar masaƙar, don haka wanda zai iya samar da tuffa zai iya samar da lokacin kaka, domin tuffa ɗaya ƙaramin samfuri ne na bishiya, ko ma a ce na lambu, ko kuma ma na duniya baki ɗaya, ita kuwa halitta ce mai shallake hankali ta fuskar kasancewar ƙwallonta yana ɗauke da dukkan tarihin rayuwar bishiyar gundumemiya, domin wanda ya halicce ta bisa wannan surar ba zai gaza ba wajen halittar kowane abu,hakanan kuma wanda yake halittar wannan yini zai iya halittar ranar Alƙiyama, kuma wanda zai samar da lokacin kaka ya kamata ya kasance mai iko bisa halittar tashin Alƙiyama, kuma wanda ya rataya dukkan duniyoyi na lokacin da ya wuce bisa turba ta zamani cikin hikima da tsaruwa kuma yake bayyana su, babu shakka shi zai iya rataya wasu duniyoyi da ban a kan turabar zamani mai zuwa kuma ya bayyana ta, kai tabbas ma zai bayyana ta.
Kuma haƙiƙa mun tabbatar a cikin da yawa daga cikin "kalmomi"Musamman ma kalma ta ashirn da biyu"tabbatarwa kai tsaye; cewa wanda ba shi da iko bisa halittar kowane abu, ba shi da iko bisa halittar wani abu komai ƙanƙantarsa, kuma wanda yake da iko bisa halittar wani abu ɗaya yana da iko bisa halittar dukkanin abubuwa, sannan kuma idan aka jingina samar da abubuwa zuwa abu ɗaya to halittar dukkanin abubuwa za ta zama mai sauƙi kamar sauƙin halittar abu ɗaya, kuma za ta zama sassauƙa, amma idan aka jingina ta zuwa abubuwa masu yawa kuma zuwa yawa to samar da abu ɗaya zai zama mai wahala mai matsala kamar wahalar samar da dukkan abubuwa, kuma zai zama mai wahalar da ta kai matakin abin da ba zai yiwu ba (mawallafi).
79. Page
Babin alƙawarin rahama da narko
Wanda shi tajalli ne na sunan Mai kyau da sunan Mai girma
Shin abu ne mai yiwuwa ga mai ƙera waɗannan ababan ƙerawa kuma mai ƙirƙirarsu, wanda shi ne masani mai sani na sake babu ƙaidi, mai iko iko na sake babu ƙaidi, a ce ba zai cika alƙawarin rahmarsa da na narkonsa waɗanda yake ambatonsu a kai akai ba, waɗanda kuma dukkan annabawa suka ba da labarinsu bisa haɗuwar maganarsu bi-da-bi, kuma dukkan siddiƙai da waliyyai suka shaida da su bisa ijma’i, da sai ya nuna gazawa da jahilci tsarki ya tabbata gare shi? Tare da cewa lamuran da ya yi alƙawarin rahamarsu ko narkonsu ba za su nauyayi ikonsa ba tun asali, a’a sai dai su masu sauƙi ne ƙwarai irin sauƙin dawo da abin da ba zai ƙirgu ba kuma ba zai iyakantu ba, na daga samammun abubuwa na lokacin kakan da yawuce a kaka mai zuwa, wasunsu su ne da kansu[1], wasunsu kuwa kwatankwacinsu[2].
Shi kuwa cikawa da alƙawari abu ne da ya zama na lallai ƙwarai garemu da ma kowane abu, da ma masarautar ubangijintaka, shi kuwa saɓa alƙawari abu ne da yake karo da buwayar masarautar ikonsa, da kiwayewar saninsa, domin saɓa alƙawari ko dai yana faru ne saboda jahilci ko kuma gajiyawa.
[1] Kamar jijiyoyin bishiyu da ciyayi.(mawallafi).
[2] Kamar ganyayyaki da ‘ya’yan itatuwa.(mawallafi).
80. Page
To ya kai mai inkari, shin ko ka san yawan laifin da kake aikatawa cikin wautar inkarinka da kafircinka, haƙiƙa kai ka na gasgata ruɗinka maƙaryaci, da hankalinka mai tamɓele, da ranka mai ruɗi, kuma kana ƙaryata wandaba ya buƙatar saɓawa da saɓani ta kowace fuska, kuma wanda saɓa alƙawari ba ya dacewa da buwayarsa da jalalarsa ta kowace fuska; kuma wanda dukkan abubuwa da lamura da a ke gani suke shaidawa bisa gaskiyarSa da cancantarSa!Haƙiƙa kai, duk da matuƙar ƙanƙantarka, kana aikata laifi babba wanda girmansa ba ya misaltuwa, don haka babu makawa cewa kai kana cancantar uƙuba ta har abada mai girma, kuma haƙiƙa an rawaito cewa turmin haƙorin wasu daga cikin ‘yan wuta zai kasance kamar girman dutse[1], daidai da girman laifinsa, don haka misalinka kamar misalin wannan matafiyin ne; da yake runtse idanunsa ga barin hasken rana, kuma ya koma yana kallon hoton zuci da ke cikin kansa, kuma yana son ruɗaninsa ya haskaka masa hanyarsa mai ban tsoro da fitilar hankalinsa kamar maƙesuwa, kuma tun da sarki na gaskiya maɗaukaki wanda waɗannan samammu kalmominsa ne na gaskiya masu furuci da gaskiya, kuma abubuwa masu faruwa a halitta ayoyinsa ne masu furuci da gaskiya, tun da dai wannan sarki ya yi alƙawari; to babu makawa
[1]Ya zo a cikin Sahihu Muslim 4/2189:Daga Abu Hurairata ya ce:Manzon Allah (S.A.W) ya ce:”Turmin haƙorin kafiri ko fiƙar kafiri kamar dutsen Uhudu ne, kuma kaurin fatarsa tafiyar uku ne”(kwana uku).
81. Page
da sannu zai cika alƙawarinSa, kuma da sannu zai buɗe wata kotu babba, kuma zai ba da rabauta babba.
HAКIКA TA TARA
Babin rayawa da matarwa
wanda tajalli ne na sunan Rayayye da Tsayayye da zatinsa da Mai rayawa da Mai kashewa
Shin yanzu mai yiwuwa ne ga mai iko mai jin-ƙai, kuma masani mai hikima, wanda ya raya ƙasa ɗibgegiya gundumemiya bayan mutuwarta da bushewarta, kuma ya bayyana ikonsa cikin wannan rayuwar; ta hanyar tashi da yaɗa nau’o’in ababan halitta waɗanda suka haura nau’i dubu ɗari uku, da kuma tashin kowanne daga cikinsu a kan kansa mai ban mamaki ne kamar tashin ɗan’adam,kuma ya bayyana kewayewar saninSa ta hanyar banbancewa da rarrabewa marasa iyaka a cikin wannan tashin da yaɗawar, da kuma cikin cuɗanya da sassarƙafuwa marasa iyaka, kuma ya fuskantar da kallo da hankalin bayinSa zuwa rabauta ta har abada ta hanyar yin alƙawarin tada bil Adama da umarce-umarcenSa na sammai dukkaninsu, kuma ya bayyana girman ubangijintakarsa ta hanyar sanyawarSa ga dukkan samammun abubuwa masu tallafar juna-hannu da hannu, yana mai jujjuya su cikin da’irar umarninSa da nufinSa, da sanyawarSa ga kowanne daga cikinsu mai taimako ga sashi, kuma ababan horewa sashinsu ga sashi, kuma ya bayyana damuwarsa ga bil Adama ta hanyar halittarsa a matsayin mafi tattaruwar ɗan ita ce na bishiyar halitta, kuma mafi taushinta, mafi tsananinta a laushi da yanga da kuma mafi yawanta a ƙasƙantar da kai, yana mai riƙarsa, abokin magana ga kansa, mai hore masa kowane abu.


