HAКIКA TA TARA
NAVIGATION
81. Page
da sannu zai cika alƙawarinSa, kuma da sannu zai buɗe wata kotu babba, kuma zai ba da rabauta babba.
HAКIКA TA TARA
Babin rayawa da matarwa
wanda tajalli ne na sunan Rayayye da Tsayayye da zatinsa da Mai rayawa da Mai kashewa
Shin yanzu mai yiwuwa ne ga mai iko mai jin-ƙai, kuma masani mai hikima, wanda ya raya ƙasa ɗibgegiya gundumemiya bayan mutuwarta da bushewarta, kuma ya bayyana ikonsa cikin wannan rayuwar; ta hanyar tashi da yaɗa nau’o’in ababan halitta waɗanda suka haura nau’i dubu ɗari uku, da kuma tashin kowanne daga cikinsu a kan kansa mai ban mamaki ne kamar tashin ɗan’adam,kuma ya bayyana kewayewar saninSa ta hanyar banbancewa da rarrabewa marasa iyaka a cikin wannan tashin da yaɗawar, da kuma cikin cuɗanya da sassarƙafuwa marasa iyaka, kuma ya fuskantar da kallo da hankalin bayinSa zuwa rabauta ta har abada ta hanyar yin alƙawarin tada bil Adama da umarce-umarcenSa na sammai dukkaninsu, kuma ya bayyana girman ubangijintakarsa ta hanyar sanyawarSa ga dukkan samammun abubuwa masu tallafar juna-hannu da hannu, yana mai jujjuya su cikin da’irar umarninSa da nufinSa, da sanyawarSa ga kowanne daga cikinsu mai taimako ga sashi, kuma ababan horewa sashinsu ga sashi, kuma ya bayyana damuwarsa ga bil Adama ta hanyar halittarsa a matsayin mafi tattaruwar ɗan ita ce na bishiyar halitta, kuma mafi taushinta, mafi tsananinta a laushi da yanga da kuma mafi yawanta a ƙasƙantar da kai, yana mai riƙarsa, abokin magana ga kansa, mai hore masa kowane abu.
82. Page
Shin mai yiwuwa ne ga irin wannan mai iko mai jin ƙai, kuma masani mai hikima, a ce ba zai kawo ranar Alƙiyama ba, kuma ba zai farar da tashin Alƙiyama ba, ko a ce ba zai iya farar da shi ba, kuma ba zai rayar da ‘yan’dam ba, ko ba zai iya raya su ba, ko a ce ba zai iya buɗe kotu babba ba,kuma ba zai halicci Aljanna da wuta ba?Tsarki ya tabbata gare shi bisa haka faufau! Na’am, haƙiƙa mai sarrafa wannan duniya ma’abocin sha’ani yana samar da misalai da samfura da ma’aunai masu yawa ƙwarai n tashin Alƙiyama babba, da kuma fagen Alƙiyama a kowane zamani, da kowace shekara da kowace rana a doron wannan ƙasa ƙuntatacciya ta ɗan lokaci.
Ga misali:Haƙiƙa mu a cikin tashi na lokacin kaka muna ganin cewa shi yana tasar kuma ya yaɗa fiye da nau’i dubu ɗari uku na dabbobi da tsirrai ƙananansu da manyansu, cikin kwanaki biyar ko shida, kuma yana raya ya maido da jijiyoyin dukkan bishiyoyi da ciyayi da wasu dabbobi su kansu, kuma yana samar da wasunsu daban cikin surar kama wadda ta kai matakin a ce su su ne da kansu, kuma duk da cewa ‘ya’yan iri-waɗanda sashinsu yake sassaɓawa da sashi, sassaɓawa mai zurfi ƙwarai ta ɓangaren halittarsu-duk da cewa su masu cakuɗuwa ne masu shisshigar juna ne ƙwarai da gaske; duk da haka su ana raya su da cikakkiyar banbanta da bayyanawa ɓalo-ɓalo kuma cikin sauri mai matuƙar ban mamaki, kuma da yalwatuwa da sauƙi cikakke, da cikar tsaruwa da ma’auni cikin kwanaki shida ko makwanni bakwai.
83. Page
To shin mai yiwuwa ne a ce wani abu zai wuyata ga wanda yake yin waɗannann abubuwa?! Kuma a ce ya gaza wajen halittar sammai da ƙasa cikin kwanaki shida?! Kuma a ce ba zai iya tada ɗan’adam da tsawa ɗaya ba?!Tsarki ya tabbata gare shi ga barin haka.
To ya jama’a, da a ce akwai wani marubuci wanda lamarinsa ya shallake hankali da yake kwafar littattafai dubu ɗari uku da haruffansu suka dusashe ko suka goge, a ce yana kwafarsu a takarda ɗaya ba tare da sun sarƙe ba, ba kuskure ko rafkanuwa ko tawaya, kuma yana rubuta su gaba ɗaya a tare cikin matuƙar jeruwa da ɗanɗasawa cikin awa ɗaya, kuma wani daga cikinsu ya ce maka:lallai wannan marubuci zai sake rubuta littafinka da ya faɗa cikin ruwa daga cikin ƙwaƙwalwarsa cikin sakan ɗaya, wanda daman shi ya wallafa shi tun asali, to shin za ka iya cewa:A’a ba zai iya ba, ba zan gasgata ba?!
Ko kuma a ce akwai wani sarki ma’abocin mu’ujizozi da ka ga cewa yana ɗaga duwatsu, ya caccanza garuruwa, yana sassauya tekuna zuwa saharori ta hanyar nuni kawai daga gare shi, don bayyana ikonsa, ko don wa’azantarwa ko don shaƙatawa, sannan ka ga wani dutse murgujeje ya mirgino zuwa kwari, ya toshe hanyar baƙinSa da ya gayyace su zuwa keɓantacciyar walimarsa,kuma ya hana su wucewa, sai ɗayansu ya ce maka:Haƙiƙa wannan sarki zai ɗauke wannan dutsen ko ya rugurguza shi duk girmansa da nuni kawai, kuma ba zai bar baƙinsa a kan wannan hanyar ba, to shin za ka ce ne:ba zai ɗauke shi ba, ko ba zai iya ba?!
84. Page
Kuma da a ce wani mutum yana sake tara runduna mai girma a rana ɗaya, sai wani ya ce maka:wannan mutum zai tattara sahu-sahun ƙungiyoyin da ɗaiɗaikunsu suka warwatsu domin hutawa, zai tara su da sautin kakaki; duk wannan sahu-sahun su shiga ƙarƙashin tsarinsa, to idan ka ce:Ba zan gasgata ba; to haƙiƙa za ka fahimci cewa ka yi tasarrafi cikin wauta.
To idan harka fahimci waɗannan misalai uku to dubi:Haƙiƙa mai zane na tun fil azal yana jujjuya takardar lokacin sanyi fara a gaban idanunmu, kuma yana buɗe takardar lokacin kaka da zafi koriya, kuma yana rubuta fiye da nau’i dubu ɗari uku a shafin doron ƙasa da alƙalamin iko da ƙaddara cikin mafi kyawun sura, yana rubuta su gaba ɗaya a lokaci guda, sashinsu na shiga sashi ba tare da cakuɗuwa da juna ba, kuma ba tare da wani abu a cikinsu ya hana wani ba, kuma ba ya kuskure, tare da cewa sashinsu yana saɓawa da sashi a sura da kamanni.
To shin zai yiwu a ce game da mai hikima mai kiyayewa wanda yake kiyaye manhajar ran mafi girman bishiya, yana mai sanya shi a cikin mafi ƙanƙantar ƙwallon ɗan itaciya wanda yake kamar girman ɗigo, a ce:Ta ya ya zai kiyaye rayukan matattu?!
85. Page
Kuma shin zai yiwu a ce game da mai iko wanda yake jujjuya ƙasa kamar marmarar gwafar harbi a ce: Ta ya ya zai ɗauke wannan ƙasar daga hanyar baƙi matafiya zuwa lahira, ko ta ya ya zai rugurguza ta?!
Ko kuma shin mai yiwuwa ne a ce game da maƙagi ma’abocin jalala wanda ya samar da rundunoni, ma’ana ya sake samar da rundunonin duk wasu abubuwa masu rai daga babu, kuma ya shigar kuma ya adana ƙwayoyin zarra a cikin sahu-sahu na jikkunan dukkan masu rai cikin cikakkiyar tsaruwa da umarninكُن فَيَكُونُ Kasance sai ya kasance, a ce: Ta ya ya zai iya tattara ƙwayoyin zarra na tushe da sassa na asali na jiki, waɗanda sashinsu ya jitu da sashi ta hanyar dunƙulewarsu ƙarƙashin tsarin jiki da ya yi kama da sahu-sahu na taron ‘yan makaranta ko sojoji, ya tashe su da tsawa ɗaya?!
Sannan kai kana gani da idanunka cewa shi mai girma da ɗaukaka da yawa yana samar da samfuri da misali da alamomi game da tashin Alƙiyama daga cikin zane-zane-ma’ana halittun da yake yi-, da abin da ya yi kama da tashin wannan lokaci na kaka cikin kowane kewaye daga kewaye-kewayen ƙasa, da kuma kowane zamani daga zamunanta, kai har a cikin caccanzawar dare da rana, da cikin samar da giza-gizai da rasar da su a cikin sararin samaniya, kai har ma da ka ɗauki kanka-bisa riyawa-kafin shekara dubu, ka kwatanta tsakanin lokacin da ya wuce da lokaci mai zuwa, waɗanda su ne fuka-fukai biyu na zamani, da ka ga samfura na Alƙiyama; da misalai na tashin Alƙiyama daidai da adadin zamunna da kwanaki; sannan da za a ce kai ka musa tashin jikkuna kana mai nesanta yiwuwarsa a bisa hankali duk da ganinka na wannan adadi na samfura da misalai; to da da sannu za ka riski ta yadda hakan zai zama wauta!Kuma kalli abin da wannan doka mafi girma ta ke cewa game dawannan haƙiƙa: To ka yi duba zuwa guraban rahamar Allah yadda yake raya ƙasa bayan mutuwarta, haƙiƙa wannan mai raya matattu ne, kuma shi mai iko ne a bisa kowane abu
86. Page
فَٱنظُرۡ إِلَىٰٓ ءَاثَٰرِ رَحۡمَتِ ٱللَّهِ كَيۡفَ يُحۡيِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَآۚ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰۖ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
A taƙaice dai:Babu wani abu da zai hana faruwar tashin Alƙiyama, abin da ke wajabta shi kuwa shi ne komai.
Na’am; haƙiƙa wanda yake matarwa ya rayar da waccan ƙasa gundumemiya wadda ita ce matadar abubuwan mamaki kamar matarwa da rayar da dabba sababbiya sassauƙa, kuma wanda ya sanya ta shimfiɗa mai sanya hutu, kuma ya sanyata jirgin ruwa tsalele ƙayatacce ga bil Adama da dabba, ya sanya rana gare su a wannan gidan saukar baƙin a matsayin fitila mai haske, kuma mai ba da ɗumi, kuma ya sanya taurari jirage ga mala’ikunSa.
Na’am; babu shakka cewa ubangijintaka mai girma ta har abada irin wannan, da sarauta mai girma mai kewayewa ta wannan ubangiji ba a gina su ba don su tabbata bisa al’amuran duniya masu gushewa marasa tabbata, mawofinta, masu caccanzawa, masu tawaya, waɗanda babu kamala ko dawwama ko wanzuwa a gare su, kenan ba makawa daga cewa akwai wani gida da wata masarauta da ban da ta dace da Shi madawwamiya wanzajjiya, matabbaciya mai ƙayatarwa wadda babu gushewa gare ta.
Don haka Shi yana sanya mu aiki ne saboda wancan gida, kuma yana kiranmu zuwa gare shi, kuma yana shaidawa dukkan rayuka masu haske game da ciruwarmu zuwa gare shi, hakanan dukkan ƙuɗubai ma’abota zukata ababan haskakawa, da dukkan iyayangijin hankula na haske waɗanda suka keto daga zahiri zuwa haƙiƙa, kuma suka darajtu da kusancin halartowa ta ubangiji, kuma suke bamu labari bisa haɗuwar zantukansu cewa Shi mai tsarkin mulki ya tanadi lada da sakamako, kuma suna rawaito mana a maimaice cewa Shi mai tsarkin mulki yana alƙawarin rahma alƙawari na tabbas, kuma yana alƙawarin narko narko mai tsanani.
Shi kuwa saɓa alƙawarin rahma to ƙasƙanci ne da ƙasƙanta, don haka ba zai iya kusantar jalalar abin tsarkakewa ba, shi kuwa saɓawar alƙawarin yin narko ko dai ya faru saboda afuwa ko kuma gazawa alhali kuwa kafirci laifi[1] netsantsa wanda
[1] Na’am, haƙiƙa saboda shi kafurci wulaƙantawa ne ga dukkan duniya, da dukkan halittu, yadda yak e sarayar da ƙimar samammun abubuwa, ya tuhume su da wasa a manufar samar da su, kuma saboda shi jirkitawa ne dangane da sunayen Allahntaka ta inda yake inkarin bayyanar sunayen Allahntaka a kan maduban samammu, kuma saboda shi ƙaryatawa ne ga dukkan ababan halitta, ta yadda yake mai da shaidojin samammu bisa kaɗaitaka, don haka shi yana ɓata tanadin halittar ɗan’adam, ta yadda babu wata mashiga ta karɓar gyaruwa da alherin da za ta wanzu ga ɗan’adam.
Kuma haƙiƙa zalunci ne mai girma, ta yadda ya zama ta’addanci ne a kan dukkan ababan halitta, da kuma dukkan sunayen Allahntaka, don haka kiyaye waɗannan haƙƙoƙi da kuma ƙin karɓar ran kafiri ga alheri suna wajabta ƙin yin afuwa bisa kafirci:{Haƙiƙa Shirka zalunci ne mai girma} [Luƙman:13], tana fa’idantar da haka.(Mawallafi).
87. Page
bai cancanci afuwa ba,shi kuwa mai sakakken iko to shi ne abin tsarkakewa daga gazawa, su kuwa shaidu da masu ba da labari haƙiƙa sun yi ittifaƙi cikakken ittifaƙi a kan tushen wannan mas’alar, duk da yake su masu saɓawa ne a tafarkunsu da ra’ayoyinsu da matafiyoyinsu, ta ɓangaren yawansu sun kai matakin ruwan dare gama duniya, ta fuskar ƙarfin hujjarsu kuwa sun kai ƙarfin ijma’i, ta ɓangaren matsayi kuwa kowane ɗaya daga cikinsu tauraro ne na dangin ɗan’adam, kuma ido ne wajen wata ƙungiya, kuma maɗaukaki na wasu mutane,ta ɓangaren muhimmanci kuwa to su ma’abota ƙwarewa da tabbatarwa ne a cikin waccan mas’ala, sanannen abu ne kuwa cewa mutum biyu daga ma’abota ƙwarewa a cikin wani ilimi ko sana’a ababan rinjayarwa ne a kan dubban wasu da ba su ba, kuma cewa mutum biyu masu tabbatarwa cikin ba da labari ana rinjayar da su a kan dubban masu korewa, ga misali:Haƙiƙa mutum biyu da suke ba da labarin tabbatar jinjirin watan Ramadana suna mai da inkarin dubban munkirai da suke inkarin tsayuwarsa.
A ƙarshe dai:Haƙiƙa abu ne mara yiwuwa a ce akwai wani labari mafi gaskiya ko wani batu mafi ƙarfi da gwaɓi ko wata haƙiƙa mafi bayyana da fayyacewa a duniya daga wannan batu; kenan babu shakka cewa duniya gona ce, shi kuwa tashin Alƙiyama magirba ne, su kuwa aljanna da wuta ma’ajiyu ne.


