Ishara ta farko:
NAVIGATION
30. Page
Ishara ta farko:
Akwai "haƙiƙoƙi guda uku" ga dolon mutumin da abokinsa amintacce a cikin hikayar:
Ta farko: Raina mai yawan umarni da mummuna da zuciyata.
Ta biyu: Almajiran falsafa da almajiran Alƙur'ani mai hikima.
Ta uku:Al'umar Musulunci da al'umar kafirci.
Haƙiƙa mafi tsananin ɓatan almajiran falsafa da addinin kafirci da rai mai yawan umarni da mummuna shi ne rashin sanin Allah Ta'ala wanda shi ne gaskiya, kuma kamar yadda abokin amintacce ya faɗa a cikin hikayar cewa ba zai taɓa yiwuwa ba a sami harafi ba tare da marubuci ba, ko wata doka ba tare da mai mulki ba, to mu muna cewa:haƙiƙa yana daga mafi nisan abin da ba zai yiwu ba a sami wani littafi ba tare da marubuci ba, musamman ma littafin da a game da kowace kalma da ke cikinsa an rubuta wani littafin da wani alƙalami ƙarami, kuma an rubuta wata ƙasida mai ban sha'awa ƙayatacciya game da kowane harafi daga cikinsa,kamar yadda yake ba mai yiwuwa ba matuƙa da gaske a ce wannan duniya da waɗannan ababan halitta sun samu ne ba tare da mai ƙerawa ba; domin wannan halittar wani littafi ne wanda kowane shafi daga cikin shafuffukansa ya ƙunshi littattafai masu yawa, koma a ce a cikin kowace kalma guda daga kalmominsa akwai littafi, kuma cikin kowane harafi guda daga cikin harufansa akwai ƙasida, misali doron ƙasa shafi ne mai ɗinbin littattafai ƙwarai! Kuma kowace bishiya kalma ce mai ɗimbin shafuka birjik! Kuma kowane ɗan ita ce harafi ne, kuma kowane ƙwallo ɗigo ne, kuma cikin wannan ɗigon akwai manhaja ta samuwar wata bishiyar da fihirisarta, to lallai littafi irin wannan zai iya kasancewa ne kawai zane na alƙalamin mai iko ma'abocin buwaya mamallakin siffofin jalala da jamala da iko da hikima marasa iyaka, ma'ana dai kallon ababan halitta na sanya a yi imani, sai fa wanda ya yi maye da sababin ɓata.
31. Page
Kuma kamar yadda cewa ba zai yiwu ba a sami gida ba tare da magini ba, musamman ma gidan da aka ƙawata shi da fasahohi masu shallake hankali, da abubuwan mamaki na zane-zane da abubuwan ta'ajibi na ado, har ta kai a cikin kowane tubali daga cikin tubalansa an sanya wata fasaha kwatankwacin abin da ke cikin fadar gaba ɗayanta, kuma babu wani hankali da zai yarda cewa irin wannan gida ya samu haka ba tare da magini ba,kai haƙiƙa ma yana buƙatar samun injiniyan zanen gine-gine mai fasaha maƙirƙiri gwani, Musamman ma in aka yi la'akari da cewa shi a cikin kowace sa'a yana gina masaukai na gaske a cikin waccan fadar kamar ka ce su allon kallo ne na silima, kuma yana canza su cikin cikakken tsari kamar yadda yake canza tufafi, har ta kai akwai ƙananan gidaje da yawa a cikin
32. Page
kowane allo na gaske; to haka ma wannan halittatana buƙatar samuwar wani mai samarwa mai hikima masani maiiko, wanda hikimarsa da iliminsa da ikonsa ba su da iyaka; domin wannan duniyar mai girma ƙayatacciya wata fada ce wadda wata da rana su ne fitilunta, taurari su ne kyandiranta, zamani kuma zare ne da tif da mai samarwa ma'abocin jalala yake rataye wata duniyar a kansu kowace shekara kuma yake bijiro da ita, kuma yana sabunta surorin waɗancan duniyoyi ƙayatattu tsararru da zubi ɗari uku da sittin a waccan duniyar da ya ratayata a jikin wancan tif, kuma yana canza ta da cikakken tsari da hikima, kuma haƙiƙa ya sanya doron ƙasa wani kaɓaki ne na ni'ima da yake ƙawata shi a kowane lokacin kaka da nau'i dubu ɗari uku na ababan ƙerawarsa, kuma yana cika ta da abin da ba zai ƙirgu ba ko ya iyakantu na daga dangogin kyautayinsa ta hanyar da ta ke kammala cikin matuƙar cuɗanya da gauraya, domin sashinta yana warewa ya banbanta daga sashi cikin matuƙar warewa da banbanta, don haka ka kwatanta ragowar fuskokin da wannan, to ta yaya za a iya gafala ga barin mahaliccin irin wannan fada?!
33. Page
Kuma kamar yadda musa fitowar rana yake surunbahana ne na mahaukaci mai ban mamaki, a yayin da ake ganin ta ake kallon surarta a yanayin faifayewa a tsakiyar lokacin yini a kan dukkan ƙwaya-ƙwayan ruwa da kumfarsa a kan doron kogi, da kan dukkan wani abu mai ƙyalƙyali a kan doron ƙasa, da kan dukkan wani sashi na sassan ƙanƙara; domin a sannan ya wajaba in an yi inkarin rana guda ɗaya kuma an ƙi yarda da samuwarta,ai a yarda da samuwar ranaku na haƙiƙa masu ɗinbin girma na asali, adadin ɗigo-ɗigon ruwa, da kuma adadin ƙwaya-ƙwayan ruwa, da kuma adadin sassa, kuma ya wajaba a sami wata rana ta haƙiƙa a cikin kowace ƙwayar zarra tare da cewa ita ba za ta yalwata ga fiye da ƙwayar zarra ɗaya ba, to hakanan kallon waɗannan ababan halitta waɗanda suke caccanzawa a ko yaushe da hikima da jeruwa, kuma suke sabunta a kowane lokaci cikin tsari da jituwa, sannan rashin gasgatawa da samuwar mahalicci ma'abocin girma tare da siffofinsa na kamala haukan ɓata ne, da surunbahana na hauka mafi firgici da tsanani daga haka;domin a wannan lokaci ya wajaba a amince da Allantaka ta sake babu ƙaidi a cikin kowane abu har a cikin kowace ƙwayar zarra; domin-bisa misali-kowace ƙwayar zarra daga ƙwayoyin zarra ta iska za ta iya shiga cikin kowane fure da ɗan ita ce da ganye kuma ta yi aiki a cikinsu,to idan ita wannan ƙwayar zarra ba ta kasance abar umarta ba; to ya wajaba kenan ta san yanayin samuwar wannan ababan samarwa da take shiga cikinsu ta yi aiki, kuma ta san ƙirarsu da kamanninsu don ta iya yin aiki a cikinsu, ma'ana ya wajaba (ita wannan ƙwayar zarra) ta mallaki sani mai gewayewa da iko gamamme har ta iya aikata dukkan hakan.
34. Page
Ga misali:Ƙwayoyin zarra na turɓaya za su iya zama mafarin dukkan ƙwallayen da ke cikin halittu da ire-iren shuka masu sassaɓawa mabambanta,-To idan dai ita ƙwayar zarra ba ta zama abar bawa umarni ba ce game da yadda ta ke jujjuyawa a rayuwarta-, to zai zama tilas ne ta ƙunshi injina da na'urori na ma’ana gwargwadon adadin ciyayi da bishiyoyi, ko kuma ya wajaba a jingina mata ƙwarewa da iko wanɗanda da su za ta san dukkan tsarin samuwarsu da kuma ƙeruwarsu, kuma ta san dukkan kamannin da ake lulluɓa musu ake kuma saƙa su da su, to ka misalta ragowar ababan halitta da wannan, harka fahimci cewa a cikin kowane abu akwai dalilai masu yawa mabayyana masu matuƙar ban mamaki na ɗayantaka.
Na'am, haƙiƙa halittar kowane abu daga abu ɗaya, da sanya kowane abu abu ɗaya ya keɓanta ne da mahaliccin kowane abu, don haka ka yi tsokaci a cikin babban saƙo ma'abocin babban sha'aniبِحَمۡدِه[1]ِوَإِن مِّن شَيۡءٍ إِلَّا يُسَبِّحُ, ma'ana ƙin amincewa da samuwar ubangiji ɗaya ƙwal yana janyo yarda da iyayangiji masu yawa adadin samammu.
( Kuma babu wani abu face yana tasbihi da gode masa)[1]


