Ishara ta huɗu:
NAVIGATION
40. Page
yake shi musu ne da inkari ga dukkan sunaye na tsarkaka waɗanda a ke kallo kuma a ke ganin zane-zanensu da bayyane-bayyanensu a cikin waɗannan samammun abubuwa, kuma shi ƙaryatawa ne ga dukkan dalilai wanda ba sa ƙarewa waɗanda suke nuni zuwa ga cancantuwa na sarkin gaskiya Ta’ala da kuma gaskiyarsa, don haka shi kafirci laifi ne da ba shi da iyaka, shi kuwa laifin da ba shi da iyaka yana janyo azaba da ba ta da iyaka.
Ishara ta huɗu:
Kamaryadda muka gani a cikin hikayar : Misalai goma sha biyu cewa:
Ba abu ne mai yiwuwa ba har abada a ce irin wannan sarki yana da wata masarauta da ta yi kama da gidan saukar baƙi na ɗan lokaci, sannan a ce ba shi da wata masarautar daban madawwamiya matabbaciya wadda ita ce bigire na bayyanar girmanSa, kuma matattarar masarautarSa mafi girma ba.
Hakanan ba abu ne mai yiwuwa ba ta kowace fuska daga fuskoki a ce wanzajje mahaliccin wannan duniya mai ƙarewa ya samar da wannan duniyar kuma a ce ba zai samar da wata duniya madawwamiya ba.
Kuma ba zai yiwu ba ga mai samarwa mara ƙarshe da ya samar da wannan ƙayatacciyar duniya mai gushewa, a ce ya halicci wannan duniya, kuma a ce ba zai samar ko ya halicci wata duniyar matabbaciya madawwamiya ba.
Kuma hakanan ba abu ne mai yiwuwa ba ga maƙagi mai hikima mai iko mai rahama wanda ya ƙagi wannan duniyar wadda ita ce fagen baje koli kuma filin jarrabawa, kuma gonar aiki, a ce ya halicce ta amma ba zai halicci gidan Lahiraba wanda shi ne gurin bayyanar dukkan manufofinsa.
Yanzu za a iya shiga cikin wannan haƙiƙa da babuka sha biyu, kuma waɗannan babuka za a buɗe su ne da haƙiƙu sha biyu.
Za mu fara da mafi gajartarsu kuma mafi sauƙinsu.


