HAКIКA TA UKU

45. Page

Kuma shin zai yiwuga mai rahama mai jin ƙai a ce ba zai tanadi gidan yin kyakkyawan sakamako ba, kuma ya ba da rabauta ta har abada ga muminai ba waɗanda suka sakawa sanar da su kansa da ya yi ta hanyar saninsu gare shi ta hanyar yin imani da shi, kuma suke sakawa soyantar da kansa gare su da sonsu gare shi ta hanyar bauta da ma sanya sonsa a zukatan wasu, kuma suke sakawa rahamarsa gare su ta hanyar girmamawa da godiya?

 

HAКIКA TA UKU

 

Babin Hikima da Adalci

 

Wanda shi ne tajallin suna na Mai Hikima da Mai Adalci

 

Shin mai yiwuwa ne[1] ga sarki na gaskiya maɗaukaki ma'abocin jalala wanda ya bayyana masarauta ta ubangijintaka da hikima da tsaruwa da adalci, da ma'auni mai

[1] Na'am,haƙiƙa jumlar "Shin mai yiwuwa ne" tana yawan maimaituwa; saboda ita tana ba da fa'idar wani sirri mai girma kuma muhimmi, wanda shi ne:Haƙiƙa mafi yawan kafirci da ɓata suna faruwa ne daga nesanta yiwuwar abu, ma'ana dai su ma'abota kafirci da ɓata suna ganin cewa abu ba mai yiwuwa ba ne kuma manesanci ne daga hankali, sai su yi inkarinsa, don haka ne ma a cikin "saƙo na tashin Alƙiyama" aka bayyana wannan da bayani fayyatacce yanke cewa, nesantawa ta haƙiƙa, dakoruwa ta haƙiƙa, da nisanta daga hankali, da wahalta ta haƙiƙa, kai har ma mushkiloli da suka kai matakin rashin yiwuwa, duk waɗannan suna cikin tafarkin kafirci ne da turbar ɓata, kuma cewa yiwuwa ta haƙiƙa, da karɓar hankali ga abu ta haƙiƙa,kai har ma sauƙin yiwuwar abu da ya kai matakin wajabci, duk waɗannan suna kan tafarkin imani ne, da turbar Musulunci.

A ƙarshe dai:Haƙiƙa ma'abota falsafa suna jawuwa ne zuwa inkari ta hanyar ƙaimin nisantuwa, kuma "batu na goma" yana bayyana maɓoyar nisantuwar, kuma ya yi musu ɓarin makauniya.(mawallafi).




46. Page

gudana a cikin kowane abu, farawa daga ƙwayoyin zarra, da tiƙewa zuwa ga rana-rana, a ce ba zai yi wa muminai kyakkyawan sakamako ba, waɗannan da suke fakewa zuwa ga inuwar kariya ta ubangijintakarsa, kuma suke kai kawo da imani da bautatuwa bisa dacewa da waccan hikimar da adalcin, kuma a ce ba zai yi uƙuba ba ga masu munana ladabi waɗanda suke yin tawaye ga waccan hikimar da adalci ta hanyar yin kafirci da ɗagawa, haƙiƙa shi baa ɗabbaƙawa ɗan’adam a cikin wannan rayuwa 'yar taƙaitacciya na abin da ya dace da waccan hikima da adalci face ɗaya daga cikin dubu, sai dai shi yana jinkirtawa ne ya ba da tazara, domin mafiya yawa daga ma'abota ɓata su yi ƙaura daga wannan duniya ba tare da sun sami uƙubar su ba, hakanan galibin ma'abota shiriya su yi ƙaura ba tare da sun sami kyakkyawan sakamakonsu ba, kenan lamarin ana jinkirta shi ne zuwa wata kotu babba da kuma rabauta babba.

 

Na'am; haƙiƙa yana bayyana ƙarara cewa mai tasarrufi a cikin wannan duniya yana aikata abin da yake aikatawa ne da hikima mara ƙarewa, shin ko kana buƙatar hujja a kan haka?Hujja a kan haka ita ce kulawarsa da maslahohi da fa'idoji cikin kowane abu, yanzu shin  ba ka  ganin cewa kulawa da fa'idoji da hikimomi cikin dukkan gaɓɓan ɗan’adam da ƙasusuwansa, da jijiyoyinsa, kai har ma cikin ƙwayoyin halittar jikinsa, da cikin duk wani bigire a cikinsa, da cikin duk wani sashi nasa,kai har ma ratayawa wasu gaɓɓansa hikimomi da fa'idoji gwargwadon yawan 'ya'yan ita ce na bishiya, duk yana nuna cewa waɗannan lamura suna gudana ne ta hannun wata hikima mara ƙarewa.

Sannan samuwar tsaruwa mai matuƙar tantancewa da ƙayatuwa cikin ƙera kowane abu na nuna cewa lamura na gudana ne a cikin hikima mara ƙarewa.


47. Page

Na'am, haƙiƙa shigar da manhaja wadda aka ƙwalƙwale ta samuwar fure kyakkyawa cikin ɗan irinsa, da kuma rubuta takardar bayanin ayyukan ƙatuwar bishiya da bayanai a kanta, da tarihin rayuwarta da fihirisar na'urorinta cikin wani ƙwallo ɗan ƙanƙani ƙwarai ta hanyar alƙalamin ƙudura na ma’ana, yana bayyana cewa akwai wani alƙalami na hikima wadda ba ta da ƙarshe da yake aiki cikin waɗannan lamura kuma yake tasarrufi a cikinsu.


48. Page

 

Na'am, haƙiƙa shigar da fihirisar dukkan halittu da mabuɗan dukkan taskokin rahama, da maduban dukkan sunayansa cikin jikin wannan bil Adama ɗan ƙanƙani ƙwarai, lalle yana bayyana wata hikima cikin kyawun ƙira da ƙirƙira waɗanda ba su da iyaka.

To yanzu shin abu ne mai yiwuwa a ce wata hikima mai iko da take aiwatar da irin waɗannan tsare-tsare na gudanarwa na ubangijintaka, ba za ta yi kwaɗayi wajen girmama waɗanda suke fakewa zuwa inuwar waccan ubangijintaka kuma suke bin ta da imani ba, kuma a ce ba za ta karrama su ba karramawa madawwamiya?

 

Kuma shin kana son wata hujja ne a bisa cewa lamura ana gudanar da su ne da adalci da kuma ma'auni?

 

 Hujja bisa haka ita ce haƙiƙa ba da samuwa ga kowane abu, da lulluɓa masa kamanni, da sanya shi a bigirensa da ya dace da shi da ma'aunai masu tsananin tantancewa waɗanda aka ƙwalƙwale su, da kuma wasu magwadai na musamman,yana nuna cewa lamura kawai ana zartar da su kuma suna aiwatuwa ne da adalci da ma'auni waɗanda ba su da iyaka.

 

Haka nan ba wa duk wani mai haƙƙi haƙƙinsa daidai da tanadin halitta da aka yi masa, ma'ana ba shi dukkan abubuwan da samuwarsa ta rataya da su, da dukkan na'urorin da suka zama ba makawa sai da su zai wanzu cikin sura mafificiya, na nuni zuwa ga hannun adalci sakakke.


49. Page

Hakanan amsawa duk wata buƙata da a ke nema kuma a ke tambayarta da harshan tanadi na halitta da kuma harshan buƙata ta halitta,da kuma harshan matsuwa amsawa madawwamiya, na nuna wani adalci da hikima waɗanda ba su da iyaka.

To yanzu shin abu ne mai yiwuwa ne ga adalci da hikima da suke kai kawo wajen yin agaji da ba da gudummawa ga mafi ƙanƙantar buƙata ta mafi ƙanƙantar halitta a ce za su wofintar kuma su bar mafi girman buƙata kamar buƙatar wanzuwa ta mafi girman abin halitta kamar mutum, kuma a ce ba za su amsa ba ga mafi girman abin da yake neman gudummawarsa ba, kuma mafi girman abin da yake fatansa yake nemansa ba?kuma a ce ba za su kiyaye kuma su kare girman ubangijintaka ta hanyar kiyaye haƙƙin bayi ba?

 

Sai dai kuma shi mutum wanda yake rayuwa gajeriya a cikin wannan duniya mai ƙarewa, ba zai iya samun haƙiƙanin wannan adalci a cikinta ba, kuma ba zai iya samunsa ba, sai dai za a jinkirta shi ne zuwa wata kotu babba, domin shi adalci na haƙiƙa yana wajabta wannan bil Adama ɗan mitsitsi ƙwarai ya sami wani kyakkyawan sakamako, ko ya sami uƙuba ba wai daidai da ƙanƙantar jikinsa ba, a'a 

50. Page

sai dai daidai da girman laifinsa da nauyinsa, da kuma muhimmancin zatinsa, da girman aikin da aka ɗora masa.

 

Kuma tun da yake wannan duniya mai ƙarewa ta ɗan lokaci nesa ta ke ƙwarai daga kasancewa guri na bayyanar irin wannan adalci, da wannan hikima game da mutum wanda aka halitta saboda rayuwa ta har abada; to ke nan ba makawa cewa wannan mai ɗaukakar ma'abocin kyawu mai adalci, kuma kyakkyawa ma'abocin jalala da hikimazai samar da wata Jahannama madawwamiya da wata aljanna madawwamiya.