JUZU’I NA BIYAR NA RATAYEN
NAVIGATION
161. Page
JUZU’I NA BIYAR NA RATAYEN
Haƙiƙa dubu ɗari da ashirin da huɗu na annabawa tsira da aminci su tabbata a gare su waɗanda su ne mafifitan ‘yan’dam kuma zaɓaɓɓunsu da nassin hadisi suna ba da labari bisa haɗuwar kan maganganunsu suna masu haɗuwa, sashinsu suna dogara da shaidu, sashi kuma zuwa gaskiyar yaƙini game da samuwar lahira, kuma cewa mutane za a kora su zuwa can, kuma cewa mahaliccin halitta zai zo da Lahira wadda ya yi alƙawari da ita alƙawari mai yanke shakku, kuma cewa miliyan ɗari da ashirin da huɗu na waliyyai waɗanda suke gaskatawa bisa kashafi kuma bisa sura ta ilimin yaƙini da abin da annabawa suka ba da labari game da shi, suna shaidawa bisa samuwar lahira.
Kuma cewa dukkan sunayanالصانع الحكيمmai samarwa mai hikima na wannan halitta suna nuni bisa samun Lahira da abin da yake bayyana na tajalloli a cikin wannan duniya; domin su suna buƙatar samuwar wata duniyar ta wanzuwa da dauwama kamar yadda yake sananne ga kowa.
162. Page
Kuma haƙiƙaالقدرة الأزليةƙudura ta fil azal wadda ba ta da iyaka wadda ta ke rayar da jana’izozin bishiyu matattu kafaffu tsayayyu waɗanda ba su da adadi a doron wannan duniyar; da umarninكُن فَيَكُونُ-Kasance sai ya kasance-cikin dukkan wani lokacin kaka daga kowace shekara, kuma take sanya su su sami tajallolinالبعث بعد الموت-tashi bayan mutuwa-, kuma take tayarda nau’i dubu ɗari uku na daga nau’o’in gungu-gungu na tsirrai da al’umomin dabbobi, kuma ta yaɗa su a matsayin dubban samfura na tashi da yaɗawa, kuma haƙiƙa hikima ta har abada wadda ba ta da iyaka wadda babu ɓarna a cikinta, da rahama wanzajjiya basarmadiya, da kulawa madawwamiya waɗanda suke azurtawa suke ciyar da dukkan ma’abota rayuka mabuƙata zuwa arziƙi da cikakken tausayi, azurtawa da ciyarwa waɗanda babu tamkarsu, kuma suke bayyana nau’o’in ado da kyawu marasa iyaka cikin lokaci gajere cikinkowane lokacin kaka, lallai kamar yadda kowa ya sani suna lazimta samuwar lahira, kuma cewa ƙaunar wanzuwa da kwaɗayi cikin zama na har abada da shauƙantuwa zuwa gare shi, da burace-burace basarmadai masu tsanani tabbatattu kafaffu madawwama da suke cuɗanye da mutum-wanda shi ne ɗan ita ce mafi ƙayatarwa na wannan halitta, kuma mafi soyuwar abin ƙerawa ga mahaliccin wannan halitta, kuma wanda shi ne mafi yawan alaƙa da ɗamfaruwa da samammun wannan halitta-suna tabbatarwa da isharorinsu da nuninsu cikin yanayin sanin kowa tabbatarwa mai yanke shakku cewa akwai duniyar wanzuwa da dawwama da gidan Lahira, da gidan rabauta bayan wannan duniya mai ƙarewa, don haka suke lazimta yarda da gidan Lahira a matsayin abin da kowa ya sani kamar dai samuwar duniya[1].
[1] Cikin wannan misali yana bayyana cewa ba da labari game da lamari tabbatacce abu ne mai sauƙi ƙwarai, kuma kasancewar inkarinsa da koreshi abu ne mai wahala kuma mai kawo ruɗani kwarai, wannan kuwa kamar misalin idan wani daga cikin mutane ya ce, haƙiƙa a doron ƙasa gaba ɗayansa akwai wani lambu mai ban sha’awa mai ƙayatarwa ‘ya’yan marmarinsa kamar girman gwangwanin madara, wani kuma ya ce, a a babu wannan gonar, to mai tabbatarwa sai ya tabbatar da da’awarsa cikin sauƙi ta hanyar nuna inda wannan gona take, ko bayyana wasu daga ‘ya’yan itaciyarta, shi kuwa mai inkari to domin ya tabbatar da korewarsa da inkarinsa lallai ya wajaba ya zagaye ƙwallon duniya kuma ya nunawa mutane shi dukkaninsa; to haka nan shaidar waɗanda suke ba da labari da samuwar aljanna bisa tabbatarta, ya ishesu don tabbatar da ita su kawo shaidar masu gaskiya ba tare da ma an dubi ɗaruruwan dubban naso na aljanna da ‘ya’yan marmarinta da gurabanta ba, shi kuwa mai inkari to zai iya tabbatar da inkarinsa ne kuma ya bayyana rashin samuwar aljanna idan ya ga halittu marasa iyaka da zamani na har abada wanda ba shi da iyaka, kuma ya tankaɗe su, to ya ku ‘yan’uwa dattijai ku riski irin ƙarfin da imani da lahira take da shi. (Mawallafi).
163. Page
Kuma tun da mafi muhimmancin darasin da Alƙur’ani mai hikima yake koyar da mu shi shi ne imani da Lahira, kuma wannan imani mai ƙarfi ne irin haka, kuma cikinsa akwai sayayawa da kwantar da hankali, har idan tsufa dubu ɗari ya sami mutum ɗaya, to haƙiƙa kwantar da hankali da ke fitowa daga wannan imani ya ishesu, don haka mu tsofaffi ya wajaba mu yi farin ciki da tsufanmu muna masu cewa:
الحمد لله على كمال الإيمان
Godiya ta tabbata ga Allah bisa cikar imani


