Ishara ta biyu:
NAVIGATION
35. Page
Ishara ta biyu:
Haƙiƙa a cikin hikayar an ambaci manzo mai karamci, kuma an ce: haƙiƙa duk wanda yake gani zai fahimta ta hanyar ganin lambobin yabonsa cewa shi yana tasarrufi ne da umarnin sarkin, kuma cewa shi hadiminsa ne na musamman, wannan manzo kuwa shi ne Manzo mafi girma S.A.W.
Na'am; ya lazimci mai ƙerawar nanmai tsarki na irin wannan halitta da aka ƙawata ta da ya sami irin wannan manzo mafi karamci, kamar yadda haske yake lazimtar rana; domin ba zai yiwu rana ta zama ranaba sai idan ta yaɗa haske; to haka Allantaka ba ta zama Allantaka ba sai da bayyana kanta ta hanyar aiko mazanni.
Sannan shin zai yiwu ga wani kyawu da ya kai matuƙa wajen cika a ce bai yi kwaɗayin bayyana kansa ba ta hanyar wani manuni da zai nuna shi, da mai sanarwa da zai sanarwa da mutane shi?
Kuma shin zai yiwu ga wata samarwa cikakkiya mai matuƙar kyawu a ce ba za ta yi kwaɗayi cikin fito da kanta ba ta hanyar wani mai tallatawa da zai janyo hankula zuwa gare ta ?
Kuma shin zai yiwu ga wata masarauta matattariya ga ubangijintaka magamiya a ce ba za ta nemi bayyana kaɗaitakarta da samadaniyancinta ba[1] a cikin Gungun 'yan yawaitaka, da ɓangarori ta hanyar wani ɗan saƙo mai fuka-fukai guda biyu?.Haƙiƙa wannan ɗan saƙon manzon Gungun 'yan yawaitaka ne a wajen halarar ubangiji ta fuskar bauta matattariya, kamar yadda yake shi ma'aikaci ne abin aikowa daga wajen
[1]Kalmar samadaniyanci ta zo ne daga suna ko siffar Allah ta Assamadu "wato wadatacce ga barin kowa, wanda kowa ke komawa wajansa don neman biyan buƙatarsa".
36. Page
halarar ubangiji zuwa gungun 'yan yawaitaka ta fuskar kusancinsa ga Sarkin gaskiya Maɗaukakin sarki da saƙonninsa.
Kuma shin zai yiwu ga ma'abocin kyawu na kan kansa mai matuƙar kyawu a ce ba zai yi kwaɗayin gani da nuna ababan yabo na kyawunsa da ɓoyayyun sirrikan kyawun sa a cikin madubai ba?ma'ana shin shi ba zai nemi hakan ba ta hanyar manzo abin ƙauna?! Domin shi masoyi ne da yake soyantar da kansa zuwa gare shi da bautatuwarsa, kuma yake aiwatar da aiki irin na madubi, kuma manzo ne da yake sanya sonsa a cikin ababan halittarsa kuma yake bayyana kyawun sunayensa.
Kuma shin zai yiwuga wani akawu ma'abocin wasu taskoki shaƙe da ababan ta'ajibi na mu'ujizozi da kuma wasu abubuwa masu ban mamaki masu tsada a ce ba ya nufin bayyana kamalolinsa ɓoyayyu ta hanyar bijiro da su ga idanuwan ababan halitta, da fito da su sarari a birbishin kawunansu ta hanyar wani mai iya siffantawa mai iya kwatance, ƙwararran mai ƙira, mai iya baje koli, gwanin talla ba?
37. Page
Kuma shin zai yiwu ya ƙawata wannan halitta da ababan ƙerawarsa waɗanda ke bayyana kamalolin dukkan sunayensa, kuma ya sanya ta saboda masu gani kwatankwacin wata fada da aka ƙawata ta da fasahohi ƙayatattu masu ban mamaki waɗanda aka kyautatasu ƙwarai da gaske sannan a ce ba zai sanyawa wannan fada malami kuma mai shiryarwa ba?
Kuma shin zai yiwuga mamallakin wannan duniya a ce ba zai bayyana kullallan ɗalsami (sirri)n da yake nuna manufa da maƙasudi na caccanzawar wannan halitta ta hanyar wani manzo ba, kuma a ce ba zai warware ƙulun ƙulufitar tambayoyi uku masu matuƙar wuya ga ababan halitta ba; wato dai:Daga ina muke ? Kuma ina za mu je ?kuma mu su waye?
Kuma shin zai yiwuga mai samarwa ma'abocin jalala wanda ya bayyana kansa ga ma'abota ji a zuci ta hanyar waɗannan ababan samarwar nasa masu kyawu, kuma ya sanya soyayyarsa gare su ta hanyar ni'imominsa masu daraja, sakamakon haka a ce ba zai iya isar da abun da yake soko zai yardar da shi ga ma’abota ji a zuci ta hanyar wani manzo ba ?
Kuma shin zai yiwuya halicci ‘yan’dam ababan fitinuwa da yawaita ta fuskar ɗabi'un zuciya da ganewa, kuma ababan kintsawa don bautatuwa magamiya ta ɓangaren kintsi, a ce kuma ba zai yi nufin ya karkatar da kallonsu daga yawaitar ba zuwa kaɗaita ta hanyar wani malami mai shriyarwa ba?
Kuma akwai wasu ayyukan masu yawa ga annabta makamantan waɗannan;kowane daga cikinsu dalili ne kai tsaye da yake nuna cewa Allahntaka ba ta kasancewa ba tare da manzanci ba.
38. Page
Yanzu kuma, ya jama'a shin akwai wani da ya bayyana a duniya da ya fi yawan cancanta, kuma ya fi tattara siffofi da ayyuka da aka ambata a baya daga Muhammadu balarabe S.A.W?!
Shin zamani ya taɓa yi wa duniya kyautar wanda ya fi shi cancantar matsayin manzanci da aikin isar da saƙo, shin ya taɓa yin kyautar wanda ya fi yin katari daga gare shi a cikinta? Kayya, tutur kuma faufau! Lalle shi S.A.W shi ne shugaban dukkan manzanni, kuma limamin dukkan annabawa, kuma jagoran dukkan zaɓaɓɓu, kuma mafi kusancin zuwa ga Allah mai girma da ɗaukaka, kuma mafi cikar dukkan ababan halitta, kuma sarkin dukkan masu shiryarwa.
Na'am; Haƙiƙa babbar mu'ujiza kamar Al-Ƙur'ani mai Girma wanda shi ne tekun haƙiƙa ta fuskoki arba'in; lalle ya isa wajen bayyana manzancinsa tantarwai kamar rana,ballantana alamomin annabcinsa waɗanda ba za su ƙirgu ko su ƙiduddugu ba, daga mu'ujizozinsa da suka kai mu'ujiza dubu, waɗanda ma'abota tabbabtarwa daga cikin malamai suka haɗu a kai, kamar tsagewar wata, da tsattsafowar ruwa daga tsakanin yatsunsa S.A.W.
Za mu taƙaice batun a nan, domin mu a "Kalma ta Ashirin da Biyar" za mu ambaci fuskokin mu'ujizancin Al-Ƙur'ani da suka kusan kaiwa fuska arba'in.


